Free chapter · Read without an account

Chapter 1

by Salis M Reza · ƳAN MATA

*ƳAN MATA 1*


_By S Reza...✍️_

*🥏Whasop Channel*


*TSOKACI!*
_Labarin Ƴan Mata ƙirƙiraran labari ne. Sannan gajere. Jan hankali ne ga ƴan mata masu tunani irin na waɗannan ƴan matan dake cikin wannan labarin. Ina fatan Allah ya bani ikon rubuta abun da zai fahimtar da al'umma._

_Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai_

*Chapter 1️⃣*

Kallonta tayi cike da gajiyawa ta ce "Na gama magana muddin na isa dake to ban yarda kije ba, idan kuma ban isa dake ba to ga hanya nan" Uwar tata ta faɗa tana cigaba da cin dabinon dake hannunta. Siyama ta sake lanƙwaɓe murya kamar zatayi kuka ta fara faɗin "Yanzu shekenan gaba ɗaya ƙawaye na zasu je sai ni kaɗai ce za'a hana, kowacce fa an barta a gidan su, kuma kwana ɗaya kawai zamuyi, shine ni za'a ce ba zanje ba, ni dai Allah sai naje kwana ɗaya kawai da mutum zai yi sai an hana shi kamar wata karamar yarinya". Ta faɗa tana kafe uwar da ido kamar zata yi kuka. Matar ta ɗan gyra zamanta kasancewar tana cikin hali na ciwon ƙafafu da suke hana ta takawa da kyau. Ta sake faɗin "Siyama yanzu kamar ke zan bari ki tafi har wani gari wai zuwa rakiyar amarya? Gaba ɗaya nawa kike da kike cewa sai kace yarinya, to ko a nan cikin gari ne ba zan bari kije ki kwana ba bare har wani gari, kuma suma sauran ƙawayen naki sai dai ko sunfi ƙarfin iyayensu ne, amma babu uwar da zata bar yarinya kamar dai ku zuwa wani gari da sunan rakiyar amarya, a nan ma yaya aka ƙare daku da shegen rawar kan ku da giggiwa". Siyama ta ce "Wai Umma kina ta cewa wai kamar mu, to mu ɗin yara ne, ƙawarmu ce fa tayi aure, shine har yanzu a yara muke, sannan wallahi Umma gaba ɗaya kowacce an barta a gida, ai ba dadewa zamuyi ba, kuma ai a kwai ƴan uwan su Abida a Kadunan a cen zamu kwana fa idan mun je" Siyama ta faɗa duk domin ganin ta shawo kan Umma.  ta sake ce wa "To ni dai ban yarda ba" ta faɗa tana ƙoƙarin miƙewa. Siyama tabi ta da kallo kamar ta fasa ihun takaici. Tun kafin ranar bikin take faɗawa Umma akan cewar za'ayi bikin Amera ƙawarsu wacce Umma ɗin ta san da ita, domin ƙawaye ne sosai har ta kai zumuncin ga iyaye. Ta sha fadawa Umma cewar mijin ba ɗan Kano bane ɗan Kaduna ne, kuma ta na ta faɗa mata cewar cen za'a kai Amera. Duk lokacin da zata fadawa Umma haka bata taɓa ce mata komai, hakan yasa ko lokacin da aka fara shagalin bikin kullum sai ta tuna mata, bata taɓa kawo cewar zata bata matsala ba har sai ana gobe za'a tafi wato yau, ganin dai tana ta shiri ne yasa Umman tambayar ta ina zata je. A lokacin kamar ta fasa ihu jin abun da yake shirin faruwa da ita kamar an sa mata hannu. Domin sun gama shirya komai dukkansu akan iyayen kowa sun yarda zasu je, ita dama bata kawo cewar zata samu matsala ba sanin cewar ta san da maganar. Kuma abun burgewa ma shine angon da kansa ya ɗauki nauyin yi wa gaba ɗaya ƙawayen amaryar kuɗin mota zuwa da dawowa su huɗun da suka fi kusa da amaryar tasa kaman yadda ita amaryar ta sanar musu. Da ita aka dinga bi gidan ƙawaye ana bawa iyayen haƙuri har kowacce ta samu tikitin zuwa daga gurin iyayensu. Za'a je gidan su tace ita ai Umma ta san da maganar kuma ta barta akan taje. Hakan yasa yau da yamma bayan an ɗaura aure suka zauna su huɗu harda amarya suka shirya komai, harda kayan da zasu saka na kwana uku domin haka suka shirya akan idan sunje sai sunyi kwana uku inji ita amaryar. Su huɗu ne ƙawayen Amarya mai suna Amera, sai Abida, sai Haura sai ita Siyama. Yara ne ƙanana domin gaba dayansu ba zasu wuce sha shida ba, domin Amera auran wuri akai mata. Mahaifinta ɗan gargajiya ne na gaske, yaransa gaba ɗaya basa kaiwa ashirin yake aurar dasu, hakan yasa itama suna kammala secondary school yace da saurayin nata ya fito muddin da gaske yake. Daga lokacin da aka saka ranar aure ƴan ƙwailayen amaren suka fara jin kansu a manyan mata, domin rawar kai sai abun da ya ƙaru, hakan yasa ƴan unguwar gaba ɗaya suke musu laƙabi da ƴan mata. Duk wata rawar kai da rashin ji da iyayi an yi shi a wannan bikin, domin kowacce tun safe idan ta baro gida sai yamma take komawa tsabar chashewa da shagali domin kuwa sun ɗauki wannan auran a gadon bayan su, ranar kamu kuwa anyi bidiri kamar babu gobe, duk da cewar angon ma yana ɗan hana su rawar gaban hantsi domin kuwa a cewar su bashi da kirki. Anci uwar sabada da warkajami da rashin ji na rawa kamar kwankwaso zai karye, sannan babu wata ƙawa da suka gaiyata daga su sai su domin dama haka suke, sai kuma wasu daga cikin dangin amarya sa'annan su. Ko saboda shegen iyayinsu da rawar kansu kaɗai ta isa aja jiki daga gare su domin sun ɗauki wani irin girma na manyan mata sun ƙwamawa kawunansu. Yayin biki kuwa kowacce kala uku-uku ta ɗinka, banda ƙananan kaya da suka yi na kamu, sai kuma zani da riga na ƙwauyawa da suka yi. Duk wannan abun nasu basu da samari wanda za'a ce suna so, sai dai irin wanda baza'a rasa ba domin kuwa bayan ita amarya Amera da tayi aure yanzu sai kuma Abida itama da take ɗan tsayawa da wani haka sama-sama. Babban abun ma shine ko babbar waya basu da ita, waya ɗaya ce babba ta Amera da mijin nata ya saya mata, da ita suke takama.

Tashi Siyama tayi ta baro ɗakin tana jin hawaye sun cika mata ido. Ƙannante guda biyu ta gani suna kallonta suna dariya domin suna jin duk abun da ake yi. Sannan duk gidan babu wanda bai san da wannan tafiyar ta Ƴan mata ba, hakan yasa kanwarta mai suna Saddiƙa ta ke ta dariya tun ɗazu, ganin ta fito ne yasa ta fara toshe baki, ai kuwa ta saki dariyar ta ganin hawaye a fuskar ta. Da gudu Siyama ta bita tana zaginta akan idan ta cika mara kunya ai tsayawa zatayi ba gudu ba. Shima ƙaramin ganin haka yasa ya koma ciki da gudu gurin Umma. Fashewa da kuka tayi tana guna-guni ita ɗaya, tana jin ita wallahi sai taje ko da kuwa Umma bata barta ba, haka kawai ace ita ɗaya ce bata je ba. Ɗakinsu ta shiga ta kalli jakar tafiyar tata ƴar ƙarama da ta wanke, ga kayanta kala huɗu da ta goge kowanne da gyalansa, sai takalma suma gudu huɗu. Sai kawai ta sake fashewa da kuka ta baro ɗakin ta koma dakin Umma ta shiga bubbuga ƙafa ta na fadin "Haba dan Allah, yanzu ace ni kaɗai ce ban je ba, gaba ɗaya fa duk zasu je sai ni ɗaya, dan Allah kiyi hakuri, ko kuma kizo muje gidan su Abida sai kiji idan har mamarta bata barta ba?" Siyama ta ƙarasa tana kuka wurjanjan. Umma ta ce "Na ce dai babu inda zaki ke, babu ruwana da cewar an barsu ko ba'a barsu ba, ni dai nace ba zaki je har wani gari rakiyar amarya ba, kuma ki bar buga min ƙofar ɗaki na faɗa muki" ta faɗa da ɗan ɓacin rai!. Ai kuwa ta ta bar ƙofar ɗakin tana ƙara fashewa da kuka. Tana shiga ɗaki ta sunkuya a gaban gadonsu taci uban kuka kafin ta ɗauko jakarta ta fara cigaba da shirya kayanta, tana yi tana shessheƙar kuka tana maganganu ƙasa-ƙasa. Sai da ta shirya komai kafin ta zuge jajar ta ajiye ta tashi ta fito waje. Haka suka cigaba da zama a palo ba tare da an tada maganar ba. Umma dai tai mata banza itama bata sake cewa komai ba, sai kakalen abun magana take yi.  Misalin ƙarfe takwas na dare bayan anyi isha sai ga kira ya shigo wayarta, ganin number Abida yasa ta ɗaga fuskar nan a haɗe har lokacin. Suna gama wayar ta kalli Umma kamar kar tayi magana ta ce "Amarya ce take kiranmu duk suna gidan ni ake jira?" Kasancewar duk a cikin unguwar ne, kuma dama ita Umma bata da matsala da gaba ɗaya ƙawayen nata, domin kowacce ba laifi ta samu tarbiyya daidai gwargwado, kuma ko mutanen unguwa basa shedar su da wani abu na raina manya ko rashin ɗa'a ko shigar banza haka. Umma ta ce "Karki ɗade, domin ban yarda ki kwana a cen ba yau, ki dawo da wuri, idan kuwa har Ɗan nan(wato yayansu babban) ya dawo zan sa yazo har gidan ya zano min ke ku dawo" Umma ta faɗa da gaske, duk da kuwa tasan ba zai dawo ayau ba. Siyama dai ta miƙe ta fita bata ce komai ba. 

Haka suka haɗu a gidan su Amera aka cigaba da shirya yarda tafiya zata kasance, ita dai Siyama bata nuna cewar tana da matsala ba, tana dai jin yadda kowacce take fadin yadda zasu dinga daukar wanka da yawo unguwa-unguwa a cikin garin Kaduna idan sunje. Daga haka kuma aka koma hirar yadda amarya zata zauna da mijinta, kowacce sai kawo tata shawarar take yi kamar dai yadda suka saba, abu dai na shirme da shiririta irin nasu. Abida ta ce "Mijinki naki ne, babu batun jin kunya, kuma karki ce zaki tsaya nuna masa cewar ke yarinya ce, a'a ki zage ki nuna masa love da lubaiya, kuci abinci tare kuyi wanka tare har kaya ki saka masa..." Ta na zuwa gurin suka kwashe da dariya. Haura ta ce "Ke Abida harda saka kaya da yin wanka, a'a dai mai laifi aci abinci tare amma wanka kam ai sai ta raina shi, kuma ita sai ta iya yin wanka a gaban ƙato babu ko kunya?" Abida ta ce "Mijin nata ne ƙato?" 

Haura ta sake faɗin "To ba ƙaton bane, haka kawai, to shi saboda bashi da kunya sai ya iya tuɓewa a gaban ta yana ƙato da shi". Amera ta ce "Karki ƙara kiran mijina da ƙato, wannan ai cin mutumci ne, kin san mai ake nufi da ƙato kuwa? Irin fa ƙataƙatan mutanen nan ne ake cewa ƙato".  Abida ta ce "Ato dai gara da kika katseta domin ita bata sani ba". Siyama dai na jinsu amma bata ce komai ba sai dariya da take yi. Haura ta ce "To naji ba ƙato bane abar maganar, gobe iwar haka dai muna cikin KD" Sai lokacin Siyama ta ce "Hammm nifa yunwa nake ji, a kwai abinci?" Amera ta ce "Yanzu za'a kawo"  Abida ta amsa da "Kunga yanzu tun ma kafin muje KD mu tsara yadda zamu amshi kuɗin sayan bakin mu, domin wallahi ba zamu karbi kaɗan ba, ai munji yadda ake bawa ƙawayen amarya kuɗi masu yawa, wasu fa wai harda mota ake haɗa musu". Siyama ta ce "Ai akan wannan kuɗin sayan bakin wallahi idan har basu bamu da yawa ba sai dai mu kwana gaba ɗaya a ɗakin amaryar, ko kuma mu ɗauketa mu gudu da ita har sai ya biya yadda muke so". Tana faɗa suka hau shewa Haura da Abida suna fadin wannan shine daidai haka ma za'ayi wallahi, kunga idan yaga zamu kawo masa cikas dole ne yaje duk inda kuɗi suke ya nemo ya kawo. Ita dai Amera tana sauransu yadda suka cigaba da ɗora buri akan kuɗin sayan bakin nan. Suna cikin haka aka kawo musu abinci suna ci suna shewa ana ta shirin cin kuɗin abokan ango a garin Kaduna. Har lokacin dai Siyama bata ce musu komai ba game da hanata zuwa da aka yi...📝

Ina mana Barka da Sallah yan amanar S Reza.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol