Free chapter · Read without an account
Page 38
by Shamseeya Rabi'u Garba · AKASIN TSAMMANI (Beyond All Odds)
Zahra ta shafe kwanaki uku kwance ba ta buɗe ido ba. Hankalin Imam ya fara tashi fiye da yadda zai iya ɓoye wa kowa. Ya kalleta na ɗan lokaci cikin damuwa, sannan ya juyo ga likitan da ke tsaye kusa da gadon.
“Zan iya ganin magungunan da aka yi mata amfani da su?”
Likitan ya ɗaga kai, ya buɗe wani ƙaramar kabad ɗin da ke gefen gadon, ya ɗebo kwalaben magungunan da ake haɗa mata a ruwan drip. Imam ya karɓi kwalaben ɗaya bayan ɗaya, yana dudduba su a hankali. Bayan ya gama, ya girgiza kai.
“Magungunan sun yi,” ya ce cikin muryar damuwa, “but why is it taking her so long to wake?”
Likitan ya sauke numfashi "Wallahi, Ni ma abin da ban gane ba kenan, Sir.”
“ina ga lokaci yayi da za mu canza mata magungunan,” Imam ya ce yana duban kwalaben da ke hannunsa. “Maybe wannan ba su karɓeta ba. I’ll get some new drugs da za a ba ta daga baya.”
“Okay, Sir,” likitan ya amsa.
Imam ya juya ya kalli Sa’ud da A’isha da ke zaune gefe suna kallonsa. “Can we go?” ya tambayi Sa’ud.
Sa’ud ya miƙe, ya leƙa Amal da ke kwance a cikin stroller, ya sumbaci goshinta. “Of course, mu tafi.”
Suka kusan kaiwa bakin ƙofa sai Imam ya tsaya ya waiwaya. “Sorry for inconveniencing you, A’isha,” ya ce cikin ladabi. “Na san zaman jinya ba daɗi ba.”
A’isha ta yi murmushi mai sanyi. “Wani irin inconveniencing kuma? Wallahi babu komai, Yaya.”
“Na gode. Allah ya saka da alkhairi,” ya ce yana ɗaga kai ya fita daga ɗakin. Sa’ud ya ɗaga mata hannu yana murmushi kafin ya bi bayansa.
---
Bayan kusan awa guda da fitarsu, A’isha ta tashi domin goge wa Zahra jiki kamar yadda take yi kullum. A hankali hasken Zahra ya fara dawowa a fuskarta. Ta zubo ruwa a kwano, ta zuba Dettol, ta saka bathing gloves a hannunta. Ta matsa shower gel a tafin hannunta, tana shafa wa Zahra jiki cikin kulawa har ta gama. Sannan ta ɗauko tawul, ta jiƙa shi a ruwan da aka sa wa Dettol, ta matse shi sannan ta goge mata jikinta tsaf.
A hankali ta kawo ɗaya daga cikin dogayen rigunan da ta fitar mata. Ta kira wata nurse domin ta taimaka musu, suka saka wa Zahra riga cikin kulawa.
Bayan sallar Isha, A’isha ta idar da sallah, tana zaune kan darduma tana ba Amal nono. Cikin nutsuwa sai ta ji Zahra na sauke ajiyar zuciya mai nauyi, numfashi ɗaya bayan ɗaya. Cikin firgici ta cire nonon daga bakin Amal, ta tashi da sauri ta karasa bakin gadon.
Zahra ta tarar tana riƙe da kanta, tana jujjuyawa cikin rauni. “Baiwar Allah, ya jikin naki?”
Zahra ta tsayar da kanta waje guda, cikin matuƙar ƙoƙari ta buɗe idanunta masu nauyi, kanta na barazanar tsagewa gida biyu. A hankali ta sauke idanunta akan A’isha da take murmushi cikin tausayawa. Ta so buɗe baki ta yi magana, amma sai ta ji kamar an ɗaure mata harshe.
A’isha ta ƙaraso kusa, ta riƙe hannunta cikin kulawa. “Ba sai kin yi magana ba yanzu,” ta ce cikin taushin murya. “A hankali za ki iya. Alhamdulillah, yau kin buɗe ido.”
A’isha ta ɗauki wayarta ta kira mijinta, ta sanar masa cewa Zahra ta farka.
A lokacin Sa’ud da Imam na fita daga masallaci. Imam ya ce, “Mu wuce mu siyo maganin da za a canza wa Zahra.”
Sai Sa’ud ya dubeshi, ya ce, “Bana ganin akwai buƙatar siyo maganin yanzu. My wife just called, yarinyar ta farka.”
Imam ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi, “Alhamdulillah,” ya furta a hankali. Shi kaɗai ya san irin tashin hankalin da ya shiga tun ranar da hatsarin nan ya faru. Babu wanda ya san ta a wurin hatsarin, ya rasa yadda zai fuskanci iyayenta idan ta mutu. Tambayar da ta fi damunsa ita ce: What if she never opened her eyes again? Would that make me the cause of someone’s death?
Sa’ud ya ɗora hannu a kafaɗarsa cikin kwantar da hankali. “Man, ka kwantar da hankalinka. Mu gode wa Allah. Tunda ta farka yanzu, sauran komai a bayan wannan ne. Yanzu mu tafi asibiti mu ganta.”
---
Suka tsaya a bakin wata mashaya ‘yar kasuwa, suka ɗan yi siyayyar ‘ya’yan itace da za su iya amfani da su wajen ciyar da marar lafiya. Daga nan suka nufi asibiti.
Suna isa ɗakin suka tarar da A’isha tana ƙoƙarin ciyar da Zahra, amma tunda Zahra ta buɗe idanunta, sai kuka take yi, ta ƙi magana.
Sa’ud ya ƙarasa kusa da matarsa, yana tambayar ta cikin damuwa. “What happened? Me yasa take kuka?”
A’isha ta girgiza kai. “Wallahi nima ban sani ba. Tunda ta buɗe idanunta ko magana bata yi ba, sai kuka kawai.”
“Kin kira likita?”
“A’a.”
“Ba za mu iya zuba mata ido tana kuka haka ba,” Sa’ud ya ce. “Let me get the doctor.”
Imam ya katse shi cikin nutsuwa. “No need. I’ll handle her.”
Ya yi ɗan tafiya a hankali zuwa bakin gadon. A’isha ta matsa gefe. Imam ya tsaya yana kallonta na ‘yan daƙiƙu. Idanunsa sun tsaya kan yadda eyelashes ɗinta suka jiƙe da hawaye, yadda idanunta suka kumbura, ga launin pink na lebenta da yake ɗan rawa yayi.
Ya kai hannunsa zuwa wuyanta, ya ji zafin jikinta daidai. Sannan ya gyara murya. “Stop crying,” ya faɗa kai tsaye.
Zahra ta yi kamar ba ta ji shi ba, ta cigaba da kuka. Imam ya yi shiru, ya ci gaba da kallonta. Har Sa’ud ya ce, “Yanzu haka za mu zauna mu zuba mata ido tana kuka?”
“Barta tayi kukanta,” Imam ya ce ba tare da ya kallesa ba. “Ba mu san damuwarta ba. Maybe tana buƙatar kukan.”
Suka kyale ta har ta yi kuka mai isarta, ta yi shiru da kanta ba tare da kowa ya matsa mata ba. Sai Imam ya zaro handkerchief daga aljihunsa, ya mika mata.
“Wipe your face. We need to talk,” ya ce a taƙaice.
Ta karɓa tana zumɓuraa baki. Haushi ya kamata saboda bai lallasheta ba, kuma ya hana kowa lallashe ta. Ta goge fuskarta tana ayyana a ranta: Lallai wannan mutum duk yadda aka yi, irin su Kassim ne.
Ta miƙa masa handkerchief ɗin, amma ya girgiza kai. “Hold it. Maybe za ki buƙace shi idan kika ƙara yin kuka.”
Sa’ud da A’isha suka yi murmushi, suna yaba irin rashin taushin Imam.
Zahra kuwa ta ajiye handkerchief ɗin a gefe, ta yi ƙoƙarin miƙewa. A’isha ta yi saurin taimaka mata, ta saka mata pillow a baya ta jingina.
A hankali ta buɗe baki, muryarta na fita da ƙyar kamar wacce ke koyon magana. “Ban san ku ba,” ta ce cikin raunana, “but please… ku taimake ni ku kira min brother na.”
Imam ya tsaya cak, yana kallonta kai tsaye cikin ido, muryarsa cike da izza da kwanciyar hankali.
“Iya abinda kike buƙata kenan?” ya tambaya cikin ladabi amma da ɗan nauyin murya.
Kai ta ɗaga a hankali, kamar wadda take yin shirin ɓoye gaskiya. Imam ya gyara tsayuwarsa, ya matsa ɗan kusa da ita, yana ci gaba da kallon fuskarta.
“Me sunanki?”
“Zahra,” ta furta da ƙasa-ƙasar murya, tana wasa da yatsunta kamar mai jin nauyi.
“Fatima?” ya sake tambaya, yana kallonta kai tsaye cikin ido.
Wannan kallo nasa ya yi mata nauyi, zuciyarta ta yi wani irin tsalle, sai ta sunkuyar da kai tana gyada shi a hankali.
“Zan kira miki brother ɗinki,” Imam ya ce cikin tsantsar natsuwa, “amma dai akwai sharudda.”
“Zan bi duk sharuddan idan har ba su kauce wa addini ba,” Zahra ta ce tana haɗe kalmarta da kuka mara sauti.
“Good,” Imam ya ce, muryarsa ta ƙara samun ƙarfin ikon jagoranci. “Na farko, sai kin daina wannan kuka marar amfani. Abu na gaba kuma, za ki shiga banɗaki ki yi wanka, saboda you look dirty. Ki wanke baki, ki fito ki ci abinci, sannan ki rama sallolin da kika rasa. Bayan nan ne sauran komai zai biyo baya.”
Zahra ta ci gaba da kuka ba tare da cewa komai ba. Imam ya yi gyaran murya, ya ƙara sauke kalamansa a hankali;
“Well… tunda sharudɗan ba su miki ba, sai ki jira ranar da aka sallame ki, sannan ki yi waya da brother ɗinki.”
“A’a!” ta faɗa da rawar murya. “Na yarda, wallahi! I will do just as you say.”
Imam ya kalleta, idanunsa na nazarin yanayin ta. Wannan rashin ƙwarin gwiwa da ta nuna ya ba shi mamaki, irin yadda take da ƙarfin son magana da ɗan uwanta har take yarda da komai.
Ya ɗauke kallon shi daga gare ta, ya mayar da shi kan su Sa’ud da ke gefe suna kallonsu kamar suna kallo a fim. Ya karɓi Amal daga hannun A’isha cikin nutsuwa, yana murmushi kaɗan;
“Sorry for bothering. Please, help her freshen up,” ya ce cikin salo na umarni mai taushi.
A’isha ba ta ce komai ba, ta wuce ta gefen Imam, ta ƙarasa wajen Zahra da ke zaune bakin gado. Da kulawa, ta kama hannunta tana taya ta tashi, sannan suka nufi toilet ɗin cikin natsuwa.
A cikin bandakin, A’isha ta taimaka mata sosai. Ta zuba ruwan zafi da ruwan sanyi a cikin bokiti, ta haɗa sabulu da tawul, sannan ta ce da ita cikin tausasawa;
“Ki cire kaya ki watsa ruwa a jikinki, Zahra. Zaki ji sauƙi sosai.”
Zahra ta yi shiru, hawaye na silalowa, amma ta amince. A’isha ta yi mata wanka da hannunta da kulawa kamar ‘yar’uwa, tana wanke kanta da jikinta a hankali, tana yi mata addu’a a ranta. Bayan sun gama, ta taimaka mata ta saka kaya masu tsafta, ta shafa mata mai a fuska da hannayenta, sannan ta saka mata dogon riga mai kyau.
Da suka fito, A’isha ta saita ta kan kujera mai taushi, ta ɗauko ƙaramar flask ɗin shayi. Ta zuba tea ɗin mai ɗan kauri a cikin kofi, ta ɗora shi a kan ƙaramar tray, ta zauna kusa da Zahra.
“Ki sha mana kaɗan, please. Ko ɗan ɗumi ne zai shiga jikinki,” ta ce tana saka ƙaramar murmushi.
Zahra ta girgiza kai da rauni, tana son ƙin sha. Amma A’isha ta dage da taushi, tana ce mata, “Please, Zahra, ki sha. Ki ƙarfafa ranki.”
A ƙarshe, Zahra ta ɗaga kofi tana taɓa bakin tea ɗin a hankali. Wannan ɗan ɗumin shayin ya zauna mata a ciki kamar wani ƙaramin ta’aziyya. A’isha ta gyara mata zama, ta saka mata hujja, ta fara rama sallolin da ba ta yi, tana ji a zuciyarta tausayin yarinyar da take zaune gabanta cikin rauni.
Sa'ud da Imam sun fita tun lokacin da ta shigar da Zahra banɗaki suka koma mota, suka zauna cikin nutsuwa, suna ba su lokaci su kammala shirinsu. Sa’ud ya kalli Imam da ke rungume da Amal yana wasa da ita cikin salo, fuskar shi a washe kamar ba shi ne ya gama bayar da tsauraran umarni ba mintuna kaɗan da suka gabata.
Ba tare da wani tunani ba, Sa’ud ya fashe da dariya.
Imam ya yi banza kamar bai ma ji shi ba, fuskar shi a tsuke. Daga ƙarshe, ganin dariyar ta dame shi, sai ya buɗe ƙofar mota yana shirin sauka.
“Hey, hey!” Sa’ud ya yi saurin riƙe hannunsa, yana dariya har yana danna ƙirji. “Kai fa matsalarka kenan, Imam, saurin fushi! Kana yin wani abu har ya sa mutum ya yi dariya, amma kai sai ka fusata.”
Imam ya ɗan ɗaga gira, muryarsa cike da bacin rai: “Oh… wato ni ke baka dariya kenan?”
“Of course!” Sa’ud ya ce yana dariya sosai. “Did you see how you reacted in there?” ya ƙara daɗa dariyar yana nuna kofar shiga asibitin.
Imam ya ƙara tsuke fuska. “What’s funny about my reaction?”
“Imam, for crying out loud,” Sa’ud ya ce yana buɗe hannuwansa. “That lady is a patient! Amma ka tsaya tsaye a kanta da tsauraran dokoki kamar wani alkali. Ba rarrashi, ba lallaɓa...Duk ka tsoratar da yarinyar mutane.”
“See,” Imam ya amsa cikin tsananin natsuwa, “I don’t have time da zan tsaya rarrashinta. Kuma na tabbata, da na tsaya ina lallashinta, da har yanzu ina nan ina fama.”
Sa’ud ya girgiza kai, ya yi dariya kaɗan. “You’ll never change, Imam.”
“Yes, I won’t,” Imam ya ce, yana sauka daga motar cikin hanzari. Ya maida ƙofar mota ya rufe da ƙarfin gaske, ya nufi gaba abinsa dauke da Amal a hannunsa, fuskar shi a ɗaure kamar ba shi da lokacin duniya.
Bayan one hour ɗaya suka koma ɗakin.
Zahra, sanye da bakin hijabin A’isha, tana kan daddumar Sallah, ta tsunduma cikin addu’a. Imam ya zuba mata ido, yana kallonta har ta gama raka’ar ƙarshe, sannan ya sauke kallonsa zuwa wurin Sa’ud da ke zaune kusa da matarsa, suna magana a hankali. Ya miƙa Amal ga A’isha, wacce ta karɓa cikin kulawa, ta tashi don ta basu wuri.
“Yi zaman ki,” Imam ya ce mata cikin natsuwa, yana isa bakin kujera mai roba da ke gaban gadon, ya zauna yana dannar wayarsa.
Zahra ta sallame raka’ar karshe, ta zauna tana shafa addu’o’inta. Ta nadar da kafafunta gefe ɗaya, ta jingina kanta cikin tafukan hannayenta saboda tsananin ciwon kai.
“Har yanzu ciwon kan bai sake ki ba?” A’isha ta tambaya cikin tausayi.
Kai kawai Zahra ta ɗaga, ba tare da ta iya magana ba.
Sai a wannan lokacin Imam ya lura da ita, ya ɗaga kai ya kalli A’isha. “Ta ci abinci ne?”
“Eh, shayi kawai ta sha,” A’isha ta amsa.
“Babu abinci ne?”
“Akwai fa, wai ita ta ce ta ƙoshi.”
“Please, ki ɗebo mata abinci,” Imam ya ce a hankali amma cikin umarni.
Zahra ba ta ko ɗago kanta ta dubi Imam ba; ita kaɗai ta san irin zafin da jikinta ke yi da kuma nauyin zuciyarta.
A’isha ta ɗebo shinkafa da miyar kayan lambu kaɗan, ta kawo mata a faranti. Ta durƙusa a gabanta, tana mika mata tare da lallashi. “Ki daure ki ci, Zahra.”
Zahra ta karɓa ta ajiye a gabanta. Amma sai hawaye suka cika idonta. Wannan rayuwar da take ciki tamkar sabuwar duniya ce a gare ta—ba lallashi, ba tambayar me take so. A maimakon haka, umarni kawai ake yi mata, sai kace ba ta da gata.
“Stop wasting my time and eat that food,” Imam ya ce cikin muryar nutsuwa amma da ɗan ɗanɗano na umarni.
Zahra ta fashe da sabon kuka.
“Then you are not ready to speak to your brother,” Imam ya ce a sake.
Cikin hanzari ta ja farantin abincin, ta fara cin abinci a hankali. Da ƙyar ta iya cin rabin sa, ta ɗago kai, idonta cike da roƙo.
“Wallahi na koshi,” ta ce cikin rauni. “Idan na ƙara, amai zan yi.”
Hannunsa ya miƙa, ta ajiye masa farantin, shi kuma ya ɗora a kan drawer ɗin gefen gadon. Imam ya ɗan ja numfashi yana ci gaba da danna wayarsa, yayin da Sa’ud da A’isha ke zaune suna kallonsa cikin shiru.
Da ya gamsu da zuciyarsa, sai ya mika mata wayarsa. “Saka min lambar yayanki.”
Zahra ta karɓi wayar, hannunta na rawa. Ta rubuta lambar Musharraf, ta miƙa masa tana roƙon Allah a zuciyarta da ya ɗaga kiran.
---
A wani ɓangare kuwa, Musharraf na zaune a falo tare da Zainab, suna kallon labaran talabijin. Zainab ta kwanta bisa cinyarsa tana wasa da waya, shi kuma yana kallon TV cikin nutsuwa. Sai ga kira daga sabon lamba ya shigo masa.
“Allah ya sa Zahra ce,” ya furta a hankali, tun da duk lokacin da ya ga sabon kira, hakan ke masa tunanin ita ce. Ya karɓi wayar.
“Take,” muryar wani namiji ta amsa a ɗayan ɓangaren, sannan aka mika mata wayar.
“Hello, Yaya…” muryar Zahra ta fito daga kunne.
“Zahra! Where are you, please?” Musharraf ya tambaya cikin tsananin damuwa. Zainab ta miƙe da sauri jin sunan Zahra.
Zahra ta fashe da kuka mai ƙarfi. “Yaya, wallahi mutuwa zan yi. Zuciyata ciwo take mini… maybe babu farin ciki a cikin littafin ƙaddarata. I’m so tired of this world.”
“Shhh… is okay, princess. Tell me, ina kike? I’ll come pick you up tonight,” Musharraf ya ce cikin damuwa.
“I had an accident… a hanyar escaping daga gidan Kassim. Ina asibiti yanzu… amma ban san inda ma nake ba. I was unconscious when they brought me here.”
Musharraf ya ɗan gyara zama. “Wa ya kai ki asibitin?”
“Nima ban san shi ba,” ta ce cikin kuka.
“Okay, bashi wayar, zan yi magana da shi.”
“Yaya… he’s grumpy fa,” ta furta a hankali.
Sa'ud da A’isha suka yi dariya da jin maganarta, wanda yasa ta gane sun ji abin da ta faɗa. Da kunya ta miƙa masa wayar, tana share idonta da bayan hannu.
Imam ya ɗauki wayar, ya sa a kunne. “Assalamu alaikum.”
“Wa’alaikumussalam. Barka da warhaka. I’m Zahra’s elder brother,” Musharraf ya ce cikin nutsuwa.
“Eh, haka tace,” Imam ya ce, yana fita daga ɗakin don yin magana, dai-dai lokacin da likitan dake night shift ya shigo don dubata.
Zahra ta taɓe baki cikin jin haushi. “Sai ka fita ka yi waya da yayana, kaman wani yayanka ne,” ta ce a hankali.
Sa’ud ya yi murmushi. “Ai za ki yi bayani, yarinya. Ba Imam kika kira grumpy ba?”
“Ba da shi nake yi ba,” Zahra ta ce tana jin kukan yana taso mata.
“Ki kwantar da hankalinki. Babu abin da zai miki. Idan ya shigo, ki yi kamar haka,” A’isha ta ce tana nuna mata yadda za ta ɗaure fuska.
Sa’ud ya yi dariya ya miƙe ya gaishe da likitan, suka yi musabaha. Likitan ya ce cikin annashuwa, “I can see the patient is awake. She’s looking good.”
“Yes, all praise be to God,” Sa’ud ya ce cikin murmushi.
Likitan ya ƙara dubata sosai, ya ce ba za a sallameta ba sai jibi. “Jininta ya ɗan hau, so let’s keep examining her for a few days.”
Da zarar Zahra ta ji wannan, ta kumbura fuska. Ba ta so ko kaɗan.
Imam ya dawo ɗakin, yana mai miƙa mata waya. Zahra ta sanya a kunne, ta fashe da kukan shagwaɓa.
“What is it, princess? Menene kuma?” Musharraf ya tambaya, jin kukan da take yi kamar yaro da aka cire mishi nono a baki bai ƙoshi ba.
“Yaya… likitan ne wai ba zai sallameni ba sai jibi. Ni kuma gida nake son dawowa… I missed you all,” ta ce tana zumɓura baki.
“A’a, ba wani jibi. Dr. Imam said he’s coming to Kaduna tomorrow. Tare za ku taho. Idan ma akwai treatment da bai ƙare ba, za a yi miki a nan. Kin ji?”
Kai ta gyaɗa kamar yana gabanta.
“Please don’t cry again. Ki kwantar da hankalinki. At least, tonight I’ll have a peaceful sleep,” ya ce da lallashi.
Suka yi sallama, ya kashe wayar. Ta miƙa wa Imam wayarsa ba tare da ta ce komai ba. Ya karɓa, ya saka a aljihunsa sannan ya kalli Sa’ud.
“Mu tafi, ko?”
---
Bayan fitarsu, A’isha ta yi wanka ta kwanta. Bacci mai nauyi ya ɗauke ta, tana rama gajiyawar kwana biyu tana kula da Zahra dare da rana. Amal kuwa ta dawo wajen Zahra, suka yi wasa har ƙarfe ɗaya na dare kafin su yi bacci.