Free chapter · Read without an account
Chapter 39
⚫ *MUMINA KO AZZALUMA*⚫
Available on:wattpad&arewabook
⚫ _SADISAKHNA_⚫
🖤🖤🖤
⚫ _PART 39_⚫
Abbansa ne yayi maganar cikin bacin rai,Ahmad baice komai ba sai ɗan ɗaga murya dayayi yacewa su Surayyah su shigo.
A tare kuwa suka shigo Surayyah ce a gaba a ta ɗauki Abdurrahim a kafaɗarta yayinda ɗaya hannunta take riƙe dana Jurayyah wacce itama ɗaya yaronne a ƙafaɗarta,saidai duk jikinta yayi sanyi babu wannan dakewar da izzar,duk da dama wani abun akwai saka hannun aljanin dayake jikinta tsawon wannan lokacin.
Kowa sakin baki yayi yana kallonsu,gashi sun saka kaya iri ɗaya,kowa tana riƙeda jariri a kafaɗa kuma,sai abun yazama kamar waya tarabasu ta hanyar editing.
Nimrah kam da take gaba ganin sun kusa isota tashi tayi da gudu ta koma jikin ummi wacce itama tayi suman zaune saboda kiɗima.
Ɗan murmushi Ahmad yasake ganin yanda suka ruɗe da shigowar su surayyah. Gyaran murya yayi a lokacin da su surayya suka zauna a tsakar falon suma.
Nuna su yayi domin gabatar dasu.
"To jama'ar falonnan ga surayyah wacce nayi nemanta shekara Bakwai dasuka wuce kuma aka bani aurenta mukayi zaman aure da ita harda rabo a tsakaninmu na farhana,har Ila yau kuma tasake haifamin wasu ƴan biyun Abdurrahim da Abdurrahman. Wannan kuma sunan ta Jurayyah wacce ƴar uwar Surayyah ce da aka haifesu tare,an rabasu ne tun a wajen haihuwa batareda sanin iyayensu ba saboda wani dalili,ita ce wacce aka turo t zauna dani bayan an sace Surayyah da ƙaramin ciki. Itama tayi goyon ciki nawa,amma anyi amfani da kimiyyar zamani ne wajen dasa mata ragowar ƙwayoyin halittar da muka bari a asibiti lokacin da akayi extarnal fertilization na haihuwar su farhana,saidai ta haihu kwana huɗu da suka wuce amma ɗan baizo da rai ba"
A taƙaice yayi bayanin,duk da yabar abubuwa da dama a binne wanda sai a hankali za'a bada labarinsu,amma hakan bai hana mahaifiyar su Surayyah tashi ta isa inda suke ba. Hannayensu dukka takamo a cikin nata tana kallo.
"Furtawa ne banyi ba,amma naso nagane Jurayyah ba Surayyah bace lokacin data zauna a wajena,saidai kuma ina jinta a jikina sosai kaman yanda nakejin Surayyah. Sai nayi tunanin to ko cikin dayake jikinta ne yasaka ta yin wasu abubuwan da bata saba yinsu a baya ba,ashe ........ba ita bace amma ita ma ƴa ta ce,bansan da ita ba amma ashe tana taredani. Kuma shiyasa surayya take haihuwar ƴan biyu ashe itama ba ita kaɗai ta zauna a ciki ba.Wanne marar imaninne ya rabani dake a lokacin da kike tsananin buƙata ta haka?"
Ta ƙarisa maganar tana fashewa da kuka mai tsuma zuciya.
"Hajiya zakiyya ce,wanda a yanda take faɗin labarinku inada tabbacin kuma kun santa,sannan tana ta ikirarin fansa dani kaina bansan wacce fansa bace"
Daskarewa kukan da takeyi yayi tareda ɗago kanta a sauri ta kalli Jurayyah,shin taji da gaske kuwa. Waigawa tayi ta kalli Alhaji wanda shima da alama yaji sunan da kyau,kuma fuskarsa ta bayyana hakan ƙarara.
"Zakiyya!!! Yanzu dama tsawon wannan lokacin zakiyya tana nan a cikin duhu tana bibiyarmu, dan rashi imani ta raba jaririya da uwarta a wannan matakin. Lallai anyi gaskiya da akace mutum da halinsa bazai taba sanjawa ba"
A Lokacin kuma sai hankalin kowa yakoma kan son jin labari wacece zakiyya sannan mai yasakata ta aikata wannan aikin.
"Ahah wannan inaga abinda yashafi gidane bai kamata a buɗeshi anan ba"
"Ahah yashafi kowa,ko bai shafi kowa da farko ba yanzu kam yashafi kowa,tunda abinda yafarune shekaru talatin da suka wuce,shine bai mutu ba yaketa haifar da wadannan matsaloli. Zakiyya aminiyata ce damuka tashi tare,saboda mu maƙwantai ne,kuma mun taso da son karatu sosai. Hakan yasa muka jajirce duk da a lokacinmu ba kowane yake karatu ba. Mun samu ƙalubale da dama kasancewarmu gamu mata,a haka muka gama digirinmu a jami'ar Ado bayero,a wajen services ɗinmu ne ya fito a nan garin abuja,saida aka kai ruwa rana kafin iyayena ni suka barni nazo,kuma kasancewar ga ita ƙawata zakiyya zamu tafi tare,gashi lokacin babu dama mutum ya sauya inda aka turashi haka muka taho. Kasancewar Environmetal muka karanta sai muka samu aiki a companyn Su babanku lokacin shima bai dade da dawowa daga karatu a ƙasar waje ba aka naɗashi managern companyn,ga ilimi ga babban matsayi ga kuma ƙananun shekaru sai hakan ya ruɗi ma'aikata mata dayawa a wajen marasa aure,ciki harda ƙawata zakiyya. Kasancewar tanada dakiyar zuciya kai tsaye ta miƙa masa tayinta,shikuma ashe ya tunda ya ɗora idonsa akaina yaji na kwanta masa a rai,yana kula zakiyya ne inta cikashi da surutu saboda ni da muke tareda ita a kullum. A hankali a hankali soyayyata take zurfi a ransa,nima kuma bazance na ƙishi ba,saidai bazan bashi dama ba saboda ƙawata tana sonsa.
Itama a nata bangaren soyayyar sa na zurfi a ranta,duk da so makaho ne har idonta ya buɗe tagano ni yakeso nikuma ina ja da baya saboda ita. Hakan ba ƙaramin bata mata rai yayi,sai ta fara yimin maganganu wai ina cin amanarta,wanda ni na rasa ta ina naci amanarta ta. Ina dai ƙyaleta saboda banaso zumuncinmu ya tabu saboda namiji.
Katsam ranar muka tashi da wani al'amari,an kama zakiyya a office ɗin Dr. Salihu ta bugar dashi da ƙwaya kan lallai sai yayi lalata da ita,saboda hakan yasa ya aureta idan ta samu cikinsa,nikuma ya rabu dani. Wannan makahon tunaninnnata shine maƙasudin faruwar komi. Bayan an kawo masa ɗauki ya farfaɗo sai ya ɗauki tsatstsauran mataki akanta.
Ya koreta daga bautar ƙasar da takeyi,yakai report ɗinta headquarter na NYSC,sannan ya fito muraran yace mata ni yakeso kuma ina gamawa za'a ɗaura mana aure. Nima ganin abinda tayi sai na janye jikina daga nata,kuma na bawa Dr. Salihu dama muka fara soyayya har mukayi aure.
Wannan ne abinda ya faru,nayi zaton ta manta dani da ahalina ashe ba haka bane,kashe maciji mukayi bamu sare kansa ba. Wannan kanne yacigaba da saranmu har zuwa yau"
Kowa numfashi yaja lokacin da mahaifiyar su Surayyah tagama basu taƙaitacce labarin mai yafaru kuma wacece zakiyya a wajenta.
Itama Jurayyah taƙaitaccen labarin abinda yafaru ta bayar kaman yanda ta bawa su Surayyah. Ko ya jinjina lamarin matuƙa.
"Toh bayan wannan akwai hukuncin danake so na yanke a gaban kowa kafin a tashi. Na bawa Surayyah izini taje gidansu idan akayi suna tayi arba'in ta ɗan huta sannan su samu sabo itada ƴar uwarta. Sannan kuma na saki Safeenah saki ɗaya,itama taje gida tayi idda ta haife abinda yake cikinta in yaso daga baya idan taso saita auri shi baban cikinnata"
Ba kowa a wajen ba hajiya Hunaiza tafi kowa kiɗima da furucinnasa na ƙarshe,saboda ita a zatonta babu wanda yasan mai yake faruwa ballantana ma Ahmad da baya zama. Ganin babu wanda ya tambayeshi mai yasa ko miye dalili yasa tasake shan ruwan jikinta,wato kowa yasan mai yake faruwa,shuru kawai akayi aka zuba mata ido aga iya gudun ruwanta. Gaskiya bata taba muzanta irinna yau ba,tayi zaton zaman bazai shafesu ba ashe su zaifi shafama,da tasan haka zata faru da bazata zo ba kuwa.
Safeena kuwa jin abinda yace yasa ta kifa kanta a cikin gwiwoyinta ta fashe da kuka,babu wanda yako kalleta har tayi mai isarta,dan mai rarrashinnata itama jikinta a sanyaye yake.
Ana shirin tashi ɗaya daga cikin security ya shigo falon.
"Assalamu alaikum ayimin afuwa wata matace tashigo tace ayi mata iso zuwa wajenku"
"Wacece haka,tabari sai angama family meeting tukunna"
"Ehh tace wai itama family ce ai"
Kowa mamaki ne yakamashi to wacce family ce,Mutum ɗaya ce kawai bata wajen yayar nimrah,ita kuwa bata ƙasar ma,in itace kuwa ai kawai shigowa zatayi.
"Kace ta shigo"
Shine abinda baban su Ahmad yace.
Zeezah ce tashigo tasha hijabi har ƙasa kamar ta Allah,idanunta zururun kaman ta wuni tana zawayi.
Da Jurayyah suka haɗa ido wacce takeyi mata kallon tuhuma na mai yakawota nan bayan bata fara zuwa takanta ba.
Ƙarewa mutanen wajen kallo tayi,da farko tayi zaton zata iya dakiyar tunkararsu, can gidansu Surayyah taje amma sai akace mata suna nan,da bazata jeba amma kuma wata zuciyar yace mata ta zafi zafi ake dukan ƙarfe,gwara ta nemi ahalinta tunkafin waccar guntun gawar ta margaya.
Bakinta yana rawa tanason furta wani abu amma ta kasa,haka kawai taji mutanen ɗakin sunyi mata kwarjini sosai.
Zubewa tayi akan gwiwoyinta da takarda a hannunta, wanda ta sato a drawer mahaifiyarta na sperm donation da akayimata da kuɗin data siya dakuma saka hannun likitan wanda family doctorn sune ya munafirceshi akan za'a yimasa check up ne,ya ɗiba yayiwa Hakiya zakiyya aikin data zuba masa tsubun kuɗi.
"Kuyi haƙuri ku gafarceni banzo wajennan da niyyar cutarwa ba"
"To dama idan cutarwar kikazo zaki sake samun damane,ai ba'a saran maciji a waje ɗaya"
"Dan Allah kiyi haƙuri Rayyah,nasan nayimiki butulci mungun butulci amma dan Allah ki yafemin a matsayina na ƴar uwarki dan Allah"
"Ƴar uwa? A ina nazama ƴar uwarki Zeesha,duk abinda kikayimin kinada bakin faɗin haka?"
Ganin hawayen dayake gangarowa a idonta yasa tasan cewar akwai abinda yake faruwa,don ruwa bazai taba tsami banza ba,koda yake ashe fa bangonnata ta faɗi tana asibiti,amma ai da hakan zai bata damar fantamawa ne ta mallake komai.
Jijjiga kai zeeza tayi tareda cigaba dacewa.
"Nasan abinda nayimiki ba ƙarami bane,nice nake kai sirrinki wajen mommy,na cutar da cikin jikinki da hanyar sakamiki guba,sannan na boye miki wacece ni saboda sauya halittar danayi. Amma duk nayine saboda a haka aka ginani,banayi komai sai abinda tasakani,na damace ta kamani da danasani saboda wani labari danaji daga gareta,wannan labari ya tarwatsa zuciyata,ya jefani cikin matsanancin tunani,ban taba tuhumar rayuwar danakeyi ba sai a ranar,naji tamkar ƙasa ta nutse na shige a ciki. Kaman yanda kikaji na ƙiraki ƴar uwata da gaske nakeyi Rayya,shiyasa ma abinda nayi miki yasake yimin ciwo. Hanyar dakikabi kika samu cikin ki hanyar akabi nima aka samu nawa cikin,saidai ki ɗauke matsayin Ahmad a cikin lamarin ki saka na Abbanku a ciki"
Amin magana ta wannan layin
***
Sadi-sakhna ce.