Free chapter · Read without an account

Page 14

by Shamseeya Rabi'u Garba · AKASIN TSAMMANI (Beyond All Odds)

Ruwan sama ke saukowa kamar da bakin kwarya. Aɗaidaita (keke-napep) ya yi parking a ƙofar gidan Alhaji Bashir. Wata tsohuwa ta sauko daga adaidaitan tana jan numfashi, tana gyara ɗaura zaninta da ya kusa faɗowa, tana faɗin

"Kai yaro, bari in shiga ciki sai in sa a kawo maka kuɗinka. Yanzu dai zo ka cire min akwati na."

Ta gyara ratayar jakarta a kafaɗa.

"Mama, ki shiga daga ciki mana, kin ga ruwa ake yi sosai. Idan an kawo kuɗin sai a shigo miki da akwatin," in ji direban adaidaitan.

"A'a wallahi! Ba zan bar maka kayana in shiga ciki ba, salon ka gudu min da kaya in shiga uku!"

"Toh shikenan Mama, bari in ciro miki kayanki tunda ba ki yarda da ni ba."

Direban ya sauka kenan zai ciro mata akwatin kamar yadda ta buƙata, sai suka ji horn a bayansu.

"Yauwa! Kamar ga mutanen gidan. Bari su ba ni kuɗin in ba ka," cewar Iya tana nufo motar da ta tsaya tana jiran adaidaitan ya matsa gefe.

A cikin motar akwai Raflah (a mazaunin driver) da Raudat a gefenta, sai yaran su a baya.

"Ya Raflah, kamar Iya ce fa," in ji Raudat.

"Ita ɗin ce ma. Amma me yasa take tsaye a ruwa comfortably?"

"Gata, ta nufo mu."

Raflah ta sauke gilashin motar. Ta ce, "Iya, shigo ciki! Ruwan nan da ƙarfi fa."

"Kar ki damu, 'yar nan. Dubu biyu za ki ba ni in kai wa mai adaidaita."

Raudat ta ce, "Shigo kawai, Iya. Ni zan kai masa."

Ƙofar baya aka buɗe, Iya ta shige ciki, jikinta duk ya jiƙe. Raudat ta fito ta ɗauki umbrella a boot ɗin motar. Har za ta tafi, Iya ta ce, "Ya ba ki akwatina? Kar ya gudu da shi!"

Raudat ta yi murmushi. "Toh."

Bayan ta biya mai adaidaita, sai ya ciro mata akwatin ya ajiye, ya ja adaidaitarsa ya tafi. Raudat ta dawo da jakar ta sa a boot kafin ta zagayo ta shiga ta zauna. Raflah ta danna horn.

Maigadi ya fito da ɗan lemar sa ya leƙa ya gani ko waye. Da sauri ya koma ciki ya buɗe musu gate.

Bayan ta yi parking ta ce "Ku tsaya daga ciki; bari na je na samo more umbrella,"

Musharraf, da ke zaune a corridor na apartment ɗinsu, ya ga lokacin da motar ta shigo. Ya ga Raflah ta fito da umbrella ta doshi ƙofar main flat.

"Ya Raflah, welcome!" ya ɗan ɗaga murya ya faɗa.

"Bro, ya ne?"

"Fine, dear."

"Don Allah, do you have an umbrella there?"

"Eh, akwai."

"Please use it to pick up Iya from the car."

"Ok."

Ya shiga ciki ya ɗauko umbrella ya kai wa Iya.

Raflah kuwa, da ta shiga ciki, babu kowa a falon; sai motsi da take ji daga kitchen. Kitchen ɗin ta nufa. Mama Ladi ce tana ƴan aikace-aikace.

"Sannu da aiki, Mama Ladi."

"Ahh, barka da mutanen Abuja! Marhaba, sannu da zuwa. Yaushe a gari?"

"Yanzu muka iso, Mama. Don Allah, ina su ke ajiye umbrellas?"

"Duba ƙarƙashin staircase za ki gani."

"Ok, thank you. Ina zuwa, za mu gaisa properly, amma yanzu bari na kai wa su Raudat umbrella."

"Ba damuwa, sai kin zo."

Umbrella biyu ta ɗauko ta kai musu a mota. Ita da Raudat suka yi pairing; yaran ma aka haɗa su biyu-biyu. A hakan suka shige ciki.

Iya har ruwa ke ɗiga daga jikinta; a haka Musharraf ya taimake ta ya rako ta har ɗakinta, gudun kar ta faɗi saboda santsi na tiles.

Su Raudat ma a ɗakin Iya suka sauka, because rooms ɗinsu sun ya yi ƙura sosai,ba su sanar da zuwan su ba balle a share. Za su zauna a ɗakin Iya kafin a gyara na su.

---

Musharraf ya rufe windows ɗin ɗakin, ya sauke blinds, ya juyo ga Raudat.

"Ya Rauda, I think ya kamata ki haɗa wa Iya ruwan zafi sosai ta yi wanka, kar sanyi ya kamata."

Raflah ta goyi baya. "Eh, hakan ya kamata sosai.

Saboda ruwan saman da ya rutsa gari tun da sassafe, yawancin mutanen gidan ba su sauko ƙasa ba tukuna.

Iya dai ba ta ce komai ba; sai fitar da kayan ta take yi daga cikin akwatin—duk sun jiƙe. Musharraf ya ɗan yi wasa da yaran yayyunsa kafin ya tafi sashensu riƙe da mai sunan Daddy.

Misalin ƙarfe goma na safe (10:00am) ruwan ya ragu zuwa ɗan yayyafi. Mommy ta sauko ƙasa don haɗa wa Zahra breakfast, sai ta tarar da yara na wasa a parlour. Da fara'a ta ƙaraso tana faɗin

"Su waye wannan kamar jikoki na?"

Da gudu yaran suka yo kanta suka rungume ta cike da murna. Ƙaramar cikin su ta ce, "Grandma, where's Aunty Zahra?"

Mommy ta ja kumatunta. "Is it only Aunty Zahra that you missed?"

"No, but she's the one I missed more."

"Toh, yayi kyau haka. Ina Mommy ku?"

"Tana ɗakin Iya," suka amsa.

Mommy ta nufi ɗakin Iya da sallama.

"Ina kwana, Iya. Sannu da zuwa. Ya hanya?"

Iya, kwance cikin bargo, tana lulluɓe, tana lallaba jikinta da man zafi har warinsa ya cika ɗakin, ta taɓe baki

"Ai ba yanzun na zo ba da sai yanzu za ki zo wai kina min sannu da zuwa!"

Mommy ta yi murmushi, ta saba da irin rikicin Iya. "Ki yi haƙuri. Ban san kin iso bane; da tun farko na zo miki sannu da hanya."

"Ina za ki sani? Tunda duk kuna kwance kamar gari bai waye ba. Ana ruwan sama ba za ki fito ku ɗan yi aikin gida ba, sai ku kwanta! Ki cigaba da biye wa Sahura kina shirme. Ita Sahura da na yi ta mata magana ta rinƙa motsa jiki ta ƙi; Baga ta yanzu—hiim! Kamar an hura mata iska. Ke ma, idan baki kiyaye ba, hakan za ki zama wallahi."

"Zan kiyaye, In Sha Allah. Ya kika baro mutanen gida?"

"Lafiya ƙalau wallahi. Sai kukan munafurci suke yi wai za su yi kewata, bayan a kunne na na ji Ladingo na faɗa wa Sallame cewa tana Allah-Allah na tafi ko za su huta da sababi. Ni dai ban ce musu ƙala ba; na bar su da halinsu."

"Allah ya kyauta."

"Aameen. Ya jikin Zahran?"

"Da sauƙi. Tana bacci."

"Yanzu ke Amina da ba don na kira Bashir mu yi gaisuwar Jumma'a ba—shine ya ce min ga abin da ya faru. Da haka za ki laɓe ki yi shiru ki ƙi faɗa wa kowa? Ba ki san ko sannu aka ce mata zai sa ta ji sanyi a ranta ba? To ga ni, na kira dangi na, na sanar da su; kowa sai fatan Allah ya ba ta lafiya yake yi. Ga 'yan uwanta nan,vda daddare na faɗa musu, amma ga shi sun zo. Ai haka ake yi; ba wai ki ja baki ki yi shiru ba! Kai, Allah ya wadaran wannan zurfin ciki naki, Amina!"

Raflah ta katse masifar Iya da gaisuwa 'Ina kwana Mommy? Da fatan mun same ku lafiya? Ya mai jiki?"

"Lafiya ƙalau, Alhamdulillah. Jiki kuma da sauƙi. Ya kuka baro gida?" Mommy ta amsa.

"Lafiya ƙalau wallahi," in ji Raflah.

Raudat ma ta gaishe ta. Mommy ta ce, "Ga shi ban san za ku zo ba, ba a gyara masaukin ku ba."

"Babu komai wallahi. Za mu zauna a nan kafin a gyara," cewar Raudat.

Iya, da ta rufe ido kamar mai bacci, ta ce "Ni dai ku yi ku tattara kafin yaran ku su yi min kaca-kaca da wuri!"

Mommy ta yi murmushi ta tashi ta fita daga ɗakin.

Dining ta nufa; ta buɗe abincin da Mama Ladi ta jera; boiled yam da egg sauce, sai shayi da yaji kayan ƙamshi a flask. Mommy ta ɗauki plate ta zuba abinci sosai sannan ta tsiyaye ruwan shayi a cup; ta ɗora a kan tray tare da bottle water ɗaya, spoon da fork. Ɗakin Iya ta koma da abincin.

"Iya, ga breakfast na kawo miki," Mommy ta ce tana kallon Iya; idonta a rufe, amma da alamun ba bacci take yi ba.

Iya ta miƙe zaune. "Sannu da ƙoƙari."

Mommy ba ta ce komai ba; ta juya zuwa ga su Raflah. "Ga breakfast a kan dining; ku je ku ci."

"Ok, thank you," suka ce.

Mommy ta fita daga ɗakin ta tattaro yaran da ke wasa a parlour ta kai su dining, ta yi musu serving.

"Where's Akram? Ban gan shi ba," ta tambaya.

"Uncle Musharraf ya tafi da shi," in ji A'isha.

Yaran huɗu ne: A'isha da Akram (Muhammad Bashir)—yaran Raflah; sai Iman (Khadijah) da Ukti(Raflah)—yaran Raudat.

"Ok. Toh, ku ci abinci; anjima sai mu yi hira, ko?"

"Eh! Sai mu je garden mu yi wasa!" Ukti ta faɗa cikin annashuwa.

"Alright, eat for now," Mommy ta ce.

---

Mommy ta koma ɗakinta ta tarar har Zahra ta farka daga bacci.

"Mommy, ina kika tafi kika bar ni ni kaɗai?" Zahra ta shagwaɓe.

Mommy ta zauna kusa da ita; ta janyo ta jikinta, ta shafa kanta. "Good morning, my princess."

"Good morning, Mommy."

"Ya jikin ki?"

"Da sauƙi, kawai dai hannun ne. Ina jin shi kamar ba a jikina ba."

"Sorry, dear. Allah ya ƙara miki lafiya."

"Aameen. Mommy, where did you go to?"

"Na sauko ƙasa. Iya and your siblings are here."

"My siblings?"

"Eh, Raflah da Raudat."

Idon Zahra ya buɗe cikin farin ciki. "Taron me za a yi yau ɗin?"

"Babu wani taro. Iya ce ta kira su ta broadcast musu cewa ba ki da lafiya."

Zahra ta saki dariya. "Iya can do more than that."

"Na zo in kawo miki breakfast amma tunda 'yan uwanki suna nan, zai fi da kin karya tare da su. So, get up and have your shower; sai ki sauko ƙasa ki same su. Ko dai na miki wankan ne?"

"A'a, zan iya. Kawai ki haɗa min ruwan, sai ki taimake ni in cire kaya."

---

Bayan wanka, Mommy ta taimaka mata da shiri cikin wani three-quarter gown ja da ratsin baƙi.

A ƙasa, su Raudat na zaune a dining suna cin abinci; Iya na zaune a centre rug na parlour, su A'isha na mata surutai. Zahra ta sauko a hankali daga stairs.

Ihun murna yaran suka yi suka ruga suka rungume ta suna faɗin: "Anty Zahra, oyoyo!"

Iya ta saki sallati "Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji'un! Raflah, kun haifi jarfa! Wai ba ku ganin hannunta ba lafiya ba? Ko sai kun fama hannun a bar min ɗa da kashe kuɗi!"

Zahra ta yi murmushi; ta shafa kansu da hannunta mai lafiya. "Welcome, my kids. I'm so happy to see you."

"We're happy to see you too, our favorite aunty!"

A'isha ta ce, "Me ya ma hannunki, Anty Zahra?"

"Faɗi wa na yi."

"Eyya, sorry. Da zafi?"

"A'a, ba sosai ba."

Iya ta taɓe baki. "Kai, wannan yarinyar Raflah akwai surutu wane Aku. Takwara, ƙaraso na gan ki!"

Zahra ta kama hannun Ukti suka ƙaraso cikin falon. Ta zauna kusa da Iya, tana faɗin, "Barka da zuwa, Iya. Ya hanya?"

"Lafiya ƙalau, Zahra. Ya jiki?"

"Da sauƙi."

"O'o ni, Fatu! Ciwon kwana ɗaya shine kika rame haka? Sai ido zuru-zuru kamar wacce ta shekara tana jinya! Anya Amina ta damu da ba ki abinci kuwa?"

"Iya, ya haɗu da stress na makaranta ne fa."

"Allah ya daɗa kiyayewa, amma gaskiya ban ji daɗin ganin ki haka ba. Ke da Bashir ya ce min an zo neman aurenki, kwanan nan za a kawo sadaki a sa rana, a haka za ki yi auren? A bushe! Sai ƙashin wuya da ido zuru-zuru?"

Zahra ba ta ce komai ba; ta miƙe ta nufi dining inda su Raflah ke zaune.

"Miskila kawai! Je ki da baƙin halinki," Iya ta faɗi a bayanta. Sarai Zahra ta ji, ta yi kamar ba ta ji ba.

Da ta iso dining, Raflah ta ce, "Zahran Mommy, ya jiki?"

"Da sauƙi, Anty. Ya hanya?"

"Alhamdulillah, Zahra."

Raudat ta sipping shayin hannunta ta ce, "Takwarar tsohuwa, ya jikin?"

Zahra ta ɗan kwaɓe fuska. "Ni ba zan amsa ki ba, Anty Rauda. Ai ba haka muka yi da ke ba."

"Ta saɓa miki alkawari ko?" Raflah ta tambaya.

"Eh fa! Tun yaushe ta ce za ta zo, amma ba ta zo ba sai yau, duk na yi missing ɗin su Imani."

Raflah ta yi dariya. "Ai idan Raudat ce akwai saɓa alkawari."

Raudat ta yi murmushi. "Shikenan. Tun da ba za ki amsa gaisuwata ba, sai in mayar da turaren da kika ce in taho miki da shi."

Zahra ta kama baki tana dariya. "Haba, wasa dai! Wallahi har Abuja sai na bi ki!"

Suka kwashe da dariya.

"Na zuba miki abincin?" Raflah ta tambaya.

"Eh amma kaɗan."

"Zahra, gaskiya ya kamata ki rinƙa cin abinci fa. Kin rame sosai."

"Ina ci fa, Anty. Matsalar gidan nan ne kawai ba zai bar ni na yi ƙiba ba."

"Hmmm, ki ce har yanzu gidan nan yana nan yadda na san shi?"

"Yana nan dai yadda kika san shi, babu abin da ya sauya; sai ma wanda ya ƙaru."

"Allah ya kyauta."

Zahra ta lumshe ido. "Anty Raflah, could you believe cewa su Habiba dukkansu Mama ta koya musu yadda za su raina ni? Ba sa ganin ni da wani ƙima na yayarsu. Ba su gaishe ni; kai, in fact, ba su ma magana da ni! And I dare not correct them if they're wrong, idan na yi, Mama ta fara balai; the whole neighborhood must hear. Like, gaba ɗaya sun raina ni."

Raflah da Raudat suka tsaya suna kallonta da mamaki.

Raudat ta ce, "Ba ki taɓa zane 'yan iska ba ne? Shi ya sa abin ya ci gaba. By the time kin yi dealing da ɗaya daga cikinsu, sauran zai zama musu example."

"Hmmm, Anty Rauda kenan. You won't understand, even if I explain from today till tomorrow. Idan na musu faɗa, sai ya haddasa matsala. Ina ga duka? So I just decide to respect myself: na fita harkar su. Idan abin na su ba wanda zai taɓa mutuncin gidan nan ba ne,to ba na ce musu komai."

Raflah ta ce, "When will Mama stop behaving like this?"

"Babu rana. Mama will never change. Recently ta yi min abu biyu da ya hurting ɗi na sosai."

Suka yi chorus "Me kenan?"

Zahra ta ja numfashi. "Da farko, Salim, my fiancé ya zo gidan nan gaishe da Mommy. Mama ta faɗa masa cewa ni yar iska ce; bin maza nake yi, yau a fannin da wannan, gobe da wani."

"What!" suka faɗa a tare.

Iya, da ta kwanta a carpet har bacci na ɗaukar ta, ta ɗago kai "Lafiya?"

"Eh, lafiya. Wani abu ne muke gani a waya," Raudat ta faɗa tana daga wayarta kamar tana duba wani abun.

Mama ta koma ta yi kwanciyar ta.

Raudat ta juya ga Zahra. "What did Daddy do about it?"

"Bai ma sani ba. Nobody told him. Amma Mommy ta ce za ta handle ɗinta in her own way."

Raflah ta girgiza kai. "Hmmm. Allah ya kyauta. But Mama is becoming devilish."

"Ai ba wai tana becoming ba—she's already devilish! Wannan mata..." Raudat ta ce cikin haushi. "Sai me kuma ta ƙara miki?"

Zahra ta gyara zama; ta tauna doya a bakinta, ta haɗiye, ta ɗan sha shayi kafin ta cigaba

"Yau da asuba bayan mun yi sallah, Mommy ta ce in kira friend dina Sofi in ba ta haƙuri. Wai jiya ta zo duba jikina amma unfortunately ba mu dawo daga asibiti ba; don haka Mama suka tarar a gidan. Babu wulaƙanci da bata musu ba; harda kiran su almajirai, ɓarayi; har searching bags ɗinsu! Har cewa ta yi za ta kira 'yan sanda su tafi da su!"

Zahra ta ce cikin baƙin ciki; muryarta ta karye, ta share ƙwalla.

Raflah ta dafa kafaɗarta. "Is okay, Zahra. Kar ki yi kuka, kuka is never a solution. Daman kwana uku muka ce za mu yi, amma yanzu za mu ƙara. Mu yi kamar one week tunda yaran nan na hutu, mu keeping dinki company, ko za ki samu natsuwa. Right, Raudat?"

"Eh, hakan ma ya yi. In fact, idan mun tashi tafiya, da ita za mu tafi. She should leave this environment for now, ta yi healing tukuna,"

Zahra ta share hawaye. "Anty Raflah, is it a crime not to marry early? Na yarda wannan ƙaddarata ce—amma me ya sa mutane ba sa yi min uzuri? Me ya sa suka ƙi gane cewa ba yin na ba ne, ƙaddara ta ce?"

Raflah ta rungume ta. "Zahra, stop crying. Kin ga wannan baƙin halin na Mama ba wai saboda baki yi aure ba. A'a, she's just evil ne mu ma haka ta rinƙa yi mana, she don't want anybody to be happy aside yaran ta. Kar ki bari maganganun ta su karya ki."

"Anty, ba Mama kawai ba, even friends dina da suka yi aure suna canza min. A angwan nan, yarinyar da muke tafiya Islamiyya tare, mamarta ta hana ta tafiya da ni wai kar in buɗe mata ido itama ta ƙi yin aure irina. A department ɗin mu ma, gulma ake yi wai bin maza nake yi shi yasa na ƙi aure. The only person I have by my side in school is Sofi, and I know, from the moment ta yi aure, itama canza min za ta yi."

"Zahra, don't mind what people say. Live your life how you want. Ki sa tsoron Allah a dukkan lamurranki; sai ki zuba ido ki ga ikon Sa. Kar ki damu da abin da mutane ke faɗi. Na san maganganunsu yana miki zafi—but you have to be strong, kin ji?" Raflah ta rarrashe ta.

Zahra ta gyaɗa kai a hankali.

Mommy, da ta daɗe a tsaye tana sauraren su daga baya, ta ce "Thank God your siblings are here. Ƙilla idan su ne suka faɗa miki, za ki ji." Ta ɗauki cup ta wuce abinta.

---

Daddy ya sauko don yin breakfast; ya tarar da Iya kwance a parlour tana bacci, yaran su Raflah kuma sun kunna TV suna kallon cartoon.

"Su wane nake gani kamar 'yan mata na?" ya faɗa da dariya.

"Grandpa!" suka yi ihu suka taru a kansa.

Iya ta firgita ta tashi. "Lafiya?"

Daddy ya ɗauke su daga jikinsa ya ƙaraso wajen Iya. "Lafiya, Iya. Ihun yaran nan ne ya firgita ki."

"Kai, amma yaran nan an yi fitinannu. Idan suka ƙara kwana ɗaya a gidan nan ai sai jinin mutum ya haura! Billahillazi!"

"Sannu, Iya. Ya hanya?" Daddy ya tambaya.

"Lafiya ƙalau, Alhamdulillah. Kai kuma, sai yanzu ka tashi daga bacci? Ka ma yi sallar asuba? Kai! Ina ganin duniyanci a gidan nan!"

"Wallahi na raba dare ina wani aiki ne; shi yasa ban fito da wuri ba."

"Amma dai ka yi sallar asuba?"

"Eh, na yi."

"Toh shikenan. Allah ya dafa."

"Aameen."

"Sahura itama raba dare ta yi tana aiki ko dai ban isa ta zo ta yi min sannu da zuwa ba ne?"

"Ba ta sauko ba?"

"Ina na kai matsayin da za ta sauko ta gaishe ni? Da dai uwata Hanne mai ƙosai ne, da ta zo ta gaishe ta!"

"Bari na kirawo ta," Daddy ya miƙe zai koma sama.

Iya ta tsaida shi. "A'a, yi zaman ka. Ni zan haura saman da kaina; na ji me take nufi, daga ita har 'ya'yanta!"

Iya ta miƙe ta nufi stairs tana grumbling. Daddy ya je dining ya zauna tare da su Zahra; jikokinsa na biye da shi. Sun gaisa, ya tambayi Zahra lafiyarta, suka ci gaba da hirar rayuwa. A haka Musharraf da Abdul Hakim suka zo suka same su; hirar ta ƙara daɗi.

Iya na isa bakin ƙofar ɗakin Mama ta tsaya. Ta jiyo muryar Mama a waya tana faɗi da haushi:

''Turai, wallahi na rasa yadda zan yi, ga wannan fitinaniyar tsohuwa ta zo gida..."

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol