Free chapter · Read without an account

Page 12

by Rahma Kabir · MIJIN ARO

Sarac Stars R Pen...✍️

Haj. Ladi tana ɗaga kiran nan suka gaisa kana ta tabbatar masa da maganar da Shamsu ya shaida masa sai dai ta buƙaci ya fara kawo kayan amma ba tada kuɗi a hannunta har sai mijinta ya dawo daga ƙasar waje, Mahmood ya jinjina kai kana yace mata ba damuwa suka yi sallama ya sauke wayar jiki a sanyaye, dan yasan akwai damuwa saboda bayi da kuɗin da zai kawo wannan kayan, wannan shine ga ƙoshi ga kwanan yunwa wato rijiya ta bada ruwa amma guga yana niman yin gardama, haka ya samu guri ya zauna ya rafka tagumi da tunanin makomar halin da yake ciki, duk da ance in duka yayi yawa na ka ake karewa amma shi ko na kan ya kasa karewa, ga matsalar mama gana Nuratu ga kuma na rashin kuɗi, yana zaune a haka abokinsa Mustapha ya shigo shagon ya ƙaraso ciki yana mai cewa.

Angon Nuratu bada kanka a sari in kaje gida kace ya faɗi, da fatan munyi sallah lafiya.

Alhamdulillah Mustyn Dije dan Tijjani uban Tijjani, kuma dan Tijjaniyya. Ashe ka fito kasuwa yau.

Mutumina ba dole ba ai ba zama an saci ɗan ɓarayo, wlh da kyar na samu na mai na saka a mota na fito, yanzu haka ko karfamfana bani da shi a aljihu.

Ai sallar nan sai hamdala amma wlh mutane na cikin yanayi, Allah ya cigaba da rufa mana asiri ya bamu shuwagabanni nagari.

Amin dan alfarmar sayyidina Rasulillahi, ya zan samu ɗari biyar a gunka.?

Cewar Musty yana jan gemu, Mahmood ya ɗan yi murmushi kana ya ciro kuɗi a aljihunsa dubu biyu ya zare dubu guda yace.

Kayi canji ka kawo mini dan ɗari biyar ɗin dashi zanci abinci, nima suke nan mini dubu biyun nan a aljihu.

Musty ya amsa yana godiya kana suka cigaba da hira wanda nan Mahmood ya koro masa halin da yake ciki na auren da mama ta saka shi sannan ya bashi labarin Nuratu akan ta dage sai dai ya auri wata ba Malika ba, sai ya samu kansa da ɓoye asalin maganar dan ba zai tonawa kansa asiri ba tunda Allah ya rufa masa, ya ɗaura da cewa.

Dama akwai wata 'yar bazarawa da nake tunanin ko kawai na yaɗa manufata na tura gidansu, kaga komai zai zo mini da sauƙi tunda auren Bazawara ba kashe kuɗi kamar na budurwa, babban matsalata yadda zan tunkari mamanmu da maganar tunda ita ta dage akan Malika.

To kai meye aibun Malika? ga sabon jini meye zaka yi da sauran wani.

Nuratu ce bata son Malika kuma nima yarinyar bata kwanta mini ba, kaga kuwa tunda ta bani damar na ƙara dole nayi mata abinda take so.

Hmmm wannan Nuratu dai ta gama shanyeka Mamuda.

Ba zaka gane bane Musty amma Nuratu matar rufin asiri ce, kai ma kasan labarin irin abubuwan da take yi mini, da sallar nan fa duk itace tayi hidimar komai hatta ragon layya ita ce ta siya.

Cike da mamaki Musty ya jinjina kai yana cewa.

Gaskiya wannan 'yar aljanna ce kuma a haka ta yarda ka ƙara aure? na sara mata! Ba ko wace mace ce zata iya haka ba, dan Allah abokinsa karka ci amanarta ka ƙara riƙe ta da kyau dan irin wannan matan a wannan zamanin sai an tona. Amma Allah yasa kayi bincike akan me ya kashe auren bazawarar da zaka aura.

Mijinta ne ya rasu kuma na wayeta sosai shiyasa ma kaji ina zancen zan aureta, sai dai fa bana jin ta a zuciyata zan yi auren ne domin faranta ran Nuratu na kuma cikawa mama ƙudurin ta nason da take yi na ƙara aure.

Ka ga ka jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya, mutumina kace ka kusa fara ɗaga mana kafaɗa saboda zaka ƙara ɗaura igiya.

Musty ya faɗa yana dariya, Mahmood ya yi murmushi kana suka cigaba da tattaunawa, wanda daga bisani Musty ya bashi shawarar yaje ya samu mama kaitsaye da maganar idan kuma taƙi yarda ya duba acikin family ɗinsu yaga wanene mama zata ji maganarsa ya kai ƙararta can yadda za a rarrasheta ta yarda, da wannan shawarar suka saki hirar Musty ya tafi shagonsa da yake siyar da 'yan kunne da sarƙa da kayan kwalliya, Mahmood ya yanke shawarar yana tashi daga kasuwa gidan mama zai nufa.

*****

Zuhura.

Tun a hanya ta shiga dokawa yaya Salima kira sai dai kira uku ta yi mata bata ɗaga ba, dan haka ta yanke anjima in bata biyo kiran ba zata kuma kiranta. Bayan ta ƙarasa aiki ta shiga ta yi signing kana ta fito ta nufi ɓangaren aikinta nan ta hangi Salame tana ta zubawa wani masifa ta ƙarasa gurin tana cewa.

Iya masifa da sassafe kin fara kumfar baki.

Salame ta ja tsaki.

Ke dai Allah ya wadaran naka ya lalace, mutane ne ba a iya musu kamar mune muka gadar musu da talauci. Muje ciki na baki labari dan kinyi sabon kamu fa?

Dagaske? fara bani nasha da ɗumi ɗuminsa.

Ba shekaran jiya nasa hotonki a status ba, hmmm! To kin dafi zuciyar wani matashin mai arziki, a jiya kawai dubu ɗari ya bani akan na shawo kanki ki amince masa, kawai na bari sai kin zo ne sai muyi maganar dan zancen bana waya bane.

Allah ƙawata? kice watan cin naira ya tsaya, amma fa wani hanzari ba gudu ba ni dai aure zanyi.

Zuhura ta ƙare maganar tana taɓe baki, wani kallo Salame tayi mata sheƙeƙe tana son ji ƙarin bayani dan tama kasa Magana, Zuhura ta saki dariya.

Allah da gaske nake yi, kuma auren bai wuce nan da sati uku ba, yazo mana a bazata ne.

Lallai ma Zuhura to wlh baki isa ba taya ina ganin kayanmu ya tsinke a gindin kaba amma zaki yi mana baƙin ciki, to da sake gwara tun wuri ki aje zancen aure nan, waima tsaya ba ke kika ce kin aje aure ba sai nan da wani lokaci to meye ya sauya miki ra'ayi?

Mijin besty Nuratu zan aura.

Wani irin tsalle Salame tayi ta koma gefe kana ta dafe ƙirji tana salati ta ƙare da cewa.

Ke ban son iskanci me hakan ke nufi?

Muje ɗakin nurses na baki labari kafin mutane su taru, kinsan ke ƙawar cin mushe ce dole kiji komai daga nan ma ki bani shawara.

Gyaɗa kai Salame tayi kana suka wuce ɗakin nurses suka shiga ciki, sunyi sa'a ba kowa dan haka suka zauna, Zuhura ta fara bata labari tun daga farkon abinda ya wakana a tsakaninta da Mahmood har zuwa ɗazun data je gidan Nuratu, ta ɗaura da cewa.

Wlh irin zazzafar kiss ɗin da Mahmood ya mini ba ƙaramin tsaya mini yayi ba a zuciya, na kasa mantawa shiyasa nake so na aure shi domin na kashe ƙishin ruwan sha'awata dan na tabbatar zai jiyar dani daɗin dana jima ina muradi.

Amma yin aure a yanzu bai yi wuri ba, karki yi wasa da damarki dan wlh Fahad dan gidan Ministan tsaro ba ƙaramin shegen kuɗi ke hannunsa ba, karki manta gomnati tana hannunsu sai sun so ƙasa zata zauna lafiya.

Salame ina so asirina ya rufu akan abinda na aikatawa aminiyata dan wlh har cikin zuciyata ina jin ban kyauta ba kuma ina gudun tsinuwar iyayena, sannan Mahmood komai nashi yayi mini ba ni da wani dogon buri akan auren mai kuɗi, nafi so na auri matashi kuma wanda zai ririta soyayyata.

Hmmm Zuhura amma kika ce mini yace baya sonki, wani irin aure za kiyi haka? kuma fa dole mutane su zage ki dan wannan ai cin amana ce ƙarara, gwara ma ta tona muku asirin ai ba kanki farau ba to se me? nifa ina miki fatan ki kama Fahad ram har ki samu ya aureki.

Ki daina yaudarar kanki waɗannan yaran masu kuɗin ba kasafai aure ya dame su ba, sun fi son samun na titi suci su yarda kwallon mangoro, dan haka aure shine suturar ko wace mace, kuma shima Mahmood da rufin asirinsa baki ga yadda yake bautawa Nuratu da 'ya'yanta ba gurin hidimarsu.

To yanzu kina nufin Fahad ba zai samu shiga ba.?

Eh gaskiya dan na ɗauki hanyar tuba dama banyi nisa ba a ciki, kuma na jima rabona da na bawa wani ƙato ya dirjeni tun kafin azumi, kinga yayi daidai da na yi istibra'i, idan zaki bani shawara ki bani na yadda zan baza mulki a zuciyar Mahmood, dan wlh ina son aurensa nasan ya ishe ni jin daɗin duniya.

Hmmm shikenan ba zan matsa miki ba amma dai kin cuceni dan kin rufe mini hanyar samun kuɗi dake, yanzu shawarar da zan fara baki shine ki ɓoye maganar auren nan sai dai kwatsam aji kinyi aure saboda masu ɓata suna, kinsan yanzu kiwon mutum ake yi ba dabba ba, dan sai kiji an samu wani ɗan shegiya yaje ya ɓata ki a gun Mahmood ɗin, sannan ki bari ayi miki ɗinkin HQ ta yadda zaki matse ya jiki kamar sabuwa, saiki ɗaura da shan magungunar gyara.

Wow kin kawo shawara mai kyau, aiko da zafi zafi ake dukan ƙarfe bari zanje gidan yaya Salma ta haɗani da Ummu Sultan mai RKtestybite nayi oder ɗin tsumin 'yar gata da kuma dafaffiyar kazar Amare, ke harda Sabaya zan siya na haɗa na sha.

_Dan samun tsumin 'yar gata, ko saiwowin tsumin ki dafa da kanki, ko kazar amare, ko yajin jaraba, ko maganin sanyi. Dangin kayan motsa baki snacks, samosa, doughnut, spring rolls, cookies, cin-cin to a tuntunbi wannan number *** RKtestybite. Muna tura kaya a ko ina. A tabbatar an shirya kafin a nimemu._

Shegiya kinsan kan tsiya ina kyautata zaton da wannan haɗin zaki tashi kan bawon Allah ya susuce miki, gaskiya Nuratu tana ruwa dan wlh sai tafi fulawa laushi tunda ita ba lafiyar yin abun, ohhh Zuzuu kin kwashi dami a kala.

Ta ƙare maganar suna tafa hannu tare da sakin dariya, Zuhura ta miƙe tana Cewa.

Shiyasa ba zan bari wannan damar ta kuɓuce mini ba. Kin ga muje mu fara aiki kafin azo ana surutu da mita.

Zuzuu bakinki ƙanin ƙafarki ki ɓoye maganar auren nan hatta su mama karsu san mijin Nuratu ne dan nasan suka sani zasu iya hana auren.

Hmmm ai da nayi niyyar faɗawa yaya Salima amma itama na fasa dan karta ɓata mini shiri. Sai dai suyi haƙuri amma fa naga gidan aure. Yo ni na aiketa da ta yarda na auri mijinta.?

Zuhura tayi maganar tana 'yar dariya, sai Salame ta bata hannu suka tafa kana suka fito suna ƙara tattauna maganar a hankali dan kar wani yaji.

****

Nuratu.

Suna shiga falo autanta Ashraf ya rugo da gudu ya rungumeta yana yi mata oyoyo, sai ta ɗauke shi tana dariya kana suka ƙarasa ciki ta zauna a cushing tana sauke Ashraf cikin nishi.

Babana me kake ci haka naga kayi nauyi tubarakallah.

Tuwo Umma ke dafa mamu, anty Jalili ke bamu nama mu ci da tin-tin me da'i.

Cewar Ashraf yana dariya, suma dariyar suka yi Umma tana cewa.

Saifa tin-tin me da'i, wannan me gidan nawa zanga randa zaka iya mag QQana, shekara huɗu amma baki duk tsami.

Sai suka ƙara sakin dariya suka cigaba da gaishe gaishe cikin raha, yaran suka zo ɗaya bayan ɗaya suna gaishe da Nuratu tana amsawa fuska sake kana suka basu guri, Nuratu ta kalli Zulfa tana cewa.

Da girman kujerarki Antynmu, ke waya ce miki ana yaji lokacin sallah, yanzu dai ragon layya kin yiwa kanki asararsa haka kurum, bayan kin san ki na da umma da mu ai dole zamu mara miki baya da kin kawo ƙararsa garemu, dan haka a riƙa haƙuri da rayuwa mazan nan namu sai ana haƙuri da su, karki yarda ki fara sakawa mijinki tunanin ƙara aure dan yaya Hafiz bai da ra'ayi mata biyu a yanzu, amma sakacinki zai iya saka shi yayi tunanin ya ƙara, da yawan mata suke sanya wa mazan su tunanin matan waje saboda sakacinsu da kuma riƙon sakainar kashin da suke yi musu.

Wannan gaskiya ne big Anty.

Cewar Jalila tana yi mata jinjina da hannu, Nuratu ta danƙara mata harara.

Bar gurin nan, manya na magana kina saka baki.

Kwana nawa ne zan bi sahu, ai gwara tun yanzu na riƙa jin maganar manyan dan na riƙe a kwanyata a gaba zai mini amfani.

Cewar Jalila tana 'yar dariya, nan suka sa dariya suna yi mata tsiya Nuratu ta ɗaura da cewa.

Lallai Jalila ai sai mu cewa Haisam yayi gaggawar fitowa tun kafin ki fara shawarar kai kanki gidansa. Yauwa Zulfa na dawo gareki, tunda kin san kina zuwa makaranta kamata yayi ki tsarawa kanki time table na yadda zaki gudanar da ayyukan cikin gidanki. Musali kin kwanta ƙarfe goma zuwa da rabi na dare, kin tashi da asubahi to sai karki koma barci bayan kinyi sallah, sai ki shiga kitchen ki ɗaura sanwar abinda zaku karya da shi, sai ki fito ki gyara falo da ɗakuna ba wani lokaci zai ɗauka ba duba da ba wani datti tunda ba yara gareku ba, ki koma kitchen ki ƙarasa breakfast sannan ki gyara inda kika ɓata a kitchen ɗin, sai ki koma kiyi wanka kiyi shirin makaranta, na tabbatar kafin takwas na safe kin gama sai ki karya kiyi sallama da mijinki ki tafi abunki, idan ya karya tare da ke to in kuma sai ya tashi daga barcinsa ke dai kin sallame shi tunda kin bar masa komai na buƙatarsa. Kinga kinyi maganin duk wani ƙorafi, Kuma ko da yara kike dasu suka fara zuwa makaranta ba zaki sha wahalar shirya su ba duba da kin sabawa kanki aikin safen, kuma ko ba ki da makaranta ki tabbatar da kin yi aikinki kin haɗa breakfast sai ki koma gado kiyi barcinki, ko yayanmu ya fito ba ƙorafi domin ya san kin gama sallamarsa abincin da zai ci.

Jinjina Beena tayi mata tana cewa.

Gaskiya anty kin more wato duk huɗubar umma babu wanda kika yar a ciki, a wannan dogon zancen naki nima na ɗauki gyara, wato in mace tana son zaman lafiya da mai gidanta sai ta cire son jiki kan a zauna dai dai.

Sosai kuwa domin Namiji baya son jira musamman a abinci, baya so ya dawo ba a gama ba ko bama a ɗaura ba, rashin mayar da hankali wajen girki wlh ba ƙaramin saɓani yake kawowa ba a aure, akan girki sai ayi ta ɗauki ba daɗi daga ƙarshe kan dalilin haka namiji ya ƙara aure, dan maza basa jure yunwa kuma akansa zasu iya yanke ko wani irin hukunci musamman in suna cikin fushi.

Nuratu ta ƙare maganar tana jan fasali.

_Bance Nuratu bata kuskure ba, domin duk ɗan Adam tara yake bai cika goma ba Amma dai Ina da tabbacin ko yaya ne zaku ƙaru._

Ayi haƙuri da rashin posting kullun Wlh uzuri ke riƙe ni, Amma In Sha Allah zan yi maganin haka.

Rahma Kabir ce matar MG. [5/9, 4:11 PM] Rahma Kabir: *MIJIN ARO*

Na

©®Rahma Kabir MrsMG.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol