Free chapter · Read without an account
Chapter 5
by Salis M Reza · ƳAN MATA
*ƳAN MATA*
_By S Reza...✍️_
*🪀Whasop Channel*
***
*Chapter 5️⃣*
Ganin dai har ƙarfe huɗu tayi basu dawo bane yasa ran Ango ƙara ɓaci. Ya kalli sauran matan da gaba ɗaya suma suna cikin damuwa, wasu kuwa sun shirya da nufin tafiya abunsu amma Ƙasim ɗin ya ce babu wacce ta isa ta bar gidan nan har sai matarsa ta dawo lafiya. Ya ƙulle gidan suka tafi masallaci har suka dawo shiru. Bayan ya buɗe gidan ne yake tambayar wai ina suka ce zasu je ne domin shi dai ya fara zuwa karshe, tabbas sai ya ci mutuncin yaran nan wallahi. Wata daga ciki ta ce "To wa ya isa su faɗa masa, kai kanka kasan halin yaran nan wa ya yasan ina zasu je, yaran da kina faɗa musu A zasu faɗa maka Z, su wai yan mata, gasu gaba ɗaya basu wuce ayi musu wanka ba sai shegen manyance, ai kawai a jira su idan ma har dare zasu kai". Ƙasim ya ciji yatsa ya cire hular kansa ya dawo ƙofar gida yana kaiwa da kawowa ya tafasa har ya fara ƙonewa. Matar da take babba a cikinsu ta ce "Duk wannan abun laifinka ne Ƙasim, idan ba wulaƙanci ba, ta yaya za'a kawo maka amarya tun jiya ka banzatar da ita, dama ma mu da muka kawo maka, kawai saboda an kaita gidan kishiyar mamarka shine zaka huce haushin a kanmu, haka ake yi, tun fa jiya muke a gantale kamar marasa gata marasa mutunci da ƙima sai kace almajirai, badan ma munki sanar da gida irin abun da kayi manaba kana tunanin idan suka sani zasu yarda da wannan abun, ko babu Komai ace kazo tare da abokanka ka tarɓe mu zamu ji dad'i musan ka girmama mu..." Kafin ta sauke numfashi a zuciye ya ce "To shi gidan da kuka fara kaita ɗin ni nace a kaita, ina ce duk wasu iyayena kun gansu a Kano, wacce kike magana ɗin ko gidan bikin su sun zo ne, ban haɗa komai da su ba, karki ƙara haɗa ni dasu na faɗa miki, ni nan Kaduna bani da kowa aiki ne ya kawo ni, duk wani biki an gama a Kano, to akan me zaku kai ta gurin wasu banzaye marasa ƙima da mutunci a idona, kunsan Irin tanadin da nayi a daren jiyan ne kuka wargaza min, kun san me dame muka shirya da kun kawo ta a ranar amma kuka bata komai, na rantse da Allah da kun sake kun kwana a gidan da sai dai ku koma da amaryar wallahi, ai tun daga gida an faɗa muku cewar gidana zaku kawo ta, har ma lokacin da zaku sauke ta dreban ya kira nace kar a kai min Mata ko ina ko ba'ayi haka ba, ba'a ce ku tafi da ita yawon banza da wofi ba, kuma a yau ɗin nan kowacce mata ta shirya Komai dare idan mata na ta dawo zaku bar min gida wallahi". Ya ne rufe baki gurin ya karaɗe da salatin mata da ihu. Kowacce na faɗin albarkacin bakinta ganin Irin wannan rashin albarkar na wannan Angon zamanin da suka haɗu da shi. Matar da tayi maganar ta ce "Eh dole ka faɗa haka tunda an kawo maka ita har gida, kuma kaine matsiyaci da kake tunanin sai ka samo mana Mota zamu tafi, bari yanzu nayi sallah naga uban da zai hana ni kwana a garin Kano yau, kuma in sha Allah wannan yaran Ƴan Mata suna daidai da rashin albarkar ka, Allah yasa ma su gudu da ita muga ƙarshen abun, kuji mun yaro mara kunya fa, ni wallahi sun yi min daidai ma da suka tafi yawo da ita". Ai jin haka kamar an sawa Ƙasim batiri, Nura na jansa yana ƙwacewa har dai ya fito da shi waje. Su kuwa sauran matan Jin wannan matar ta basu ƙwarin gwiwa ne yasa gaba ɗaya aka fara mayar wa da Ƙasim magana, kowacce na tofa nata. Sai kuma gaba ɗaya kowacce take goyon bayan Yan Mata akan abun da suka yi.
Har ƙofar gida suka biyo shi suna jefa masa magana, wasu kuwa tuni suka saɓo kayan su da nufin tafiya. Ana wannan dambarwar ne keke Napep ya sauke Yan Mata a ƙofar gidan suka fito da sauri ganin kamar su ake kira. Tsabar sauri ma ko mai keken ma basu sallama ba, amma suka ga ya ja ya bar gurin. Basu bi ta kansa ba suka ƙaraso gurin, ita dai Siyama hankalin ta naga su haɗu da Amera ta faɗa musu ina aka tura kuɗin su, kuma Mai yasa ta dawo gida bata faɗa musu ba. Tun ma kafin ayi magana Ƙasim ya watso musu tambayr da tasa gaba ɗaya suka kalli juna. A fusace ya kutuntumo musu wani zagi haɗi da tambayar matarsa ganin mai keke ya juya Amera bata fito ba. Ya ce "Dan abu ta kazar ku ina kuka baro Amera ɗin, yan iskan yara wawaye marasa hankali kawai?" Ya faɗa yana nuna Siyam da yafi jin haushinta, kamar ya mazgeta yake ji ko zai huce. Kafin su samu bakin magana sauran matan ma suka shiga tambayar ina amaryar ganin dai babu ita suka dawo. Abida, Haura, Siyama, Gaba ɗaya sun ma rasa abun da zasu iya cewa, wannan shi ake kira da Lukutar lala'i mai lasisi. Nura ne ya sake cewa "Wai ana magana kunyi shiru kamar kurame, ji wata kwalliya da kukayi wai ku a hakan yan mata, ina ita Amera ɗin, kuma ma ina kuka je yawo harda amarya fissabillahi?" Ya faɗa shima yana jin wani takaicin yaran. Siyama ta sauke ajiyar numfashi. Haura ta ce "Wai Amera ɗin bata dawo gida ba kuke nufi ko me?" Ta faɗa da sigar tambaya da kuma mamaki duk a lokaci guda. Ai Ƙasim ji yayi kamar ya zabga Mata mari, ya ce "Gidan ubanki zata dawo bayan tare kuka fita, wai ma uban waye ne yace ku fita min da mata, a ina kuka taɓa ganin haka idan ba ku wawaye marasa Kunyar yara ba". Siyama ta ce "A'a fa Malam dakata meye abun zagi bayan matarka ta dawo gida tun ɗazu, mu shiga gidan ka duba da Kyau domin kuwa ta dade a gida dama tace tana tsoro ne yasa ta dawo abunta". Ta faɗa cike da tsiwar da ya santa da shi. Wata ta ce "Babu wata Amera da ta dawo gidan nan fa, tunda kuka fita ina nan babu idon wacce na gani a cikinku". Siyama ta ce "To kuwa baki gani da Kyu ba, Amera na gidan nan wallahi, to ina zata je mu da tace mana zata gida, muna tare fa tace mana zata je gida, to ina ta sani a Kaduna da ya wuce nan ɗin, wallahi tana ciki". Ta ƙarasa maganar a tsorace domin kuwa izuwa yanzu ta fara yarda da cewar akwai matsala, amma saboda ƙifaɗi irin nasu da kuma son tabbatarwa sai suka nufi cikin gidan kowa ya biyo su a baya. Shi dai Ƙasim yana tsaye zuciya na ɗibansa akan ya fara kutubal da Siyam ɗin ko zai samu zuciyar sa ta daidaita.
Babu inda ba'a duba ba a cikin gidan amma babu Amera. Tsabar tashin hankali ma Siyama har karkarshin gado ta leƙa. Haura kuwa ta duba toilet ya kai sau biyar. Abida kam salati kawai take tana kiran sunan Amera ko zata amsa, harda kiranta da sunanta na gayu wato Mera. Kowa yayi cirko-cirko ana ta binsu da kallon yadda suke yin abun kamar yan shirin Film. Abida ta kalli Haura ta ce "Yauwa ina jakar mu, wayata na hannunta sai a kirata da ta Siyama". Ta faɗa tana tambayar Abida. Abida ta ɗago da sauri ta ce "To ina kika ajiye jakar?" Siyama ta ce "Mun shiga uku gaba ɗaya suna keke Napep fa harda wayar". Ta faɗa a rikice saboda lokacin da suka shiga keken jakokin na cinyarta. Abida ta ce "Harda tawa jakar?" Ta amsa da "Gaba ɗaya harda ta Amera ɗin ma da ta bari". Ta ƙarasa tana yin waje da gudun tsiya. Suma suka rufa mata baya. Sauran matan ma kamar masu kallon yan wasan Kura, sai kuwa suka biyo su. Amma ina babu mai keke Napep babu ko ƙurarsa. Haura ta ce "Tsinnanne ashe shine dalilin da yasa ya tafi bai amshi kuɗin sa ba, Allah ya isa jakokinmu da wayoyinmu". Ƙasim ya ƙaraso gurin ganin sun sake fitowa babu Amera. Ya ce "Ina take a cikin gidan?" Ya faɗa babu alamun wasa yana kafe Siyama da jajayen idanunsa, wanda take ta haɗiye wani yawun tsoro tana ja da baya, su dai sun shiga jalala yau, wannan shine ba'a rabu da bukar ba an haifi abu, komai nasu na cikin jakokinsu, wayoyi da kayan kwalliya harda ɗan chanjinsu, to ta jakokin zasuyi ko ta rashin sanin ina wannan ameran ta shiga zasuyi. Suma gaba ɗaya Abida da Haura a tsorace suke suna kallon ƙasim ɗin dake gabansu. Siyama tayi ƙarfin halin faɗin "Kana gani dai mai keke Napep ya gudu mana da wayoyi da jaka, kuma da wayar zamu tambaye ta, domin dai ai muma bamu san inda ta..." Kafin ta karasa sai ji kayi "tass" Ya ɗauke fuskarta da marin da yasa sauran maganar komawa.
Ya ce "Ina tambayar ki inda kuka baro min Mata kina min maganar an sace muku waya, wayar banza wayar hofi, to ma tun farko uban waye yace ku ɗauke ta ku tafi yawan banzan ku, kuma ma ina ne kuka je, to ma ta yaya kuna tare ita kadai kuce baku san inda tayi ba, sai dai ko kune kuka ɓoye ta wallahi". Ya karasa yana nuna Abida da Haura suma kamar ya mare su. Siyama ta rike kumatu kanta a ƙasa ta faɗa tunanin ita tunda take ma kuwa an taɓa marinta, bama wannan ba, shi a matsayin wa zai mare ta, ba Uba ba ba yaya ba ba wani shaƙiƙi ba, duk da irin abun ma da yayi musu, ko dai ya manta ne, ko bai san su kansu haushinsa suke ji ba. Duk da marin ya shigeta sosai, domin bata taɓa kawowa zai mareta ba sam, bata san ashe shima ɗan zafin kai bane haka, tabbas yau zata nuna masa girma-girma ne amma na Allah shine babba. Suma kansu matan gurin sosai marin ya tsorata su, suka fara faɗin mai yayi zafi ai sai ya tsaya yaji yadda aka yi kafin ya yanke hukunci. Jin Siyaman bata ɗago ba, kuma yana ta magana basu tamka masa ba sai ya kama kanta ya ɗago da ita yana ƙara faɗin ta yaya aka yi ita Amera ɗin ta ɓata, kuma ina ne da ina suka je. Ta ɗago da karfi ta ce "Gidan uwar ka da gidan ubanka muka je, ɗan iska wawa wanda bai san darajar mutane ba, kuma ka sake taɓa ni ka gani na rantse da Allah sai ka gane kuranka, kuma Amera ce bamu san inda tayi ba, idan ka damu da ita kaje ka nemo ta". Ta na faɗa tayi hanyar cikin gidan. Amma taku biyu kafin tayi na uku Ƙasim ya riko mata hannu ya dawo da ita baya. Ya daga hannu ya ƙara mata marin domin yaga karshen rashin kunyar ta. Sai dai kafin ya furta abun da zai furta bayan marin itama ta rama, sai kuma ga Abida ta bada nata gudun mawar marin. Ƙasim ya rike gurin yana kallon yar yarinyar da ta iya marin sa, harda Abida itama, duk mamaki ya hana shi magantuwa. Siyama cikin kuka ta ce "Ko ubana bai taɓa sa hannunsa a jikina ba bare wane banza, kuma idan har sarki baiji kunyar hawa jaki ba..." Abida ta karasa da faɗin "Jaki ba zaiji kunyar wantsalo da ɗan banza ba". Ƙasim yayi kanta Nura ya rike shi. Ya ce "Nura sakar min hannu idan ba haka ba wallahi zan dawo kanka, har ni wannan yaran zasu mara Nura, kallesu fa, nawa suke, kuma sumin laifi su zage ni kuma su mare ni, to wallahi tallahi sai naci uwarsu dukkanin su dan durin uwarsu, kuma sai sun nemo min mata a yanzu nan, ba dai su marasa kunya ba, zan nuna musu naci uwarsu danyen kai". Abida ta ce "Ai kowa na san kansa, ita da ka mare ta ai bata san zafin jikinta ba sai kai ko". "Nura zanci abu ta kazar ubanka fa idan baka sake Ni ba Nura". Sosai Ƙasim ya rikice har wani tada jijiyar wuya yake kamar zayi faɗa da maza yan uwansa, domin dai abun da kunya ace wai yan yaran nan sun mare shi a gidan sa fa. Ganin sauran matan suna tura su Siyama gidan ne ya ce "Idan baku fito min daga cikin gida ba na rantse da Allah zan halaka yarinya a gidan nan". Ganin haka Nura ya kira sauran abokansu domin su taya shi ji da shi.
Bayan sun shiga har cikin ɗakin amarya inda dama anan kayan su yake. Bakin Siyama har ɗan fashe wa yayi. Sauran matan suna ta musu faɗa kuma suna cewa suyi shuru karsu kara magana, saboda shi namiji ne, kuma nan gidan sa ne, sannan su baƙi ne basu san kowa ba, ko haka ma da suka yi ya isa. Haura dai itama yar bada hakuri ce dan ita tana da tsoro ba kamar su ba. Dama a cikinsu Siyama da Abida sune wanda suka fi baki da surutu da rashin tsoro. Haura kuwa surutunta sai idan a cikinsu take, ko kuma sun shiga cikin mutane tare da ita. Amera kuwa ta fisu hakuri gaba ɗaya, hakan yasa wasu lokutan suke ce mata yar ƙauye bata waye ba, bata da magana kamar su. Bayan kamar minti goma, lokacin Siyama ta wanke bakinta sunyi shiru sun ma rasa me ya dace suyi. Wannan tafiya dai tasu ta zama tafiyar bala'i. Abida ta ce "Itama yar iska kawai Amera ɗin ina to taje zata jawo mutane masifa daga kokarin kare mata mutunci, matsala ta da ita bata da wayo kamar wata tunku a gurin, ni wallahi duk tafi bata min ma rai". Siyama ta ce "Zai wuce a garin dolancinta ne ta je ta ɓata a hanya, ni wallahi ko dan saboda shi wannan mahaukacin mijin nata ma Allah ya ƙara yasa bata ɗin tayi". Abida ta ce "Amin wallahi, shege gaɓon banza". Haura ta kallesu ta ce "Dan Allah ku daina wannan fatan naku, kuzo mu koma gurin da muka je koma yanzu haka ta koma gurin tana neman mu, kunga fa ko ta kira number mu ba waya a gurinmu, kusan halinta Allah inaga manta hanya da sunan unguwar ma tayi". Abida ta ce "Sai ki tashi kije ai, wallahi babu inda zanje, ai ita ba yarinya bace, aure ne fa da ita, ai ta girma yanzu". Ana cikin haka sai ga yan sanda sun shigo har cikin gidan wai ina ƙawayen amarya suke...?✍️
Yan Mata masu abun mamaki. A kwai fa rikici a wannan yar tafiyar ta Yan Mata