Free chapter 路 Read without an account

Chapter 25

by ZAHRAA 路 Bayan Murmushi

page 25鈱笍馃挰


Gently AK yake rike da hannuna har zuwa bakin mota inda security ya bude mana kofa ,Bayan mun yi settling na juyo na kalle shi with pleading eyes nace ,Uhmm pls mu biya gida naga diddi Nasan ba lalle tazo hall ba na furta a sanyaye ,har yanzu hannuna na cikin nasa .its fine zamu je amma amma ba dadewa zamuyi ba kin San mommy tace no African time .

Kiran sauran drivers din AK yayi tare da basu umarnin  binmu a baya .within 15 mins muka karasa gently ya bude mun kofa ,tare da taimaka mun Wajan lifting gown dina.naga dai baya shirin sakin hannuna haka muka shiga Gidanmu tare hannuna a cikin nasa .ba mutane sosai a gidan ,am assuming Sun tafi Wajan dinner daga diddi sai mami sai nene da sauran tsofaffi.sakin hannun AK nayi tare da rungume diddi kam a jikina ,Kallona tayi cike da soyayyah kana tace ,kar kiyi kuka farhana ,don鈥檛 spoil your makeup nafeesah zata wakilceni a Wajan dinner  (qanwar diddi ce dake aure a Italy ,Sun  koma Italy 5 years ago tare da yaranta Bayan mijinta ya sami aiki a Chan  nayi mamaki sosai da akace zata zo bikina All the way,biki da rasuwa nawa aka yi tin tafiyar ta bata leko Nigeria ba sai yanzu ,Adda Sabrina dai tace dan taji dan governor Zan aura ne.

Nene na gefe an sha dungulmi da sabuwar atamfa sai zuba takewa AK .Sun gaisa da mami ma a mutunce.

Mun fito na tarar da convey motocin da qawaye suke ciki suna jiranmu 

Ba tare da bata lokaci ba muka dauki hanyar Cubbicle Marquee a maitama .


Hanadi ce cikin hadadden HKG lace dinta sai walkiya take  ,makeup artist din da yaya Safiyya ta kawo ta mata light makeup  .an mata dauri ta zabo gashinan na buzaye har baya .gefenta kuma kausar da intisaar cikin Cinderella gown dinsu ,dan har yanzu AK yaki bari a fara sa masu atamfa daga English wears sai abaya .yaya ramla Sun fito cikin irin lace din hanadi inda suka nufi parking lot suna shigewa  well clean car din da ke jiran su .


Mun shigo  Cubbicle Marquee inda aka ba kowa umarnin shiga ,baa son kowa a harabar hall sai bridesmaid dina .sai a sannan naga few of abokan AK harda turawa ,cikin nasu suit din.

Kiran mommy ne ya shigo wayar AK inda take sanar dashi karasowar su ita da tawagar ta.

Mu qarasa ku gaisa da momy Kafin mu shiga AK yace yana matsowa kusa Dani .gabana ne ya fadi ba tare da sanin dalili ba.

Wayarsa ta qara ringing mommy na sanar masa Sun shiga hall din already .masu hoto professional keta faman dauka ta ko Ina flash ne .Mc yayi sanarwa shigowar amarya da qawayenta tare da abokan ango,jafar na hango tare da wata a gefensa ,da dan visable ciki a jikinta ,take jikina ya bani itace Yasmin .kuma gashi naga suna gaisawa da fateeha ta tabbata yasmin din ce kenan

Mun zauna a sit din da aka tanadar wa da amarya da Ango .

Kalle kalle nake cikin hall din inda naga masu anko yan danginmu wajansu daban ,sai manyan mata qawayen mommy Suma Wajan zaman su daban .an fara event lafiya idan MC ya bukaci nida Ango mu fito  fili ,Frist lady da qawayenta na bukatar mu ,hannuna AK ya rike cike da kulawa Kamar Kwai muka tsaya a tsakiyar fili ,Ak ne ke mun rada tare da gabatar mun da momy ,dan runtsunawa nayi alamun gaisheta,camera nata flashing ,rungumeni tayi a jikinta suka cigaba da lika mana kudi ,Ak yayi mamakin yadda mommy ta rungume farhana amma daya juya yaga camera sai ya gane dalili .uwar amarya aka kira sai a sannan na Lura da anty Nafeesa Yaushe tazo garin ,har ta Sami mai makeup aka mata dinki har da gayyar qawaye ?kenan duk a waya ta tsara yadda abin zai kasance wannan lamari da mamaki yake ,meaning da qawayenta na abuja sukayi planing suka mata komai .amma fa ta hadu .sanye take cikin lace mint green tasha head da high hill gold ne a jikinta Kamar zasuyi magana haka friends dinta Kina ganin su Kinga rich abuja anties , a BUK yawanci ta hadu dasu ,Chan ta hada degree dinta a cewar ta Gara ta dan matsa daga illorin shi yasa ta zabi BUK .ta taba aiken mu gidan daya daga cikin friends dinta amso sako friend tata taje Italy shine anty Nafeesa ta bata tsaraba ta kawo mana ,a lokacin tare muka je da Hamma fahad a tsorace na shiga gidan Sabida ganin girman sa .

 Cike da isa suka qaraso ,ruwan 1k notes ne ke ta tashi anty Nafeesa da friends dinta sai barin naira suke min.Ak ya gaishe su cike da girmamawa.bayan mun koma sit dinmu aka fara refreshment,abinci ne tin ina kirga har na bata lissafi.rada AK yake min inda yake nuna min wata farar mata da ash mayafi ,hanadi kenan Itace uwargidana ,bazan iya tantace kamaninta ba,amma Abu daya nake hangowa daga nesa  fara ce tas.

Bridesmaid dina da yan uwana aka ba fili inda precious ta cire mints din dari biyar sabbi fill Tana sauke su a kaina ,a kalla precious ta lika kusan 100k sauran ma baa barsu a baya ba su zee ,fateeha Adda Sabrina abun sai San Barka .lastly yayyen ango aka Kira .sai yanzu uwargidan AK matso kusa Naga kyaunta .tare suke da su yaya Safiyya .hada ido mukayi da ita .take gabana ya fadi wani sanyanyen murmushi ta mun tare miki min hannu da niyar musabaha. Hannunta laushi Kamar na jarirai,bance bani da laushin hannu ba amma nata on another level ne.Ak yana gefe sai murmushi yake ,ya gabatar da yaya safiya da ramla .inda ramla na Lura da kyar ta amsa gaisuwata.na mata uzuri maybe dan Wajan bikine,be kamata AK ya gabatar damu a cikin wanan yanayin ba .ga kausar da intisaar mai hoto sai daukan mu yake .Abdulkarim ma yazo har sit dinmu tare da matarsa Halima idan ya  qara gabartar min da ita .fadila auta Dama ita ce kirjin biki itama naga da nata gayyar.

Biki yayi biki anchi ansha  anyi rawa an jagije 

A hararbar hall din na tarar da anty Nafeesa da su mommy ana hira,karfin halin anty Nafeesa na bani mamaki ,First Ladies ne fa da ministers qawayen mommy amma ji yadda take sai kace wata saaar su.

 Yanzu dai hanadi ki kwantar da hankalin ki ,Kinga dai farhanan ba wata Kayan gabas bace yaya ramla tace  Bayan Sun isa gida,Kayan gabas ce a Wajan AK Tinda tasan kalar macen da AK yake so,kuma farhana ce daidai da taste dinsa ,yana son mace doguwa mara Kiba mai boobs Kamar farhana.abu daya tasan maybe tafi ta farhana dashi shine maybe hips da baya.dan farinta ba damun AK yayi ba ,shida yataso  cikin turawa ,gashin ma damesa a cewar sa baya cikin abinda yake birgeshi sosai .ni dan yan Ethiopia ma take mun Kama ,muryar yaya Safiyya ya kaste tunanin hanadi .

qawayen nata ma yan duniya ,ni wacce aka ce maman amarya ita da kawayen Kamar renting dinsu akayi ,basu dace da  family farhanan ba ,yaya ramla ta cigaba da ranting 

.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol