Free chapter 路 Read without an account
45
by ZAHRAA 路 Bayan Murmushi
page 45鈱笍馃挰
***
Tafiyar su a cikin mota ta kasance cike da nishadi. Inda Ak da farhana suka biya da yaran aka jido masu uban shopping.Mimi da Abeed suna ta surutu a bayan mota, yayin da AK yake jifan Farhana da kallon alfahari lokaci zuwa lokaci. Suna isa kofar gidan Abdulkarim, AK ya yi parking, suka fito tare.
Abdulkarim yana zaune a falo yana kallon labarai lokacin da suka yi sallama. Ganin AK da Farhana tare da yaransa ya sa shi saurin mikewa, fuskarsa dauke da mamaki da murna.
"Lallai big bro ne yau a gidan namu! Yayanmu ne da kansa?" Abdulkarim ya fada yana mika wa AK hannu suka gaisa, sannan ya juyo ga Farhana. "Sannu da zuwa anty Farhana. Nagode sosai da kika debe wa yaran nan kewa yau."
"Ba komai Abdulkarim, ai yaranmu ne," Farhana ta amsa cikin kunya da ladabi.
Halima dake jin muryoyinsu daga daki, ta fito da sauri tana gyara mayafinta. "Ah lallai yau kam akwai babban bako! Sannunku da zuwa."
Bayan sun gaisa a falo, Halima ta ja hannun Farhana suka wuce daki don su dan taba hira ta mata, yayin da AK da Abdulkarim suka cigaba da tattaunawa a falo.
Suna shiga daki, Halima ta gyara zama tana kallon Farhana da wani irin murmushi na tsokana.
"Sannu Queen din yaya AK ,naga posting din da yayi a handles dinsa. Gaskiya Farhana kin cire tuta! Kowa ya sani AK mutum ne mai wuyar sha'ani, amma gashi nan yanzu ya zama 'Gentle Soul' a kanki."
Farhana ta sunkuyar da kanta kasa, fuskarta ta yi jawur saboda kunya. "Anty Halima kema kin gani? Wallahi ni kaina na sha mamaki, ban san ma zai yi ba."
"Ai baki gani ba tukuna," Halima ta karfafa mata gwiwa. "Gaskiya ne, abin ya girgiza su Yaya Ramla sosai, amma ni da Abdulkarim mun ji dadi. Kinga yadda kika dauki yaran nan suka miki yini ,ya kara miki daraja sosai a idon mijinki da ma namu baki daya. Kar ki damu da maganganun mutane, kawai ki rike mijinki da kyau."
Farhana ta ji dadin wadannan kalaman. Ta ji kamar ta samu abokiyar shawara a cikin dangin mijin nata. "Insha Allah Anty Halima, zan yi kokari."
Bayan sun dan jima suna hira, suka yi sallama da su Abdulkarim suka nufi gida. A hanyar dawowa, AK ya kalli Farhana yace, "Wifey, naga kin saki jiki da Halima. Hakan ya mini dadi sosai. I want you to be happy."
Suna shigowa harabar gidan su, Hanadi tana nan inda take a balcony, har yanzu tana lura da duk wani motsi. Ta ga yadda suka fito daga mota cikin natsuwa, tana kallon yadda suka nufi part din Farhana tare.
"Queen din banza ..." Hanadi ta fada cikin ranta, tana tuna yadda Jauhar ta fada mata cewa hoton nan ya zama viral. "Tana tunanin ta gama samun kowa. Tana tunanin Halima zata iya kare ta. Kowa yana murna yanzu, amma bari mu ga idan wannan murnar zata dore idan kuka isa Amurka."
"Idan Farhana tana tunanin ta zama Sarauniya, to ni zan nuna mata cewa ni ce mai mulkin gidan nan."
Bayan Ak yayi wanka Ya nufi bangaren Hanadi kai tsaye. Ko da ya shiga, ya iske ta tana gyara wasu littattafai, fuskarta dauke da wata irin natsuwa ta karya.
AK ya zauna a daya daga cikin kujerun dakin, idanunsa suna yawo akan kowane lungu. "Hanadi, har yanzu zuciyata ba ta ba ni cewa Farhana ce ta fadi maganar receipts dinnan ba. Akwai wani abu da nake ji a jikina, kuma ina so ki gaya min gaskiya."
Hanadi ta juyo, ta dan yi murmushin takaici. "Har yanzu dai zargin ne AK? Na riga na yi maka rantsuwa. Me ya sa kake son raba kanka da gaskiyar cewa matarka ce ba ta da sirri? Ni dai na riga na gaya maka abin da na sani."
AK bai sake cewa uffan ba, amma ya lura da yadda idanunta suke kauce wa nasa. Ya kura wa drawer din teburinta ido, yana tunanin ko akwai sauran wasu takardun da ta boye, amma rashin hujja ya sa ya tashi ya fice, ransa a jagule.
Washegari, Farhana ta tashi cikin natsuwa. Ta cigaba da daukar darasin tuki (driving lessons) tare da malaminta. Yau ta kara kwarewa sosai, har tana iya tuka motar cikin natsuwa ba tare da fargaba ba. Tana jin dadi yadda take kara samun yancin kanta kafin su tafi USA.
Yau ranar girkin Farhana ce. Da misalin karfe hudu na yamma, ta shiga kitchen dinta na part dinta don fara shirin abincin dare. Ta bude deep freezer dinta tana neman kayan miya (tattasai da tumatir) da aka riga aka nika aka ajiye, amma sai ta ga wajen wayam.
Ta kira Ruth "ina kayan miyan da aka kawo jiya? Na gani a kitchen din nan amma yanzu babu su."
Ruth ta shigo Tana sosa keya, fuskarta cike da fargaba. "Hajiya... dama Hajiya Hanadi ce ta zo dazu. Ta ce in kwashe duka in kai mata nata bangaren, wai nata ya kare kuma ke ba kya bukatar mai yawa tunda kwanaki kadan ya rage muku ku tafi."
Farhana ta ji gabanta ya fadi. Wannan fili yake wulakanci ne. Ta dauki wayarta ta tura wa AK sako ta WhatsApp:
"AK, kayan miyan da aka siyo jiya duka sun kare. Ruth tace ce Hanadi ta kwashe kaf ta kai part dinta. Ina bukatar wasu yanzu don in yi girkin dare."
AK yana ofis ya ga sakon. Wani irin bacin rai ya ji ya turnuke shi. Ya san Hanadi tana da nata kayan miyan da aka siyo mata lokaci daya da na Farhana. Ya kira layin Hanadi nan take.
"Hanadi! Me ya sa zaki kwashe kayan miyan Farhana ki kai part dinki? Bayan jiya naga Kayan mita a freezer dinki
Hanadi dake zaune a falonta tana shan sanyi, ta yi dariya ta ciki. "Oh, ashe har ta kai maka kara? Darling so nake in adana su ne naga Kamar sun kusa lalacewa kuma ba dadewa zata yi ba ta tafi. Me ya sa kake yin fada akan tumatir?"
"Maida mata kayanta yanzu! Kuma kada ki sake taba duk abin da yake na part dinta," AK ya daka mata tsawa ya kashe wayar.
Hanadi ta wurga wayar kan gadonta, idanunta sun yi jawur. "Lallai farhana har kin kai ga matakin da AK zai daka min tsawa akan tumatir?
Bayan kiran wayar AK, Hanadi ta zauna ta dade tana huci a falonta. Ta ji zafin yadda AK ya daka mata tsawa akan "tumatir da tattasai." Ga ta a babban gida, amma an maida ta kamar wata mara gaskiya a gaban ma'aikata.
"Emma!" Ta kwala wa ma'aikacin kiran gaggawa.
Emma ya shigo da sauri, kansa a kasa. "Gani Hajiya."
"Kwashe kaf kayan miyan nan ka maida su bangaren Farhana yanzu! Kuma ka gaya mata, ni ba matsiyaciya bace ,kawai adana mata nake so in yi tunda ita ba ta da natsuwa. Amma tunda har ta kai kara wajen AK, to ta karbi abinta."
Emma ya kwashe bokitin kayan miyan dake shake da ledoji, ya nufi part din Farhana. Farhana tana tsaye a kitchen tana gyara wasu kwanuka lokacin da Emma ya shigo.
"Hajiya, gashi nan Hajiya Hanadi ta ce in dawo miki da su."
Farhana ta kalli kayan miyan, sannan ta kalli Emma. Ta san halin Hanadi; kalaman da ta aiko Emma da su tabbas na cin mutunci ne. "Emma, me kuma ta ce?"
Emma ya dan yi shiru, sannan ya rada, "Ta ce wai ba rowa take ba, adana miki take so ta yi... amma wai tunda kika kai kara, gashi ki karba."
Farhana ta saki ajiyar zuciya. Ba ta ji haushin kalaman ba, sai ma tausayin kanta da take ji na zama a gida daya da mai wannan halin. "Ba komai Emma, ajiye su nan. Nagode."
AK ya dawo gidan da wuri a ranar, ransa har yanzu a bace yake da abin da Hanadi ta yi. Kai tsaye kitchen ya nufa ya iske Farhana tana sanye da apron, tana ta faman girki. Kamshin miyar da take yi ya gauraye dakin.
"Wifey, an maido miki da kayan?" Ya tambaya yana tsaye a bakin kofa.
Farhana ta juyo, tana murmushi. "Eh an maido. Nagode sosai."
AK ya karaso ya tsaya kusa da ita. "I'm sorry about her behavior. Ban san me ya sa take son takura miki ba kwanan nan. But don't worry, nan da kwanaki kadan zamu bar wannan hayaniyar mu tafi inda zamu samu nutsuwa."
Daren ya kasance cike da nishadi ga AK da Farhana. Sun ci abinci tare, suna tattaunawa akan yadda rayuwarsu zata kasance a Amurka. Farhana ta fara jin dadi sosai, tana jin kamar lallai AK zai kare ta.
Hanadi ta kwanta, tana jin wani irin daci. Ta rasa me ya sa duk abin da ta kullawa Farhana yake juyawa yana kara dankon soyayya tsakanin Farhana da AK.
Kwanaki suna gudu kamar iska, yau saura kwanaki 8 bar kasar Najeriya su nufi Amurka. Farhana tana zaune a falonta tana ninka wasu kayayyaki da take son tafiya da su, sai ga AK ya shigo, fuskarsa dauke da wani irin shiri.
"Wifey," ya kira sunanta yayin da yake zama a gefen gadon. "Na yanke shawara. Kafin mu tafi, ina so mu zagaya mu yi bankwana da dangi yadda ya kamata. Gobe zamu fara da Ilorin, mu gaida kakaninki na wajen mahaifiya (maternal grandparents). Daga nan mu wuce Matazu wajen Nene. Sannan mu karkare a Sokoto wajen Daddy."
Daddy ya dade yana son ganinki tun ranar bikinmu. Kuma kinsan shi mutum ne mai son zumunci. Ina so ki shirya, gobe da sassafe zamu dauki hanya."
Farhana ta ji wani irin dadi ya ziyarci zuciyarta. Wannan karramawa ce babba gare ta da danginta. "Nagode sosai AK. Allah ya bar zumunci."
Tana cikin wannan farincikin, wayarta ta fara ruri. Halima ce (matar Abdulkarim).
"Farhana, ina so in sanar daki, upcoming week muna da Birthday din Mimi. Ina so ki sani tun yanzu don kada ki yi kuskuren rashin kasancewa a wajen tunda saura kwanaki kadan ku tafi."
Farhana ta yi ajiyar zuciya. "Allah ya nuna mana Anty Halima. Gobe zamu fara zagayen sallama da dangi, amma Insha Allah zamu yi kokarin dawowa kafin ranar."
"To madalla. Allah ya kiyaye hanya, ya kaiku lafiya," Halima ta fada tana murmushi.