Free chapter · Read without an account

Page 59

by Shamseeya Rabi'u Garba · AKASIN TSAMMANI (Beyond All Odds)

Zahra na bacci tana murmushi kamar wacce aka yi wa bushara da gidan aljanna. Mommy ta turo ƙofar ɗakin ta shigo, tsayawa ta yi akan Zahra tana kallon ta, sai ta kaɗa kai ta ɗan taɓa ta, ta ce; "*Zahra tashi ki yi sallah."

Zahra ta buɗe ido a hankali tana murmushi.

"Wannan murmushin fa? Tunda na shigo kike murmushi a bacci."

Zahra ta ɗan sosa kai tana tunoa mafarkin da ta yi, a take ta haɗa fuska ta ce; "Is just a silly dream."

Mommy ta yi murmushi ta ce; "To je ki yi sallah kar lokaci ya ƙure."

Bayan Zahra ta idar da sallah, sai ta kwanta akan darduman da ta yi sallah akai, a hankali mafarkin da ta yi da asuban nan ta fara dawo mata. Tsaki ta ɗan yi tana buɗe idanunta, ta miƙe tsaye ta folding kayan sallarta. Gaban mirror ta tsaya tana kallon kanta, ta rasa me ke damunta kwana biyun nan; Me yasa take yawan tunanin mutumin da ya wulaƙanta ta? Wai harda mafarki da shi. Me yasa a duk lokacin da ta tuna shi sai ta ji sanyi a zuciyarta instead of baƙin cikin abinda ya yi mata?

"Mtseew." Ta ja guntun tsaki ta bar gaban mirror zuwa bathroom.

Dressing ta yi cikin threequatre gown, ta combing gashinta ta parking ɗin shi zuwa baya sai ta ɗora hula, ta fesa turare ta sanya flip-flop ɗinta. A hankali ta ke saukowa daga stairs tana ɗan latsar wayarta, ɗaga kai da za ta yi gabanta ya wani irin faɗi, tsayuwa ta yi cak a wajen tana kallon mutumin da ke zaune a falon.

"Ƙaraso mana Zahra daman yanzu zan aika a kira ki." Mommy ta faɗa tana kallon Zahra da ta tsaya kamar an dasa ta. A hankali tana jan jiki ta ƙaraso cikin fakon, ta zauna daga gefen Mommy, ta ɗan sunkuyar da kai tana wasa da fararen yatsunta.

"Ba ki iya gaisuwa ba?" Mommy ta tambaya.

"Ina kwana." Zahra ta furta a hankali ba tare da ta ɗago kanta ba.

Imam ya ɗan kalleta ya ce; "Lafiya." A taƙaice.

"Serve him breakfast." Mommy ta faɗa.

"No Mama, ina da patient da zan duba yanzu, so I have to go now."

"A'a ba zai yiwu ba wallahi, ka zo har gidan nan ka tafi ba ka ci komai ba." Mommy ta kalli Zahra ta ce; "Package the food for him, ya tafi da shi."

Zahra ta tafi kitchen ta ɗauki  kula mai kyau, ta zuba mishi soyayyen irish da kwai a babban, sai ta zuba mishi pepper soup ɗin kayan ciki a ƙaramin, ƙaramin flask ta ɗauko ta zuba mishi ruwan shayi da ya ji kayan ƙamshi, arranging komai ta yi a cikin basket, ta fito da shi. Har gabansa ta tafi ta ajiye masa basket ɗin abincin.

"Ɗauka ki kai masa mota mana, ya za ki ajiye masa a nan?" Mommy ta faɗa.

Zahra ta ɗauki abincin ta fita zuwa parking space da shi. Imam ya yi wa Mommy sallama ya fita. A bakin motarsa ya gan Zahra a tsaye tana jiran sa, ya ƙaraso ya buɗe motar ya shiga, ɗayan gefen Zahra ta buɗe ta ajiye mishi basket ɗin abincin.

"Fatima."

Zahra da har zata wuce ta juyo ta kalli Imam da ya kira sunanta.

"Ki shirya mu tafi asibiti."

Zahra ta ɗan sunkuyar da kanta ta ce; "Ka yi haƙuri, amma ba zan iya zuwa office yau ba, saboda zan iya rashin lafiya a kowane lokaci."

Kallonta Imam ya yi da mamaki, ya ce; "Ashe ciwo na ba da sanarwa kafin ya zo?"

"Akwai ciwon da yake da lokacin zuwa ai." Ta faɗa a hankali kamar mai tsoron faɗi.

Imam ya ɗan kalleta, ya kasa fahimtar me take nufi, sai kawai ya ce; "Is alright, idan kin yi ciwon kin warke sai ki dawo bakin aiki."

"Thank you."

Imam ya kunna motarshi ya fita daga gidan. Zahra ta koma cikin gida. Ɗakin Mommy ta shiga direct, daga bakin ƙofa ta tsaya tana kallon Mommy da ke ɗaura lifaya.

"Fita za ki yi?" Zahra ta tambaya.

"Eh. Akwai matsala ce?"

Kai Zahra ta girgiza ta ce; "Babu komai. Kawai dai ina ɗan jin menstrual cramps ne."

Mommy ta kalleta ta ce;  "kin  sha magani?"

"Eh, amma kin san maganin ba ya aiki yanzu."

"Ki shirya mu fita tare, kar na juya baya kafin ciwon ya tsananta."

Mommy na driving Zahra na zaune daga gefenta, ta jingina kanta da glass ɗin window.

"Mommy me Yaya Imam ya zo yi a gidan mu?"

"Why are you asking?"

"Nothing, I'm just scared kar ya zamo wani laifin na yi."

"A'a babu abinda kika yi. Ya zo duba wani mara lafiya ne a anguwar nan shine ya bi ta nan ya gaishe mu."

"Oh, ya kyauta."

Da yammacin ranar Mommy ta dawo da Zahra gida, ita kuma ta wuce kasuwa. Tunda Zahra ta shiga gidan ta fara jin yadda mararta ke murɗa mata, cikin mintuna kaɗan matsinancin ciwon ciki ya riƙe Zahra, kuka ta fara yi sosai tana juyi a kan gado. Wayarta ta laluɓo ta kira Musharraf.

Musharraf da ke zaune tare da Imam a gidan Imam suna hira, ya Ciro wayarsa da ke ringing, ya yi murmushi yana faɗin; "Your staff." Imam ma ya ɗan yi murmushi.

Wayar Imam ya sa a kunne, kafin ya faɗi wani abu ya ji kukan Zahra; "Princess what is it?" Ya faɗa a rikice. Zahra ba ta iya cewa komai ba sai kuka, daga ƙarshe ta katse kiran. A rikice Musharraf ya ɗauki key ɗin motarsa ya ce; "I need to be going, Ina ganin ciwon mararta ne ya tashi tunda mun kai ƙarshen wata."

Imam ya ɗan lalle shi, ya ce; "Wane irin ciwon mara?"

"Menstrual cramps. Tun bayan aurenta da na ba ka labari, ta soma yin wannan irin menstrual cramps ɗin ko wane month."

"Ba ta shan magani ne?"

"Tana shan pain relief, but it seems shi ɗin ma ya daina mata aiki."

"Errm, ka kawota asibiti, zan tafi can na jira ku, I will examine her."

Musharraf ya tafi gida, ya taimaka wa Zahra ta shirya, ya saka ta a mota. Yana tuƙi da speed, Zahra na kwance a back seat tana kuka tana riƙe mara. Yana parking a parking lot ɗin asibitin ya hango motar Imam already parked a wajen. Riƙo Zahra ya yi, ya fito da ita daga motar tana takawa a hankali har zuwa office ɗin Imam.

Imam na zaune da laptop a gaban shi.

Ɗago kai Imam ya yi yana kallon Zahra da ke sharɓar kuka har da majina."Sit" ya nuna mata kujera, zama ta yi riƙe da mararta, Musharraf na tsaye a gefenta.

"What's wrong. Yaya marar ke Miki?"

"Yana murɗa min."

"Kin taɓa yin scanning akan wannan ciwon cikin?"

Kai ta girgiza mishi.

"And you claim to be a medical personnel."

Zahra ba ta ce komai ba, sai shesheƙan kuka take yi.

"Enter the room, let me call a female nurse." Ya faɗa yana pointing mata bedroom ɗinsa da ke cikin office ɗin. A hankali ta tashi da taimakon Musharraf ta shiga ɗakin.

Ɗakin na nan tsaf da shi, komai na ɗakin fari ne ƙal. Kwantar da ita Musharraf ya yi, sai ya fita daga ɗakin.

Imam da ke zaune yana jiran nurse da ya kira ta zo, ya ɗago kanshi jin ƙarar rufe ƙofa, murmushi ya ɗan yi ya ce; "You pet Zahra too much."

"I can't control it, jinta na ke yi sosai a Zuciyata, bana tunanin akwai wadda na taɓa so a duniyar nan irin Zahra."

"I can see, but ka rinƙa..." Maganar Imam ya katse sakamakon shigowar nurse Nafisa. Murmushi yayi ya ce; "Za mu yi magana wani lokaci, for now let me check her. Za ka iya zama a nan ka jira mu, feel comfortable please."

"Ok, sai kun fito, thank you so much Imam Ali."

Zahra na kwance tana fama da ciwon ciki, ƙamshin ɗakin Imam na shigarta ta ko ina, ta ji an Turi ƙofar. Imam ya ƙaraso kusa da ita, ya ɗan kalleta for few minutes, sai ya ce wa nurse ɗin; "Ki yi mata allurar PCM."

"Ok Sir."

Nurse ɗin ta shirya komai na allurar, ta kama hannun Zahra za ta soka allurar, ai kuwa Zahra ta fara kokuwa da nurse ɗin tana kuka. Allura na daga cikin abubuwan da ke matuƙar tsorata Zahra. Babu yadda nurse Nafisa ba ta yi ba, amma Zahra ta ƙi ba ya haɗin kai. Hannu Imam ya miƙawa nurse ɗin, ya saka mishi allurar. Ya matso kusa da Zahra, ya riƙe hannunta biyu gam yadda ba za ta iya kwacewa ba, ya ɗan yi gyaran murya ya ce; "Idan kika motsa allura ya karye miki a jiki ke ce da wahala." Zahra na jin batun allura ya karye mata a jiki ta nutsu sai zufa ke keto mata ko ta ina.

"Close your eyes." Ya furta a hankali.

Zahra ta rufe ido ta gan, sai ta ji ɗan karamar zafi kamar cizon cinnaka, sai ta fashe da kuka. Imam na cire allurar ya yi discarding ɗin shi, sai ya ɗan kalleta ya ce; "Point the exact place you are feeling pains let see."

Zahra ta yi pointing masa ƙasan mararta.

"Uhm Nafisa call Dr Farida and conduct a scan for her."

"Ok Sir."

Imam ya fita daga ɗakin don ba wa nurse ɗin damar yin mata abinda ya kamata. Zama ya yi, ya ce;"calm down Musharraf, she will be fine. Bari a yi mata scanning saboda mu gane menene matsalar."

"Thanks Imam."

Suna zaune shiru zaman jiran result ɗin scan Mommy ta kira Musharraf; "Hello Musharraf kana tare da Zahra?"

"Eh, na kawota asibiti, cramps ya riƙe ta."

"Subhanallah! Wane asibitin kuke?" Mommy ta tambaya cikin rikicewa.

"Calm down Mommy, Imam na duba ta, she will be fine."

"Gani nan zuwa..."

"No Mommy, ba sai kin zo ba, jikinta da sauƙi, I will bring her home soon."

"To sai kun dawo."

Scan result ɗin Zahra Imam ke ta kallo, scan ɗin bai nuna wani abu ba, organs ɗinta ƙalau su ke.

Ɗakin ya shiga ya kalli Zahra da ke kwance, jikinta duk ya sake, zufa take yi ta ko ina duk da sanyin AC da ke ɗakin. Kallonsa ya mayar zuwa ga nurse da ke ɗakin ya ce; "Excuse us." Nurse ɗin ta ɗauki few things ta fita daga ɗakin. Matsowa ya yi kusa da ita, ya taɓa goshinta, sai ya ɗan kalleta ya ce; "Har yanzu cikin ciwo ya ke miki?"

Kai ta gyaɗa mishi a hankali.

"Sosai?"

Ta kuma gyaɗa kai.

"Sorry." Ya furta calmly.

Hannu ya sa a marar ta saman kayan jikinta ya ɗan matsa, Zahra ta saki wani marayar kuka. "Sorry, I just want to check ko akwai kumburi a wajen." Hannunsa ya cire yana tunanin menene cause ɗin wannan severe pain ɗin, ya san cramps abu ne da yawancin mata suke yi, amma bai taɓa ganin wacce na ta yayi tsanani haka ba.

Drip ya ɗauko, ya fixing mata, ya yi mata wasu allurai. Cikin few minutes bacci ya kwashe ta. Ya fita zuwa cikin office, ya zauna yana facing Musharraf da ke zaune ya ce; "Errm Musharraf I think it's high time ku considering yi wa Zahra aure."

"Aure?"

"Eh. Saboda scanning da aka yi mata ya nuna ba ta da wani ciwo, therefore possibly sha'awa ce ke saka ta a wannan yanayin."

"Amma ai bai mata hakan da."

"Yes bai yi mata hakan da because she wasn't involved with a man, auren da ta yi possibly mijin ya arousing mata sha'awarta, wannan dalilin yasa yanzu she can't control it anymore."

"Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji'un."

AKASIN TSAMMANI

(Beyond All Odds)

YOTA ID/023

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol