Free chapter · Read without an account

Page 29

by Shamseeya Rabi'u Garba · AKASIN TSAMMANI (Beyond All Odds)

Matar Kassim ta rinƙa matsa masa akai-akai akan lallai ya dawo gida. Tace jikin ɗansa ya ki, kuma yaron yana buƙatar kulawarsa, don haka ya kamata yazo a san abin yi. Sau da dama take kiran sa, ba ta bashi breathing space kwata-kwata.

Wannan ne yasa, cikin gajiya da yawan matsin lamba, Kassim ya ɗauki waya ya kira Alhaji Bashir. Ya sanar da shi cewa gobe zai koma Legas. Hutun da ya ɗauka a wajen aiki ya ƙare, kuma tuni ana kiransa daga ofis.

“Ina ganin idan lokacin da kuka ga ya dace Zahra ta tare, sai ka tuntuɓe ni ta waya,” Kassim ya ce cikin ladabi.

Amma Alhaji Bashir ya girgiza kansa yace;

“Sam, baza mu yi hakan ba. Idan ka shirya goben, sai ka zo ka tafi da matarka gaba ɗaya.”

Da Alhaji Bashir ya kawo wannan magana wajen Iya, sai ta tsaya cak tana binsa da kallon mamaki.

“Bashir, ashe haka rashin hankalin naka ya kai? Za ka dauki ‘yarka ka haɗa ta da wani ƙato, su tafi har wata uwa duniya babu abokin rakiya? Yanzu da kace goben zasu tafi, ka san anguwar ne? Ko ka san gidan ne? Ta yaya baka san komai game da inda zasu zauna ba za a sa musu idon da kuka ce?”

Alhaji Bashir ya yi murmushi mai dan zafi.

“Iya, sanin anguwar ko gidan ba zai zama matsala ba, tunda zamani muke, akwai waya. Bayan sun tafi, cikin sati daya, sai a tafi a duba su.”

Iya ta riƙe haɓa cikin rashin yarda.

“Lallai yaro, yaro ne. To, bari kaji; babu uban da ya isa ya tafi da Zahra wani gari ba tare da ni ba.”

“Da ke kuma, Iya?” ya tambaya.

“Eh, ni fa. Yanzu haka zan fara haɗa kaya. Kuma zan faɗawa Salima itama ta shirya. Gobe idan yazo, sai muyi musu rakiya. Ba zai yiwu mu bar yarinya ta tafi gidan miji babu abokin rakiya ba. Sai kace wacce ta rasa gata, salon a yi mata gori nan gaba.”

Alhaji Bashir ya yi yunƙurin yin magana;

“Da dai kin bari daga baya sai ku tafi ganin…”

“Dakata, Bashir!” ta katse shi da murya mai cike da iko. “Ni na haife ka, ba kai ka haife ni ba. Don haka dole umarni na zaka bi. Ba ni zan bi taka ba. Ka fahimce ni?”

Ya gyaɗa kai cikin miƙa wuya.

“Allah ya kaimu goben.”

“Ameen,” Iya ta amsa, tana miƙewa. “Bari naje na fadawa Salima ta fara shiri tun yanzu.”

---

A hankali take takawa, tana mita akan yadda hawa stairs yake bata wahala, har ta isa ɗakin Mommy. Ta same su zaune, Anty Salima na ƙoƙarin kwantar wa Mommy da hankali.

Tun lokacin da Daddy ya sanar da Mommy cewa gobe Zahra zata bi mijinta zuwa garin da yake aiki, hankalin Mommy ya tashi. Duk abin da take yi, ba ta jin daɗin sa.

Iya ta shigo ta zauna a kan soft centre rug ɗin dake tsakiyar ɗakin, tana maida numfashi kamar wadda tayi dogon tafiya. Sun gaisheta cikin girmamawa, suna bin ta da kallo, don sun san Iya bata hawowa sama sai da dalili mai girma.

Mommy ta kalle ta da mamaki.

“Iya, da kanki kika hauro? Ai da kin aiko, a kira ni na sauko.”

“A’a, Amina. Tunda kika ga na hauro, kinsan magana mai muhimmanci ya kawo ni,” Iya ta ce tana gyara zamanta.

Ta yi shiru na ɗan lokaci, sannan ta cigaba!

“Na lura mijinki hankali bai gama isar sa ba. Ke kuma wannan shiru-shirun naki wallahi cutar ki zai yi. A wannan zamani, kina yi kamar baki waye ba. Haba, Amina, ta yaya za ki zauna ki naɗe hannunki, a kai miki ‘ya gidan miji ba tare da rakiyar ‘yan uwa ba, kuma ki yarda da hakan?”

Mommy ta sauke idanu kasa.

“Iya, bai nemi shawara ta ba. Hukunci kawai ya yanka. Ni kuma ban da damar ja da hukuncinsa.”

“To, ni ban yarda da wannan sokoncin ba,” Iya ta ce tana karkar da kai. “Idan ku yara ne, ni ba zan biku mu yi yaranta ba yauwa. Ke, Salima, ki shirya da 'yarki, Fariha ce sunanta ko? Ku shirya gobe idan mijin Zahran yazo, zamu yi musu rakiya har kudun. A san tana da gatan ta, kuma mu gan wurin zamanta saboda gaba.”

Mommy ta ji wani sanyi ya ratsa zuciyarta, amma ba ta ce komai ba.

Anty Salima ce ta yi murmushi ta ce;

“In Sha Allahu, yanzu kuwa zan shirya. Hakan ma zai fi kyau, muma hankalinmu zai kwanta.”

“Yauwa, Salima,” Iya ta ce da kwarin gwiwa. “Shi yasa nake cewa kina da hankali. Ai ba zai yiwu mu bar yarinya ta bi miji a gantale babu kowa nata ba. Sai kace daga bishiya ta faɗo.”

“Gaskiya kam,” Anty Salima ta amsa.

“Na rasa irin rashin tunanin Bashir da Amina,” Iya ta ƙara faɗi. “Yanzu ki tashi ki je ki faɗawa Fariha ta fara shiri. Killa gobe da sassafe zamu tafi. Ki faɗa mata ta shirya fa, kar ki ce kin manta.”

Bayan fitan Iya, Anty Salima ta kalli Mommy;

“To, yanzu sai ki kwantar da hankalinki, tunda gashi zamu bisu gobe.”

---

A dakin Zahra, Anty Salima ta iske su Farhana suna tsifa.

“Me yasa kuke tsefe kitson?” ta tambaya, tana kallon su.

Farhana ta amsa;

“Wai kanta ciwo yake mata. Na taya ta tsefewa, killa ya daina.”

“Ok. Allah ya sauwake,” Anty Salima ta ce, tana zama gefen Farhana akan gado. Zahra kuwa tana zaune akan pillow a ƙasa.

Ta fara taya Farhana yin tsifan, suna yin tsifan suna hira. A cikin hirar ta kawo maganar tafiya, ta yi wa Zahra nasiha da kalaman kwantar da hankali.

Sai karfe sha biyu na dare suka kammala tsifan, sannan suka shirya duk abubuwan da za su buƙata. Anty Salima ta tabbatar komai ya kammala kafin ta tashi, ta koma ɗakin Mommy don shiryawa itama.

---

Washegari da sassafe, misalin ƙarfe shida, Kassim ya iso gidan Alhaji Bashir da ƙaramin jakar kayansa.

Alhaji Bashir da kansa ya raka su zuwa tasha tare da Musharraf, bayan ya kai su har gidan su Kassim ɗin sun gaishe da Inna Wuro. Ya yi magana da direban motar da zai kaisu, ya biya shi, sannan ya musu fatan Allah ya kai su lafiya.

Sai da Anty Salima ta ɓanɓare Zahra daga jikin Musharraf da karfi. Zahra ta rungume shi tana kuka kamar ranta zai fita, shi ma idanuwansa sun yi ja. Daurewa kawai yake, don yasan idan ya yi kuka a gabanta, hakan zai ƙara mata damuwa.

“Is ok, princess,” ya ce yana share mata hawaye. “In Sha Allah, cikin sati ɗaya zan zo na duba ki. Zan zauna kwana biyu, kafin nazo kuma kullum zan rinka kiran ki safe, rana da yamma, don na ji muryarki.”

Zahra ta fashe da sabon kuka.

“I’m going to miss you, Yaya. I’m going to miss home.”

“We will miss you too, princess. Abinda muke so kawai shi ne ki kula da kanki. Idan mijinki ya kuskura ya ɓata miki rai, just give me a call and I will come down to Ibadan and deal with him.”

Babu irin lallabar da bai yi mata ba, amma taƙi sakin shi. Sai da Anty Salima ta shigo ta kwace ta da ƙarfi, ganin tana bata musu lokaci.

Irin kukan nan ta yi ɗazu lokacin da zata rabu da Mommy da sauran ‘yan uwanta. Har tasa Khalil kuka ma.

Cikin mota suka shigar da ita, suka rufe kofar, tana hawaye. Musharraf kuwa, da zarar suka tafi, ya koma cikin motarsa ya kife kansa akan steering. Wasu hawaye masu zafi suka gangaro masa ba tare da ya iya dakatar da su ba.

Da zarar suka fice daga cikin garin Kaduna, Zahra ta ɓingire da bacci. Tafiyar tayi tsawo; suna ta wuce kauyuka da birane, sau da dama idon Farhana na duba ta, tana tabbatar tana numfashi cikin natsuwa. Sai da suka isa Lokoja kafin direba ya tsaya a wani babban supermarket, suka dan siya snacks, suka kuma ci gaba da hanya. Abin da yake tsayar da su kawai shi ne sallah.

Ba su isa Lagos ba sai misalin ƙarfe tara na dare. Zahra ta yi bacci ta farka fiye da sau hudu a hanya, kukan zuciya gajiya na kai-komo. Suna shigowa garin, Kassim ya fara yi wa direban kwatance, har zuwa unguwar da Hajiya Turai ta sa aka kama musu haya.

Direban ya yi parking a bakin gate na gidan yana faɗin, “Alhamdulillah.” Iya, wadda ta ki runtsawa ko minti daya, wai don kada ta manta hanyoyi idan za ta dawo, ita ce ta fara sauka. Ta yi hammar gajiya tana miƙa ƙafafunta; “Tunda uwata ta kawo ni duniya, ban taɓa zuwa gari mai wannan shegen nisa ba.”

Farhana ta tabo Zahra, wadda ta yi matashi da cinyarta tana barci. Zahra ta buɗe idonta a hankali, ta bi wajen da kallo.

“Mun iso,” Farhana ta ce a tausashe. “Tashi mu shiga ciki.”

Kassim ya yi gaba ya duba wajen da Hajiya Turai ta ce landlord ya ajiye mabuɗin gidan, karkashin wani katon dutse a bakin gate ne. Ya miko hannu, ya ɗauko mabuɗin, ya bude gate. Sai ya matsa ya ba su hanya;

“Bisimillah, Kaka...ku shigo.”

Ya bude main door, suka shiga ciki. Gidan cike yake da ƙura, babu ko abin amfanin yau da kullum a ciki. Iya ta bi gidan da kallo, ta rike haba;

“Wane irin gida ne wannan? Duka-datti kamar wanda aka shekara goma babu mutum a ciki?”

Kassim ya sosa keya, ya yi ajiyar zuciya. “Erm… Kaka, daman a lokacin da nake Kaduna ne na Turi kuɗi aka kama min hayar, don ba daɗe da yi min transfer zuwa nan ɗin ba.”

“Yanzu fisabilillah, da kasan zamu iso yau, me ya hana ka sa a zo a shashare guri? Ta yaya zamu fara zama a irin wannan wajen?” Iya ta ce tana binsa da ido.

“Ki yi hakuri, Kaka. Ban san haka gidan ya yi datti ba. Yanzu nan zan tafi nemo cleaning service su zo su tsaftace gidan.”

“Yi maza ka nema,” Iya ta faɗa, tana bin gidan da kallo. “Zama bai kamata mu yi a cikin wannan kurar ba, ai neman cuta ce kai tsaye.”

Anty Salima ba ta ce komai ba. Ta fara kallon siffar gidan; matsakaici ne, kuma yana da daki-ukku da kitchen da bathroom, duk dai suna bukatar tsabtacewa. Ta fara zazzaga ɓangarori tana toshe hanci saboda kurar da ke tashi. Zahra kuwa, ta tsaya jikin Farhana daga wajen kofa, ta jingina jikinta, idanu a kumbure da gajiya.

Iya ta hango wani dakali, ta zauna, tana ta mita kan yadda gida ya yi datti. A kitchen ɗin, Anty Salima ta samu guntun tsintsiya. Ta fita ta ja kofar, ta zaga har bayan gidan, ta share wani dan fili. Ta dawo ta bude jakar kayanta, ta fito da wani zaninta, ta ce;

“Iya, mu je mu zauna can a waje kafin a zo a share gidan.”

Ta shimfiɗa zanin, kowa ya zauna a kai. Iya na yin hamma-hamma saboda gajiya.

Kassim yana fitowa daga gidan ya tsaya yana kallon hanyoyi, ya rasa wacce zai bi. Godiyarsa ɗaya; yana jin Yarbanci sosai, kuma ya saba da ghetto lifestyle ɗin Ibadan; bai rikice da dare a gari ba, don kusan irin lifestyle ɗin Lagos da Ibadan duk ɗaya ne. Ya ga wani saurayi, ya tsayar ya tambaye shi da Yarbanci inda zai samu cleaning service. Ganin yaren da ya yi masa ya sa saurayin ya yarda sosai, ya raƙa shi har inda zai samu masu sharan gida.

Suka zagaya wuri wuri, har wurare huɗu, kafin su samu waɗanda suka amince za su yi musu aiki a wannan dare. Kassim ya ba su adireshin gidan, shi kuma ya wuce kasuwa domin siyan wasu abubuwan gaggawa; tabarma mai laushi guda uku, tukwane, faranti, camp gas, da sauran kananan kayayyaki.

A waje, su Iya suna jiran dawowarsa, sai ga cleaning service ɗin da Kassim ya aiko suka iso. Su ka shiga aikin shara, goge tiles, share windows, fesa freshener, duk abin dai ya kamata. Cikin ƙasa da awa daya, gidan ya canza, ko’ina ya yi Walƙiya.

Sun nemi zama su jira Kassim ya dawo ya kammala biyan su. Sun jira kusan minti talatin, bai dawo ba. Anty Salima ta fito da kuɗi, ta biya musu cikon hakkinsu, ta gode musu.

Da misalin ƙarfe goma da rabi, sai ga Kassim da saurayin nan sun shigo, niƙi-niƙi da kayan da ya siya. A parlour ya same su a zaune a kasa, har Iya ma ta yi barci a shimfidar zanin. Ya sunkuyar da kai yana sosa keya;

“Anty, kuyi haƙuri. Ban san a irin wannan condition din zan same gidan ba. Da na yi wani shiri tun farko.”

Anty Salima ta yi masa murmushi mai taushin zuciya. “Babu damuwa. In Sha Allah, gobe za mu saka komai a tsari.”

Kassim ya mika musu takeaway na abincin da ya saya, sai tabarma mai laushi guda biyu. Ya shiga ɗaya daga cikin ɗakunan. Anty Salima ta tashe Iya a hankali, suka shige ɗayan ɗakin. Suka ci abinci, suka shimfiɗa tabarmar; Iya da Zahra a ɗaya, Anty Salima da Farhana a ɗaya.

---

Washegari da sassafe, duk da tarin gajiya, Anty Salima da Farhana suka fita neman kasuwa. Tun kafin su bar Kaduna, Daddy ya ba Anty Salima kudi masu yawa, ya ce ta sayawa Zahra kayan ɗaki idan sun isa, garin ya nisa; ba zai yiwu su kwaso kayan ɗaki tun daga Kaduna zuwa Lagos ba.

Siyayya suka yi ta yi; katifa, kujeru, karamar dinning, kayan kitchen, da duk wani abu da yar gata zata buƙata a gidan mijinta. Sai da suka tabbata komai ya cika sosai, sannan suka dawo. Iya, wadda sun fita ba ta sani ba saboda bacci, ta rinƙa shi musu albarka sosai da suka dawo da kayan.

Zahra kuwa, wani zazzabin gajiya ne ya rufe ta. Bakinta na daci tun jiya; ba ta iya cin komai. Anty Salima ta zauna kusa da ita, ta taba goshinta, ta ji zafin kadan.

“Na siyo kayan ciki da vegetables,” ta ce a tausashe. “Bari in dafa miki vegetable soup ki sha, sai ki hade magani.”

Zahra ta gyada kai kawai.

“Ki kalli duk abinda muka saya. Idan akwai wanda bai miki ba, sai mu canza. Idan kuma akwai wani abu da ba a siya ba, ki faɗa, gobe da safe mu je mu suyi, kafin mu tafi.”

Zahra ta kara gyada kai, kamar wacce bakinta ke jin ciwo idan ta yi magana. Anty Salima ta miƙe ta shige kitchen don girki.

Farhana ta matsa kusa, ta rike hannun Zahra. “Zahra, In Sha Allah, this marriage is your source of happiness. Ki kwantar da hankali, ki yi zaman aure.”

“In Sha Allah,” ta amsa a hankali.

“Good. Kin yi waya da Mommy da Yaya Musharraf?”

Zahra ta gyada kai.

“Ke, malama, magana za ki rinƙa min, ba sign language ba,” Farhana tafa tana yi mata hararar wasa.

“Tom, na ji.”

“Yauwa. Kin san alkawarin da kika yi min kin saɓa, ko? Amma mu bar maganar, sai wata rana.”

“Wane alkawari ne kuma?”

“You promised za ki fada min game da duk ex ɗinki, amma ba ki yi ba.”

“Ke kin fi kowa sanin bamu samu lokaci bane."

“Shiyasa nace, sai Allah ya kai mu wani lokaci,” Farhana ta ce, ta goge mata gumi a goshi.

---

Washe gari da safe, zazzabin ya ƙara rufe Zahra sosai. A wannan rana kuma, Anty Salima ta riga ta yi wa su uku booking na flight ɗin dawowa Kaduna, jirgi zai tashi karfe goma sha ɗaya na safe. Zahra na ta yin ɓarin sanyi, jikinta kuma na kayar wuta.

Farhana ta ba da shawara; “Mu fasa tafiya har sai ta ɗan samu sauki.”

Amma Anty Salima ta ki. “A bar mijinta ya yi jinyarta. It might even help su kusanto juna.”

Iya ma ta amince da shawarar Anty Salima. Haka suka tattara suka nufi filin jirgi, suka bar su Zahra da Kassim. Sun yi masa magana da nauyin rai; “Ka kaita asibiti, ka tabbatar ta samu magani.”

Zahra ta yi kukan tafiyarsu sosai. Ta roƙa a bar Farhana ta yi mata kwana biyu, amma Anty ta ƙi yarda. “Idan Farhana ta ci gaba da zama,Zahra da Kassim ba za su yi kusa sosai ba yadda muke so.” inji ta

Bayan sun tafi, gidan ya yi shiru. Kamar duk amo ya sha kwana ɗaya. Zahra ta jingina da jikin kujera, ta rufe ido, tana jin nauyin zuciyarta, amma tana ƙoƙarin zama jaruma kamar yadda take fada 'I want to be strong'. Kassim ya dawo daga kitchen da ruwan zafi a flask, ya aje a gefe, idonsa ya tsaya a kanta, yace; " tashi ki sha sha yi ki haɗe magani, muna da tafiya a gaban mu.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol