Free chapter · Read without an account
PAGE 9
D U H U N D A R E
A 2026 N O V E L
BOOK ONE
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
AMEENA IBRAHEEM
OUM-AMEER
Arewapen: @Oumameer2671
Wattpad: @Ummu-Amir
PAGE 9
Tun bayan da ta fito wanka ta shirya Aunty Na'imatu ke ta fama da ita akan ta daure ta ci abin cin da ta zuba mata amma ta ƙi ta kalli ma inda abincin yake.
Zaune take ta tanƙwashe ƙafafunta da carbi a hannunta tare da ɗan sauko da hular hijab ɗinta ta rufe idanunta tana zubo da ruwan hawaye a hankali tun bayan da ta kambalar sallah bayan ta shirya.
A tausashe ta kalle ta muryarta a ƙasa sosai ta ce.
"Haba Anaam! Wai dan Allah miye haka ne? Gabaɗaya yinin yau ba ki saka komai a cikin ki ba tun bayan ruwan Tea ɗinda kika sha da safe...."
Ɗagowa ta yi a hankali tana mai janye hijab ɗin baya kaɗan sannan ta kalleta still idonta da hawaye ta ce.
"Aunty Na'imatu bana son cin komai....bana jin yunwa ne..."
Lokaci ɗaya Mukarram da Mubarak suka yi sallama suka shigo ɗakin.
A yanayin da suka barta da safe dai a yanayin suka sake dawowa suka tarar da ita. Wuri Mubarak ya samu dab da ita ya zauna ya yin da Yaa Mukarram kuma ya tsaya daga ƙofa yana mai jingina bayansa ya tsaya kawai yana kallonta.
Ƙara saukar da kanta tayi tana mai jin yanda zuciyar ta ke yi mata wani irin ba daɗi. Yayyunta, waɗanda ba ta da tamkar su. Su ne abokanan dariyar ta, abokanan nishaɗinta, sun cika duniyar ta da farin ciki, sun tsaya mata a lokacin daɗi sannan sun tsayu matsayin shugabannin ta a duk lokacin da ta aikata wani kuskure. Daga Abban ta, Ammienta, sai su a cikin duniyar ta. Amma waɗan nan mutane su ne yau suka dawo ababen jin kunyar ta. Ta rasa miyasa take jin nauyi da kunyar haɗa ido da su. Lokuta da dama ta yi ƙoƙarin hana kanta wannan wautar amma kuma zuciyarta taƙi aminta....
"Anaam! Are you okay?"
Girgiza kanta tayi a hankali jin irin tambayar da Yaa Mukarram ya yi mata wacce ke ɗauke da zallar tausayi da nuna kulawa.
Miƙewa ta yi taje ta faɗa jikin sa tare da fashewa da kuka a hankali ta shiga girgiza kanta tana faɗin.
"I'm not okay Yaa Mukarram...! I am not..."
"Shhhh!"
Ya faɗa yana mai ɗora hanunsa a bayanta ya shiga rarrashin ta a hankali ya ce.
"I understand dear...ki yi haƙuri kin ji, with time...everything will be fine."
Kallonsu Na'imatu ta yi ta ce.
"Yaa Mukarram ta ƙi taci abinci. Tun ɗazu na yi ta yi mata magana amma ta ƙi ta kalli ko inda abincin yake..."
Jinjina kai ya yi alamar ya fahimta sannan ya janyo hannunta suka zauna akan lallausar carpet ɗin da ƙasan ɗakin asibitin ya ce Na'imatu ta bashi abincin ya zauna ya shiga bata da kanshi.
Miƙewa Mubarak ya yi ya koma bakin corridor can ta waje ya tsaya yana waya.
Ya jima sannan daga ƙarshe ya kashe wayar tare da juyowa da nufin komawa ɗakin sai suka yi ido biyu da Na'imatu.
Ɗan murmusawa ya yi sannan ya ce mata.
"Na'imatu Alaji fa ya ce ki shirya ki koma school tun last week, and ni banga kina wani shiri ba..."
Lokaci ɗaya ta ji hawaye sun cicciko idonta tana mai tsare shi da ido ta ce.
"Wane shirin zan yi Yaa Mubarak? Kana fa ganin halin da 'ƴar uwata take ciki? Komai a tare da ita muke yi. where am I going to start without her beside me? I can't yaa Mubarak. Don Allah kada wanda ya sake yi mini zancen wata school..."
Daga haka ta juya ta koma ciki ba tare da ma ta tsaya ta saurari amsar shi ba.
Sosai ya ji wani sabon tausayinsu ya daɗa kama shi. Wai bahaushe yace kowa yaga raƙumi yaga buzu. Na'imatu duk da cewar ta ba wa Anaam ɗin tazarar shekara ɗaya, komai a tare suke yin shi. Tare suka yi primary suka yi secondary, tare suka yi sauka akayi musu walima sannan yanzu ma a tare suke jami'a wanda suna second semester ne a 100level fannin BSC nursing, exams ɗinsu saura kwana uku ne ya rage su kambala su shiga 200level wannan ibtila'in ya faɗawa Anaam. Tun da abin nan ya faru har yau ko sau ɗaya ba ta sake zancen wata school ba.
Hakan yasa Abbah yaga cancantar ace ta koma taci gaba da karatunta kada ace matsalar Anaam ta yi delaying mata karatunta,amma shi ne yanzu take bauɗewa ba ta son zancen school ɗin.
A can ɗakin kuwa, wasa-wasa sai da Yaa Mukarram ya yi nasarar sanya ta ta cinye kusan rabin abincin sannan ya ajiye ya ɗauko wayarsa ya kira Yaa Muhammad wanda sai dai ta ji muryarsa kamar daga sama yana faɗin.
"Anaam ɗin Yaa Muhammad?"
Ba ta san lokacin da wani lallausan murmushi ya suɓuce mata ba domin kalmar Anaam ɗin Yaa Muhammad sai ta ji ta zo ma ta a ba za ta.
Idan har ya zo garin ko kuma taje gidansa a Abuja muddin yana son ta yi masa wani abin to a haka yake kiranta har ya samu ta yi masa aikin da yake so.
"Anaam Are you there?"
Jinjina kai ta yi tamkar tana a gabansa ta ce.
"Uhm!"
Wayar ya miƙawa Aunty Amina daga can ɓangaren yana faɗin.
"Auntynki tana son Magana dake rabin rai. Da kuma yaran ki."
Shiru ta yi tana saurare tare da ƙura wa yatsun hannunta ido tamkar mai nazarin wani abu. Muryar Aunty Aminar ta ji tana faɗin.
"Anaam ɗin Yaa Muhammad..."
Girgixa kai ta yi tana mai jin wasu sabbin hawayen a hankali suna ƙara cika mata ido, murya a ƙasa sosai ta ce.
"Yaa Amina ina wuni?"
"Lafiya lau Anaam, ya jiki?"
Lumshe ido tayi ta buɗe a hankali sannan ta ce.
"Jiki Alhamdulillah Yaa Amina, na gode sosai..."
Wayar Farouk ya karɓa shima yana murmushi ya ce.
"Aunty Anaam good afternoon."
"Afternoon Farouk How are you?"
"I'm fine Aunty Anaam, Allah ya ƙara baki lafiya mai amfani. We miss you."
Jinjina kanta tayi tana mai lumshe ido ta ce.
"Miss more my dear, ka gaishe da su Faryat."
Daga haka Yaa Muhammad ɗin ya karɓi wayar yana faɗin.
"Yaushe ki ke so na zo na ganki?"
Girgiza masa kai ta yi tamkar tana a gabanshi sannan ta ce.
"Ba sai ka zo ba Yaa Muhammad, domin na ji doctor ya ce za'a iya bamu sallama,so kaga zamu iya dawowa a kowane lokaci....."
"Okay! Allah ya amince ya nuna mana. Allah ya baki lafiya mai amfani."
"Amin yah Allah, na gode sosai Yaa Muhammad. Sai an jima."
Wayar take ta miƙawa Mukarram ɗin bayan ta katse kiran amma ya ƙi ya karɓa, sai ma tsayawa da ya yi yana kallonta kawai yana murmushi.
Ajiye hannun tayi tana mai kawar da kanta gefe domin ba ta son ma wannan murmushin yana saka ta jin wani iri.
" Mun gode da kika saki jikinki haka Anaam. Daman rayuwa har abada mutum baya taɓa samun 100% abinda yake so. Dole sai da jarrabawa da kuma ƙalubale. You have to be strong not only for today. You have to be strong,...Now and forever. It's not the end, you have to work hard and build another tomorrow.."
*******
Alhaji Ridwan kuwa, har office ɗin Alhaji Gimba ya je ya cim masa a kamfaninsa na shinkafa.
Ya jima yana jiransa wanda sai da ya yi tamkar ba zai fito ba, can kuma sai ga shi ya fito.
Da wani irin mamaki Alhaji Ridwan ɗin ya kalle shi ya ce.
"Alaji Gimba! Yanzu ni ne za ka hana shiga office ɗin ka? Yau ni ɗin Alhaji Ridwan za ka hana shiga office ɗinka..."
Wani kallon Alhaji Gimba ya yi masa sannan ya ce.
"Ba dole na hana ka ba tunda ka zamo munafiki...tare muke amma kafin son Alhaji Galadima da ni. Yanzu bayan Kaga baya garin shi ne ka wanko ƙafa ka zo? Bayan kun gama haɗa baki kun yi munafurcin cewa wai a kawo mini hukuma...to da na aikata muku me? Ai idan za ka tuhumi mutum dole sai ka na da hujja, idan babu hujja shirmen banza ne. "
Girgiza kai ya yi cike da takaici ya ce.
"Wai dan Allah Alhaji Gimba mi ke damunka? Mi ke damunka na ce? kai shi ke nan ba za ka taɓa canjawa ba?"
Girgiza kai ya yi yana mai ƙara gyara babbar rigar sa ya ce.
"Ni ba irin ka ba ne Alhaji Ridwan ka sani! Ba zan taɓa saukar da kai na a wurin wanda muka taso tare ba na dawo binsa a baya a baya tamkar wani Bindi ba. Yanda yake jin kansa namiji nima haka nake ji na, kasuwa ce kuma ya handame komai ya tattare shi kaɗai ya janye customers da komai...."
"To ai kaji inda matsalar take! Wallahi matsawar kana hangen abin wani kana ƙyashi da hassada har abada ba za ka taɓa godewa Allah da ni'imar da ya yi maka ba...."
Katseshi ya yi tare da nuna masa hanyar waje yana faɗin.
"Shi ke nan abin da ya kawo ka Alaji Ridwan? Idan shi ke nan dan Allah ka fita ka bani wuri na gode da ziyara."
Girgiza kai Alhaji Ridwan ya yi ya ce.
"Ba ziyara ba ce, gaskiya ce nake faɗa maka, kaji tsoron Allah ka daina cin amanar aminantaka. Wallahi dukkanku amanar juna muke kuma watarana sai Allah ya tsayar damu ya bincikemu akan hakan..."
Hannu Alhaji Gimba ya ɗaga ya shafa fuskarsa yana faɗin.
"Tuf-tuf...sadaƙallahul azeem alaramma Ridwan..Allah ya bada lada. Sai an jima."
Juyawa ya yi ya koma wurin P.A ɗinsa dake ta faman jiransa tunɗazu yabar Alhaji Ridwan nan wanda sai da ya jima a tsaye sannan daga ƙarshe ya fice ya nufi gida.
Alhaji Gimba na shiga P.A ɗin nasa Ishaq ya miƙo masa wasu hotuna cike da girmamawa ya ce.
"Ranka ya daɗe waɗannan su ne hoton 'yan matan da kace a samo maka."
Karɓa ya yi ya kalli ta farko, ta biyu sannan ta uku daga ƙarshe ya kalle shi ya ce.
"P. A ya haka? Ya naga mata guda uku kawai?"
"ahm! Ranka ya daɗe naga kace cikin gaggawa ka ke so, to sai naga tun da ba passion parrate za'a yi ba ai dai guda ukun nan sun isa..."
Wani kallon mamaki ya yi masa yana faɗin.
"ikon Allah!...yanzu P.A don Allah saboda na ce ka samo mini en mata in zaɓa a gaggauce shi ne za ka kawo mini hoton waɗan nan kaɗai? Kai P.A kalle ni fa har yanzu da saura na sannan kuma ga kuɗi...to magana ta gaskiya waɗannan musakan ba su yi mini ba. En kyawawa za ka samo mini tsala - tsala sai na zaɓa kuma na darje..."
Hannu ya miƙa ya sake ɗaukar hotunan yana dubawa yana faɗin.
" cab! Ji wata nan dan Allah wuya kamar mariƙin lema,...wannna kuma..."
Shiru ya yi tare da ƙure kallon hoton sannan daga ƙarshe ya kalle shi ya ce.
" Eh to! Wannan ɗin ma fa itama ta yi ko?"
Jinjina kai ya yi ya ce.
"Sosai Ranka ya daɗe, duk cikin su fa babu wacce ba ta da kyau. Kuma kowaccen su daga gidan kuɗi ta fito, ƙasaitattun mata ne Alhaji, sai da na bincika na hanga na duba sannan na kawo maka su."
"Eh to, ita wannan ɗin ya sunanta?"
Murmushin nasara P. A ya yi sannan ya ce.
"Sunanta Halisa Ranka ya daɗ.."
Wani irin dangware hoton ya yi tare da kau da kansa gefe ya ce.
"Cab! Ai an samu short P. A..."
Cikin mamaki P.A ya ce.
"Alhaji shot kuma? Shot kamar ya? Halisa fa suna ne mai kyau..."
Jinjina kai ya yi yana mai ƙara jinjina sunan a ransa a fili kuma yace.
"Halisa...Halisalamatu...Kai Ina? Sunanta fa ya yi kama da na salamatu gaskiya bana so. Ni fa ko kaɗan bana son su haɗa hanya da Hajiya Salamatu ta kowace fuska, saboda haka wannan ɗin sunan su ya yi shige bana sonta..."
Wani hoton ya nuno masa yana faɗin.
" To ga wannan, sunanta Maimuna..."
Karɓa ya yi yana faɗin.
" Eh to, wannan ɗin za ta yi. Daman kuma a aure ba'a son a fiye ruwan ido ko ba haka ba P.A?"
"Sosai kuwa Ranka ya daɗe...ka yi zamanka da wannan wallahi za ka ji daɗin..."
"Kai P.A bana son fa zaƙewa. Wallahy duk ka turani na aure ta wani abu ya biyo marar daɗi da kai zan yi kuka...kai tsaya ma.."
Ya faɗa yana mai ƙara fuskantar P.A Ishaq da kyau ya ce.
"Wai P.A ko dai haɗa baki kayi da en Matan nan ne?"
Ido P.A ya zaro tare da dafe ƙirji ya ce.
"Ni kuma ranka ya daɗe? Kai ma kasan har abada ba zan taɓa cutar ka ba kuma ba zan bari a cuceka ba. Wannan ɗin na san gidan da ta fito gidan mutunci ne da tarbiyya shiyasa naga dacewar ku da ita."
Jinjina kai ya yi yana mai yarda da kalamansa ya ce.
"Shi ke nan. Gobe idan Allah ya kaimu sai mu shirya ka kaini gidan nasu a saka rana da komai..."
"To ya yi Alhaji. Allah ya kaimu rai da lafiya."
Daga haka ya tattara ya kama hanyar waje. Har ya kusa fita sai yaji ya sake kiran sunansa. Yana juyowa bayan ya amsa ya ce masa.
"Ka na ji P.A....ka tura mata dubu ɗari kace na ce ta saka kati kafin na zo goben."
"To ya yi, an gama ranka ya daɗe Allah ya ƙara girma."
Cikin jindaɗin addu'ar sa ya yi murmusa sannan ya ce.
"Amin amin. Kai ma in sha Allahu kana da dubu biyu."
"Godiya nake ranka shi daɗe. A huta lafiya."
******
Gefen Anaam kuwa, sai da suka ƙara tsawon sati biyu a asibitin bayan ta ƙara warwarewa sannan aka basu sallama. A yanzu ta warke sosai, sai dai rashin walwalarta da son kasancewa ita kaɗai ne abin da yake damun su. Suna trying sosai wurin ganin ta saki jikinta but daga zaran ta ganta ita kaɗai sai kawai mood ɗinta ya canja lokaci ɗaya sai ta ji abubuwa suna dawo mata ma su ɗaci da raɗaɗi a rai.
But likitan ya tabbatar musu da cewa, matuƙar dai za su ci gaba da bata kyakkyawar kulawa to In Sha Allahu a hankali komai zai wuce.
******
Emerald Residency Apartments,
Street 12, Green Park area.
New Delhi,
India.
Zaune suke a babban parlourn gidan Mukarram ɗin suna cin abincin dare. Ammie, Na'imatu, Anaam, Aysher, Mubarak, da kuma su Mufida ne kaɗai a wurin.
Suna nan suna cin abincin suna ɗan taɓa fira kaɗan sai ga Abbah da kuma Mukarram sun yi sallama sun shigo.
Cikin farin ciki Hajiya Nasmah ta kalli Alhaji Galadima ganin an kwance ɗaurin da aka yi masa a hannu ta ce.
"Masha Allah! Hannu ya yi kyau kenan?"
Jinjina kai ya yi shi ma da murmushi ya ce.
"Alhamdulillah! Sai godiyar Ubangiji, hannu ya warke, kinga takardar sallama nan aka bani, saboda haka gobe In Sha Allahu za mu tafi gida. Duk mai wata siyayya ko wata ziyara ya yi ta a daren nan, gobe gida zamu juya."
A tare suka kalli Anaam sannan mukarram ya ce.
" Anaam would like to visit your Favorite Supermarket?"
Da sauri ta girgiza kanta alamar a'a.
Ajiyar zuciya Mubarak ya sauke a hankali tare da ajiye spoon ɗin hannunsa ya janyo hannunta yana kallon ta ya ce.
"Ya kamata ki je, an ƙara gyaran wurin nan an ƙawata shi sosai fiye da yanda kika san shi a baya, za ki yi farin ciki da nishaɗi sosai idan kika ga wurin a yanzu, rabon ki da can tun kafin ki fara karatu..."
Jinjina kai Aysha ta yi tana murmushi ta ce.
"And we will all go together..."
Ɗago kanta ta yi ta kalli Aunty Ayshar. Ganin hakan yasa ta yi mata murmushi sannan tana mai bata assurance ta ce.
"Yes! We are going together...let's go and change..Kowa ya je ya shirya."
Nan cin abincin ya watse suka je suka shirya ba ɓata lokaci suka fito suka wuce.
******
Bazaar-Ambience Mall,
New Delhi,
India.
Tun da suka shiga favorite mall ɗin ta zuciyarta ta cika da nishaɗi. Da gaske wurin ya ƙayatar da ita sosai fiye da baya.
Wurin tidy beers ta zaga ta shiga zaɓa kamar yanda ta saba, wanda a duk lokacin da suka shigo su ne first choice ɗin ta, duk da cewa su Mufidah ba su barin ta da su, kai ko ta yi nasarar tsallakawa da su su ma su Fatima idan sun zo ba barin su suke ba.
Ta ɗauko wata kenan ta tsaya tana dubawa ta ji muryar mutum a bayanta a hankali yana faɗin.
"Hlo..."
Waigowa ta yi a ruɗe tare da ɗan ja baya kaɗan ta zuba ido tana kallon shi.
"How are you??"
Baya ta ƙara yi sosai tana mai fasa ihu wanda nan take jikinta ya hau ciccira ta ƙanƙame tidyn da ke hannunta sosai.
Rige-rigen isowa suka yi wurin ta harda ma'aikatan wurin suna bincikar abin da ya same ta.
Shi kuwa guy ɗin, tsayensa Kawai ya yi tare da saƙala hannayensa cikin aljihun wandonsa ya tsaya yana kallon cike da mamakin ganin irin reaction ɗin ta. Ta ya ya daga magana haka za ta gigice tana wannan kukan?
Wani kallon Mukarram ya yi masa sannan ya matso a fusa ce ya saka hannayensa biyu ya ture shi ta ƙirjinsa ya ce.
"Who are you? And why are you here?"
Lumshe idanunsa ya yi a hankali ya buɗe sannan ya girgiza kai ya ce.
"Ba abin da na yi mata, tambayar ta na yi kawai ya take..."
Cikin zafin rai ya ce.
"and why did you do that? duk matan da suke wurin nan, ba ka ga wacce za ka tara ba sai ita?..."
Hannunsa Aysha ta riƙo hankalinta a tashe ta ce.
"Abban mufeed please is ok...please let's go.."
Hannun Anaam Ammie ta ja da sauri suka fice daga mall ɗin ganin irin yanda ta tsorata sosai tana wani kuka tamkar numfashinta zai ɗauke.
Sayayyar da ba su tsaya yi ba kenan suka koma gida.
Ya jima a tsaye yana kallon su har saida suka ɓacewa ganin sa sannan shima ya wuce ya hau mota ya tafi.
Su Anaam kuwa, bayan sun koma gida ta gama shirin bacci kenan ta ji an turo ƙofa an shigo, Yaa Mukarram ta gani.
"Anaam! Miye wannan mutumin ya yi miki? Ya faɗa miki wata magana ne?. Did you know him somewhere?"
Da sauri ta girgiza kai alamar a'a sannan a rauna ne ta ce.
"Ba bu abinda yace min Yaa Mukarram, I'm just scared."
"Is okay! Ki kwanta ki huta, Allah ya tashemu lafiya."
"Zan je wurin Abbah ne"
"Okay to."
*******
Gidan Alhaji Gimba kuwa. Hajiya Salamatu na zaune a parlour ita da mai aikinta tana yi mata lissafi za ta aike ta kasuwa taga ana ta shigowa da saitin akwatuna.
Mamaki ne da al'ajabi ya kamata domin ita dai kaf cikin dangin ta dana Alhaji Gimban ba ta san da zancen cewa wani na neman auren da za'a kai masa lefe nan kusa ba.
✍️ OUM-AMEER ✍️