Free chapter · Read without an account
Page 52
by Shamseeya Rabi'u Garba · AKASIN TSAMMANI (Beyond All Odds)
Ranar wata asabar Yusuf ya zo ya ɗauki Sen suka kama hanyar Kaduna. Iya na zaune a falo da su Zahra, Farida, Musharraf da Zainab suna hira, Sen ya yi Sallama, Zahra da gudu ta je ta rungumeta shi; "Wai tsoho daga ina?"ta faɗa tana kallon sa.
Kumatunta ya ɗan ja ya ce; "Daga Abuja, na zo na gan amaryata."
Ya ƙarasa shiga fakon, Iya ta washe baki, ta ce; "Barka da zuwa manyan Abuja."
"Hajiya Iya na same ku Lafiya?"
"Lafiya ƙalau wallahi, ina ita Fatun?"
"Masha Allah. Fatima na gida."
Sen ya amsa gaisuwar da su Musharraf ke masa, ya kalli Zahra ya ce; "Bashir na gida?"
Zahra ta harare shi ta ce; "Ai ka sakaya sunan ko don ƴaƴansa da ke gaban ka."
Iya ta riƙe haɓa tace"Lallai Zahra wuyan ki ya isa yanka." Ta kalli Sen; "Yanzun Bashir ɗin ya fita, amma bari a kira shi ya dawo ƙilla bai yi nisa ba."
"Ok, Musharraf kira min shi, ke kuma" ya faɗa yana pointing Farida"Ki fita ki cewa baƙon da mu ka zo da shi ya shigo."
Iya ta kalli Zahra ta ce; "je ki ki kirawo su Aminan."
Zahra ta haura sama don sanar da Mommy da Mama zuwan Sen.
Zahra na saukowa daga stairs ba ta lura da Yusuf da ke zaune ba ta fara faɗin; "Wai Ni kam Grandpa menene ya kawo ka, don na san ba ka zuwa sai da dalili mai..." Tsit ta yi tana kallon Yusuf da ya ƙura ido yana kallonta.
"You...me ka zo yi a gidan nan?" Ta faɗa cikin inda inda tana nuna Yusuf da hannu.
"Ni ya yi wa rakiya. Kin sa shi ne?" Sen ya faɗa yana kallonta. Kai ta girgiza ta ce; "a'a ban san shi ba. Ta koma sama da gudu, ɗakinta ta faɗa tana tunanin; A ina Sen ya san Yusuf? Kuma me dalilin kawo shi gidan su.
Mommy ta sauko ta gaisa da mahaifinta, sai murna ta ke na ganin sa, tunda ta yi aure wannan ne karo na biyu da ya taɓa zuwa gidanta, hakan ya sa babu sangarcin da ta manta ba ta yi mishi ba. Mama ta sauko ta gaisa da shi gudun masifa da Iya za ta yi mata idan ba ta sauko ba.
Daddy ya dawo gida sakamakon kiran da Musharraf ya yi masa ya sanar da shi Sen na neman shi. Duka yaran fakon suka tashi don ba su waje, Sen ya ce; "Musharraf kai ka tsaya, don duk maganar da za a yi akan rayuwar Zahra ya kamata a yi shi da kai because you're the closet person to her."
Musharraf ya dawo ya zauna yana mamakin; wacce magana ce za yi akan Zahra. Yusuf kuwa a nashi ɓangaren zura ido ya yi yana kallon Musharraf da aka referring to as mafi kusanci da Zahra.
Sen ya yi gyaran murya ya fara koro bayani; "Ba komai ne ya sa na zo Kaduna a yau ba face dalilin wani abu da ya shafi Zahra. Zahra wata sashe na zuciyata ce da ba na wasa da duk abinda ya shafe ta, wannan dalilin ya sa na tako da kaina na zo ban yi saƙo ba. Wannan bawan Allah." Ya nuna Yusuf da ya sunkuyar da kai, "Sunan shi Yusuf, ya zo min ne da magana akan yana son Zahra, ya fara mata magana a lokacin da take wajena amma ba ta saurare shi ba ta ce masa tana Idda." Ya ɗan yi mu su takaitaccen bayani akan Yusuf da duk yadda suka yi da shi, sai ya ci gaba da faɗin; "Alhamdulillah na yi duk binciken da ya kamata a kan shi, na gane cewa mutum ne mai natsuwa da sanin ya kamata, hakan ya sa na ji wa Zahra sha'awar kasancewa da shi. Shine na umurce shi da ya shirya yau na kawo shi na gabatar mu ku da shi a matsayin mai neman auren Zahra, idan ku iyayenta kuka amince sai ku haɗa shi da Zahran ya je can ya nemi soyayyar ta."
Gaban Mama ne ya yi mugun faɗuwa, ganin haɗaɗen mutum da ke neman Zahra, nan take ya ji wani zafi da ɗaci a zuciyarta.
"Alhajin Abuja kenan, wani amincewa kuma ka ke nema a wajen ƴaƴan ka? Ai umarni kawai za ka ba su." Iya ta faɗa.
"A'a Iya ba na son na nuna mu su isa a kan ƴar su, shiyasa nake neman amincewar su."
Daddy ya sunkuyar da kai cikin jin kunya da ganin mutuncin surukinsa ya ce; "Abba kamar yadda Iya ta faɗa umarni kawai za ka bamu, ai da mu da Zahran duk a ƙarƙashin ka mu ke. Tunda ka yarda da nagartar sa to fa ni ba ni da wata ja, zai iya zuwa ya nemi soyayyar Zahra na amince masa."
Mommy ta ɗan kalli Yusuf da kan shi ke sunkuye, ta ce a zuciyarta; "Idan alkhairi ne Allah ka tabbatar, idan akasin hakan ne Allah ka watsar."
Sen ya ce; "Madallah na gode da karanci, amma abu ɗaya na ke buƙata daga gare ku; ban son ku nunawa Zahra kun san da wata magana. Musharraf..."
"Na'am Grandpa."
"Kai za ka same ta da maganar bayan kwana biyu. Dalilin haka shine; ku iyaye ne, ko da Zahra ba ta ra'ayin Yusuf idan har ku ka tunkareta da maganar za ta ji nauyin ce da ku a'a, amma shi kuwa Musharraf kamar abokin shawarar ta ne idan ba ta ra'ayi zata iya faɗa mi shi gaskiyar abinda ke ranta."
Iya ta gyaɗa kai ta ce;"Wannan haka yake, don Zahra kam akwai zurfin ciki."
Bayan sun gama duk tattaunawar da ta kamata Sen ya yi mu su sallama suka koma Abuja. A hanyar komawar su Sen ya daɗa jan wa Yusuf kunne akan kar ya kuskura ya ji ba daidai ba daga ɓangaren shi, saboda girmama shi da iyayen Zahra su ke yi bai son su zo suna kuka da shi.
***
Tunda Mama ta kyallara ido ta gan Yusuf ta ji ba ta da sauran nutsuwa, hankalin ta ya tashi, yanzu babu abinda ta sa a gaba irin ta gan maganar Zahra da Yusuf ta lalace. Ba ta son ma su kai ga fara soyayya balle har a kai ga aure. Amfani da Farida ta ke son yi su bi ta ko wace hanya wajen ganin sun ɓata Zahra a wajen Yusuf amma Farida ta ƙi ba ta haɗin kai. Yau ta haɗu da Hajiya Turai a wani eatry da ke wajen gari akan batun Zahra da Yusuf.
Hajiya Turai ta ture plate ɗin gabanta ta ce; "Kar ki damu video da mu ka yi amfani da shi lokacin Jameel shi zamu yi amfani da shi a wannan karon. Sanin gidan yaron kuma wannan ba matsala ba ce, zan yi amfani da amintacce na, zan sa ya bi bayan shi a duk lokacin da ya shigo Kaduna ta yadda ba zai lura har ya gano mana gidan su, daga nan sai mu san abu na gaba."
"Amma ƙawata ɗan Allah a wannan aikin kar ki sa wanda za su iya zama mana barazana don har yau a tsorace na ke da ƙawarta Safiyar nan."
"Kar ki damu za mu kiyaye a wannan karon."
"Yauwwa na gode sosai Allah ya bar mini ke."
Hajiya Turai ta yi murmushi, ta buɗe purse ɗinta ta fito da karar sigari, tana kunnawa Mama ta miƙe, tana yamutsa fuska ta ce; "Bari na tafi za mu ƙarasa a waya."
Dariya Turai ta yi, ta kashe sigarin ta ce; "Mu je na sauke ki tunda har yanzu Bashir ɗin naki ya kasa siya miki abin hawa amma ya iya siyawa kishiyar ki."
"Na faɗa miki ba shi ya siya mata ba, mahaifinta ya aiko mata dashi."
Turai ta taɓe baki ta ce; "Ki ci gaba da yarda da su."
***
Babu hanyar da Musharraf bai bi wajen lallashin Zahra akan ta yi haƙuri ta saurari Yusuf ba amma ta ƙi, tun yana lallashinta har ya koma faɗa. Zahra ta kafe akan ba ta so. Sau biyu Yusuf na zuwa tana ƙin fitowa. Yau da ya zo sai da Musharraf ya yi mata tatas kafin ta fita tana tura baki. Yusuf na cikin mota ya hango ta tana zuwa rai a ɓace, bisa ga dukkan alamu dole a ka yi mata. Daidai booth ɗin motar ta tsaya, ta jingina da boot ɗin tana kallon street ɗin su da ya yi shiru. Yusuf ya yi murmushi ya fito ya sameta.
"Ranki shi daɗe Allah ya sa ban takura ki ba?"
Zahra ta yi niyyar ta yi banza da shi, amma sai ta gan rashin dacewar hakan, wulaƙanta ɗan Adam ba halinta ba ne.
Ba tare da ta wani kalle shi ba ta ce; "Sannu da hanya Mallam Yusuf. Gaskiya idan na ce ba ka takura ni ba na yi ƙarya."
"Subhanallah, ai da kin ce na tafi kawai zan cigaba da dawowa har lokacin da kika ji zuciyar ki ba ta takura da gani na ba."
Zahra ta ɗan kalle shi ta ce; "Dole ce aka min na fito, amma with what you say now na gan dacewar fitowa ko hakan zai sa mu yi maganar fahimta."
"Allah ya ba mu ikon fahimtar juna."
"Aameen. Da farko dai ina son na fara da ba ka haƙuri akan zuwan da ka yi kwanakin baya ba ka samu gani na ba, sai kuma ina son na roƙe ka kar ka sake zuwa wajena Please."
"Zahra, ba zan taɓa iya daina zuwa wajen ki ba saboda ina son ki."
"Ni kuma ba na sonka!" Ta faɗa a fusace"Bama kai kaɗai ba, ba na jin son ko wane namiji a rayuwata. Please let me be."
"Dan Allah Zahra kar ki min haka, ki ɗan ba ni dama Please."
"Ka yi haƙuri na riga da na rufe babin soyayya a rayuwata."
"Please ki ba Ni damar buɗe sabuwar shafin soyayya a zuciyar ki."
"Ka daina ɓata lokacin ka a kan abinda na ba mai yiwuwa ba ne. Sai an jima." Ta tafi ta bar shi a tsaye. Ya kai kusan minti goma a tsaye kafin ya shiga mota ya bar unguwar, jikin shi ya yi sanyi da lamarin Zahra.
Zahra na shiga ɗaki ta gan Musharraf a zaune akan gadonta yana jiranta. Hijabin jikinta ta cire, ta zauna a gefensa. "Ya tafi." Ta faɗa tana tura baki.
Shiru Musharraf ya yi kamar ba zai ce komai ba, can sai ya ce; "Me ya sa ba ki son Yusuf?"
"Babu komai, Ni kawai ba na son na yi soyayya kuma."
"Amma kin san ba za ki ci gaba da zama a gidan nan ba ko?"
"Me zai hana? Idan maganar mutane ne I'm used to it already, garin gudun maganar mutane ba shine na faɗa auren Kassim ba?"
"Zahra ba maganar mutane na ke mi ki ba. You're just a young girl, ta yaya za ki ci gaba da zama babu aure?
"Yaya aure fa ba dole ba ne, da irin auren da na yi ai gwara babu."
Musharraf ya yi ƙasa da murya, cikin lallashi ya ce; "princess na fi kowa sanin halin ƙuncin da ki ka shiga a dalilin auren Kassim, amma ki sani ba kowane aure ba ne babu daɗi, just take Me and Zee for instance ba mu ba ki sha'awa, look at Grandpa and Inna suma tsofaffi kenan, look around the world they're several happy couples, so why not give it a try again? Don't you want to have kids?"
"Yaya ko da zan yi aure ba yanzun ba, maybe nan da wasu shekaru, and not with Yusuf, saboda bana jin komai a kan shi."
"Tabbas ba za ki ji komai a kan shi ba saboda ba ki ba wa zuciyar ki daman hakan ba. Abinda na ke son ki fahimta ba wai cewa za ki yi kina son shi ba, a'a kawai dama za ki ba shi ya gwada sa'ar shi ko zuciyar ki zata aminta da shi. Please Zahra do this for me, Yusuf is a good man, I'm sure you will find happiness with him In Sha Allah."
Zahra ta yi shiru na kusan minti goma sai ta sauke numfashi ta ce; "I will give it a try." Rungumeta Musharraf ya yi ya ce; "Finally. You're such a stubborn girl."
***
"Yusuf I'm talking to you, wani dangi ka ke da su a Kaduna? Da ka tsiri tafiya can kwana biyun nan?"
Yusuf da already ba daidai ya ke ji ba saboda yadda Zahra ta nuna mishi rashin son sa ƙiri-ƙiri ya ɗan tsaya ya ce; "Maryam I have a stressful day can I rest please."
"Ya nuna cewa you had a stressful day, amma hakan ba zai hana ka amsa min tambaya ɗaya tak da na maka ba."
"Aiki ke kai Ni Kaduna." Ya yi mata ƙarya ko zai samu ya huta.
Baki matar shi ta buɗe; "Yusuf! Ƙarya!? Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji'un."
"Me haka Maryam a gaban yara ki ke faɗin ina ƙarya?"
"Kai ba ka ji kunyar yin ƙarya a gaban su ba ni ce zan ji kunyar faɗin ka yi ƙarya? Na daɗe ina zargin ka idan ba ka sani ba, kuma an tabbatar min da cewa wajen wata ka ke tafiya a Kaduna, wata ɗin ma wacce ta doshi shekaru talatin kafin ta yi aure saboda tsabar rashin kamun kai, sannan a cikin watanni uku kacal auren ya mutu, yanzu in neman mata za ka fara da irin wacan nan za ka fara?