Free chapter · Read without an account

PAGE 93

by Shamseeya Rabi'u Garba · AKASIN TSAMMANI (Beyond All Odds)

Sosai Abba ya ci wainar saboda ya kwana biyu bai samu abinci mai kyau haka ba. Zuciyar Anty kamar yayi bindiga ya fashe saboda haushin yadda Abba ke cin abincin kamar wani mayunwaci, salon yarinya ta raina su.

A ɓangaren Imam kuwa ya dawo daga ward check kenan, ya ɗauki wayarsa zai kira MD ya ji ya jikin patients dake ɗayan branch dake under control ɗinsa, sai ya gan message ɗin Zahra, sai ya kira lambarta yaji me za ta je yi a gida. Tana ɗagawa kafin tayi magana muryar Anty ya fara ji tana faɗin; Wai me haka Alhaji?

Zahra na faɗin hello, yace; "Ina kike?"

"Na tafi gida gaida Abba." Ta amsa honestly.

"Da uban wa yace ki tafi!?"ya daka mata tsawa.

Rikcewa Zahra tayi ta fara kame-kame; "Errm...daman...nayi....errm" sai kawai ta katse kiran.

Miƙewa Imam yayi, ya ɗauki key ɗin motarsa ya fita daga office, hanyar gida ya ɗauka direct, don yana gudun Anty ta yi wa Zahra irin maganganunta da basu da filter.

Abba ya kalle Zahra dake zazzare ido, yace; "Ya ce ki koma gida ko?" sai yayi murmushi, ya cigaba da faɗin; "Daman na san ba da sanin shi kika zo ba, da ya sani ba zai bari ba."

Zahra tayi ƙoƙarin controlling kanta, ta ƙaƙƙalo murmushi, tace; "Bai ce na koma ba fa?"

Abba ma yayi murmushi kawai, don ya fi ta sanin waye Imam, daga ya gan yadda ta rikice lokaci guda ya san faɗa yayi mata akan zuwan da ta yi, don ya san dama  Imam na neman dalilin yanke alaƙa dashi ne, kuma yana son yayi amfani da daman shi yanzu.

Zahra kuwa a zuciyarta tana son ta fahimci abinda Abba ke nufi da idan Imam ya san zata zo nan zai hanata.

Anty da Abba ya ƙi kulata, duk yadda taso yin rigima dashi a gaban Zahra, ya ƙi ba da daman hakan, taɓe baki tayi, tace; "Allah ya taimake ki kar ya lakaɗa miki na jaki yau tunda kika zo gidan maƙiyansa."

Abba yayi mata harara, itama ta galla masa hararar, tace; "Ai ba ƙarya na yi ba. Abu da mashayi kuma, ai mai kwatarta yau sai Allah."

Wani irin zafi Zahra ta fara ji a zuciyarta, amma tana ganin ya fi dacewa ta manna wa Anty hauka, tayi kamar ba ta fahimci akan wa take magana ba, ta sunkuyar da kanta kawai tana latsa wayarta. Abba ma kiran shi aka yi a waya, ya receiving call ɗin.

Yana wayar Imam ya shigo, ko sallama bai yi ba, ya kalle Zahra da ta ɗago kai sakamakon buɗe ƙofar da aka yi, yace; "Tashi mu tafi gida."

Zahra ta maƙe kafaɗa tace; "Ni ban gama hira da Abba ko ba, kayi tafiyar ka idan na gama zan zo."

Imam ya kalleta, sai ya juya baya zai fita, Abba dake waya amma yana jin su, yace; "Tsaya Imam." Cak Imam ya tsaya ba tare da ya juyo ba. Abba ya lalle Zahra, yace; "Tashi ki bi mijinki ƴata, nagode da abinci kuma naji daɗin shi sosai, Allah ya yi miki albarka."

"Aamen Abba." Ta furta a hankali, ta tattara basket ɗinta, ta bi bayan Imam da yayi gaba.

Bai ce mata komai a hanya ba, har sai da suka iso gida, ta nufi hanyar ɗakinta za ta shiga, sai yace; "Kar ki sake tafiya gidan nan."

Juyowa tayi da mamaki, tace; "Meyasa."

"Na dai faɗa miki, idan kika ƙi ji kuma duka abinda aka faɗa miki, ko aka yi miki to kiyi kuka da kanki."

Zahra ta zumɓura baki, tace; "Ni kam naji daɗin hira da Abba yau, kuma gobe ma ina son na tafi."

Matsowa dab da ita yayi, ya riƙe kunnenta amma ba da ƙarfi ba, yace; "Kince baki jin magana ko, to ki tafi, amma idan shashashar matar nan ta gaya miki wata magana don't dare come and cry in this house, don rufe ki zan yi a wajen sai kin gama kukarki kafin ki shiga min gida."

Yana faɗin haka ya sake mata kunne yayi gaba.

"At least you should have greet Abba, ko ba komai mahaifinka ne." Zahra ta faɗa ba tare da wani tsoro ba.

Juyowa yayi, ya kalleta straight into the eyes, yace; "Ba ke zaki faɗa min abinda zan yi ba, I know rights and wrong."

Ba tare da ta cire idonta daga nashi ba, tace; "I doubt if you know, Mahaifi ne fa, amma babu komai Allah ya sa kaima kana da ɗan nan, kuma Kama tudini gidan, zaka ji daɗi ko ɗacin abinda kake yi." Ta raɓa ta gefen shi ta shige ɗakinta.

Imam ya kasa motsawa daga inda Zahra ta bar shi a tsaye, mamaki ya hana shi kwakwaran motsi, tunda yake babu wanda ya taɓa yi mishi magana akan shi da Abba sai Ammi da kuma Sa'ud, su ɗin ma ba su taɓa mishi yadda Zahra ta fito mishi yau ba, babu wanda ya taɓa saka ɗanshi a maganar nan sai ita. "Wai ma yaushe yarinyar nan ta san Abba ne, ta san me Abba ya yi min a rayuwar nan, ta san irin riƙon agola da aka yi mishi a gidan ubanshi kuma akan idon uban nashi, ta san cewa duk halin da ya shiga yau saboda sanadiyyar mahaifinshi ne, ina ruwanta da duk yadda ya treating mahaifinshi." duk a ransa yake wannan tunanin, rai ɓace ya bi ta zuwa ɗakinta, buɗe ƙofar yayi ba tare da sallama ba. Zahra ta tuɓe riga kenan, ta ɗora towel za ta shiga bathroom ya shigo, juyowa tayi, tana ganin shi, ta nufi wardrobe da sauri, fisgota yayi, tayi tangal-tangal kamar zata faɗi, ya tarota, ya riƙe kafaɗunta.

Zahra ta fara turjewa, ta ce; "Me haka? Ka sakeni mana."

Kallonta yayi strictly, yace; "This should be the first and last time da za ki ƙara involving kanki akan abinda bai shafe ki ba," ya saketa yana jifarta da mugun kallo. sai da ta ɗan ja da baya kafin tace; "Daman gaskiya ɗaci gareta, ban yi mamamkin reaction ɗinka ba."tana faɗin haka ta shige bathroom da gudu.

Duk da yadda maganganunta suka ɓatawa Imam rai hakan bai hana shi lura da fine body structure ɗinta ba, da kuma fatarta mai kyau da sheƙi, guduwar da ta yi zuwa bathroom ne ya ƙara tafiyar da imaninsa yadda mazaunanta suka yi wani irin rawa, guntun tsaki ya yi, ya fita daga ɗakin.

Leƙa ɗakin Zahra tayi, ta tabbatar da Imam ya bar ɗakin kafin ta fito daga bathroom ɗin, murmushi tayi, ta tafi gaban wardrobe ta cire kayan da zata saka.

Imam na fita daga ɗakin zuwa falo, zai fita ya koma office kenan ya hangi basket ɗin abincin da ta kaiwa Abba, duƙawa yayi gaban basket ɗin, ya buɗe kulolin abincin, ƙamshin pepper chicken ya daki hancinshi, instead of fita da zai yi, sai ya tafi kitchen ya ɗau plate ya ɗebi raguwa wainar kaɗan a plate ya zuba pepper chicken ɗin kaɗan daga gefe. Daɗin da abincin ya yi wa Imam bai san lokacin da ya ƙara ba, sosai ya ci ya suɗe plate, bai taɓa tunanin Zahra ta iya girki haka ba, a tunanin shi shagwaɓa kawai ta iya, amma a yau ya fahimci cewa ta iya sa kai a abunda bai shafeta ba, kuma ta iya girki. Miƙewa yayi, ya ɗauki ruwa a fridge, ya fita daga gidan.

Zahra na gama shiryawa cikin doguwar riga mara nauyi ta fito falon don cin ragowar wainar Abba, amma to her greatest surprise ta tarar da empty kula, murmushi kawai tayi don ta tabbata babu wanda zai ci sai Imam, tunda su biyu ne a gidan. Kitchen ta shiga don neman abun da za ta ci, a sink ta gan plate ɗin da yaci wainar a ciki, wanke plate ɗin tayi ta ajiye a wajen zamansa, sai ta ɗora indomie a wuta. A kitchen a wajen ta jira indomie ɗin ya yi, ta juye a plate ta dawo falo, TV ta kunna, tana cin abincinta tana kallo.

Da rana jollof rice da wake da ya sha bushashen kifi tayi, da cucumber juice, sai da ta kimtsa kitchen ɗin tsaf kafin ta shiga ɗaki yin sallar azahar. Tana idar da sallar azahar, akan darduman ta kunna data ɗinta, message ta turawa Imam;'Wani lokaci zaka dawo?'

Message ɗin na shiga ya buɗe, kamar ba zai reply ba da farko, sai ya tura mata; 'Ban sani ba.'

Zahra na ganin reply ɗinsa ta kashe datar ta, ta miƙe daga kan darduman. Kitchen ta nufa ta packaging lunch a basket biyu, ta kira delivery man da ke kawo mata abinci a office wasu lokutan idan aiki yayi wa Musharraf yawa.

Mayafi ta yafa ta fita wajen gate ɗauke da basket biyun. Delivery guy ɗin ta bashi, tace; "Gidan mu zaka kai ɗaya, ɗayan kuma za ka kai wajen aikina, ka bawa DR Ali, kace inji matar shi, ga lambarsa nan." Ta faɗa tana karanta masa lambar Imam.

Ba wai reply ɗin Imam bai ɓata mata rai bane, amma ba yanzun zata rama ba, a hankali za ya dafa shi da ruwan jikinsa, shi yasa ta aika masa da abinci tunda ta riga da tayi niyya.

Imam na office, receptionist ta ce mishi yana saƙo, amma delivery guy ɗin na neman isowar kawo saƙon da kansa. Duk da Imam ba ya expecting wani saƙo, amma yace a shigo da shi.

Imam was more than surprise da mai delivery yace masa saƙo daga Zahra, amma bai nuna hakan a fuskarsa ba, godiya yayi wa mai delivery, zai biya shi, yace Zahra ta riga da ta biya shi. Mai delivery na fita, Imam ya buɗe kulan, lumshe idonsa yayi saboda ƙamshin busashen kifi da spices da ya daki hancinsa, kawai sai ya ji amsar da ya bata ɗazun bai dace ba, wayarsa ya ɗauka, sai kuma ya ajiye wayar kawai. Plate ya ɗauko ya ɗeba shinkafar enough, a hankali ya fara taunar abincin yana lumshe ido, da ya gama cin shinkafar sai ya kora da cucumber juice that was so natural and taste nice.

Sai da ya cinye abincin da ke kular tas, a da yana tunanin bai da ci, amma yanzu ya tabbatar saboda bai samu dama bane.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol