Free chapter · Read without an account
Page 5
by Shamseeya Rabi'u Garba · AKASIN TSAMMANI (Beyond All Odds)
Kawar Mama Hajiya Kubra ce ta iso gidan misalin ƙarfe uku na rana. Mai gadi ya buɗe mata ƙofa, ta shigar da motarta kamar yadda ta saba. Bayan ta yi parking, ta fito cikin nutsuwa. Matar fara ce, doguwar, kyakkyawa, kana ganinta ka san ba karamar 'yar bariki ba ce, amma ta goge a salo me tsada.
Tana sanye da doguwar rigar shadda mai ƙyalli, an yi mata zubi, haɗe da ɗaurin da ake ganin jelar kitson attachment da ta yi.Ta saka gilashi mai girma, hannunta cike da zoɓɓa da sarka na zinare. Kai tsaye ta nufi kofar parlour, ta murɗa kofar, amma a rufe. Ta ɗanyi knocking.
A lokacin Zahra ta farka daga bacci, tana kan hanyar zuwa dining domin cin abinci. Amma da ta ga tuwon semovita da miya, sai ta juya zuwa kitchen don kwaɓa fulawa zata yi pancakes.
Tana Cikin kwaɓin ne ta ji knocking a ƙofa. Sai ta ɗauraye hannunta, ta je ta buɗe. Haj Kubra ta gani, sai kawai Kubra ta watsa mata wani kallo ta wuce ciki ba ko sallama, har kamar zata buge Zahra. Zahra ta bita da kallo har ta haura sama zuwa shashin Mama. Ita kuma ta koma kitchen ta ci gaba da aikinta.
---
Hajiya Kubra tana shiga dakin Mama ta tarar da ita tana cin fruit salad daga bowl. Ta zauna a kan couch cikin izza tana faɗin
“Hajiya Sahura, uwargida a gidan Alhaji Bashir mai dala.”
Mama ta murmusa, ta ce
“Wato kin zo da zolaya kenan.”
“A'a fa! Wannan ba zolaya ba ce, wallahi da gaske nake. Amma ki bar wannan... Wai me ke faruwa ne?”
Mama ta sauke ajiyar zuciya, tace
"Kubra, 'yar kallo ake son a mayar da Ni da 'ya'yana a gidan nan,yanzu haka fa idan yaran nan suka yi kuskure, Alhaji sai ka ga ya hau sababi. Amma idan Zahra ce, sai ya nemi kare ta kamar wata ruwan zinariya. Ni dai na gaji. Na kira ki ne saboda mu haɗa shawara, ko zan samu mafita.”
“Ƙawata kenan! Wallahi matsalar ki da nawa ɗaya ce. Sai dai ke ba ki son bin shawara. Ai tuni na gaya miki mu kai sunan Zahra da uwarta wajen malamin bayan tsauni amma kika ƙi.”
“Kubra, ke kin fi kowa sanin ba na shirka. Me zai sa na ɗauki kuɗina na kai wa wani makaryaci? Ya shiga min ƙarya aiki ya zo be yi ba.”
“To ke kika sani. Amma ki sani, tun da na kai sunan kishiyata wajen malamin nan, komai ya sauya. Gashi yanzu ni da bana gidan Alhaji ni ke da iko da shi. Duk da aure ya mutu, amma fa ikon da nake da shi yanzu, ko lokacin ina gidan ba Ni da shi.”
Mama ta girgiza kai
“Mu bar batun malamin nan. Ki ba ni wata mafitar.”
"To tunda kin ƙi wannan hanya, to ga wata. Chemist zamu je mu siyo maganin sa zawo.”
“Maganin sa zawo? Me kuma zamu yi da shi?”
Kubra ta leƙa falo da sauri
“Da fatan ba kowa a ciki?”
“Babu. Ki ci gaba da maganar ki”
Sai Kubra ta matso kusa da ita cikin sirri tace
“Za ki ba ɗaya daga cikin masu aikin gidan, amintacciya, ta zuba mata a abincinta ranar final exams ɗinta. Hakan zai hana ta rubuta jarrabawar. Kuma hakan zai iya janyo ta ƙara shekara. Bayan haka sai mu tsara yadda za mu ruguza karatunta gaba ɗaya.”
Mama ta dan jinjina kai cikin ɗaukar shawarar, ta ce
“Shawararki akwai kyau… amma ta yaya za mu sa mata maganin?”
“Ki bar hakan mai aikin. Kawai ki ba amintacciyar mai aikin kuɗi mai tsoka. Ita zata san yadda zata aiwatar.”
“Shikenan. Ina da Saude, amintacciyata ce. Komai zai zo da sauƙi.”
Sai suka yi dariya suka tafa hannu suka ci gaba da shirin su na mugunta.
---
Mommy na office kenan ta idar da sallar la’asar, ta ɗauki wayarta ta kira Zahra.
Zahra da ke dining tana cin pancakes ɗinta ta ɗaga cikin fara'a:
“Hello Mommy na!”
“Na’am autar Mommy da ba ta san ta girma ba.” Mommy ta ce cikin dariya.
“Mommy, da fatan kina lafiya?”
“Lafiya lau. Me kika tanada don zuwan Jameel?”
“Ban tanadi komai ba. Daman akwai bukatar hakan ne?”
“Haba Zahra! Ko small chops ba za ki shirya masa ba? Me ma aka dafa a gidan?”
“Tuwon semo da miyar kubewa.”
“Ga shi lokaci ya ƙure. Zan tsaya sayo masa small chops a eatery kawai. Ki yi wanka, ki shirya kafin na iso.”
“Ok, that's why I keep saying you're the best Mom in the entire universe. I love you!”
“Love you more dear.” Mommy ta faɗa, ta katse wayar.
Ta ɗauki key ɗin mota, ta rufe ofis ɗinta ta nufi eatery. Bayan ta siya samosa, spring rolls, da meat pie, ta koma mota.
Karfe 3:54 pm Mommy ta shigo gida. A dining area ta tarar su Mama da Kubra suna cin abinci. Ta gaishe su da sallama, amma babu mai amsawa. Shiru ta yi ta wuce sama ba tare da ta ce komai ba.
---
Bayan ‘yan mintuna, Jameel ya kira Zahra yana sanar da ita cewa yana bakin gate.
Zahra ta feshe turare a jikinta, ta gyara rigarta baƙa mai ado da fararen fursuna, ta yafa gyale a kanta. Ta saka baƙin slippers, ta wuce ta fita, ba tare da ta gan su Mama da har yanzu suna zaune ba.
“Wannan kuma ina zata?” Kubra ta tambaya.
“Yawon ta zubar mana.” Mama ta ce tana ciro nama daga hakoranta.
---
Zahra ta fita ta ga Jameel a mota. Ta leƙo daga window
“Shigo ciki mana malam.”
“Nagode Hajiya.”
Ta umarci maigadi ya buɗe masa ƙofa. Yana parking ya fito, ya ce
“Gaskiya wankan nan ta yi gimbiyar mata.”
Zahra ta yi masa fari da ido. Suka wuce zuwa visitors' side na gidan.
“Bismillah. Welcome to my house.”
“Thanks dear.”
“What should I offer you?”
“Nothing, seeing you is enough.”
"You’re not serious,” ta ce tana dariya. Ta fita ta nufi main flat.
---
A ɗakin Mommy, ta sameta tana shafa humra a jikinta. Zahra ta ce
“Mommy, Jameel ya iso.”
“Ok, ga small chops nan a take away, ki sa a plate, da ɗan fruit ki kai masa.”
“Thank you, Mom.”
Zahra ta sauka ta haɗa small chops da fruit, sai ta ɗora drinks a tray. Tana wucewa parlour sai ta gaishe da su Mama da sai yanzu ta gan su. Amma sai suka watsar da ita,ba wanda ya amsa.
Ta kai tray ɗin shashin baƙi. Ta ajiye a gabansa
“Ga wannan, ba yawa. Ka ɗan taɓa.”
“Oh my God, you shouldn’t have bothered. I already ate.”
“sai fa ka ci wallahi,” ta ce da kwarjini.
“Toh, na ji Madam.”
Bayan ya ci kaɗan, ya ce
“Thanks for the food.”
“My pleasure.”
“So how have you been?”
“Alhamdulillah. You?”
“Fine too. But you’ve been punishing me with no time.”
“Exams ne suka cika min kai. But once I’m done, you’ll have my full attention.”
“Allah ya sa a gama lafiya. Da zarar kin gama, zan zo neman aure. I can't wait ki zama Mrs. Jameel.”
Zahra ta rufe fuskarta da gyale. Ya ce
“Kunya kuma? Hmmm kina da aiki ashe.”
Suka ɗan tattauna kafin suka nufi main flat domin ya gaishe da Mommy.
---
A parlour ya zauna, Zahra ta haura sama don kiran Mommy. A lokacin su Mama suna gefe amma ta watsar da su. Jameel ya ɗaga kai ya gansu
“Ina wuni.”
Mama ta kalle shi cikin ido, ta kau da kai.
Zahra na shiga ɗakin ta tarar da Mommy ta na latsa wayarta, sai ta ce
"Mommy ga Jameel ya shigo ya gaishe ki"
“Ok, je ki, gani nan zuwa kar ki bar sa shi kaɗai.”
Mommy ta sauko cikin hijabi. Suka gaisa da Jameel, cikin ladabi da kulawa. Sannan ta ce
“Barin koma sama ina wani aiki.”
Ta tafi ta bar Jameel da Zahra. Bayan ƴan mintoci kaɗan, Jameel ya ce
“Gimbiya na, I should be going. Na ji daɗin ganinki.”
“Nima na ji daɗin zuwan ka. Allah ya saka da alheri.”
Yayin da za su fita, suka ji dariya a bayansu. Juyowa suka yi, sai suka ga Mama da Kubra suna dariya har da tafi.
Mama ta ce
“Bawan Allah, idan aure kake so to fa ka je ka nema mata ta gari, domin wannan ba ta shirya aure ba,bata gama yawon banza ko ba. Yau da wannan ne, gobe wani, haka rayuwar ta ya lalace ya kai."
Zahra ta tsaya shiru, zuciyarta na bugawa. Jameel ya ce
“Na san komai. Kuma da hakan na ke sonta."
Ya juyo zuwa ga Zahra da ta tsaya kamar statue saboda tsabar mamaki da takaici.
"My love, sai anjima. Ki huta lafiya.”
Zahra ta ruga sama cikin kuka, zuciyarta kamar zai fashe.