Free chapter · Read without an account
Chapter 20
by ZAHRAA · Bayan Murmushi
page 20💬⌨️
bayan murmushi….
zahraB(Mrs)
Farhana ta farka da safe, zuciyarta cike da rikice-rikice. Duk da hawayen da ta zubar cikin dare yanzu tana ƙoƙarin daidaita kanta
Tana zaune a ɗaki, tana kallon wayarta. Saƙonnin rommies dinta sun cika screen: “Ki yi hakuri, ki dauki kaddara Allah yana tare da ke :from fateeha :yanzu zaki fara Sabuwar rayuwa :from precious
Zee adetayo ma tana yawan kiranta inda take sanar mata sun fara communicating da fadila qanwar AK.ga Adda Sabrina kullum cikin turo mata Duas take Akan ta lazamci yinsu zata sami sauki ,Hamma fahad ,Muhammad kullum cikin lallabata suke,already Hamma sajid ya Koma Zaria jia .
Karar bude kofar dakin ne ya dawo da farhana daga tunanin ta,autar su sameena ta shigo Yau bataje school ba ,suna mid term break ,
Adda farhana Wai abbi yace ki shirya yaya AK yana falo zaku tafi yin passport,sameena ta fada Tana kokarin shigowa dakin
Ban gane yana falo ba ?Yaushe yazo ta tambaya a jere ,Uhmm gaskia ina ga zaiyi 20 min da shigowa ta bata amsa tana kokarin fara share masu dakin ,Tinda aka fara maganar auren nan sameena ta fara kwana a dakin diddi ita da inna Jamila ,a cewar diddi farhana Tana bukatar privacy.wato yanzu yafi karfin ya kirata sai dai ya kira abbi kenan?
wanka farhana tayi ,ta shirya cikin Riga da skirts na atamfa batayi kwalliya ba ko kadan sai dan kwalli da lipgloss ta dan shafa,sai hijab dinta har kasa tare da handbag
A falo ta tarar da nene rashe rashe a carpet sai zuba take
“Good morning, Farhana,” AK ya ce, muryarsa cike da izza amma mai natsuwa.
Good morning,” ta amsa, muryarta a hankali.
Ta lura da smile ɗin AK, da kallon da yake binta dashi .
“Ready?” ya tambaya.
“Eh… ina shirya ta furta, tana ɗan wasa da zoben hannunta .
Nene sai mun dawo na furta ,already diddi da inna Jamila Sun shiga kasuwa tin Wajan 10.
A dawo lafiya yar albarka ,to dan gidan gomna Ka gaishe da gomna dan Allah ,kuma kar Ka manta da maganar mu . Murmushi AK yayi yana cewa inshaAllah nene kuma Zan fadawa dady sakon ki ,bundles ya ajiye mata sai zabga godiya take Kamar sabuwar marokiya.
Fitar su ke da wuya AK ya kalli farhana ,je ki cire hijab din nan bana son kauyenci yace cikin ko in kula ,da mamaki ta kalle shi ,hijab din ne kauyenci ?
Do as i say Kina bata mun lokaci
Ya fada tare da shiga cikin Motar
Fuuu ta shige cikin gida ,nene ta tarar tana kirga kudi tana Jin motsinta ta boye,ke zo nan har kun dawo?ko dai bakin halin kika masa ya koroki?banza farhana ta mata tana Kara gyara zama.sai dai ya gaji ya tafi,amma bazan cire hijabin ba .
Dan ubanki ba magana nake miki ba?dan gomna kika wulakanta ko me?dan Allah nene ki kyale ni,farhana ta fada a harzuke ,ya zaayi yace nasa hijabi Kamar yar kauye na koma nasa mayafi ?
Ay dole yace haka ,ni kaina shiru nayi miki farhana kar ace na cika takura ,amma Kina amarya ace ganin farko ya ganki Kamar mai takaba?kallon nene farhana tayi cike da mamaki ,nene da ita ta koya masu sa hijabi tin basa so har suka Saba? Kiran sameena nene tayi ,maza jeki dauko mata mayafin da zai shiga da atamfar ,ta barshi a waje shi kadai ,Nifa ba inda zani sai dai ke ki bashi kuje yin passport din farhana tafada tana kwanciya a kujerar
Wallahi wallahi sai kinje Shegiya mai bakin Hali ,idan baki tashi ba kuma sai na tsinewa iro yabi duniya ,banza farhana ta mata ,iro Allah ya ts….zubur ta mike yanzu nene sai ta tsinewa abbi dan na mata lefi,mayafin ta sa ta fita ranta a bace ,yayinda nene Keta zage zage
Bayan shigar farhana Ak ya fara tunanin yadda sukayi da hanadi Kafin ya fito
Ina zaka haka darling kai da Baka tashi da wuri tunda ba office zaka ba ?hanadi ta tambaya cike da mamaki ,almost 2 months Kenan da zuwan AK naija ,he’s working from home ,sai azahar yake tashi
Wajan farhana zani ,zamu fara process din visa dinta ya fada yana gyara zaman agogon sa ,
Wani Abu ne ya tsaya a zuciyar hanadi ,wato Sabida farhana AK ya tashi da wuri ?mutumin da baya hada baccin safen sa da komai?tsaki taja tana kokarin ficewa daga dakin,janyo ta AK yayi with full force ,what the hell ni kike yiwa tsaki ?kin fara Raina ni kwana biyun nan ,Sabida Kinga mommy da su yaya ramla suna bayanki ko.kayi hakuri darling ban San ya fito fili ba a cikin Raina nayi am sorry ta fada a marairaice ,get lost ya ce tare da nuna mata kofa
Sum sum ta fice ba tare da Musu ba
Bude motar da farhana tayi ya dawo da AK daga tunaninsa
Murmushi yayi tare da cewa ko Kefa wifey yanzu Kinfi kyau
Kala ban ce ,driving ya fara yana kokarin fita daga unguwarmu
Allah sarki farooq dina,ko me yake yi yanzu?ya chi abinci ?me mamma za tace ?tunanin da nake yi kenan ,burkin da aka ja da Karfi yasa na juyo na kalli AK da mamaki
Tunanin me kk haka nafi 3 mints Ina magana kinyi shiru AK ya tambaya yana tsare ni da ido .
Uhmm ba komai nace a sanyaye
Wayata ce tayi kara message din zee ne ya shigo ,kwace wayar naji anyi da Karfi,ya kamata mu yar da phone din nan wifey ,ba class dinki bane Kina Inlaw din governor da old phone ,danne danne ya fara a cikin wayar .danace Miki kar kiyi magana da farooq sai da kk yi ko?ga calls dinshi nan na gani a WhatsApp call logs Kunyi 25 mins kuna magana ,Muryar Ak ke fita a zafafe ,dago wa nayi na kalle shi ,idonsa har ya canza launi ,for the first time naji tsoron AK
Answer me ya qara fada cikin Tsawa,shiru nayi sai hawaye,what is mine is mine ,I don’t fucking share you’re mine alone damn it .
Maste jikina nayi a gefen kofa ina kuka, har yanzu Kina sonsa ko?ya fada murya a kasa ,kaina na gayda alamun eh ,matsowa Ak yayi kusa dani ,ba zato ba tsamani kawai naji Shaka ,ya shake mun wuya ,idan kika qara tunaninsa sai na kashe ki ,tari na fara ina gyada kai ,saki na yayi yana maida Numfashi ,ni kuma Ina gefe Ina tarin wahala ,Bottle water ya miko min Bayan ya bude ,cikin karamar murya Kamar bashi ba ,ya fara sorry Kinji wifey bazan kara ba ,ke kika ja ki Dena tunaninsa sai mu zauna lafiya Kinji ya fada a tausasai ,kallon mamaki na kara binsa dashi yanzu ya gama yunkurin kashe ni ,next mint ya Koma rarrashi,am so sorry Kinji soul forgive your husband, ya fada tare da kissing din goshi na , hanunsa daya a cikin nawa ,haka ya fara driving da daya hannun jefe jefe yana juyo wa tare da min kalllon soyayyah,a lokacin na rasa tunanin mai zanyi ,wayata Dama already ya wullata titi
Mun iso An kira mu counter ɗin office. Na tashi , AK ya tsaya kusa Dani , yana tabbatar da na tsaya lafiya Kamar wani bodyguard,Yayin da muke cike forms da officer ya bamu ,idanuwana sun hadu dana AK sau da yawa, ina ganin yadda yake kulawa dani da tsantsa – ba kamar saurayina ba ,amma mijina tunanin Farooq ya fado min
“Yanzu dole ne na fara rayuwa da AK… ya zanyi da son farooq ?
Maganar Officer ta dawo dani daga tunanin na
“Ki jira ɗan lokaci, passport ɗinki zai kasance ready cikin few days.”
AK ya kalli Farhana, yana murmushi
Bayan mun fito shagon waya muka nufa ,inda ya siya mun latest iPhone 7+ (2016)muka biya aka saya sabon SIM card tare da register daga nan ya ajiye ni a kofar gida tare da qara bani hakurin abinda ya faru dazu.mamakin Kansa AK ya dinga yi ,shine ya lalace yana ba mace hakuri haka?gskia soyayyar farhana ta masa kace kace 😂
A bangaren biyun an fara shirye shiryen biki shanun Nene Guda 5 aka sayar domin yin kayan daki. A haka ma sai da baffan su diddi ya aiko da 500k na kayan kitchen yayinda maman diddi wacce ake kira mamii ita da sauran yan uwan diddi Sun dauki nauyin yin kayan Gara duk da auren yazo Musu a bazata sunyi alkawarin halartar bikin inshaAllah,babu abinda abbi zai ce wa dangin matarsa sai ,Addua kullum cikin rufa masa asiri suke . sadakin farhana kuwa diddi gold ta siyo mata a cewarta bazaaa taba kudin ba,Tinda hakin tane,car key na hannun Hamma fahad Tinda aka kawo Motar suka kai ajiya gidan abokin abbi,abbi ya bada umarnin idan ta tare sai a kai mata motar gidanta .
Farhana tana zaune kusa da Inna Jamila ,yayinda kwana biyu inna ta sa ta a gaba da gyaran jiki da magunguna ,yanzu ma Dilka aka gama ita kanta tasan ta canza skin dinta sai glowing yake .Ak ya turo kudin gyaran jiki ta account din Adda Sabrina .
A daya bangaren , roomies ɗin Farhana – Fateeha, Precious, Nusaiba suna shirye-shiryen biki tuni har ankon su ya iso ta hannun Zee Adetayo ,sunyi mamaki da zee ta fada masu cewa AK dan governor ne ,farhana bata taba fada Musu waye AK ba .dik a sanyaye suke zasuyi kewar farhana ,amma haka suke daurewa dan karfafa farhana .ta Kira su da new number ta, Bayan Hamma sajid ya turo mata number precious .sauran family members duk an aika masu da nasu ankon .
Yayinda Ango AK ya turo one of the best designers a abuja shine In charge of duk Kayan da amaryarsa zata sa har a gama biki
Jiya su inna Jamila ,inna asiya da inna hajara sisters din diddi ,sai kannen abbi mata ,mama sabuwa da hadiza suka tafi Jeren farhana a asokoro ,jikin su duk a sanyaye a lokacin da suka ga gidan wannan Katon gida haka ? A haka suka fara abinda ya kawo su already Ak ya tanadi duk abinda suke bukata tunda ya Kira exams officer yana tambayar sa yadda ake Abubuwan al ada ,shi a auren hanadi ba abinda yayi ,a lokacin zuwan masu jeren ma hanadi da yaran suna gidan yaya ramla ,sunyi jere Sun gama lafiya an dawo dasu gida ,Ak ne yake dube dube Bayan fitar su ,cos yana kallon su ta camera,a raine yake kallon Kayan ,this needs to be changed yace yana kallon kujerun falon .
Bayan kwana biyu
Yau dai rana ce mai cike da girma a gidansu Farhana.
Zaa kawo lefen Farhana daga gidansu Abdulkadir (AK), wanda zai haɗa da Halima(matar Abudlkarim ,kanin Ak) yaya Safiya da sauran yan uwa mommy.
Halima tafi kowa murnar wanan aure a cewar ta at least ta Sami farhana ,tunda hanadi bata kulata ,ga banbancin da su mommy suke nuna wa tskaninta da hanadi ,sunce hanadi yar uwar su ce ba suruka ba
Already Dama Kayan lefen suna abuja gidan yaya safiyya ,boxes 24 suka cika da luxury items Kaya Kala Kala harda golds ,aljuhun AK yayi kuka ba rage ba sassauci tskanin sa da yaya safiya.mommy ma ta tawagar ta nanda 3 days zasu iso dan a abuja ayyi dinner sai budar kai a sokoto.