Free chapter · Read without an account

Page 84

by Shamseeya Rabi'u Garba · AKASIN TSAMMANI (Beyond All Odds)

Imam na zaune very confused a falon, Iya ta kawo mishi lemu da ruwa. Ko kallon inda ta ajiye su bai yi ba, kawai yana son ya fahimce abinda Zahra ta aikata ne.

Sen. ya miƙawa Imam hannu suka ƙara yin musabaha, sannan ya ce; "Welcome to our home Imam, ko ban tambaya ba na san kaine ka ke son kwace mini mata."

Murmushi Imam ya yi, ya ɗan sosa kai, ya ce; "Tuna na ke Baba."

"Naƙi amsar tuban, sai ka siya min ƙaton sa."

"Babu damuwa, zan siya tunda ina son mata."

Sen. ya yi murmushi, ya gyara zaman shi, ya ce; "Zaka yi tunanin meyasa Zahra ta haɗaka da mu ta yi tafiyarta ko? To tayi hakan ne saboda na buƙaci son ganinka, kuma in yi magana da kai idan ba damuwa."

"Babu komai Baba."

Cikin hikima Sen ya yi wa Imam tambayoyi game da rayuwarsa, dama Deen, ta hanyar da ba zai ji kamar an ci mishi fuska ba. Imam ya amsa iya gaskiyarsa, don ya fahimci bincike Sen. ke son yi akan shi. Daga baya kuma suka faaɗa hiran rayuwar duniya, da business don Sen ma business man ne, a nan ne ya ba wa Imam shawarwari sosai na hanyar da zai bi wajen bunƙasa business ɗinshi.

Imam ya ji daɗin lokacin da ya yi spending da Sen. sosai, saboda a ƴar hirar da suka yi ya koyi abubuwa dayawa, he just wish this is his grandfather or father. Kiran sallar maghriba ne ya sa suka tashi, suka tafi masallaci. A lokacin da suka dawo har Iya ta kammala girkin da take yi da taimakon ƴar aikinta, suka jera good warmers da suka zuba abincin akan dining table. Suna dawowa daga sallah Sen. ya yi leading Imam zuwa dining, Iya ta yi serving ɗinsu tuwo shinkafa da mutane agushi, ta tafi ɗaki ta kira Zahra.

Zahra ta zauna a kujerar da ke kallon wadda Imam ke zaune, ta yamutsa fuska, ta ce; "Tuwo kuma?"

Iya ta tura mata wani plate da ke rufe ba tare da ta ce mata komai ba. Zahra na buɗewa ta gan freshly baked pancake ne, an zuba condesed milk a kai. Ta miƙe ta ɗauki orange juice daga fridge, ta zauna, ta ɗan kalle Imam, ta ce; "Idan ba ka son tuwon we can share my pancakes."

"I like the tuwo, it's so delicious."

Imam ya faɗa yana mata murmushi.

Taɓe baki Zahra ta yi, ta fara cin pancakes ɗinta.

Sen. da Iya suka fara tashi daga dining, suka bar Zahra da Imam.

Kallonta ya yi, ya ce "Ya kan?"

"Da sauƙi."ta furta a hankali.

Gyaɗa kai ya yi, ya ciro waya daga aljihunsa ya fara latsawa. Zahra kuwa tana cin cake ɗinta tana satan kallonsa, yana ɗaga kai kuwa idonsu ya haɗu karaf, da sauri ta kau da kanta, ba ta ƙara ɗago kuma ba. Can ya miƙe, ya ce; "I will be taking my leave."

Zahra ta tura plate ɗin gabanta gefe, ta miƙe ta bi shi a baya. A falo ya tsaya ya yi wa su Sen. Sallama, sannan ya gode wa Iya for the delicious meal, kafin suka ƙarasa zuwa wajen da ya parking motarsa a waje. Back seat ya buɗe, ya Ciro wata babbar leda ya miƙa mata. Ɗago kai ta yi ta kalle shi kafin ta miƙa hannu a hankali ta karɓa, ta ce; "Na gode, Allah ya ƙara buɗi."

"Deen told me you like chocolate." Ya faɗa yana shiga mota.

Murmushi ta yi, ta ɗaga masa hannu bayan ya kicking motar, ta juya ta shige gida.

Tana shiga, ta zauna akan ɗaya daga cikin one-sitter dake falon, tana wani tsare gida ta ce; "Me ka ce mishi Grandpa?"

"Na cewa wa?" Ya tambaya kamar bai san wa take nufi ba.

"Saurayina" ta faɗa kai tsaye.

"Au shine kike wani tsare gida? kamar mamata. To ce mishi na yi ya nema wata matar don ke kam na yi miki miji a Abuja. Ko kina tunanin na hakura da maganar Yusuf ne?"

Zahra ta wani haɗa rai tana kallon Grandpa kamar ta kai mishi duka, don ta san ba maganar da suka yi da Imam ba kenan, kawai yana don ta magantu ne. Iya bata san lokacin da ta kwashe da dariya ba, Zahra ta miƙe a fusace ta wuce ɗaki, Sen. ya harare Iya, ya ce; "Dariyar me kika yi? Gashi kin ɓata mata rai."

"A'a wallahi ba ni na kar zomon ba."

Sen. ya mike ya bi bayan Zahra zuwa bedroom.

A lokacin da Imam ya koma gida, ya tarar da Abba a farko a zaune ya cika fam. Imam ya gaishe shi, zai Abba ya ce; "Saƙonka ya iso gareni, kuma na gode. Kayan da na riga da na siyo kuma idan na bayar sai ka watsar da su."

Imam ya sunkuyar da kanshi bai ce komai ba, don daman ya san dole Anty za ta sauya magana, ko kuma ta yi ƙari.

"Za ka iya tafiya." Abba ya faɗa, yana kallon Imam ko zai yi masa wani bayani, amma Imam ya juya ya yi tafiyarsa. Hakan bai ba shi mamaki ba, don ya saba da irin wannan halin na Imam, zai yi laifi ya ƙi ba da haƙuri, wani lokaci kuma yana sane ba laifinsa bane, zai ba sa laifi don ya kare kansa, amma ba zai ce komai ba.

Imam na shiga ɗaki, ya yi wanka ya kwanta, duk yadda zuciyarsa ta so ta damu akan maganar da Abba ya yi masa, ya hana hakan, sai ma nazari da ya fara akan wasu abubuwan ci gaba da Sen. ya ba shi hint.

A ɓangaren Mommy kuwa, ta hana kanta bacci, ta kwana a darduma tana kai kukanta ga Allah, da ya kawo dawwamammiyar farinciki a rayuwar ƴarta, ya kareta daga wani auren da zai sa ta cikin ƙunci, ya kawar da Imam daga rayuwarta idan har zai zama sanadiyyar saka ta hawaye.

Grandpa kuwa tunda ya samu ya lallashe Zahra ta yi shiru, ta kuma ba shi yardarta, ya koma ɗakinsa ya zauna yana tunanin ta yadda zai fara bincike akan Imam, duk da ganin da ya yi wa Imam bai yi kama da mutumin banza ba, amma ba duk mutumin banza ake ganewa daga kallo ɗaya ba.

Washegari Zahra ta yi shiri, ta zauna jiran Imam ya zo ya ɗauke ta. Shiru-shiru ba ta ji daga gare shi ba har ƙarfe goman safe. Fita tayi bakin hanya, ta tare taxi zuwa asibiti. Tana shiga asibitin ta hango motarsa a wajen da ya saba parking. Office ta nufa, ta murɗa handle ɗin ƙofa, ta shiga da sallama. Yana tsaye a gaban coffee maker, ya ji an turo ƙofar, juyowa yayi suka haɗa ido, sunkuyar da kai ta yi, ta ce; "Ina kwana." Tana zumɓura baki.

Juyowa yayi ya cigaba da haɗa coffee ɗinsa.

Zahra ta nema waje ta zauna don ta san ba amsawa zai yi ba dama. Ya gama haɗa coffee ɗinsa, ya zauna yana sipping a hankali, yana kuma kallon Zahra da ke duba file ɗin patients ɗinta, tana ɗaga kai suka haɗa ido, gira ɗaya ya ɗaga mata, ta sunkuyar da kai, ta zumɓura baki, ta ce; "Shine ka yi zuwanka ka bar ni."

"Shine kike ta zumɓura dogon bakin ki?"

Zahra ta marairaice fuska kamar za ta yi kuka jin abinda ya faɗa, Imam kuwa kawar da kansa ya yi kamar ba shi yayi maganar ba.

Zahra ta fito da mirror daga handbag ɗinta, ta ƙure ma kanta kallo, tana son ta tabbatar ko tana da dogon baki, a hankali ta ɗora hannun a kan bakinta. Da ƙyar Imam ya iya danna dariyar da ya zo masa, ya ce; "Ya kike jin jikin ki?"

"Da sauƙi." Ta amsa a ƙasan maƙoshi.

Murmushi Imam ya yi, dan ya san yau mutumiyar tasa ta shaƙa. "I thought you're still not feeling well, shiyasa ba zo na dauko ki ba."

Zahra ba ta ce mishi komai ba, ta ɗauki file ɗin patient da za ta dubo yanzu, ta fice daga office ɗin. Da kyar ta iya mayar da hankali ta duba patients ɗinta, a hankali ta ƙarasa zuwa wani staircase da ba a cika amfani da shi ba, ta zauna zuciyarta fal da tunani, "Ashe daman kallon bakina yake dogo shi yasa ya kasa sona." Ta saƙa a zuciyarta, shesheƙa ta fara yi ƙasa-ƙasa. Imam da ya shiga ward ya yi round check, bai gan Zahra ba, hakan yasa yayi tunanin ko tayi fushi ta tafi gida ne, amma ba zai yiwu ta tafi gida ta bar handbag ɗinta da wayarta a office ba. Asibitin ya fara zagayawa office by office, har reception sai da ya je ya duba bai ganta ba, har zai koma office zuciyarsa ta raya masa ya duba ta staircase ɗin back door na asibitin da ba a fiye amfani da shi ba.

A zaune ya hangota tana backing ɗinsa, takowa ya yi, ya ƙaraso gaf da ita. Kamar a mafarki Zahra ta fara jiyo ƙamshin turaren Imam, da sauri ta juyo da hawaye shaɓe-shaɓe a idanunta, tana ganin shine ta ƙara fashewa da sabon kuka.

"I can see that you are still not well, don haka ki tashi na mayar da ke gida." Ya faɗa yana kallon Zahra da ke kukan zallar sangarta da shagwaɓa. Babu musu Zahra ta miƙe, don at this point gida kawai take buƙatar tafiya.

Office ta tafi, ta tattara kayanta, ta ƙulle office ɗin, sannan ta tafi parking space inda Imam ke jiranta. Buɗe mata ƙofa yayi ya, ta shiga, ya rufe kafin ya koma side ɗinsa. Zahra ta zumɓura baki, ta furta a zuciyarta; "Oho dai duk da dogon baki na sai da aka buɗe min ƙofa."

Instead of gida, Babban shopping mall suka tafi. Imam kaɗai ya shiga, Zahra na zaune a mota. Siyayya ya ɗan yi, sannan ya fita ya tafi sashen ciye-ciye dake jikin mall ɗin, ya siya abinda yake buƙata ya fito. A lokacin da ya dawo motar, Zahra ta gaji da zumɓure-zumɓuren da take yi har ta yi bacci, murmushi ya yi, ya ce; "Drama Queen."

Sai da ya yi parking a ƙofar gidansu kafin ya ɗan taɓata, a hankali ta buɗe idanunta da bacci bai gama sakinta ba.

Sauka ya yi, ya buɗe mata mota, ya ciro shopping da ya yi, ya miƙa mata, ƙin karɓa ta yi, ta yi wucewarta gida. Imam ya yi murmushi, ya san tabbas yau ya ɓata wa Zahra rai. Maigadi ya ba wa shopping ɗin ya ce ya ba ta.***

AKASIN TSAMMANI

(Beyond All Odds)

Young Talented Writers Asso...YOTA

YOTA ID/023

Zahra na zaune da Iya a falo tare da su Iya da Farida, suna mata tsiya wai ta ba ta jin daɗi amma ta nace sai da ta tafi asibiti saboda ta gan masoyinta. Ba ta kula su ba, ta kwantar da kanta a kafaɗar Mommy.

Mommy ta taɓa goshinta, ta ji da zafi.

"Me ke damunki?" Ta tambaya cikin kulawa.

Wani irin sanyi Zahra ta ji a zuciyarta, ganin kulawa a idon Mommy, tun jiya rabon da ta yi mata fara'a, ko ta ji lafiyarta yadda ta saba, ta san tabbas Mommy ba ta son auren nan, Amma idan ba ta auri Imam ba gani take yi kamar za ta mutu. ƙara lafewa a jikin Mommy ta yi, ta ce; "Kaina ke ciwo."

"But kika tafi asibiti just to see that guy."

Zahra ta zumɓura baki, ta ce; "I wasn't there to see him, I went to check on my patients."

Baki Mommy ta taɓe, ta mayar da hankalinta TV.

Baba Maigadi ya yi sallama ya shigo falon hannunsa ɗauke da ledodin kayan da Iman ya ba shi. Tsugunawa ya yi har ƙasa, ya gaishe da mutanen falon cikin girmamawa, kafin ya ajiye ledodin hannunsa, ya ce; "Ga saƙon Hajiya Zahra, Alhaji Imam wai a bata."

Farida ta tashi, ta kwashe kayan, ta ce; "Ka ce mishi an gode, Allah ya saka."

Zahra ko ɗagowa ba ta yi daga kafaɗar Mommy ba, sai ma lumshe ido da ta yi, tana feeling mix emotion; haushin ce mata da ya yi tana da ƙaton baki, da kuma wani irin ƙaunar shi da ke azalzalar zuciyarta.

Farida ta fara buɗe kayan. Ledar farko turaruka ne kala-kala da maiyuka, shower gels da ribbons, ɗayan kuma su kayan ciye-ciye ne; chocolate, sweet, gum, shawarma, yoghurt da sauran kayan ciye-ciye. Farida ta saka na fridge a cikin fridge, ta ɗauki na ɗaki za ta kai ɗaki. Zahra ta ce; "Ki ɗeba wa kowa komai."

Farida ta raba abubuwan wa kowa, har Mommy da Mama sai da ta cire musu, sannan ta kai sauran abubuwan zuwa ɗakin Zahra.

"Tashi ki je ki sha magani." Mommy ta faɗa da ta ji yadda jikinta ke ƙara zafi.

Zahra na shiga ɗakinta ta yi wanka ta sha magani, kwanciya ta yi akan gado, ta ɗauki wayarta, lambar Imam ta dialing, har ya fara shiga da ta tuna abinda ya faɗa mata sai ta katse kiran da sauri, ta fara typing masa message ɗin godiya abinda ya siya mata, ba ta gama typing message ɗin ba sai ga kiran shi ya shigo.

Shiru ta yi bayan ta yi picking, shi ɗin ma ya ƙi ce mata komai, can dai da ta gan ba shi da niyyar yin magana sai ta ce; "Ina wuni Yaya, thanks for the stuffs you got for me."

"Ki sha paracetamol, ki kwanta ki huta." Ya faɗa without responding to her thanks.

Kai ta gyaɗa mishi kamar yana kallonta.

"And don't think too much about what I said earlier, I was just pulling your legs."

Still ba ta responding ba, sai ya katse wayar kawai yana murmushi.

Sati biyu Sen. Ya yi a Kaduna yana bincike akan Imam, mutanen da ya saka su yi masa binciken told him nothing but kyawawan halayensa, duk abinda za a faɗa a kansa was good idan aka cire rashin son mutane. Ba abinda aka faɗa wa Sen. kawai ba, a binciken da ya yi da kansa ma hakan ya gani, ya kuma ji. A iya zaman da ya yi da Imam ya tabbata shi ɗin ne perfect person for Zahra, domin Imam have been coming to the house, kwana ɗaɗɗaya ya ke skipping bai zo ba, hakan ya sa suka samu wani irin bond, Imam bai ɗauke Sen. A matsayin kakan Zahra kawai ba, but also a father and a mentor.

A ranar da zai koma Abuja, ya tafi har gida, ya zaunar da Mommy da Daddy, ya zayyana musu alkhairan da yake hango a auren Zahra da Imam, daga ƙarshe ya ce sune iyayyen zahra, don haka wuƙa da nama yana hannunsu, ya rage nasu su samar wa ƴar su farinciki ko akasin haka.

Imam da Zahra suka kaisu airport kafin suka wuce office.

A ɓangaren Mama kuwa murna take yi da auren da Zahra za ta yi, she's so happy saboda yadda ta gan Mommy is against it, ita daman duk abinda Mommy ke so ne ba ta so, ga kuma tambarin ɗan iska da yake da shi, tunda har ya ke da ɗa a waje, kuma tana addu'ar Allah ya sa kar ya daina iskancin.

Mommy kuwa tunda Sen. ya ce ya yara da nagartar Imam, ta zubar da dukkan makaman yaƙinta, ta duƙufa da addu'ar Allah ya sa alkhairi ne auren. Kullum raba dare take yi a darduma tana roƙa wa ƴarta alkhairi.

Saura wata guda auren Zahra da Imam, shirye-shirye ake yi ta ko wane ɓangare. Kuɗi daddy ke kashewa sosai fiye da wanda ya kashe lokacin aurenta na fari, saboda yanzu ya fi samun fiye da daa, kuma a wannan lokacin aure ɗaya ne gabansa, wancan lokacin kuma ita da Habibah ne.

Imam ya bawa Zahra hutu har sai bayan aure, bisa ga umarnin Ammi.

Gyara sosai Iya ke yi wa Zahra, wanda bata samu a auren fari ba, saboda a tunaninta Zahran ta taɓa wani mu'amalar aure da Kassim. Jikinta ya ƙara yin fresh ya yi ɓul-ɓul, haskenta ya ƙara fitowa da kyau, gashinta ma ba abar shi a baya ba, gyara sosai aka ɗauko mai gyara daga Maiduguri take yi mata, sumanta yayi kyau sosai, sheƙi yake yana fitar da ƙamshi mai daɗi. Duk inda Zahra ta zauna sai ta bar ƙamshinta a wajen, ita kanta ba ƙaramin dadin jikinta take ji ba. Rabon da ta gan Imam yau sati guda kenan, tsakaninta da shi sai kyauta da yake aika mata da shi akai-akai ta hannun Mai gadi.

Zahra na zaune a falon Ammi suna hira da Farhana, Imam ya kirata,kallon Farhana ta yi, ta ce; "Yau ya ga daman kira."

Farha ta yi murmushi, ta ce; "Ɗauka mu ji."

Zahra ta sa wayar a kunne, ta ce "Hello...Ina wuni."

"Fatima yaushe rabon da ki ji daga gareni?" Ya tambaya murya ƙasa-ƙasa.

"Sati ɗaya I think."

"You think? Yayi kyau hakan....What do you need for the wedding preparation?" Ya tambaya, yana jingine maganar da ya ɗauko da farko a gefe.

Zahra ta ɗan kalle Farha, ta gan yadda ta zuba mata ido tana kallonta, tashi ta yi, ta fita daga falon zuwa ɗakinta

"Duk da na san ba auren soyayya zamu yi ba, ina roƙon alfarmar yin biki, ko da kamu ne kawai, saboda ban samu daman yin haka a auren fari na ba."

"It's ok, ki shirya komai, ki faɗa min how much it will cost."

"No kar ka damu, approval ɗinka ne kawai daman nake nema."

"Fatima ban son dogon magana, just do as I say."

Shiru Zahra ta yi tana kallon Farhana da ta shigo ta zauna a kujerar mirror. Zahra ta kawar da kai gefe, ta yi ƙarfin halin cewa; "Me yasa ba ka kira ba kwana biyu?"

"You should have call to ask me why."

"I'm sorry." Ta furta a hankali.

"Just do the right thing." Ya katse kiran shi.

Cire wayar Zahra ta yi daga kunnenta kamar za ta yi kuka. Farhana da ke kallonta, ta ce; "Menene?"

"He's angry at me." Ta faɗa tana goge hawayen da ya gangaro mata.

"Kukan na me to? Me kika mishi?"

"Ban kira na ji dalilin da yasa bai kira ni ba for one whole week."

"Gaskiya ba ki kyauta ba...yanzu ki kira shi, ki lallashe shi."

Zahra ta langwaɓar da kai, ta ce; "Bai taɓa fushi da ni ba."

"That's why you should do the needful."

Imam na katse wayar, ya cire drip da ke hannunsa, ya shiga bathroom ya yi alawla ya fito. Yana fita daga bathroom ya ji wayarsa na ringing, yana ganin mai kiran yayi murmushi, ya ce; "Idan na bi naki bazan yi sallah yau ba Ammi."

Ya shimfiɗa darduma ya ta da sallah. Bayan ya idar da sallah, ya ɗauki wayarsa, ya kira Ammi video call.

"Ina ka ajiye wayar ina ta kiranka."

"I was praying."

"Sallah kuma? Ya aka yi lokacin sallah ya wuce ka?"

"Na yi bacci ne."

"Ok...Me ya haɗa ka da Zahra."

Zaro ido yayi, ya ce; "Ƙarana ta kawo miki kenan?"

"Ba wannan na tambayeka ba."

"Ammi wallahi babu abinda na yi mata, gori kawai na yi mata akan ba ta kirana, shine ta kawo ƙarana."

"An kawo ƙararka ɗin...Idan ita bata kiraka ba, kai ba za ka kira ba, har sai ka yi mata gori. To ban son haka, ka saka min yarinya ta shiga damuwa."

"Ki yi haƙuri Ammi, ba zan sake ba."

"Ka kirata ka ba ta haƙuri yanzu."

"In Sha Allah."

Girgiza kai yayi, yana yaba rigima irin ta Zahra.

#Jikargarba

******

***

AKASIN TSAMMANI

(Beyond All Odds.)

Young Talented Writers Asso...YOTA

YOTA ID/023

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol