Free chapter · Read without an account
PAGE 18
D U H U N D A R E
A 2026 N O V E L
BOOK ONE
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
AMEENA IBRAHEEM
OUM-AMEER
Arewapen: @Oumameer2671
Wattpad: @Ummu-Amir
PAGE 18
***
*Albishirinku jama'a shin ko kuna da labarin katafaren group ɗin mu, da mu ke tura KAYAN KITCHEN da KAYAN ƊAKI, har ma da KAYAN YARA MAZA DA MATA, ba mu tsaya a nan ba duk wasu abubuwan da UWAR GIDA DA AMARYA HAR DA 'YAN MATA masu CAPACITY ke bukata muna turawa, kayan mu na kasashen ketare ne kama daga Kayan kitchen, Kujeru da gadaje har da atamfofi, laces da Abaya, fashion net da bedsheets, hijabs gowns, caps, ribbons duk muna da su akan farashi mai RAHUSA, ga masu sayen ɗaya ko sari muna turawa ko'ina a cikin aminci, mutanen mu na kasashen waje kamar Chadi, Nijar, Kamaru, Ghana duk ba'a bar ku baya ba muna tura muku kaya har kasashen ku. Farashin kayan mu tamkar sari ne zaku saye har ku ɗaura ta ku riba kuma muna discount.
Ga masu bukatar kayan mu sai ku hanzarta shiga wannan link.💃💃💃
Sai da ya sauka daidai ƙofar gidan sannan ya tabbatar da cewa ya tabka babban kuskure. Haƙiƙa idonsa ya rufe, babu abin da ya ke so ya ji ya gani fiye da ganin Anaam ido da ido, it take him long to see her, tun ganin da ya yi mata a India. Ya kasa baccin kirki ya rasa nutsuwar sa. Haƙiƙa sai yanzu ya ƙara fuskantar miye ma asalin rayuwar bayan wacce ya fito a baya, ɗan Adam girma ne da shi daraja ce da shi, idan ka zalunce shi sai haƙƙinsa ya ɗaiɗaita maka rayuwa ya hana maka zama lafiya. Da ace ya ɗauki maganar mahaifiyarsa tabbas da duk wannan ba ta faru ba.
Idan sau dubu ya tuna abin da ya faru tsakanin shi da Anaam sai ya ji har cikin zuciyar shi tamkar zai mutu, dare da safiya a yanzu duk ɗaya ne a wurin shi, tunanin halin da take ciki ya hana mishi sukuni. To amma yanzu da ya zo gidan su as matsayin waye ya zo? Wa yake nema? Idan ya ce Anaam miye alaƙar da shi ita? Idan yace wurin ahlin gidan ya zo mi zai ce ya kawo shi? Ya ce shi ne wanda rapping na ta? Oh no! Babu abin da ya yi making sense daga ciki...
"Malam Ya dai?"
Ya ji muryar Adam ta karaɗe masa kunnuwa a lokacin da bai tsammata ba.
Shi kuwa Adam ɗin ƙara kusanto inda yake ya yi yana mai ci gaba da yi masa kallon tuhuma ya ce.
"Tambayarka nake waye kai? And wa kake nema a nan?"
Shiru ya yi tare da tsura masa ido na wasu en daƙiƙu sannan daga ƙarshe ya jinjina kai ya ce.
"Gidan wani friend ɗina nake nema yace a nan Layin suke..."
"But you are just standing here since, Kuma sai wani kallon gidan nan kake, ai idan baka san abu ba tambayawa za ka yi..."
"Eh to, haka ne, I'm sorry."
Jinjina kai Adams ya yi ya ce.
"Ya ya sunan friend ɗin naka?"
Ka ji kuma wata sabuwa! Waye zai ce yana nema a wannan Layin? A yanda gidajen nan suke a jere bisa tsari da burgewa baya tunanin akwai gidan da zai ambaci sunan wani ba'a san shi ba. And idan kuma ya ce bai san wani ba dole zai zarge shi kuma....
"Tambayar ka nake malam miye sunan shi?"
"While..abokin karatu na ne a London, to ya taɓa bani labarin garin su da gidansu sau ɗaya, shi ne na ce bari na yi masa ba za ta tun da har Allah yasa yau na shigo ƙasar su kuma garin su, shi ne nake bin labarin da ya bani ina neman gidan. Sunan sa Ahmad Usman..."
Ɗan Jim Adam ya yi na ɗan lokaci alamar yana nazarin sunan sannan daga ƙarshe ya kalle shi ya ce.
" Daman da na ganka ban ma yi tsammanin cewa kana jin Hausa ba, amma kai kuwa ka yi kasada da kace zaka gano gidan su ta wannan hanyar. And magana ta gaskiya kuma babu wani gidan su Ahmad Usman dai a wannan Layin, sai dai ko za ka bincika wancan second line ɗin ko kuma ka kira shi a waya."
Ɗan murmusawa ya yi tare da jinjina kansa yana kallon Adam ɗin ya ce.
" Thank you so much. Bari na je na gaba na bincika, I just want to surprise him ne."
"Okay...Allah yasa a dace."
Juyawa ya yi kai tsaye ya je gari ya kama Hotel ya shige ya kwanta akan gado tamkar wani marar lafiya. Wai yau Maheer shi ne wanda ya ƙware da yin Ƙarya? Hirar su da Adam ba ƙaramin wahala yasha ba, domin ya kasa fitowa ya faɗa masa cewa ga wanda yake nema. Ko kaɗan ba zai yi kuskuren ambatar sunan Mas'ood Galadima ba, domin a duniya ba shi da wani maƙiyin da ya wuce shi. 'yarsa ce wacce babu ruwanta a ciki ya yi wa laifi, saboda haka ita kawai zai nema ya faɗa mata gaskiya sannan kuma ya roƙi gafararta ko Allah zai sa ya samu sukunin rayuwa.
To amma ta ya ya zai ganta? Tamkar wani magani daga bayanan ya rasa kowace hanya zai bi wurin ganinta. But wata ƙil idan ya ci gaba da zuwa ƙofar gidan yau da gobe zai iya ganinta a waje ko kuma a mota. To kuma yaushe hakan zai samu? Ga shi ya katange Maamin sa daga samun damar magana da shi domin kada ta gano inda yake a yanzu, but har tsawon yaushe kenan zai ci gaba da hana ta magana da shi? Dole yana buƙatar mafita da gaggawa.
*******
Gidan Alhaji Gimba.
Tun ranar da Hajiya Hadiza ta zo gidan Hajiya Salamatu ba ta sake sanya Faris a idonta ba. Kiran duniya ta yi mishi amma ta kasa samun wayar shi, ta yi kuka har ta gaji, ta bincika ko'ina dangi da mutanen kasuwancin su amma ta rasa ina ne ya shiga.
Shi kuma gogan ko a jikinsa, damuwar sa ɗaya ce Maimunarsa. Idan yana tare da ita baya ji baya gani, duk tsawon lokacin nan da suke shafe yana ɗakin Maimuna zaman shi hankalinsa kwance, wata ƙila ma tana tunanin ya manta da cewa raba kwana ake tana da haƙƙin kwananta a kansa. Sai dai rashin jituwar da ke tsakanin su yasa ko kaɗan ba ta sa wannan a ranta ba. Damuwar ta ɗaya ce ɗan ta tilo da take da shi. Maimuna Sam babu alheri a tare da ita. Idan tasan girma da muhimmancin iyali Sam bai kyautu ace ta nemi shiga tsakaninsu ba da zuwanta na jiya-jiya.
Ta Yi kuka har ta gaji, wanda daga ƙarshe ta kawo na gani ta zuba musu, iyaka idan ya fito su gaisa kuma ko shi tana ji tana gani watarana ko gaisuwar ta ta baya amsawa,abinci kuma har yau ita ce take girka shi idan kuma ba ta yi ba ya hauta da zagi da cin mutunci.
Yau ma tana zaune misalin ƙarfe goma na dare sai ga kiran Faris tamkar a mafarki. Hannu na rawa ta ɗaga da sauri ta ce.
"Faris....! Haba Faris miye ya yi zafi haka?"
Cike da jin kewarta a ransa ya ce.
"Ya ce na bar masa gidansa...mi zan zauna na yi kenan? Barin gidan shi ne maslaha a garemu gabaɗaya."
Kuka ta fashe da shi tare da girgiza kanta tamkar suna gaban juna ta ce.
"Idan yace ka bar masa gida ni ba gani ba! Idan shi baya da buƙatarka ni ina da, domin bani da wani ɗa a duniya sai kai,miye amfanin zama na a nan yanzu?"
"Mum..."
Ya ambata a rauna ne.
"Ki zauna a gidan ki kasa ki damu dani, ina nan lafiya lau, ki kwantar da hankalinki."
"Faris..Ina jin tsoro, zuciyata ta karye da waɗan nan ɗabi'un mahaifin naka..."
"Ki yi ta haƙuri, watarana sai labari, ki daina saka matsalolin sa a rai domin ba yau ya saba ba, kin fi kowa sanin waye shi, saboda haka ki ƙara haƙuri kin ji Mum."
"Dan Allah ni dai ka dawo gida, kada ka biye zancen sa dan Allah ka dawo..."
"I will...kada ki damu."
Daga haka ya tsinke wayar ya bar ta da sharar hawaye.
******
Na'imatu.
Tun da Abbah ya sanar da ita zancen aurenta ta hanawa kan ta sukuni. Tun ranar ta yanke waya da Haisam tamkar wanda ya aikata mata wani mummunan laifi.
Yanzu ma wanka ta fito bayan an gama mata gyaran jikin da take jin idan ana yinsa tamkar ana ƙonata ne, domin sam bata ra'ayi bata kuma muradi. Da Ammie ta ji roƙon ta da yanzu ba ta ɓannata kuɗin ta wurin wannan aikin ba domin babu wani amfanin da zai yi mata.
Wayar ta dake gefen ta ne ta ci gaba da ringing ba tare da samun wani sarari ba, a ran ta mamaki take halin naci irin na Haisam, da ace yana da zuciya da yanzu ya haƙura ya daina kiranta. Ga mata a duniya mi zai dole sai ita bayan ta ce ta fasa.
A zuciye ta ɗaga cikin rashin mutunci ta ce.
"Wai Haisam ana dole ne?"
Daga can ɓangaren Haisam ɗin ya girgiza kan sa cikinn sanyin sa ya ce.
"A'a! Ba'a dole Na'imatu, amma ya kamata zuwa yanzu ace kin haƙura, na san na aikata miki kuskure na rashin sanar dake amma ki yarda dani, wallahy ko a ranar da muka yi waya da daren nan ban san cewa an saka ranar ba har an bugo IV..."
"Wannan kuma kai ta shafa..."
Jin tayi an warce wayar daga hannun ta an wanda ba shiri ta ɗago ta kalle ta, tana ganin Anaam ce ta ɗauke kai tare da zura hannu ta ci gaba da aikin shafe-shafen da take.
Kashe wayar Anaam tayi gabaɗaya tare da jinginawa jikin dressing mirror ta ɗan ɗosana ɗuwawunta kaɗan ta zuba mata ido tana kallonta na tsawon lokaci sannan daga ƙarshe ta jinjina kanta ta ce.
"Aunty Na'imatu hakan sam ba daidai bane. Kuma na san ba halin ki ba ne, Haisam bai da laifi a wannan maganar, ni banga wani abin tada jijiyar wuya ba da har kika zaƙe kina ta wannan fushin alhali kuma kin san ba bu fashi auren nan dole za'a yi..."
Ranta a ɓace ta ce.
" But why yake min ƙarya cewa wai ban san da zancen ba? Akwai wanda zai shige gaba ya yi masa zancen auren sa idan bai nuna yana da ra'ayi ba?"
Murmushi Anaam tayi tare da girgiza kai tana kallon Na'imatun ta ce.
" Yaa Na'ima ki yarda kawai cewa ba ki da gaskiya,amma ni banga laifi a nan ba. Kuma wallahy mun yi magana da shi ya rantse mini da Allah cewa shi ma bai san da zancen ba sai da yayansa ya kira sa ya sanar masa cewa an gama saka rana..."
Faɗowa ta yi ta zauna a gefenta ganin yanda take ta wani ƙara ɓata rai tana ciccika kamar an kwaɓa fulawa ta ce.
" Yaa Na'ima ni fa ina jiye miki wannan abin kunyar da kike neman janyowa kan ki, domin watarana idan kika zo kina mana ƙafafa da Haisam wallahy har ya Mubarak ba zai ƙyale ki ba, sai ya dinga miki tsokanar da sai kin yi kuka. Ki yi haƙuri ki lallaɓa zuciyar ki ki kori shaiɗan...."
Wata harara ta maka mata a ƙasan ido sannan ta yi ƙwafa ta miƙe taje ta ɗauko kayan ta a closet ta saka.
" Wallahy Yaa Na'ima kin fito amaryar Haisam sak! Kamar yau ne bikin ma..."
" Wai Anaam dan Allah ba za ki iya fita harkata ba ne?"
Miƙewa ta yi tana ci gaba da dariya ta ce.
"Allah ya huci zuciyar amaryar Doctor Haisam Usaid..."
Towel ɗinda ta cire ne ta raruma ta jefe ta da shi da ƙarfi sai ga Anaam ɗin ta zuba da gudu ta yi waje tana dariya.
Tana fita ta shige ɗakin Ammienta ta ɗauko wayar Ammien ta kira Haisam ta ce.
"Kana ji Likita? Kada ka damu da abin da take dan Allah kar ka ji haushi...komai zai wuce."
Cikin jin daɗin irin karar da Anaam ɗin ke masa ya ce.
"Ba damuwa, ni ko kaɗan ban ji haushi ba daman, na san ɓacin rai ne watarana zai wuce in sha Allah. Na gode sosai Ƙanwata, Allah ya bar zumunci."
"Amin. Ango Yaa Na'imata,sai an jima."
*******
Maheer.
Washe gari tun misalin ƙarfe sha ɗaya na safe ya sauka a farkon Layin gidansu.
Bakin gate ɗin wani gidan ya samu ya tsaya tare da ciro wayarsa ya kira Hamad ya ce.
"Hamad na kasa yanda zan yi na ganta...and I need to see her."
Cike da gatse Hamad ɗin ya ce.
"Miye ya hana ka shiga gidan kai tsaye?"
"No! Kai ma kasan hakan ba zai faru ba, jiya ma common Mai gadin gidan na su na kasa faɗa masa gaskiyar cewa Ita nake nema....Allah dai ka rabamu da mugun ji da mugun gani Hamad. Imagine wai ni a gaban gate man and ya tambayeta sai ƙarya na shirga masa tsabar rashin gaskiya."
"Shiyasa na yi ta ƙoƙarin dakatar da kai Maheer. Ta ya ya kake tunanin ka tsaya ido da ido ka faɗa mata cewa kai ne and ta yafe maka kawai ka wuce? Hauka kake na gaya maka! Leave that Gurl and go back home, kaje ka yi ta istigfar....."
"Hamad ba za ka fahimci halin da nake ciki ba. A yanda na fahimce ta tana da sanyi da sauƙin hali, ya kamata na sauke girman haƙƙin ta da yake kai na..."
"Duk na ji fa! But ta ya ya?"
"while....ni na san yanda zan yi handling komai da kai na."
"Okay oo! Fatan alheri Maheer Tahameer Alee. But idan aka yi rashin sa'a aka kama ka aka rufe ka, kasan fa kai da iskar duniya mai daɗi har abada."
"Fatan da kake min kenan?"
"No! I'm just telling you the real truth Saboda naga alamun cewa kanka ya kwance..."
Lumshe idonsa ya yi a hankali sannan ya buɗe ƙarshe ya ce.
"Sai an jima."
Kusan wuni ɗaya zungur ya shafe a nan tare da mai gadin da ya zauna tare da shi a bakin gidan da ya tsaya, a masallacin gidan suka yi azahar suka yi la'asar but ga mamakin sa tun zaman sa wuni ɗaya ko mota ɗaya bai ga ta fito ko ta shiga gidan Alhaji Mas'ood Galadima ba. And ko mutum ɗaya bai ga ya shiga ko ya fita daga gidan ba.
Kallon Matashin mai gadin da suke zaune a benci ɗaya ya yi ya ce.
"Wancan gidan kamar ba kowa?"
Kallonsa Matashin ya yi ya ce.
"Miyasa ka ce haka?"
"Kawai dai na ga, wuni ɗaya amma ko tsuntsu ban ga ya shiga gidan ba."
Waigawa Matashin ya yi ta kowane ɓangaren wanda sai da ya tabbatar ba kowa sannan ya yi ƙasa da murya ya ce.
"Ai sun ji ma da yin Hijira bawan Allah."
Cike da zaƙuwa Maheer ɗin ya ce.
"Hijira? Hijira as how?"
"A'a fa! Kada ka laƙa mini jakar tsaba kaji su bini bawan Allah, kada ka zo ka wuce ni ka bar ni cikin jalala alhali ko saninka ban yi ba haɗuwar bakin gate rabuwar kan benci..."
Hannu Maheer ya zura a aljihun wandonsa ya ciro kuɗi masu matuƙar yawa ya ɗora masa a jikinsa.
Wani irin dafewa matashin ya yi yana wani zare ido.
✍️ OUM-AMEER ✍️