Free chapter · Read without an account
PAGE 96
by Shamseeya Rabi'u Garba · AKASIN TSAMMANI (Beyond All Odds)
Imam kasa shanye hot chocolate ɗinsa ma yayi, ya tura sauran gefe, sai da ya shiga ɗakinsa ya ɗora jallabiya akan threequatre wando dake jikinsa kafin ya ɗauki basket ɗin abincin Abba ya fita dashi.
A lokacin da Imam ya kawo wa Abba abincin, har Abba ya riga da ya kwanta ko, don da sauri yake kwanciya, anty ya tarar a falon tana kallon film tana shan juice.
Kamar ya ajiye basket ɗin ya yi tafiyarsa, amma sai ya sauya tunani, ya san tabbas idan ya ajiye abincin nan Anty most eat from it, shi kuma matarshi ba baiwarta bace da zata girka mata abinci.
Wayarsa ya ciro daga aljihunsa, ya dannawa Zahra kira, tana picking yace; "I'm coming back with the food saboda Daddy ya kwanta ko "
Zahra ba ta ji daɗin hakan ba, amma sai tace; "Toh."
Anty ta rinƙa kallon Imam da mamaki, ta kasa yarda wai Imam ne yau mace ke yi masa aike kuma ya tafi.
Har Imam ya fita daga falon ya nufi gate, kiran Zahra ya shigo, tace; "Please do me a favor, ka duba dining area da kitchen ka gan ko anyi girki a gidan, if no, please ka tashe shi ya ci abinci kar ya kwana da yunwa."
Imam ya koma cikin gidan, don he can't wait ya gan kansa a gida, wani kalla yake jin kansa, yana shiga gidan upstairs ya nufa direct da Basket ɗin, Anty ta bi bayan shi da sauri, ya shiga falon Abba, har zai shiga bedroom dinsa, ta sha gabansa, tace; "Lafiyarka? Ko kanka ba ɗaya ba, ta yaya zaka wuce Ni a falo kazo zaka shigar min dakin miji, idan ma wannan shegen jagwalgwalon abincin da bazawarar matarka ta aikoka dashi ne ai ka bari har san da zai fito ko, ba wai ka ta dashi ba."
Hannu ɗaya Imam yasa ya tureta daga gabanshi, aukuwa ta fadi warwas a ƙasa, ai kuwa ta kurma ihu ta fara zage-zage, ya shige dakin ba tare da ya juyo ya kalleta ba. Yana shiga ɗakin daidai lokacin da Abba ya gama saka jallabiyya, don daman ba bacci yake yi ba, ya dai kwanta ne kawai, yana fara jin hayaniyar Anty ya miƙe ya fara saka jallabiyya don ya fita ya gan ko ita da waye a wannan daren, yana ganin Imam ya ce; "Me ya faru?"
Imam ya ajiye basket ɗin hannunsa akan table ɗin ɗakin, yace; "Abinci na kawo maka."
Anty da ta lallaɓa ta tashi saboda yadda take jin jikinta kamar ba nata ba, faɗuwa sosai tayi ba na wasa ba. Ta shiga ɗakin ta fara faɗa; "Wallahi Alhaji ka ɗauki mataki akan ɗanka, idan ba haka ba wallahi ƴan sanda zan haɗa shi da su."
Abba ya kalle Imam, yace; "What have you done this time?"
Kai tsaye Imam ya ce; "Turata na yi da ta tsaya min a hanya, saboda kamar ta mance matsayina a gidan nan, I feel it's high time na tuna mata cewa na ɗin gidan uba nane, ba agola bane ni, ko da yake dama aka bata."
Har ya gama maganansa Abba na kallonsa, sai da ya gama tukuna yace; "Ka ba ta hakuri Imam."
Imam ya kalle Abba da mamaki, me yayi mata da zai bata haƙuri,on the other hand kuma ba abin mamaki bane tunda daman matarsa ba ta lefi, cikin tsananin ɓacin rai yace; "Ki yi haƙuri."
Anty ta folding hannun a ƙirjinta tana karkaɗa ƙafa, ta kalle Abba tace; "Se me idan ya bani haƙuri? ai ba yau ya fara ba da haƙuri ba, amma idan ya tashi wani rashin mutuncin sai ya fi na da, don haka mataki zaka ɗauka akan shi ko dai na kai shi ƙara wajen da za a ɗau min mataki akansa."
Abba ya kalleta sosai, yace;" Wanne irin mataki kike son na ɗauka akansa?"
Anty ta nemi waje ta zauna, cike da isa, tace; "Ka ja mishi layi da shigowa gidan nan, daga shi har matarshi da ba ta da kunya."
Imam ya juya zai fita daga ɗakin, Abba ya ce; "Come back here." Sannan ya kalle Anty, ya ce; "Ba zan iya yin abinda kika buƙata ba."
Anty tace; "Na san matakin da zan ɗauka, idan ya fi karfinka ai bai fi ƙarfin hukuma ba, don haka duk abinda nayi masa kar ka gan laifina."
Abba na kallonta cikin idonta yace; "Ki yi duk abinda zaki iya yi Sakina, har gaba da hukuma ki kai ƙara. Imam serve me." Ya faɗa yana kallon Imam
Imam ya durƙusa ya buɗe kulolin abincin, ya zuba a plate ya ajiye akan side drawer kusa da Abba. Anty ta rinƙa kallon Abba da mamaki, ta kasa yarda wai yau itace Abba ya zabi ɗansa akanta, "Ya zama dole na ƙara shiri." Ta faɗa a zuciyarta tana mai miƙewa da ƙyar saboda yadda jikinta ke ciwo, ta fita daga ɗakin cike da baƙin ciki da mugayen ƙudirori.
__________
Mama ta ji sauƙi sosai har an sallameta daga asibiti, sai dai an ɗorata akan magunguna saboda zuciyarta da ta kamu da ciwo.
Tun ranar da aka sallameta take roƙon Abdul da ya kaita gidan Zahra ta nemi yafiyarta, amma ya ce ta bari jikinta ya ƙara ƙarfi tukuna.
Da ta ɗan ji ƙarfin jikinta, Abdul ya ɗauketa zuwa gidan Alhaji Bashir first, saboda tace tana son ta bawa Mommy da Daddy ma hakuri, ta kuma nemi yafiyarsu, amma a bakin gate Maigadi ya hana su shiga, yace umarnine aka ba shi kar ya ƙara barin Mama ta shiga gidan, Abdul ya Ciro wayar shi ya kira Daddy, amma sa sam Daddy ya ƙi amince Mama ta shiga gidan shi, haka suka juya baya suka koma gida. A ranar ba ƙaramin kuka Mama tayi ba, ya tabbata ta riga da ta lalata rayuwarta, ta yi amfani da hannunta wajen ruguwa rayuwarta, ba ta iya tafiya gidan Zahra ba ma, ta sa Abdul ya mayar da ita gida kawai akan wata rana sai ya kaita gidan Zahran don yanzu kam baza ta iya fuskantar ta ba.
Tun kafin Mama ta samu damar tafiya gidan Zahra, Farida ta kan tafi ta yi ta roƙar Zahra akan ta gafarta wa mahaifiyarta, t faɗa mata akan tabbas Mama tayi nadama, kullum idan Farida ta kawo maganar sai Zahra tace babu komai, komai ya wuce.
Yau Mama ta tashi da shirin fuskantar Zahra, ta tashi da kwarin gwiwar ɗaukar duk abinda Zahran za ta yi ko ta faɗa mata yau, Farida ta kira tace ta sanar wa Zahran suna zuwa yau.
Ko da Farida ta faɗawa Zahra,cewa tayi Allah ya kawo su lafiya.
Daman har Zahra ta shirya za su tafi gidan Ya A'i, sai kawai ta kalle Imam dake cire key daga jikin ƙofa ta ciki, tace; "I think you should just go alone, saboda zan yi baƙi, Farida is coming with my stepmom."
Kallonta Imam ya ɗan yi, yace; "It's alright, sai na dawo."
"A dawo lafiya."
Kitchen Zahra ta shiga ta ɗora girki da za ta tarɓi su Mama dashi. Rice and Stew ta dafa musu, ta arranging komai akan dining table. Tana zaune tana kallon wani India series kiran Farida ya shigo, tana picking Farida tace; "Muna gate."
Katse kiran Zahra tayi, ta fita zuwa gate, ƙaramin ƙofar ta buɗe ta fito, ta gefen Ya Abdul ta zo, tace; "Yaya sai ka fito fa, gate ɗin da nauyi ba zan iya buɗe ba."
Murmushi Abdul yayi, yace; "Lakwamiya kawai." Ya buɗe motar ya fito, Zahra ta shiga driver's seat ɗin tana murmushi.
Abdul na buɗe gate ɗin ta ja motar zuwa ciki, tayi parking a gefen ɗayar motar Imam dake parking space.
Ta buɗe motar ta fita daidai lokacin da Abdul ya gama rufo gate ɗin ya buɗe su.
Gaishe da Mama Zahra tayi tana kallon yadda Maman ta rame kamar wacce tayi rashin lafiyar shekaru.
Bata ƙara shan mamaki ba sai da ta ji yadda Mama ke amsa mata cikin kulawa, kamar dai ba Mama da ta sani ba.
Hannun Abdul ta riƙe suka ti gaba tana faɗin; "Ai na yi fushi da kai, ba ka taɓa zuwa gidana ba sai yau."
Hancinta ya ɗan jan, yace; "To me zan zo in miki Zahra idan ba neman magana ba."
Zumɓura baki tayi tana jan hannunshi, Abdul ya ce; "Zahra rigima."
A falo suka zazzauna, Zahra ta kawo musu ruwa da lemu, ta harare Farida dake kallona, tace; "Kallon na menene haka?"
"Kar na kalleki kuma?" Farida ta faɗa tana murmushi.
Zahra tazo ta zauna dab da ita, ƙasa-ƙasa yadda Faridar kaɗai za ta ji, tace; "Na me za ki kalleni, ko ke ce Imam Ali?"
Farida ta riƙe baki, tace; "Lallai kam matar Imam."
Mama kuwa sai kallon Zahra take yi, zuciyarta fal nadamar abubuwan da ta rinƙa yi mata, yanzun ta ƙara tabbatar Zahra is just an innocent little girl that deserves nothing but pure love, duk da abubuwan da ta rinƙa yi wa Zahran kalle yadda ta tarɓeta kamar babu abinda ya faruwa a tsakanin su. Hira aka ɗan taɓa kaɗan kafin Zahra ta jagorance su zuwa dining, ita da kanta ta yi serving Mama abinci kafin any other person dake wajen, duk da a zuciyarta mamaki take na yadda Mama ya saukalo lokaci guda, amma sai ba ta nuna hakan a fuskarta ba, ta dai cigaba da biye mata a yadda ta zo.
Tana kuma lura da yadda Mama ta kasa sake jiki taci abinci, sai tace; "Mama ko dai wani abun kike so, na gan kin kasa cin shinkafar."
Kai ta girgiza, tace; "A'a wannan ɗin ya yi."
Bayan an kammala cin abincin, Zahra da Farida suka clearing dinning ɗin kafin suka dawo falo.
Mama tayi ƙarfin hali ta fara magana; "Zahra na zo ne don na baki haƙuri akan duk abubuwan da suka faru a baya, na san na cutar dake sosai, wasun ma ba ki san na miki ba, don Allah ki gafarce Ni." Ta ƙarasa faɗa hawaye na gangarawa a idanunta.
Zahra ta riƙe hannuwanta tace; "Komai ya wuce Mama, daman sheɗan ne yake neman shiga tsakanin mu, amma wallahi komai ya wuce, kuma na daɗe da faɗawa Farida komai ya wuce, ki daina saka damuwa a ranki please."
Mama ta rungume Zahra ta fashe da kuka, Zahra ta cigaba da lallashinta tana jaddada mata akan ba ta riƙeta a zuciya ba, kuma tana da tabbacin a wajen Mommy ma komai ya wuce.
Ini su Mama suka yi wa Zahra, don Abdul tafiya ya yi ya bar su, sai gab da maghrib ya zo ya ɗauke su.
A ɓangare Ya A'i kuwa bata ji daɗin rashin zuwan Zahra ba, don ta kwana da tunanin halin da mahaifinsu ke ciki, ta so ta ji abinda Zahra ta noticing dashi but unfortunately Zahran bata zo ba, hakan ya sa ta shirya kayanta kala biyu, ta kira mijinta ta nemi izini akan za ta tafi gidansu ta yi kwana biyu, ya ba ta dama.
Da yamma ta kwashi yaranta sai gidan Abba.
***
AKASIN TSAMMANI