Free chapter · Read without an account

Page 92

by Shamseeya Rabi'u Garba · AKASIN TSAMMANI (Beyond All Odds)

Driving kawai Abdul ke yi ba tare da hankalin shi na jikin shi ba. A parking spot dake harabar Imam Ali hospital yayi parking, Maryam ta buɗe back seat ta fito, fita shima yayi bayan ya kashe motar, bai tsaya jiran nurses su taho da keken tura marasa lafiya ba, ya cicciɓe Mama zuwa cikin asibitin. Wata nurse tayi musu jagora zuwa ɗakin da akwai space, suka kwantar da Mama, ba a ɓata lokaci ba doctor suka fara attending wa Mama saboda a asibitin daman take amsan treatment.

MD ne likitar dake incharge a lokacin da aka kawo Mama, yana ganinta yace; "This woman again?" Don shine ya attending mata s lokacin auren Zahra da jininta yayi wani irin mugun hawa.

Dubata yayi, ya taɓa pulse ɗinta yaji bai feeling ɗinshi, duk yadda yayi ya ji heartbeat ɗinta abun ya gagara, kallon nurse dake gefen shi yayi ya ce; "Move her to emergency."

MD yafi awa ɗaya akan Mama, amma sam ba ta responding to treatment, fita yayi daga ɗakin yana sharɓe zufa, office ɗin DR Josh ya tafi, ya kira shi suka dawo ɗakin a tare. DR Josh ma ya rinƙa gwada nasa basirar da saninsa amma to no avail.

DR Josh ya cire glasses na idonshi, yace; "Ina at this point ya kamata mu kira DR Ali."

MD ya dauki wayarsa ya dannawa Imam kira. Cikin bacci Imam ya ɗauki wayarsa dake ringing, ya saka a kunne, murya ciki-ciki yace; "MD yaya ne?"

"Sir idan ba damuwa muna buƙatar ka a asibiti, patient aka kawo, bata numfashi and she's not responding to treatment."

Numfashi Imam ya ɗan ja ta cikin wayar, yau bai da niyyar fita at all.

MD yace; "Ka ba wa ƙanwata haƙuri please, matar nan na jin jiki."

"I'm coming." Imam ya faɗa yana cire wayar daga kunnensa, guntun tsaki ya ja, ya tashi ba don ya so ba, ya nufi bathroom.

Cikin few minutes ya shirya cikin shirt da jean trouser, sai baza ƙamshi yake. Yana fita daga ɗakin shi ya leƙa na Zahra, suna bacci rungume da juna da Imam, sun lulluɓu da blanket, kallon ɗakin yayi, everywhere is very neat and tidy, daga kan table ya gan cup da kayan tea wanda hakan ya tabbatar masa da Deen ya farka shan tea ɗin dare, fita daga ɗakin yayi ya rufe musu ƙofa, yana fita falo ya gan ko ina tsaf-tsaf ga ƙamshin turaren wuta da air freshner dake tashiwa, wanda hakan ke nuni da Zahra tayi shara kafin ta koma bacci.

Pen da paper ya ɗauko, ya rubuta short note ya ajiye a gaban TV stand, ya danna paper ɗin da remote.

Yana shiga asibitin, ya kira MD ba tare da ya ƙarasa office ba, don intention ɗinsa shine yana duba mara lafiyan ya koma gida.

A ƙofar emergency MD ya tarar da Imam, ya miƙa masa hannu suka yi musabaha, cikin zolaya MD yace; "Ashe dai ƙanwana ta ita kiwo, wannan irin kyau da ƙiba haka."

Imam bai kulasa ba ya buɗe ƙofar emergency ya shiga, MD ya bi shi a baya yana dariyar tsare gida irin na Imam.

Kallo ɗaya Imam yayi wa Mama ya ganeta, oxygen da aka ɗaura mata ya kalla, da yadda ta looking so pale and sick, kamar ba ita ce few days back ta zo office ɗin shi tsaf da ita, ƙaraso bakin gadon yayi, ya karɓi stethoscope ɗin MD ya rataya. Ya kai mintuna talatin yana examining ɗinta kafin ya lalle MD yace; "waye ya kawota?"

"I think yaronta ne ya kawota, yana reception."

"Ok, idan ba su zo da kaya ba, they should go and prepare because she need to be examine for some days."

Ya ɗan kalle mama dake kwance kamar fawa, sannan ya mayar da dubansa zuwa MD dake kallon Mama shima da tausayawa, yace; "Ku cigaba da treatment da kuka fara mata, she will respond, sannan ku yi scanning ɗin zuciyarta saboda kusan abinda ya dace a yi mata."

Kai MD ya gyaɗa, yace; "Angama angon Zahra ikon Allah.

Hararar sa Imam yayi, yace; "Sunan matata ya fita a bakinka."

"Raba ni zaka yi da ƙanwata kenan?"

Girgiza kai Imam yayi, yayi gaba abinsa don ya fuskanci zolaya Imam ke ji dashi yau.

Har bakin mota MD ya raƙo Imam yana zolayarsa, Imam kuwa ya ƙi kulasa, ya shiga mota abinsa, ya bar asibitin.

Yana isa gida ya tarar da Ya Hanne da wata cousin ɗinsu daidai za su tafi, ya kalle Deen da Ya Hanne ta riƙe mishi hannu yana kuka, sai ya ce; "Tare dashi za ku tafi ne?"

Ya Hanne ta gyaɗa kai, tace; "Ammi tace mu zo mu tafi dashi, amarci ya kamata ku ci ba ɗawainiyyar yaro ba."

Hannun Deen ya riƙe, yace; "Ku yi tafiyar ku, zamu zo dashi anjima."

Zahra dake zaune shiru a falo, tana tunanin wani time Imam zai dawo, tsoron zaman gidan ita kaɗai take, gashi Ammi ta aika a zo a ɗauki Deen da ke rage mata kewa, wayarta ta ɗauka za ta kira Farida, aka turo ƙofar ɗakin, a ɗan tsorace ta ɗaga kai, ta kalle ƙofar, da mamaki take kallon Imam da ya shigo tare da Deen da yanzu su Ya Hanne suka zo suka ɗauke shi.

Hannu ta miƙawa Deen dake kuka, yazo ya rungumeta, shafa kanshi tayi tace; "Baka bi su Anty A'i ba?"

Gyaɗa mata kai yayi yana daɗa lafewa a jikinta.

Imam yayi gyaran murya, yace; "Ki shirya bayan La'asar zamu je gidan Ammi." Yana faɗin haka ya nufi kitchen don yunwa yake ji. Tea ya haɗa, ya soya sausage, ya wrapping guda uku aciki three slices of bread, ya saka a plate ya ɗora kan tray, ya ɗora shayin akan trayn. Yana fita falon yazo kusa da Deen dake kwance a cinyar Zahra ta kunna mishi cartoon, yace; "Pick one."

Deen ya ɗauki ɗaya daga cikin bread da ya wrapping sausage a ciki, yace; "Thank you."

"You're welcome." Imam ya amsa yana tafiya zuwa dining.

Har Deen ya kai bread ɗin bakinsa sai ya tuna wani abu, ya ɗago ya kai bread ɗin bakin Zahra, yace; "Gutsura Mommy."

Zahra ta girgiza mishi kai, amma ya insisting sai da ta gutsura, ta lumshe ido tace; "Delicious." Deen yayi murmushi ya kai sauran bakin shi.

Da yamma bayan sallar La'asar suka tafi gidan Ammi.

Ammi tayi musu nasiha sosai, ta kuma basu shawarwarin zaman aure. Daga gidan Ammi ya kaita gidansu, farincikin da Zahra tayi ba zai misaltu ba kamar wacce ta shekara rabonta da gidan, ta wani manne a jikin Mommy tana zuba shagwaɓa kamar wata ƴar goye, Imam ya rinƙa kallonta yana mamakin sangarta irin nata, wani abun da take yi ko Deen ba ya yinsa. A gida Musharraf yazo ya same su, shima sai wani ririta Zahran ya rinƙa yi, da suka tashi tafiya, Iya, Daddy da Mommy suka kuma yin musu nasiha da Addu'oin kariya da zaman lafiya.

Tunda suka baro gidan Zahra ta fara jin wani irin kewa ya dabaibayeta, ita kenan ba ta da abokin hira, gashi Ammi taƙi bari su dawo da Deen, ta insisting akan is too early ya dawo gidansu da zama yanzu.

Bayan auren su Zahra da sati biyu Imam ya resuming office fully, da kuma kasuwancinsa, a lokacin Mama dake ƙoƙarin kulawar MD ta ɗa ji sauƙi, rikicin da suka ɗan yi da Hajiya Turai ne ya ƙara kwantar da ita. Hajiya Turai na zargin Mama ta having affairs da ɗaya daga cikin Alhajinta a lokacin da ta zauna a gidanta ba ta nan, saboda yanzu gabaki ɗaya Alhajin ya rikice mata akan lallai Mama yake so, wanda hakan ya bala'in tayarwa Mama da hankali don shine ya fi kowa ba ta kuɗi acikin abokan shashancin nata, Haj Turai ba ta iya jure har sai Mama ta warke ta dawo gida kafin ta fuakanceta ba, har asibiti ta biya, ta fara recovering kenan tazo tayi mata tattas yadda Mama ba ta taɓa tsammani ba, jama'a sosai Haj Turai ta tarawa Mama a asibitin ranar har sai da MD ya kira ƴan sanda suka zo suka fitar da ita. Wannan abinda Hajiya Turai ta yi wa Mama shi ya ƙara tada mata sabon ciwo, Mama bata taɓa tsammanin Hajiya Turai za ta iya aikata mata abinda tayi mata ba, bata taɓa tunanin duniya za ta juya mata baya lokaci guda haka ba, kullum kwana take tana kuka, tana nadamar rayuwarta, musamman da ta fahimci a asibitin mijin Zahra take, kuma mijin Zahran ke dubata wasu lokutan, kuma Maryam da ta yi wa wulaƙancin duniya ita take jinyarta yau da tausayawa, sai taji gabaki ɗaya ta tsani duniyar da duk abinda ke cikinta. Mama bata ƙara tsinkewa da lamarin duniya ba sai da ta gan zahiri yau ita ce a kwance tana jinya, amma dukka ƴaƴanta da ta nunawa ƙauna kamar me babu wacce tazo gareta face Farida, ba wai don ba su san ba ta da lafiya ba, Nadama ne ya shige ta lokaci guda. Kullum Farida tazo dubata sai ta yi ta ba ta ƙarfin gwiwa, ta yi ta faɗa mata akan ta godewa Allah da tayi saurin nadama, sannan son duniya bai sa ta kauce masa ba, kuma Ina Sha Allah Mommy da Zahra za su yafe mata, for now ta ba da haɗin kai wa likitoci ta samu lafiya tukunna, wannan ƙarfin gwiwa da Farida ke bata a kowane lokaci ne yasa take iya ƙoƙarinta wajen ganin ta cire damuwa a ranta, ko don ta samu lafiya ta je ta bawa wanda ta zallunta haƙuri.

Yau da sassan Imam ya shirya zuwa wajen aiki, a lokacin da Zahra ta farka daga bacci ta fito har ya riga da ya tafi ko. Share-sharenta tayi ta kimtsa ko ina, tana duba time ta gan lokaci ƙarfe shidda da rabi, sai kawai ta shiga kitchen.

A gurguje ta haɗa pepper meat ɗin kaza da wainar shinkafa, ta juye su acikin ɗaya daga cikin expensive kularta, ta haɗa kunun gyaɗa ta juye a flask, ta ɗauko basket ta jera abincin ta ajiye akan tebur ɗin dining. Ɗakinta ta koma sharp-sharp ta yi wanka, ta shirya cikin abaya baƙi, ta feffesa turare, ta cire slippers shoe baƙi ta saka, ta tsaya a gaban mirror tana kallon kyau da kayan yayi a jikinta, baƙin rigar ya ƙara fito da hasken fatarta, wayarta ta ɗauka a gaban mirror ta turawa Imam message; 'Zan tafi gida please.' tana ganin sakon ya shiga ba ta jira amsarsa ba ta fita daga ɗakin ta ɗauki basket ɗin ta rufe ko ina, sannan ta fita daga gidan.

Abba ya fita zai tafi wajen aiki kenan, Anty ta sauko daga sama sanye da kayan bacci, tana ɗan hamma ta ce; "Alhaji zaka fita baka bani kuɗin wanke kan ba?"

Abba yace; "Zan tura miki."

Anty t juya baya zata koma ɗaki, Abba yace; "Yanzun a gidan nan ban da mutuncin da matana za ta yi min breakfast na ci kafin na tafi aiki?"

Anty ta juyo, tace; "Haba Alhaji wane irin magana ne wannan? Kai ɗin ne muna zaune shekara da shekaru amma kullum aka yi maka girki da ƙorafin da zaka yi, ko kace Maggi ya kasa, ko yayi yawa, shiyasa gabaki ɗaya na sare da maganar wannan girki, daɗin daɗɗawa ma ban san zaka fita da wuri haka ba."

Abba ya kaɗa kai, bai ce mata komai ba ya nufi ƙofar fita, itama ta nufi hanyar ɗakinta. Abba na buɗe ƙofar ɗakin ya kalle Zahra da zata ƙwaƙwasa ƙofa kenan, matsa gefe yayi, yana murmushi yace; "Barka da zuwa ƴata."

Zahra ma tayi murmushi ta shiga ciki, ta bi bayan Abba zuwa cikin falon, tsugunawa tayi ta gaishe shi cikin biyayya. Abba ya kalleta, yace; "Daga ina haka da sassafen nan?"

Zahra ta sunkuyar da kai, tana wasa da ƙasan veil ɗinta, tace; "Daga gida Abba, nazo na gaisheka ne."

"Madallah, Allah ya yi miki albarka ƴata."

"Aameen Abba. Na gan kamar fita zaka yi."

"Eh wallahi, amma ai zan iya jinkirta fitan tunda ƴata tazo min hira."

Murmushi Zahra tayi, tace; "Abba na yi maka breakfast, na zubo maka?"

Abba ya ce; "Wani uba kika taɓa ganin ya ƙi cin abincin ƴar shi."

Zahra tayi murmushi ta miƙe, hanyar da yayi mata kamar na kitchen ta nufa, ta ɗauko plate ta dawo farko dashi, ta zauna a ƙasa tayiwa Abba dishing abincin da ta kawo mishi.

Har cikin ran Abba yaji wani irin daɗin abincin da Zahra ta kawo mishi bai san ko dan ta kawo a lokacin da yake da buƙata bane.

A ɓangaren Anty kuwa tana hawa sama ta shirya cikin haɗaɗɗen fitted gown, da take shirin sai taji kamar magana a ƙasa, amma sai ta basar ta cigaba da shirinta. Tana fita daga ɗakinta ta fara jin hira zahiri a falo, tana saukowa ta fara bin Abba da Zahra da kallo.

Abba yayi kamar bai ganta ba, ya cigaba da cin wainarsa yana ba wa Zahra labarin ƙiriniyar Imam.

Zahra ta gaida Anty murya ƙasa-ƙasa. Anty tayi kamar ba ta ji ta ba, ta rinƙa kallon Abba cike fam da baƙin cikin yadda ya wani shareta yake ta hirarsa da Zahra.

***

AKASIN TSAMMANI

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol