Free chapter · Read without an account
PAGE 97
by Shamseeya Rabi'u Garba · AKASIN TSAMMANI (Beyond All Odds)
Lectures Ya A'i ta ba wa Zahra akan yadda ake saka namiji ya bayyana abinda ke ransa dole, ko da kuwa bai shirya ba. Wani abin idan ta faɗa har rufe ido Zahra ke yi saboda kunya, Ya A'i ta buge mata hannu tace; "Ai kin gan irinta ai, wannan kunyar zai kai ki ne ya baro ki. Shi kunya abu mai kyau ne amma akwai lokacin da bai da amfani. Ni dai na riga da na faɗa miki abinda ya kamata ki yi, idan kin yi for your own good, idan kuma kin tsaya kunya kanki kika yi wa."
Abinci mai aikin Ya A'i ta kawo musu, a shago a wajen suka ci abincin, suna ci suna hirar su kamar Yaya da ƙanwa. Bayan La'asar Ya A'i ta kira Imam ta tambaye shi ko ya kusa zuwa ɗaukar Zahra, yace A'a sai bayan Maghrib, Ya A'i tace; "Yauwwa, sai ka tura kuɗi zan kai matarka saloon."
Imam yace; "kamar nawa zan tura."
"Ko 500k ka tura ai baka faaɗi ba, tunda matarka za a gyara."
Katse kiran yayi, immediately ya tura musu 500k ɗin.
Ya A'i na gani ta nuna wa Zahra alert ɗin tace; "A hakan ne bai son ki? Kawai dai mutum ne shi da bai fiye gane abinda yake so da wuri ba."
Zahra dai ba ta ce komai ba, amma ta yi mamakin 500k for just gyaran gashi.
Cikin gida Ya A'i ta shiga, ta ɗora after dressing akan kayan hukunta, sannan ta shirya yaranta suka fita a tare.
Babban haɗaɗɗen saloon na manyan mata Ya A'i ta kai su, da kanta ta yi driving, Zahra na gefenta, yaran kuma na back seat.
Tun a reception aka yi musu tarɓa mai kyau, aka kawo musu abin motsa baki, su Akram sai tsalle-tsallen su suke yi, Ya A'i na gefe tana chatting da mijinta da ba ya ƙasa, Zahra kuma an shigar da ita main wajen da Za a gyara mata gashi. Ya A'i ce ta tafi payment department, ta biya kuɗin abubuwan da za a yi wa Zahran, sai ta zo ta miƙawa wacce take incharge.
Zahra ba ta san ba iya gyaran gashi za a yi mata ba sai da aka shigar da ita main place ɗin, ta saba tana zuwa irin haɗaɗɗen saloon haka, amma ba ta taɓa sanin da akwai waje irin haka a Kaduna ba. Daga gyaran gashi, Zahra ta gan an zarce pedicure, da sauran abubuwa. Full body spa aka yi mata, ba su suka bar saloon ɗin ba sa maghrib, Zahra ta koma kamar wacce aka saka a inji aka ciro, fatarta ya ƙara wani haske da sheƙi, tafin ƙafarta da hannunta kuma kar na jarirai.
Ya A'i na shiga gida ta hango motar Imam a parking space, murmushi tayi ta ce; "Mijinki is here to pick you, ni da nake tunanin kiransa nace masa ya barki zuwa gobe."
Suna shiga cikin gidan, su ka gan shi a falo yana kallon film yana shan fruits salad.
Ya A'i ta zauna a gefenshi tana faɗin; "Waaash!"
Akram da Ikram kuwa suka faaɗa jikin shi, Zahra ta zauna a kujerar dake opposite ɗinsu, tace; "Ina wuni Yaya."
Ɗan kallonta ya yi, yace; "Lafiya."
Ya A'i ta ja mishi kunne, tace; "Very unromantic, babu ya gajiya wifey ko sweetheart, sai wani lafiya kamar boss."
Cire hannunta ya yi daga kunnensa, yace; "Ya A'i please leave me, kece za ki faɗa min abinda zan cewa matana."
"I'm just teaching you how to be romantic." Ya A'i ta faɗa tana miƙewa zuwa dining.
Zahra ma ta miƙe, tace; "Ya A'i I want to shower please."
Ya A'i ta kalle Akram da ke kallon abu a wayar Imam, tace; "Lead your favorite uncle's wife to my room. Akwai sabon towel a wardrobe ɗina ki ɗauka, sannan in ki duba kayan da zai sizing ɗinki a cikin kayana ki saka." Ta ƙarasa faɗa tana kallon Zahran.
Zahra ta bi bayan Akram da ya riga da yayi gaba abinsa.
Bayan ta fito wanka tayi shafe-shafenta da kayan Ya A'i, sai ta zauna a gefen gado tana replying messages ɗin Farha, tana wannan yanayin ɓarawon bacci ya saceta.
Shiru-shiru Zahra ba ta fito ba, har aka fara kiraye-kirayen sallar Isha, Imam ya kalle Ya A'i, yace; "Ki kirata ta fito mu tafi, dare na yi."
Ya A'i ta tashi, ta tafi ɗakinta, daga bakin ƙofa ta tsaya tana kallon Zahra dake baccinta hankali kwance, sai kawai ta juya baya ta koma falo.
Tace; "Tana bacci, I can't wake her, is better ka tasheta da kanka full of love."
Ɗan guntun tsaki Imam ya yi, ya miƙe ya nufi ɗakin Ya A'i don idan ya biyewa Ya A'i she will make him run mad.
Rufe ƙofar ɗakin ya yi a hankali bayan ya shiga ɗakin, daga bakin ƙofar ya tsaya yana ƙurewa Zahra kallo, tun daga kanta da ta sa shower cap, har zuwa yatsun ƙafarta, sai sheƙi spotless caramel skin ɗinta ke yi, A hankali ya ƙaraso gaban gadon, yana jin yadda kansa ya fara sara masa, idon shi ya sauya launi zuwa ja, ba zai iya tantance abinda ke damunshi lokaci ɗaya haka ba.
Pillow da Zahra ta ɗora kanta ya ɗan bubbuga, Zahra ta buɗe idanunta da suka yi mata nauyi saboda bacci da gajiya, tana ganin wanda ke kanta ta buɗe idon taaar.
Imam da ya ja gefe yana kallonta, yace; "Tashi mu wuce gida, it's getting late."
Har Zahra za ta miƙe, sai ta tuna towel ne fa kawai a jikinta, towel ɗinma ɗan karami wadda da ƙyar ya wuce mazaunanta, sunkuyar da kai tayi, she could feel his eyes all over her, waige-waige ta fara yi tana neman abinda za ta rufe jikinta dashi, amma unfortunately babu bargo akan gadon.
"Get up and dress, you're wasting my time."
Zumɓura baki Zahra ta yi, ta marairaice fuska kamar za ta yi kuka, tace; "To a ganka zan shirya ne?"
Matsowa dab da ita yayi, ya ɗan sunkuya, ya riƙe kafaɗunta, ya ƙare mata kallo tun daga sama har ƙasa, yace; "I paid for it, didn't I?"
Zaro ido Zahra tayi, ta tureshi, ta cire bedsheet na kan gadon ta rufe jikinta, tace; "Pay for what?"
"You." Ya ba ta amsa kai tsaye.
Yana faɗin haka ya juya baya ya fita daga ɗakin, ya ba ta daman saka kaya."
Abaya baƙi ta ɗauka a wardrobe ɗin Ya A'i ta saka, cas ya zauna a jikinta kamar daman nata ne.
Tana fita falon ta zauna kusa da Ya A'i, ta kwantar da kanta a kafaɗarta, Ya A'i ta shafa kanta, tace; "Ko zaka barta ta kwana a nan ne yau?"
Zahra tayi saurin cewa; "To wa zai ba wa Abba abinci idan na kwana a nan?"
"Wani Abban." Ya A'i ta tambaya.
Imam ya taɓe baki, yace; "Ai ta riga da ta ɗau wa kanta aikin da sai tayi da ta sanin farawa, tashi mu tafi " ya faɗa yana kallon Zahra.
Ya A'i ta tsare Imam da ido, tace; "Wane Abba shine tambayar da na yi Imam."
Imam da ya riga da ya miƙe, yace; "Abban ku."
Ya A'i ta kalle Zahra, tace; "Matarsa ba ta nan ne?"
Zahra ta sunkuyar da kai, tace; "Tana nan, amma na gan Abba na son abincin da nake kai mishi, babu ranar da zan kai masa da ba zai ci ba, ya kuma saka min albarka. With clean intention na fara kai wa Abba abinci, amma sai na lura Anty ba ta feeding ɗin Abba yadda ya kamata, ba wai ina musu shishigi bane, a'a, kawai na ɗauki Abba a matsayin mahaifina, ina sa ido akan duk abinda ya shafe shi shiyasa na fara gano wasu abubuwan."
Ya A'i da maganar Zahra ya yi grabbing attention ɗinta, ta kalle Imam ta ce; "Gobe za ka kawota ai?"
Kai ya gyaɗa mata. Ta kalle Zahra, tace; "We will talk about this tomorrow."
Kai Zahra ta gyaɗa mata, ta bi bayan Imam suka fita daga falon gidan.
Zahra na kitchen tana haɗa spaghetti da Vegetable sauce da za a kai wa Abba, Imam ya shigo kitchen ɗin, ya ɗauki cup, yazo gefenta ya ɗauraye cup ɗin a sink, ruwa ya tara a electric kettle, ya jona, sannan ya ja gefe yana jiran ya yi tafasa, kallon Zahra dake aikinta kamar ba ta san da mutum a wajen ba yake yi, mamakin yadda yau ɗaya ta canza yake yi, aside fresh da glowing da ta ke, fuskarta doesn't look sad like few days back da ya hana ta zuwa wajen Abba.
Tana zuba jajjagen attargu da za tayi sauce dashi a mai Imam ya fara tari. Tari yake sosai da har saida ya kware, fita daga kitchen ɗin ya yi yana kan tarin. Rage wutar gas ɗin Zahra ta yi, ta ɗauki ruwa a fridge da cup ta fita falon, ruwan ta tsiyaye a cup, ta miƙa masa cup ɗin. Sipping ruwan ya yi sosai, amma bai tsayar da tarin ba. Zama tayi a gefensa ta fara bubbuga masa bayansa a hankali, a hankali ya ɗora kansa a cinyarta, wani iri Zahra ta ji a jikinta, amma sai ta daure ta cigaba da patting ɗinsa a hankali kamar ɗan baby, tun yana tarin har ya subside, gyagyaɗi ya fara yi a ƙafarta, a hankali ta ɗaga kansa ta ɗora akan ɗaya daga cikin throw pillows dake kan cushion, ta miƙe tana faɗin; "I need to check my food before it burns."
Hannunta ya riƙe, yaji yadda yake da taushi kamar na jaririya, yace; "Thank you."
Murmushi ta yi masa, tace; "You're welcome."
Kitchen ɗin ta koma, tayi packaging abincin, ta juye ruwan zafin da Imam ya saka a kettle, ta kawo masa dining, daga dining ɗin tace; "Ga ruwan zafin."
Kai Imam ya gyaɗa mata, don they can see each other.
A hankali ya miƙe ya tafi dining area ɗin, ya haɗa hot chocolate, ya fara sha kenan Zahra ta fito da basket ɗin abincin Abba, tace; "I don't know if you can manage to take this to Abba?"
Kai ya gyaɗa mata, yace; "I will."
Zuciyarsa ta fara tempting ɗinsa ya riƙe hannun Zahra again, he felt comfort lokacin da ya kwantar da kansa a cinyarta tana patting dinsa, and he felt warmth a lokacin da ya riƙe hannunta.
Da sauri ya kawar da kanshi daga kallon da yake mata, ya cigaba da sipping hot chocolate ɗinsa, Ita kuma ta wuce ɗakinta.
***
AKASIN TSAMMANI