Free chapter · Read without an account

KUSKURE 4

by Fatimaoumshaheed55 · KUSKURE

*KUSKURE*


By Maman Shaheed



Shafi Na Huɗu.. 




Furucin Likita y girgiza NAWAL Dan taji Abin har ranta "dududu yaushe na haihun da yaye ƴar Tata da har wani cikin zai shige ta ? Tambayar da ta dinga yima kanta kenan. 


SAFWAN Kuwa atake ƴa hango razana a tare da ita, ya basar shiko yanata murna ,cikin farinciki Yama Likita sallama yaja matar shi suka nufi mota Dan komawa gida, gudun kar su raba abin magana a asibiti, yadda ya ɓacin rai a ruhi da fuskar ta. 



Cikin mota , SAFWAN bayan ya fahimci  dalilin ɓacin ran nata, sai ya dinga rarashin NAWAL da nasiha aKan "wasu  nema ma suke Allah ya basu Amman Allah be Basu ba ba'asan Kuma irin tanadin da ya musu ba ,ke ya baki badan munfi Kowa ba Amman kina fushi da haka ko?"


Ta kalle shi ta ƙasan ido , Tana cewa" Ni fa ba fushi nake ba"  a hanzarce ya katseta 

" tun lokacin d Likita y Faɗi sakamakon test ɗin da ya Miki Naga annurin fuskar ki ya ɗauke ,nafa sanki Sarai motsi kikayi nasan me kike nufi na gama karantar ki fiye da tunanin ki" ya ɗauke kai ya cigaba da tuƙin shi. 


 Ɗago da Kai tayi Tana kukan da kana gani kasan daga zuciyar ta yake fitowa " nifa gani nayi ko 2yrs fa banyi da haihuwa ba ko mahaifina be gama koma mazaunin shi ba har Ace na sake ɗaukan ciki?" ......sai hawaye sharshar. 


Safwan ya yi murmushi Mai ciwo ,yace "haka Likita yace Miki mahaifanki be koma ba? Koko anaki likitancin ne Haka? ko jini ne Kika gaji da haɗawa Dani ? Ina nuna Miki gabas kina nausawa kudu Ko wife?" 


Ran SAFWAN ya gama ɓaci kawai ya Mata shiru ya ɗauke Mata wuta ko rarashin ta yaƙiyi akan kukan da takeyi , tun tanayi har ta gaji ta saurara ,suka Isa gd, 


Bayan sun shigo gida Indo na musu sannu da zuwa SAFWAN ne kawai ya iya amsawa ita ko uwar ɗakin ta  ɗaki ta wuce fuuuuu. 




Shima nashi room ɗ'in ya wuce ko bi takanta beyi ba ,Dan takaici da haushi da ta bashi. 


NAWAL Bata ƙara fitowa ba sai da ta fito dinner ,shiru shiru SAFWAN zai fito yaƙi fitowa ta Aika Indo ta kirashi (kuji haukan wasu matan ,wai ƴar Aiki ce da zuwa kiran mijin ki a ɗakin shi? ) akayi sa'a Mai kunyace Kuma Abin ya Mata nauyi Dan Bata taɓa shiga ɗakin shi Yana ciki ba Tana gyara Mai dai in baya Nan ( *WANI KUSKUREN*) Sabod haka a ƙofa ta tsaya tayi knocking, azaton Shi matar shi ce jin an yi har so biyu kawai yace" shigo Mana" ,atunanin sa NAWAL ce take shakar shiga dakin ta tsaya Tana knocking , inda watace shiga zatayi  , ita ko Indo miƙa bakinta tayi ya haɗu da ƙofan ta raɗa Mai " Aunty ce tace kazo kaci Abinci Tana jiran ka" Yadda zaiji dan a ɗan tsorace take maganar ma. 


Shi kanshi sai da yaji wani iri ,cikin zuciyar shi yace "Allah ya shirye ki dear" 

"kice Mata Ina fitowa" ,ya ba Indo amsa ,sanan ta tafi faɗan saƙon da ya bata .


Bayan fitowan shi , ba Yabo ba falasa ,sukaci Abinci ,Indo nata ba Noor a baki taci wani ta zubar da wani ,hakan cin nata yake .

Bayan sun gama cin   Abincin , ya koma ɗaakin shi dake yayi sallan ishan shi ,ganin baida halin kulata yasa ta bishi ɗakin shi Dan Abin ya dameta sosai .


Tana shiga ya ɗauke kan shi  yanata latsa wayar sa , bema nuna alaman ta shigo ba , Abin ya sake  Mata ciwo har ji tayi kamar ta koka Amman ta share Dan sulhu take nema (sulhu Alkhairi ne) ta zauna kusa dashi jikin su na shafan na juna tace" my dear wai meye lefi nane da ka ɗauke min wuta? nifa ba wani Abu yasa nakejin tsoro ba kaga fa yadda Nasha fama da laulayin Noor kai ganau ne ba jiyau ba , haka nazo na dinga fama da tirtsetsen ciki Ina keta Al'umma har Kai  da kanka tausaya min kakeyi Banda ɗumbin Al'ummah da bansan adadin su ba, sanan haihuwar ma kagafa irin gumarzon da Nasha harfa kuka ka tayani ko ka manta? ko kana so ka nunamin b tausayina ne ya saka kuka ba a  ɗakin haihuwar?"



Ta fashe da kuka Mai taɓa zuciya , shima ya tuno abubuwa da dama , Dan ya tausaya Mata matuƙa , ranar da zata haifi Noor ,atake ya manta da ɓacin ran da ta sahi aciki ,ga girman son da yake mata yayi tasiri a kanshi, hannu yasa ya talabo ta ya rungume Yana shafa bayanta Yana rarashin ta da kalamai masu sanyaya Rai ,tare da wa'azantar da ita ta sigar rarashi , Jin ɗumin jikin shi ya mantar da ita Komai, ya dinga sarafata tana mayar mai har suka faɗa duniyar Ma'aurata har suka  manta da wata ƴar su Noor ma. 



Cikin Nan ya tsayawa NAWAL arai musamman idan fanc ɗinta na tsokanar ta amakaranta wai ta zama uwar iyali sai taji dama cikin ya zube (wa'iyazubillah ) haka dai taketa lalaɓawa har cikin ya shiga wata Tara ,su twins insun Zo suna tayata Aiki sosai Dan komai basa Bari tayi na hidimar kanta da Noor sune suke yi  Dan sun ɗauke Noor ma ta koma gidan Ammy hankalin NAWAL kwance wai ta huta dama takura Mata take Taita danneta Tana Mata rigima, cikin jikin ta ko dama albarkacin uban shi kawai yake ci. 


SAFWAN yanata lalaɓata musamman  yadda ya san  ba wani damuwa tayi da cikin jikin ta ba ,haka dai har watan haihuwar ta yazo , naƙuda ta Kama ta Mai zafi , Dan kasa haihuwa tayi da kanta sai da aka Mata CS kowa ya tausaya Mata, da haihuwar tazo mata a haka mussaman MIJIN ta  taga gata Har Ammy lalaɓata takeyi anga narkewa kuwa Wajen NAWAL ko Abinci ma Bata Abaki  akeyi , doctor yace baze sallame ta ba sai taji karfi , suko cewa suke a lalaɓata ta Saboda Cs ɗin. 


Ta Sami ɗanta ƙato  su twins sai murna sukeyi ,dan suna son yara SAFWAN ko yafi kowa murna da zumuɗin akoma gida, Indo nata gadin gida da ƙalƙala shi da faman girki so ɗaya tazo asibiti da su twins. 


Bayan An sallameta ta dawo gida har su twins aka dawo Dan suna hutun makaranta , Suma maƙerin budurci ya nata ƙerasu sai kyau suke ƙarawa anzama ƴan Mata. 


Ranar suna yaro yaci sunan Alhj su SAFWAN ake Kiran shi da HANEEF Anyi shagalin suna lpy , an raraba kayan rabo ,su twins an Sha shagali dangi duk sun hallara da ƙawayen nawal .


Bayan suna su twins sun koma gida aikin ya dawo Kan Indo agogo sarkin Aiki Dan bataso suka tafi ba Dan suna rage Mata wahala aikin gidan. 


Yanzu ko Aiki ya dawo kanta hatta Pampers ɗin Haneef ita take care Mai inyayi Kashi ta wanke ta mayar Mai da wani ,haka wankin shi haka na Noor dake ta dawo tun suna Taki komawa wajen Ammy dasu twins wai Tana wajen baby.


Haka Indo taketa fama da hidimar gidan , har yakai ta yi shawara da Inna akan zata bar Aiki ,Inna tayi ta Bata hak'uri Kan juriya da jajircewa Akan Mai hakuri yanada nasara  arayuwar shi , Kuma tana taimaka musu da kuɗin aikin. 

Bayan an kwana biyu wata Rana suna zaune Indo  take gayama NAWAL zata bar Aiki Aiko hankalin NAWAL ya matuƙar tashi Dan ta saba da ita tasan sunyi dacen Mai Aiki kafin su Sami kamarta za a Dade musamman in tanajin hiran Mata a group da irin gwaramar da suka Sha da Masu Aiki , sai ta ƙara jinjina ma Indo Amman haka besa ta ƙyautata Mata ta jata ajiki ta rage Mata wasu hidimomin da be cancanta Ace ƴar Aiki ce zatayi ba gashi Bata taɓa kamata da lefin ta ɗaukan Mata ƙwayar shinkafa ba bare kuɗi ko wani abu har gwada ta ta dingayi, kawai Indo itace gidan ta fanin hidiman gidan. 

Da mamaki ƙarar Nawal  ta tambayeta dalili Taƙi faɗa  , Safwan ma ya tambayeta tace "bakomai" yace "ki ƙara haƙuri indai Baki da dalili?" tace "toh!" dan tana matuƙar jin nauyin shi da ganin girman shi, atake dan ya faranta mata har ya Mata ƙarin Albashi tayi ta Mai godia sanan tace "Amman inaso zaje gida na kwana biyu Dan innan ta batajin Daɗi" nanko ƙarya ta musu ,safwan ya jajanta Mata yace taje ba wani Abu  lpy ai tafi komai itama NAWAL ta ɗan tausaya Mata Dan tasan Tana aikatuwa ƴar , sanan SAFWAN ya biyata Albashin ta lokaci ma Bai cika ba " da mamaki tamai tuni ita indon Akan lokaci beyi ba ya biya ta, yace" ba damuwa na sani" saboda  yasan ƙaramin ƙarfi ne dasu ya Bata wasu kuɗin yace ta kaima Inna ,haka tayi tamai godia ta tashi ta tafi tace "ranar litinin zan dawo ma in sha Allah" dake yau juma'a.

Duk suka mata fatan dawowa lafiya.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol