Free chapter · Read without an account
Page 54
by Shamseeya Rabi'u Garba · AKASIN TSAMMANI (Beyond All Odds)
Imam ya taso ne a hannun Anty, cikin musguna wa, kyauta, da mugunta. Anty kullum cikin zaluntar shi ta ke da wulaƙanta shi, a gaban Mahaifinsa kuwa sai ta nuna ta fi kowa son shi. Anty bazawara ce, amma bata taɓa haihuwa ba, ko a gidan Abba ba ta haihu ba, sai ta kwaso yaran ƴan uwanta tana riƙewa, Imam na ganin yadda ta ke kula da wa'yannan amma shi sai hanyar. Da Abba ya gane Anty pretending ta ke yi wai tana son Imam amma a zahiri zaluntar sa ta ke, sai ya tura shi ƙasar waje karatu, a lokacin Imam na SS2. Gwaggo Rabi ita ta aurar da su A'isha a lokacin da suka kai munzilin aure.
Ammi kuwa bayan shekara uku da mutuwar aurenta, ta haɗu da wani hamshaƙin ɗan kasuwa ta yi aure. Yana da Mata ɗaya da yara biyar;Kamal, Khalid, kabeer, khausar sai Safrah. Yarinya ɗaya Mama ta haifa a gidan; Sarah. Kishiyarta mutumiyar kirki ce sosai, ta ja ta a jiki kamar ƴar uwa, ba ta bari mummunan kishi ya yi galaba a kanta ba.
Cigaban labari...
Imam na riƙe da hannun Ammi suka shiga falonta, A ƙasa ta zauna ta miƙe ƙafafunta, Deen ya yi gudu ya ɗalle cinyarta, da sauri Imam ya ɗauke shi yana faɗin; "Ba ka gan ƙafar Ammi na ciwo ba? Ko so kake ya yi mata zafi?"
Girgiza kai ya yi, ya ce; "Sorry Ammi." Ammi ta yi murmushi ta miƙa mishi hannu alamar ya zo, ɗora shi ta yi a cinyarta tana faɗin; "Ai ƙafar ta daina ciwo, beside ko tana ciwo idan Deeni na son ya zama ai dole na daure."
Imam ya kaɗa kai ya ce; "Lallai lokacin dawowar ka Kaduna ta zo, don ba zai yiwu ka hallaka wa Ammi ƙafa ba."
Dariya Ammi ta yi ta ce; "Inda ka yi ƙarya kenan, Deen ɗina na nan da ni."
Kishiyar Ammi ta serving ɗinsu abinci da ta sa aka shirya tun ɗazu. A tsakiyar falon kowa ya baje ana cin abinci, banda Deen da ya ce shi ba zai ci tuwo ba. Yana zaune yana buga game a wayar Imam. Wayar ne ya fara ringing, tura baki ya yi, ya miƙawa Imam wayar. Ɗauraye hannu ya yi, ya amsa wayar, picking ya yi ya sa a kunne; "Hello Musharraf ya ne?"
"Lafiya ƙalau wallahi, daman I was thinking ko kana free yau mu haɗu."
"Wallahi na ɗan yi tafiya, amma idan abinda zamu iya tattauna a waya ne ina ji."
"Well daman ina son na ɗan roƙe ka wani alfarma ne."
"Toh Allah ya sa wanda zan iya ne."
"I don't know in za ka iya employing Zahra a asibitin ka, bana son yanda take zaune a gida doing nothing, zan fi son ta fara practice ta ɗan samu more experience, no need for you to even be paying her."
"Gaskiya ka yi tunani mai kyau, but the only thing is ya kamata itama tana da zeal ɗin abun, idan ba haka ba ba zata koya komai ba."
"Ni idan Zahra ce I don't have problem with that, idan Zahra ce za ta mayar da hankali sosai."
"To shikenan, if she's ready za ta iya fara tafiya ko da ba na nan I will speak to them on phone."
"Gaskiya na gode sosai. Lastly Mommy ta ce na faɗa maka ka kyauta."
Ɗan dariya Imam ya yi, ya ce; "Ka ce wa Mama ta yi haƙuri, I will find time and come immediately na shigo gari."
"Allah ya kawo ka Lafiya."
Bayan sun katse kiran, Ammi ta lalle shi ta ce; "Waye Musharraf kuma? You seem so close and I don't know him."
"He's just a new friend, bai daɗe da na san shi ba ta dalilin buge ƴar uwar shi da na yi da mota a Ibadan."
"Oh, na tuna ka faɗa min, but you need to know budurwa kake buƙata yanzu ba aboki ba."
"Here you go again." Ya faɗa yana miƙewa, "Deen tashi mu tafi."
Ammi ta bi su da kallo har suka fice, ta ce; "Allah ya shirya min kai Imam."
Kishiyar Ammi ta yi murmushi ta ce; "Ki bi shi a hankali sannan mu dage da addu'a"
***
A ɓangaren Zahra kuwa Yusuf bai zo mata kwana biyu ba, ya yi tafiya zuwa Gombe, sai yawan kira da ya ke damunta da shi, wanni lokacin ta ɗaga, wanni lokacin ta yi kamar ba ta gani ba. Har yau ba ta jin komai a zuciyarta game da shi amma ta ɗauki shawarar Musharraf; ta ba shi dama to see if it will work
Tana zaune tana arranging chocolates ɗinta da Ammi ta siya mata da su ka je shopping mall ɗazu a side drawer da ta ke tara kayan kwaɗayinta. Musharraf ya yi knocking ɗin ƙofar ɗakinta. Zahra ta yi sauri ta rufe chocolate ɗinta, ta miƙe ta buɗe ƙofar. Murmushi ta yi, ta ce; "Ashe kai ne? I thought Khalil ne har na ɓoye chocolate ɗina."
Musharraf ya bi ta gefen ta ya shiga ya ce; "ke kuma sarkin rowa."
"In dai akan chocolate ɗina ne ka kira ni da komi ma."
Zama ya yi a kan gado ya ce; "zo ki zauna mu yi magana." Ta zauna a gefen shi ta ce
"I'm listening."
"Zahra na gaji da ganin ki a gida ki na zama doing nothing, don haka na yi magana da Imam za ki fara tafiya aiki a asibitin su daga next week Monday In Sha Allah, that will enable you ki samu practical working experience." Tsalle Zahra ta daka, ta rungume shi tana ihun murna, ta ce; "Yaya wallahi you're the best brother in the whole world. Kai ka ke granting min wish ɗina tun kafin na furta. Allah ya saka maka da mafificin alkhairi."
Kwana biyun nan ta rinƙa tunanin asibitin da za ta je ta fara casual working da su kafin result ɗin ta ya fito, maybe za a daina mata wani maganar soyayya ko aure idan an gan tana aiki, sai ga shi Musharraf ya zo mata da wannan maganar. Farin ciki sosai ta yi da ta kasa ɓoyewa.
Musharraf ya ɗan ja mata kunne akan idan ta je ta kama kanta ta yi abinda ya kamata, sannan shi zai rinƙa dropping ɗinta da safe kafin ya je office, ya kuma ɗauke ta da yamma bayan ya tashi. Chocolate biyu Zahra ta ciro ta bashi ta ce; "ka ɗau ɗaya ka bawa sister Zee ɗaya."
***
Mama da Hajiya Turai sun bi diddigi har suka gano gidan Yusuf, suka haɗa hotunan Zahra a cikin mummunan yanayi da short note a envelope. Hajiya Turai da kanta ta kai envelope ɗin gidan Yusuf, Maigadi ya sanar da ita cewa Yusuf ba ya gari, matar sa kuma ta je ɗauko yara daga makaranta. Ta miƙawa Maigadin envelope ɗin ta ce; "Idan matar ta zo ka ba ta, ka ce saƙo ne daga Kaduna ta natsu ta duba."
Maryam na dawowa daga ɗaukan yara daga makaranta, tana parking Maigadi ya miƙa mata envelope ɗin, ya faɗa mata saƙon Hajiya Turai. Amsar envelope ɗin ta yi, ta ɗan jujjuya shi tana kallo, tana mamakin wa zai kawo mata saƙo daga Kaduna, ɗan leƙa ciki ta yi, ta gan hotuna, kallon Mai gadi ta yi ta ce; "Nagode."
A falo ta zazzago envelope ɗin, hotunan Zahra ce kala-kala sanye cikin pant da bra, wasu ma tsirara ta ke, tunani ta fara yi; ko dai kuskuren gida a ka yi.
Ƙaramar paper da ta gani a cikin hotunan ta ɗauka ta warware;"Assalamualaikum, da fatan saƙon nan ya same ki cikin ƙoshin lafiya? Na san za ki yi mamakin hotunan wace wannan kuma wa ta turo, to sanin wace ta turo bai da amfani wacce take cikin hotunan kuma itace karuwar da mijin ki ke bibiya a Kaduna da sunan aurenta zai yi. In kin san abinda ya dace miki to ki miƙe ki san abin yi tun kafin ya ɗauko mu ku wata cutar. Na san mijin ki baya gari shi yasa na zabi aiko miki da saƙon a yau. Ma'assalam." Wani irin zufa ne ya fara keto mata ta ko ina, ta rasa abin yi, kanta ya ƙulle, ta rasa wane irin damuwa ce Yusuf ke son janyo mu su suna zaman zamansu.
___
Ranar Monday bayan dogon tunani da shawarwari Maryam ta shirya ta tafi Kaduna. A kwai ƙawarta da suka yi makaranta ɗaya tana aure a unguwar su Zahra, ita ce ta fara faɗa mata akan tana ganin mijinta a Kaduna, ranar da Zahra ta fito wajen Imam ne ta san wajen Zahran ya ke zuwa, shine ta kira Maryam ɗin immediately ta faɗa mata. Tana shiga garin Kaduna ta kira ƙawarta ɗin ta turo mata address ɗin gidan su Zahra.
Horn ta danna a bakin gate ɗin, Mai gadi ya leƙo. "Mallam Zahra na zo wajenta."
"Ai kuwa kamar ba ta dawo daga wajen aiki ba."
"Idan mahaifiyar ta na ciki ka ce ta yi baƙuw." Mai gadi ya koma ciki, can sai ya dawo ya buɗe mata gate, a tsakiyar compound ɗin gidan ta yi careless parking, fitowa ta yi daga motar, sanye take cikin Doguwar rigar shaddar, ta sha ɗaurin ture ka ga bala'i. Cikin takun isa da ji da kai ta shiga falon ba tare da sallama ba. Mommy da ke zaune da Iya a falo su ka ɗaga kai don ganin wace irin baƙuwa ce da ba ta iya sallama ba.
"Ina Zahra ta tafi?" Maryam ta tambaya tana wani yi mu su kallon raini.
Mommy ta rasa me zata faɗa, she was shock and speechless, Iya ce ta miƙe, tana nuna Maryam da hannu ta ce; "Ke! Kar ki kawo mana fitsara da rashin kunya a nan, ya za ki shigo wa mutane gida babu sallama kamar gidan arna, sannan ba tare da gaisuwa ba ki zo kina tambayar Zahra saboda ga ki mara kunya, to ga Zahran a kaina."
Maryam ta ɗan tsorata, amma ta daure don tana son ta kawo komai ƙarshe yau.
"Baaba sallama na nufin salama, Ni kuma ba shi ya kawo ni ba. Ina Zahra ta ke? Na je na sameta ko na bar muku saƙo.
Iya ta riƙe haɓa ta ce; "Lallai yaran zamani sai a hankali, yanzu ke ki kalli kwayar idona ki ce min ba salama ya kawo ki gidan nan ba, yaƙi dai kenan ya kawo ki?"
Maryam ba ta ko amsa Iya ba ta kalli Mommy, ta ce; "I guess ke ce mahaifiyar ta, na zo ne na ja wa Zahra kunne akan ta fita harkar mijina, Yusuf mijin mace ɗaya ce tak. Wallahi idan ta kuskura ta shigar min gida to gawarta za a fitar, kuma ta kiyaye haɗuwata da ita domin sai na yi mata rauni ta yadda ba ta yi tsammani ba. And lastly idan har..." Tas! Tas! Mommy ta ɗauke ta da mari gefe bibbiyu, daidai lokacin Musharraf da Zahra su ka shigo, Zahra ta tsaya a bakin ƙofa tana kallon Mommy da Maryam da ta riƙe cheeks ɗinta.
Mommy ta nuna ta da yatsa ta ce; "In your life kar ki ƙara tunanin za ki iya zuwa gidan nan ki yi mini raini, raini is the last thing I will tolerate daga ƴar yarinya irin ki, so now get out of my house!"
Maryam ba ta daddara ba ta fara ihu; "Wallahi ba ku isa ba, dole karuwar ƴarki ta fita a harkar mijina, Ni ba zan yi kishi da kowa ba most especially balagaza, ba zai taɓa yiwu na gama building miji into the man I want na zo ina sharing ɗin shi da wata ba. Wallahi idan ta cigaba da kula mijina duk abinda ya same ta ita ta ja." Ta kalli Zahra ta ce; "Ki yi kuka da kan ki wallahi."
Daman Zahra was doubting ba dai ita ce wannan matar ke magana a kanta ba, amma da ta facing ɗinta sai ta fahimci ita ɗin ce. Wa ta ke kulawa, ita dai ta san Yusuf ne kawai, shima ba sonsa take yi ba, "could this woman be this mad akan Yusuf?" Ta faɗa a zuciyarta. Hannun Musharraf da ya ƙarasa cikin fakon yana son yin magana da Maryam ta riƙe, ta ɗan girgiza mishi kai, sai ta shiga gaban shi.
"Ga ni a gaban ki, do your worst Madam." Kowa dake falon kallon Zahra su ka yi, basu taɓa tsammanin wannan boldness daga gareta ba, sun aza ɗaki za ta shiga ta yi ta kuka. Mama da tun farkon rikicin ta fito ta tsaya a staircase ta kalli Zahra da tsananin mamaki.
"Ya kika yi shiru, ki yi duk abinda za ki yi na ce! Wait Allah ya sa ba akan Yusuf kike wannan hayaniyar ba? I'm so disappointed wallahi, mata na faɗa akan Maza da suka amsa sunan su maza and here you're shouting and misbehaving akan Yusuf. Malama ke kike ganin Yusuf a matsayin na miji but to me he's nothing but a pest da ke damun rayuwata, na fi ki son ya fita a rayuwata but ya nace, da I was wondering; me yasa Yusuf ya maƙale min? Amma yau da na gan ki na gane cewa mata ce bai da ita a gida. Yanzun za ki iya tattara ƙazaman ƙafafunki ki fita daga gidan nan."
Maryam ta ce; "Wow I see, har kina da bakin magana ko? To za ki gane ba ki da wayo."
Farida ne ta ƙaraso wajen ta fara tura Maryam tana faɗin; "Fita daga gidan nan kafin na yi miki shegen duka." Haka ta turata waje, ba ta barta a compound ɗin ba, har wajen gate ya kai ta.
Iya ta riƙe haɓa tace; "Lallai akwai aiki a nan. Alhajin Abuja ya zo da babbar abu, wai a hakan za yi auren?"
Mommy ta ce; "Babu auren da za ayi, daman Zahra ba ta son shi, ga kuma abinda matar shi ta zo ta displaying. Zan kira Abba abar maganar nan."
Maryam na shiga motarta ta kife kai a kan steering, ta fashe da kuka. Tana jin a rayuwarta ba a taɓa ci mata mutunci irin na yau ba; an zage mijinta, an zage ta, sannan aka turo ta waje. Wannan wane irin bala'i ne Yusuf ya ja mu su, wato ma shi ke bibiyar yarinyar? "Tabbas gobe zan tafi Gombe a yi ta ta ƙare."
Zahra na shiga ɗaki ta yi wanka ta shirya cikin riga mara nauyi, ta zauna shiru a edge ɗin gado,wani irin farin ciki take ji yau; ta fara zuwa aiki, gashi za a soke maganar Yusuf. Kwanciya a kan gadon ta yi, ta ware hannayen ta; "Alhamdulillah." Ta furta a hankali.
Da daddare bayan ta gama komai har ta kwanta Yusuf ya rinƙa kiran wayarta, da farko ba ta ɗauka ba, amma da ta gan kiran ya yi yawa sai ta ɗauka.
"Hello Gimbiya kin fara bacci ne?"
Zahra ta ɗan yi shiru sai ta ce; "zan dai fara."
"Ok ashe na kira a daidai. Ya labari."
"Matarka ta zo gidanmu yau."
Zabura ya yi daga jikinta da yake, ya tashi tsaye, hankali a tashe ya ce; "Me ta zo yi? Hope ba ta misbehaving ba?"
"Ashe dai tabbatace ne ba ta da hankali, well rashin hankalin ta displaying ta ƙara gaba."
"Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji'un Maryam ta kashe ni. Amma su waye a gida lokacin ta zo?"
"Kowa na gida."
"Innalillahi...ermm let me call you back." Ya katse wayar.
Zahra ta yi murmushi ta ajiye wayar, ta lulluɓe jikinta har kai.
***
Ranar Friday Imam ya shigo garin Kaduna da sassafe. Sai da ya ɗan huta a gidan shi, bayan sallar juma'a ya shiga asibiti. Parking ya yi a parking space, ya fito daga motar daidai lokacin da Musharraf ya fito.
"Yaushe a gari?" Musharraf ya tambaya yana kallon Imam.
"Yau fa."
"Sannu da zuwa. Nima lunch na kawo wa Princess." Ya faɗa yana nuna masa ɗan ƙaramin basket da aka packaging abinci."
"Oh, ta zo aikin kenan."
"Eh. Please taimake ni ka miƙa mata." Imam ya karɓi basket ɗin, ya ce; "Ok. Tell Mom I will be comfortable tomorrow evening In Sha Allah."
"Finally." Musharraf ya faɗa, su ka yi dariya.
Zahra na zaune a office da aka ba ta, suna sharing da wata doctor Rashida. Attendant ta shigo ta ce; "Dr. Zahra Oga na neman ki."
Both Zahra da Rashida su ka ɗaga kai suka kalleta. Kowa da tunanin shi; Zahra na tunanin waye kuma Oga, Rashida na tunanin yaushe Oga ya shigo da har ya ke neman Zahra.
Attendant ɗin za ta fita Zahra ta yi sauri ta tashi, ta ce; "Mu je ki nuna mini office ɗin shi."
Zahra ta tsaya a bakin ƙofa, ta karanta sunan da ke maƙale a ƙofar; Dr. Aliyu Sammani. Tsayuwa ta yi a wajen for almost five minutes tana tunanin; Waye Oga? Me yasa yake nemanta? A hankali ta ƙwanƙwasa ƙofar sai ta tura ta shiga. Sanyin AC ne haɗe da ƙamshin air freshener ya buge ta, ta ɗan ja numfashi, rufe ƙofar ta yi a hankali. Babban office ne sosai da ya ɗauki set ɗin office desk da kujeru, set ɗin cushion da kuma TV, fridge da coffee maker, ƙasar office ɗin an shimfiɗe lallausar Egyptian centre rug. Kallon Imam da ke zaune yana duba laptop Zahra ta yi, tana mamakin shine Ogan? Gyara tsayuwarta ta yi ta ce; "Good afternoon, you sent for me."
Imam ya yi shiru kamar bai ji ta ba, after few minutes ya rufe laptop ɗin ya ce; "Sit."
Zahra ta zauna kamar yadda ya umurce ta.
"Mun yi magana da Musharraf and ya faɗa min cewa you're a person that's willing to learn all the time, therefore zan engaging ɗinki sosai, because Musharraf told me he wants you to learn a lot. Daga yanzu you won't just be sitting a office, zan haɗa ki da Dr. Bilal shi zai rinƙa koya miki duk abinda ya kamata, baya nan yanzu, he's on a leave but ranar Monday zai resuming office. Mind you shine MD ɗin asibitin nan so you have to respect him, ba wai za ki rinƙa yin mishi character ɗinki na gaisuwa a lokacin da kika gan dama kawai, you have to stoop too low if you want to learn. I think that's all I have to say for now, za ki iya tafiya."
Zahra ta ce; "Thank you." Ta miƙe za ta fita, ya ce; "And this?" Yana pointing basket da ke gefen table ɗin shi.
Zahra ta ɗan kalle shi ganin lunch basket ɗinta.
"Your lunch." Ya furta yana duba wani file.
Ɗaukar basket ɗin ta yi ta ce; "Thank you."
Zahra na komawa office ta ajiye basket ɗin hannunta tana mamakin ya aka yi abincin ta ya kai office ɗin shi. Ta ɗan kalli Rashida ta ce; "Errm Dr. Rashida can I ask you a question?"
Rashida gyaɗa kai ta ce; "Ina jin ki."
Zahra ta ɗan gyara zamanta tana kallon Rashida da kyau ta ce; "Waye Imam a asibitin nan, I mean me matsayin sa?"
"Waye Imam kuma?"
"Oh sorry, Dr. Aliyu Sammani na ke nufi."
"Dr Aliyu? Ai shine mai asibitin, he owns this hospital."
Zahra ta zaro ido ta ce; "The whole of this hospital?"
"Eh. Me ya faru? Why are you asking."
"Errm babu komai, I'm just curious." Rashida ta taɓe baki ta cigaba da abinda ta ke yi.
Zahra ta janyo basket ɗin abincin ta, ta dishing ta fara ci.
Bayan sallar La'asar Zahra na kwance a kan darduman da ta yi sallah tana taɓa wayarta, Imam ya turo ƙofar ya shiga, Rashida da ke typing prescription na maganin wani patient ta miƙe da sauri ta ce; "Ina wuni sir."
Zahra ma ta miƙe daga kwancen da ta ke, ta zauna ta ce; "Ina wuni."
"Kin san ba kwanciya ya kawo ki nan ba ko?" Ya faɗa yana kallon Zahra, kai ta sunkuyar ba ta ce komai ba.
"Come and attend to a patients let me see."
Zahra ta tashi, ta ajiye wayarta a kan tebur ɗinta, sai ta bi bayan shi zuwa wani ɗaki a emergency. Wata mata ce ta yi hatsari fuskar ta ko ina jini. Imam ya kalli nurses da suka fitar da kayan aiki za su fara ya ce; "let her do it, za ku iya tafiya."
Zahra ta matso kusa da matar jikinta na ɓari, tsigan jikinta duk sun tashi, Imam na tsaye daga gefe yana kallonta; ta saka handgloves ta yanka audiga da scissors ta goge fuskar matar tasa, raunukan suka bayyana da kyau. Jikin Zahra na mata wani iri, haka ta fara wanke raunukan matar na kuka, da kyar ta ƙarasa tana jin kamar ta fashe da kuka itama, ta kalli Imam da ke bayanta yana kallon abinda ta ke yi ta ce; "tana buƙatar ɗinki a nan." Ta nuna girar matar da ya samu deep cut. "Uhum go ahead."
Zahra kamar za ta yi kuka ta ɗauki allurar kashe zafi ta yi wa matar, sai ta kalle Imam jikinta na ɓari ta girgiza mishi kai. Imam ya zo ya ɗinka wajen, ya saka wa matar drip, zai fita Zahra ta ce; "Ba ka duba blood pressure ɗinta ba."
Imam ya dawo because it's very important, ya duba blood pressure ɗinta komai normal, sai ya fita a ɗakin Zahra na biye dashi a baya.
"Me yasa kika yi karatun likitanci."
"So that I can be able to save lives."
"Shine kike tsoro?" A hankali ya fara magana yana tafiya; "To save lives sai kin cire tsoro da tausayi a ranki, ki yanka wajen da ya kamata ki yanka, ki ɗinka wajen da ya kamata ki ɗinka, ki allura a wajen da ya kamata, sannan ki feɗe a lokacin da ya kamata ki feɗe. Duk abinda za ki yi, ki yi shi cikin nutsuwa amma ki sa zafin nama, patient zai iya mutuwa a hannunki saboda sanyin jikin ki. You need to..." Ciro wayarsa da ke ringing ya yi daga aljihu ya sa a kunne; "she's here." Ya ɗan yi shiru sai ya ce; "Ok." Ya katse wayar ya ce; "Musharraf na jiran ki a waje