Free chapter · Read without an account
PAGE 71
by Shamseeya Rabi'u Garba · AKASIN TSAMMANI (Beyond All Odds)
Ammi ta rinƙa jan Zahra da hira, tun Zahra na jin kunya har ta sake suna ta hira da dariya, Deen kuma na kwance a cinyar Zahra, tun yana kallo har ya yi bacci. Imam kuwa an kira shi emergency a asibiti, ya fita.
Zahra ta ji daɗin kasancewa tare da su Ammi. Nana na tsaka da yi mata kitso Imam ya dawo tare da Musharraf. Tsayawa akan su Imam ya yi, yana kallon baƙin gashinta mai tsantsi da tsawo, da kuma yadda take kwaɓe fuska. "Zafi kitson ke yi ne?"Imam ya tambaya.
Kai ta gyaɗa masa alamar eh.
"Yaya ba wani zafi fa, kawai dai raki ne da ita." Nana ta faɗa tana ɗan dungura mata kai.
Imam ya ce; "Be careful Nana, make it loose." Yana faɗin haka ya shige ciki.
Nana ta ce; "Tabɗi gaskiya Yaya ya faɗa."
Zahra ta yi murmushi, ta ce; "Sai na faɗa mishi abinda kika ce."
"Dan Allah ki rufa min asiri matar Yaya."
Imam na shiga ya zauna a gefen Musharraf. Ammi ta kalle shi, cikin farinciki ta ce; "Imam ka faranta min yau fiye da kowane rana."
"Alhamdulillah, na yi farinciki da na ji wannan maganar daga bakinki Ammi, please continue being happy."
Ammi ta kalle Musharraf, ta ce; "Musharraf na san aikinka ne haɗa Imam da Zahra, na gode sosai da wannan ƙoƙarin naka."
Imam da Musharraf suka juya at thesame time, suka kalleta, sannan suka lalle juna cikin jin mamakin yadda aka yi ta san cewa Musharraf ne ya kawo wannan plan ɗin. Cikin ƙame-ƙame Musharraf ya fara magana; "A'a Ammi...babu ruwana... Ban ma san ya akayi suka fara soyayya ba."
Ammi ta yi murmushi ta ce; "Haba Musharraf, ni fa ba yarinya ba ce, tunda ya faɗa min Zahra ƙanwarka ce, na fahimci cewa you people are just helping him to get away from my anger, and you actually did. Two weeks back kuka zo neman alfarmar na ƙarawa Imam lokaci amma na ƙi, so ta yaya har a cikin sati biyun nan ya samu mace da yake so kuma suka shaƙu haka? Imam da na sani ba zai yi saurin sabo da budurwa in just two weeks ba, idan kuma sun fi two weeks tare me yasa ya nemi extra time? A rashin wayo irin taku kuma abin a dramar taku ku yi akan ba su gama sabawa da juna ba, amma sai kuka yi kamar wadda suka daɗe suna soyayya."
"Ammi ki gafarce mu." Musharraf ya faɗa yana sunkuyar da kai.
"A'a ba ka yi laifi ba Musharraf, abu mai kyau ka yi. Abinda nake so yanzu shine, daga wannan dramar dole su fara soyayyar gaskiya domin na gan Zahra, kuma ta kwanta min a rai."
"In Sha Allah Ammi, daman wannan abu dole zai continue, saboda mun yi addu'a akai, kuma In Sha Allah zamu gan alkhairi da ke cikinsa."
"Alhamdulillah, Allah ya tabbatar."
Imam dai yana zaune shiru, ya rasa mai zai fada. Yanzu ya san dole shi ya auri Zahra idan ta amince kuma iyayenta sun amince, amma abun dubawa shine; ta yaya za su yi aure bayan ba son juna suke yi ba, yana tsoron shiga haƙƙin Zahra, don ya san baza ta rasa wanda take so ba. Ya zama dole ya nema hanyar da wannan dramar zai ƙare a iya nan."
"Imam magana fa nake maka." Ammi ta katse masa tunanin da ya faɗa.
"Na'am Ammi."
"Na ce; ka duba ko su Nana sun gama kitson."
Imam ya miƙe ya fita zuwa frontage ɗin gidan, ya gan sun gama kitso, suna kallon abu a waya suna dariya.
Daga bakin ƙofa Imam ya tsaya yana kallon yadda suke ta dariya, Zahra ya fi ƙurawa ido, don bai taɓa ganin dariyarta ba. Taɓa ƙafarshi aka yi ta baya, ya juyi. Deen ne da ya tashi daga bacci yana sosa idonshi, ya ce; "Daddy, where's Mom?"
Nuna mishi su Zahra ya yi, ya ce; "Go and tell Mom Ammi is calling her."
Da gudu Imam ya ƙarasa wajen su Zahra, ya zauna a ƙafafun Zahra, ya ce; "Ammi is calling you."
Zahra ya shafa kanshi, ta ce; "Mu tafi."
Ta riƙe hannunsa suka nufi ƙofar fakon, Nana na biye da su tana mitar yadda Deen ya naniƙewa Zahra, ya manta da ita. Zahra na murmushi ta ce; "Yanzu Nana kishi kike yi da ni?"
"Ba komai ai zaki tafi, zamu gan wajen wa zai dawo ne."
Zahra ta yi dariya, ta ce; "Ai tare zamu tafi. Ko my boy?"
Kai Deen ya gyaɗa mata, yana murna.
Suna isa bakin ƙofa, Imam ya matsa gefe suka wuce.
Alheri sosai Ammi ta yi wa Zahra, sannan ta raƙo su har bakin mota. Rungume Ammin Zahra ta yi, ta ce; "I will miss you Ammi."
Ammi ta yi murmushi ta ɗan yi patting ɗinta a baya, ta ce; "i will miss you too my dear. ki gaishe min da Mommynki, ki ce mata zan zo mu gaisa kafin na koma Kano."
"Sai mun ganki Ammi."
Zahra ta tsuguna ta rungume Deen, ta ce; "I will miss you my love."
Hawaye ya fara yi, yana rikici wai shi bin ta zai yi.
"Haba my Deen, za mu rinƙa waya a wayar Anty Nana ai, stop crying please."
Noƙe kafaɗa ya yi, ya ce; "Mom zan biki, I want to watch Ben-Ten and play subway surf in your phone."
"Zan turawa Anty Nana, ko Ammi a wayarsu, sai ka kalla."
Kuka Deen ya fara yi yana bubbuga ƙafarsa a ƙasa. Imam ya matso zai ɗauke shi, ya fashe da kuka yana tura shi, yana faɗin; "Leave me alone, I want to follow my mommy."
"Deen please it's ok, I will take you to her tomorrow."
Babu yadda ba a lallashe Deen ba amma ya ƙi yarda, gam ya cikuikiye rigar Zahra ya riƙe ta, yana kuka. Musharraf ne ya matso kusa da shi, ya ce; "Yaron kirki kana son ka bi Mommynka ko?"
Kai Deen ya gyaɗa yana kasar majina da ya gangaro masa.
"To Mu je." Ya faɗa yana miƙa masa hannu. Da sauri Deen ya sa hannunshi a cikin na Musharraf jin abinda ya faɗa.
Musharraf ya kalle Ammi da Imam, ya ce; "Zan dawo da shi gobe."
Ammi ta yi murmushi, ta ce; "Ba damuwa, Allah ya kaimu goben."
Musharraf ya buɗewa Deen front seat ya shiga, ya kalli Zahra, ya ce; "Ki zauna a baya."
Imam ya buɗe mata bayan ta shiga, ya ɗan kalleta kamar zai yi magana sai ya fasa ya rufe mata ƙofar. Ammi da Nana na ɗaga musu hannu har motarsu ta fita daga compound ɗin gidan.
A hanya Deen ya rinƙa yi musu surutu da tsale-tsale a mota kamar ba shine ya yi kuka few minutes ago ba. Sai da Musharraf ya biya da su Ice cream joint, suka siyo Ice cream kafin suka dau hanyar gida.
A lokacin da su Musharraf suka iso gida, Daddy da Iya na zaune a falo suna hirar su ta ɗa da uwa. Deen na ganin Iya, ya nuna Iya da hannu, ya ce; "Old woman!"
Musharraf da Zahra suka kwashe da dariya. Iya ta bi su da kallon rashin fahimta, ta ce; "Ya zai nuna muku ni ku kwashe da dariya kamar kun gan mahaukaciya?"
Daddy ya yafito Deen da hannu, ya ce; "Zo nan gentleman, ya zaka kira min mahaifiya da tsohuwa."
Deen ya ɓoye a bayan Zahra. Zahra ta janyo shi gabanta, ta ce; "Ba zai yi maka komai ba, mahaifina ne."
"Your father is my grandfather right?" Ya tambaya yana kallon ta.
Kai ta gyaɗa mishi, da gudu Deen ya je ya rungume Daddy, ya ce;"Grandpa!"
Daddy ya rungume shi sosai a jikin shi, yana jin wani sanyi a zuciyar shi,har cikin zuciyarshi ya ji ƙaunar yaron ya dirar mishi.
Kallon su Musharraf ya yi, ya ce; "A ina kuka samo min kyakyawar aboki haka, wanda ya kira min uwa da tsohuwa.
Zahra ta zauna a gefen Daddy, ta ce; "Ai tsohuwar ce." Daddy ya zungure mata kai.
Musharraf ne ya yi musu bayanin yadda suka samo Deen, da irin rikicin da ya yi akan zai biyo su.
Iya ta miƙo mishi hannu, ta ce; "Zo ja'iri."
Kai ya girgiza mata, yana gyara zamansa a ƙafafuwan Daddy, A kunne Daddy ya raɗa masa; "I'm scared of old people."
Daddy ya yi dariya, ya ce; "The don't bite."
Da ƙyar aka shawo kan Deen ya yarda ya tafi wajen Iya. Yana zuwa, Iya ta ce; "Tabbas ga kamanin ubanshi. Daman shi Imamun ya taɓa aure ne?"
***
AKASIN TSAMMANI
(Beyond All Odds)
Young Talented Writers Asso...YOTA
YOTA ID/023