Free chapter · Read without an account
Page 62
by Shamseeya Rabi'u Garba · AKASIN TSAMMANI (Beyond All Odds)
Musharraf na fita daga gidan ya kira Imam a waya. Imam da ke zaune a falo yana shan fruits yana ganin kiran Musharraf ya yi murmushi ya picking yana faɗin; "Idan ka ji kira to fa ta samu."
"Ai kuwa ta samun ne. Yaron nan da nake ta jiran dawowarsa gida na ji labarin ya dawo."
"Wane yaro kenan?"
"Kassim, ex husband ɗin Zahra."
Imam ya ɗan yi dariya ya ce; "shine yaron? Kamar wani ɗan cikin ka?"
"Whatever."
"Toh yanzu ya ake ciki, ɗauko shi za mu yi mu gwada mishi namu salon iskanci ko yaya?"
"A'a hukuma na ke son na damƙa shi wa, saboda idan har ya shiga hannuna ba zai ji ta daɗi ba."
"Wane irin hukuma? Ai daman ba ta daɗi muke son ya ji ba. See Musharraf, I have a friend in Ibadan, yanzu kawai ka tura min necessary information about him na sa a ɗauko mana shi."
"Kana ganin haka nan ɗin ne daidai?"
"Musharraf har daidai kake tambaya? Ko dai labarin da ka bani akan gayen nan ba haka bane?"
"Ƙarya na maka kenan?"
"To meyasa kake son yin wasa da daman da Allah ya baka na cin ubansa, ko dai har ka manta irin pain da ƙanwar ka ta passing through a dalilin shi?"
Musharraf ya yi ɗan murmushi ya ce; "Oh my princess is loved, I can't believe you're the one standing for her now. Ai daman na faɗa maka Zahra is a lovely person da idan ka zauna da ita ko da na kwana ɗaya ne zaka so ta, ba lallai so na soyayya ba, but you'll feel the urge to always be around..."
"Dakata Mallam, nifa I'm just doing this because of you, sai kuma don mu koyar da shi lesson yadda ba zai ƙara treating wata mace haka ba, amma kai kuma sai wani zance kake da ban gane kanshi ba."
Musharraf ya yi ɗan dariya ya ce; "Shikenan, let me send you his info."
Bayan sallar maghrib Kassim ya dawo da su Musa, a daidai ƙofar salon ɗin Laure ya yi parking, Ya buɗe wa yaran ƙofa. Su Musa suka fito ɗauke da ledodin siyayyar da yayi musu. Kasssim ya ja motar sa ya bar unguwar. Driving ya ke yana bin wakar da ke tashi a motar Ba tare da ya lura cewa ana bin shi a baya ba. A wani madaidaicin gida ya yi horn aka buɗe mishi gate ya shiga.
Da daddare misalin karfe biyu, mutanen da suka bi bayan Kassim, suka dawo gidan. Ɗaya daga cikin su ya sauka daga motar ya je ya yi knocking gate. Kamar cikin mafarki maigadi ya ji ana knocking gate; "waye ne?" Ya tambaya a lokacin da ya ke fitowa daga ɗakin shi yana haska toci.
"Nine abokin kassim ne, ya ce na same shi a nan."
"Wane Kassim? Babu wani Kassim a gidan nan."
"Kasssim wanda ya shigo gidan nan ɗazun da maghriba."
Maigadi ya tuna cewa hajiyar gidan ta yi bako ɗazu da yamma, sai ya buɗe ƙaramin ƙofar gate ɗin, yana haska Murtala ya ce; "Me yasa sai a tsakiyar daren nan zaka zo kana..."
Bai ƙarasa maganarsa ba Murtala ya ture sa da ƙarfi, ya faɗa cikin gida, sai ya yi sauri ya rufa masa baya. Maigadi ya ɓare baki zai yi ihun neman taimako, Murtala ya yi saurin toshe masa baki, nan suka fara kokuwa, abokan Murtala suka zo suka danne maigadi sannan suka soka mishi allurar bacci. Suna nan riƙe da shi har bacci ya ɗauke shi. Ƙofar main flat ɗin gidan suka nufa, Ali ɗaya daga cikin abokan Murtala ya ciro wani key daga aljihunsa ya ce; "Allah ya sa basu bar key a jikin ƙofar ba." Yana sa key ɗin kuwa ya shiga, ya murɗa a hankali, sai ga ƙofar ta buɗu. Ɗakunan da ke cikin gidan suka fara duba ɗaya bayan ɗaya har suka isa wanda su Kassim ke ciki. Bacci suke yi yana rungume da Hajiya Yalli, sai da Murtala ya ɗauke su hotuna kafin ya sa kafa ya wani kicking Kassim da ke bacci, a firgice dukkan su suka buɗe ido. Kasssim na zazzare ido ya ce; "Lafiya? Daga ina? Me na yi muku?"
"Hahahahaha" Murtala ya kwashe da dariya; "za ka san lefin da ka yi idan muka kai ka gaban wanda ya sa a ɗauko ka." Ya miƙa hannu ya ce; "Ali miƙa min allurar."
Kamar a mafarki Kassim ya gan an miƙawa Murtala allura, shi kuma an fara ƙoƙarin kai shi ƙasa. Hajiya Yalli ta buɗe baki za ta yi ihu, Murtala ya kai mata wani bugu a baki, ya ce; "Ki yi mana shiru, tsinaniya kawai mai cin amanar aure, ki ɗauko kwarto ki kawo ɗakin auren ki." Shiru Hajiya Yalli ta yi kamar an yi ruwa an ɗauke. Da ƙyar Ali da Simon suka iya kai Kassim ƙasa saboda shima ƙaƙarfa ne sai dai sarkin yawa ya fi sarkin ƙarfi. Musharraf ya soka mishi wannan allurar, nan take bacci ya fara fisgar sa, suka kinkime shi zuwa mota. A daren ranar suka ɗauki hanyar Kaduna. After eight hours suka ƙara yi wa Kassim wannan allurar saboda kar ya farka.
Bacci sosai Kassim ya yi, har aka iso Kaduna bai sani ba. Gidan Imam suka kaishi following the address sent to them, a backyard ɗin gidan suka ɗaura shi da pillar.
Imam na tsaye daga gefe yana kallon yadda suke ɗora Kasssim da jikin pillar, bayan sun gama ya ce; "Give me your account number."
"Kar ka damu ogah. Oga Sa'ud ya sallame mu ko."
"Ok, thanks."
Imam ya tafi ya rufe gate ɗin gidan sa bayan fitar su Murtala, yana dawowa falo wayar shi ya fara ringing, picking ya yi ya sa a kunne; "Ya ne?"
"Imam you're yet to explain to me dalilin ɗauko gayen nan."
"Sa'ud you know I don't do things without reason."
"Na sani, shiyasa nake son jin dalilinka."
"Yanzu ina son na shiga asibiti, idan na dawo, i will brief you on what's happening."
"Shikenan sai ka dawon."
Imam ya yi shiri ya tafi office. yana office ya kira Musharraf ya sanar da shi an kawo Kassim.
Ranar zaman office ɗin was very bored for him, saboda babu patients sosai, gashi Zahra bata shigo yau ba, duk yadda Imam ya so daurewa ya kasa, hakan ya sa ya ɗauki waya ya dannawa Zahra kira. Zahra na kwance a ɗakin Mommy suna hira kiran Imam ya shigo, miƙewa tayi ta zauna kafin ta picking call ɗin, lambar is not saved a wayarta domin jiya ne first time ɗin shi na kiranta, amma daga kallo ta gane lambar.
"Hello ina wuni Yaya." Ta furta a hankali.
Imam ya ɗan taɓe baki, yana fadi a zuciyarsa "Yau kuma Yaya ne ba sir ba." Amma sai ya yi kamar bai ji ta ba, ya ce; "Me ya hana ki zuwa aiki yau?"
"Errm na tashi da ciwon kai ne yau, shiyasa ban zo ba."
"It seems baki koya komai daga suspension da kika yi kwanakin baya ba. Da kika tashi da ciwon kai wa kika sanar cewa baza ki zo ba?"
Zahra ta yi shiru tana sosa kai, yau ta tashi ne da wani irin ciwon kai saboda rashin isasshen bacci, ta kwana ne tana tunanin abinda Musharraf zai iya yi wa Kassim, da kuma tunanin shi Imam ɗin, ba ita ta yi bacci ba sai ƙarfe uku, hakan ya sa ta tashi da matsinancin ciwon kai, ya ɗan lafa mata kenan ta shiga ɗakin Mommy.
"Na baki ten minutes ki zo asibiti." Ya faɗa authoratively.
"Wallahi ciwo kaina ya ke min" Zahra ta faɗa kamar zata yi kuka.
"Kuma bamu da maganin ciwon kai a nan ko?"
"Na sha magani."
"I don't want to talk too much, find your way here." Ya katse kiran ba tare da ya bata damar sake faɗin komai ba.
Zahra ta sauke wayar kamar zata yi kuka, Mommy ta kalleta ta ce; "Imam ne?"
Kai ta gyaɗa mata.
"Wai me ya ce?"
"That I should get to work right now saboda ban ɗauki permission na absence ba."
"Zahra ba ki jin magana, in ce sai da na faɗa miki da safe akan ki kira shi ki faɗa mishi baki jin daɗi baza ki samu zuwa ba?"
Zahra ta tura baki ta ce; "Mantawa na yi."
"Ya Miki kyau. Tunda kin ɗan ji sauƙi sai ki shirya ki tafi, maybe patient sun yi yawa ne shiyasa ya kira."
Zahra ta shirya ta nufi office ba don ta so ba, intentionally ta ƙi kiran Imam ta sanar da shi ba ta da lafiya, tana son ta ɗan avoiding ɗinshi na kwana biyu ko zuciyarta zata haƙura da shi. Her plan was ta roƙi Musharraf ya nema mata one month leave, ta tafi Abuja ta yi hutu, ƙilla hakan ya sa ta manta da wani Imam because from all indication Imam ba zai taɓa sonta ba.
Tana isa cikin asibitin ta marairaice fuska irin wacce bata da lafiyan nan. A lokacin da ta shiga office ɗin Imam baya nan, tsayuwa ta yi daga bakin ƙofa ta kalli cikin office ɗin da ya gyara shi yau, it was looking very arranged and clean.
"Ina ya tafi ya bar office a buɗe?" Ta tambaye kanta a lokacin da ta ƙarasa cikin office ɗin ta zauna, ta ciro wayarta ta fara kallon TikTok videos, tana jin an taɓa ƙofa ta yi saurin kashe wayar ta kife kanta a kan desk.
Imam ya ɗan kalleta, sai ya ce; "Bacci kika zo yi?"
Kamar baza ta ce komai ba da farko, amma sai ta ɗago kai kamar za ta yi kuka ta ce; "Kaina ciwo yake min kamar zai fashe."
"Ok, kwanciyar ki a nan shine zai sa kan ya daina ciwo kenan? Wai ma tsaya ba kin ce kin sha magani ba."
"Eh na sha but is still aching."
Imam ya je gaban wani drawer da ke office ɗin, ya ɗauki allura ya ja wani ruwan allura, ya ƙaraso gaban Zahra ya ce; "Give me your hand."
Zahra na ganin allurar hannun shi ta yi narai-narai da ido ta ce; "Ciwon kai ne fa kawai, i don't think there will be need for injection."
"I'm not asking for your opinion."
Lokaci ɗaya hawaye ya fara gangaro mata, ta ce; "Yaya please, wallahi kan ya ma daina ciwo."
Fisgo hannunta Imam ya yi, ta fashe da wani kuka; "Dan Allah ka yi haƙuri wallahi ya daina ciwo."
Imam ya sake hannuta yana kallonta ya ce; "kin ce kan ya daina ciwo ko?" Kai ta gyaɗa mishi tana goge hawayen da ya ɓata mata fuska.
"Good. Sai ki fara aiki."
Ya kwaso wasu files daga kan tebur ɗinsa ya ajiye gabanta, ya ce; "Go through this." Yana faɗin haka ya fita daga office ɗin.
Zahra ta ɗan daafa kanta da ciwon ya dawo sosai saboda kukan da ta yi, a hankali ta tashi ta buɗe drawer da ya buɗe ɗazu ta ciro kwayar sudrex ta ɗauki ruwa a gefe ta haɗe. Tana cikin duba files ɗin da ke gabanta ta fara gyangaɗi, tura files ɗin ta yi gefe ta kwanta don ba fahimtar komai da ke file ɗin take yi ba.
Imam na shiga office ya gan Zahra na kwasar baccinta. Tsayawa a kanta ya yi yana kallon innocent baby face ɗinta, her lips is so pink and dry, tana sauke numfashi a hankali. Pack ɗin sudrex da ta sha da bottle water da ke gefenta ya kalla, sai ya kai hannu ya taɓa goshinta, da sauri Zahra ta buɗe ido jin an taɓa ta.
"Jikinki yayi zafi."
"Yes."
"What will you do about that?"
"Zan samu isasshen bacci yau In Sha Allah, I will feel better with that."
"Suit yourself. Tashi mu je na dropping ɗinki a gida, Musharraf is busy today."
Zahra ta tashi ta ɗauki wayarta da purse ɗinta, ta bi bayan Imam zuwa parking space.
***