Free chapter · Read without an account

55

by ZAHRAA · Bayan Murmushi

55⌨️💬


Daren farko na zuwan su Nene ya kasance dare mai cike da nishadi . AK ya dawo gida shake da ledoji, ya siyo wa Nene manyan rigunan sanyi (Long Jackets) masu kauri, sannan ya ƙaro wa Sameena wasu kayan sanyin masu kyau.

"Abdulkadir, ashe dama haka sanyin garin nan yake? Ni na ɗauka sanyi ne irin na lokacin hunturu a gida, ashe nan kankara ce," Nene ta faɗa tana ƙoƙarin sanya rigar sanyin a saman atamfar ta .

Washegari asubanci Nene ta yi. Ta shiga kitchen ta buɗe akwatinta, ta fito da garin semovita da ta taho da shi. "Ke Maryam, ba zan bari wannan tattaba  kunnen nawa ya lalace da cin abincin gwangwani ba. Ina muciyar gidan nan?"

Farhana ta yi dariya, "Nene, a nan ba a amfani da muciya, komai da wuta ake yi."

Nene ba ta yarda ba, ta shiga bincike har ta gano abin rolling ɗin cake na katako (wooden rolling pin). "Yauwa! Wannan ai zai yi muciya." Haka Nene ta tuka tuwo da abin murji, ƙanshin tuwon ya gauraye gidan Chestnut Hill, Brianna sai mamaki take yi.

Nene ta rinka ba Farhana abinci tana lallashi, tana kula da ita sosai ita  kuwa Sameena, tana maƙale da Farhana, suna ta hira da kallon hotunan mutanen gida.


The following week Ak ya dauki nene da sameena zuwa grocery 

Suna isa babban kanti, kowa ya rinka kallon Nene. Ganin tsohuwa sanye da jacket da hijabi a Amurka ba bakon abu ba ne, amma yanayin takun Nene da yadda take rarraba idanu shi ne abin kallo.

Nene ta tsaya a gaban inda ake sayar da gasasshiyar kaza (Rotisserie Chicken). "Ikon Allah! Abdulkadir, kalli kaza tana juyawa ita kadai a cikin wuta? Lallai turawan nan basu da sauran aiki. Maza kwaso mana guda biyar, kaga Maryam tana bukatar Naman kaza sosai ."

AK yana tura keken sayayya (trolley) yana dariya, ya kwaso kazar. Nene ta rinka taba kowane ganye da ta gani, tana tambayar ko "shuwaka" ce ko "yakuwa".

"Abdulkadir, su kuma wadanan masu cinye zallar ganye Kamar Akuyoyi fa?(Lettuce) , wasu couples ne ke cin abinci a gefen store din iya ganye suke chi "Nene, salat ne, haka ake cin sa danye."su ake kira vegetarians basa cin nama sai ganye 

Nene ta tabe baki, "ganye dai ? Lallai ashe har yanzu akwai sauran kauyanci a tare da turawan nan. Mu dai kwaso kaza da kifi, shine abincin mutunci."


Suna dawowa gida, Farhana ta tarar da AK yana ta faman taya Nene fito da kaya daga leda, yana mata hira . Farhana ta tsaya tana kallon sa, zuciyarta tana ta tafasa.

Bayan Nene da Sameena sun shiga daki, Farhana ta jawo AK gefe. "Honey,jia karfe takwas ka dawo. Ka gaya min gaskiya, meyasa da nake ni kadai kake dawowa sha daya na dare, amma yanzu tunda su Nene sun zo kake dawowa da wuri?"

AK ya dan daburce, ya sosa keya. "Wifey, kinsan fa baki ne, ya kamata in rinka zama dasu in debe musu kewa..."

Farhana ta kure shi da ido , "Wato kewa ta bata dame ka ba kenan? Watanni nawa  ina zaune ni kadai da ciki, Baka tunanin dawowa da wuri ka debe min kewa ba sai yanzu? Ashe kana da ikon dawowa duk lokacin da kake so, amma kake barina a nan?"

Muryar Farhana ta fara rawa saboda da bacin rai. AK ya lura cewa tabbas ya yi kuskure. Ya janyo ta jikinsa, ya rada mata a kunne. "Kiyi hakuri Wifey. Na san ban kyauta ba. Amma yanzu na gane kuskurena, kuma koda su Nene sun koma, zan rinka dawowa da wuri gareki."

Farhana ta ture shi  tana kuka-Karya kake yi, tsoron masifar Nene kake yi shi yasa kake dawowa da wuri. Tsohuwar nan ai ba abar taba wa bace , masifa gareta.

Daga daki, suka  jiyo muryar Nene, "Maryam! Ke da wa kike fada ne a dakin nan? Kizo ki ji yadda kazar nan take da dadi, lallai Amurka akwai dadi!"

Farhana ta share hawayenta, ta kalli AK tana hararar sa kana ta nufi falon ."


Kwanakin haihuwar Farhana (EDD) sun cika taf, yanzu ko numfashi take yi kowa a gidan Chestnut Hill fargaba yake yi. Farhana ta zama "Gwamna," duk abin da aka yi mata ba ya yi mata daidai. Idan ta fara masifa, daga baya sai ta fashe da kuka ta ce kowa ya tsane ta.

Tana zaune a falo, ta kifa wayarta a gaba suna Skype da Diddi ta wayar Hamma Fahad.

"Diddi, yanzu ashe haka kika sha wahala kika haife mu mu shida? Wallahi Diddi wannan shi ne na farko, kuma shi ne na ƙarshe. Ba zan sake ba!" Farhana ta faɗa tana share hawaye da gefen mayafinta.

Diddi tana can tana dariyar tausayi, "Haba Maryama, yanzu kika fara. Ai idan kika ga abin da kika haifa, zaki mance da duk wannan wahalar."

Nene dake gefe tana tauna kaza, ta ɗago kai ta harari Farhana. "Ke Maryama, me nake ji kina faɗa? Wai ba zaki sake haihuwa ba? Kin manta kina da kishiya ne? Ai gara ki haifa guda bakwai, ki cinye gidan Abdulkadir!"

Farhana ta banka wa Nene wata uwar harara, "Nene don Allah ki kyale ni, ni fa mutuwa nake gani yanzu."ko daya ban sauke ba Kina mun maganar bakwai.


Wajen ƙarfe biyu na dare, Farhana ta fara nishi sama-sama. AK ya tashi a firgice, Nene ma ta fito tana gyara ɗaurin zani. "Abdulkadir, maza kwashe ta! Ga maganin nan na taho da shi daga Matazu, kace ta sha kafin mu isa."

AK bai ma saurare ta ba, ya ɗauki Farhana ya nufi mota. Aka bar Sameena da Brianna a gida suna ta faman addu'a.

A asibiti, Farhana ta sha wuya sosae. Duk da ƙoƙarin likitoci, yanayin jikinta ya ƙi bayar da haɗin kai, ga hawan jininta (BP) da ya ƙi sauka saboda fargaba 

"Mr. Abdulkadir, we have to move her for a C-Section (CS) immediately to save both the mother and the babies," in ji likitan.

AK ya sanya hannu yana zufa, yayin da Nene take ta kai-da-kawowa a corridor tana kiran sunayen Allah. Shi dai AK ya san cewa Twins ne (mace da namiji), domin Doctor ya gaya masa tun asali, amma ya ɓoye wa Farhana don kada hankalinta ya tashi tun da ciki ne na farko.


Bayan kusan sa'a ɗaya, likita ya fito fuskarsa ɗauke da murmushi. "Congratulations, Mr. Abdulkadir! You have a healthy baby boy and a beautiful baby girl. The mother is stable and resting."

AK ya kasa magana, sai hawayen murna. Nene ta rugo da gudu, "Ina suke? Ina jariran? Abdulkadir, biyu ne?"dazu kace mun yara biyu ne?da gaske biyun ne ?

Lokacin da aka kai su dakin hutu, Farhana ta fara buɗe idonta a hankali. Ta ga AK zaune kusa da ita, fuskarsa cike da farin ciki.

"Honey... na haihu?" ta tambaya cikin muryar dasashi.

"Kin haihu Wifey. Kuma Allah ya bamu kyauta biyu; mace da namiji. Look at them," AK ya nuna mata wasu ƙananan gadaje guda biyu dake gefenta.

Farhana ta zaro ido, ta manta da ciwon dake jikinta. "Twins? Honey, dama twins ne baka gaya min ba?"

Nene ta ƙaraso tana guda a hankali (yadda ba za a kore ta ba a asibitin Amurka). "Lallai Maryam, kin zama uwa! Namiji da mace? Ai yanzu kishiya ta kade! Abdulkadir, maza kira min iro  a waya in gaya masa na zama kakan tagwaye a Amurka!"

Farhana ta kalli jariran, ta ga yadda suke sheki kamar AK, ta ji duk wani daci da kiyayyar dangin miji ya fice daga zuciyarta. Ta san cewa yanzu ne asalin yaƙin zai fara a Najeriya, amma tana da manyan makamai guda biyu a hannunta.


.

AK ya fita corridor, ya kira Mummy a waya. Muryarsa cike da farin ciki ya ce, "Mummy, an sami ƙaruwa! Farhana ta haifi tagwaye, namiji da mace."

Mummy ta yi shiru na daƙiƙa biyar, kafin ta ce, "Lallai Abdulkadir, Allah ya raya su. Allah ya sa masu albarka ne." Muryarta ba ta nuna wani babban farin ciki ba kamar yadda AK ya zata, amma hakan bai dame shi ba 

Haka ma lokacin da ya kira Yaya Safiyya. "Tagwaye kuma? Lallai Maryam ta yi babban kamun kifi. Allah ya raya su."

Farhana tana kallon AK lokacin da ya dawo ɗakin, ta ga fuskarsa ta ɗan sauya. Ta san sarai irin amsar da aka ba shi, ta maida hankalinta kan jariranta.


Nene ta gama zagaye jariran tana musu (addu'a). Ta kalli nas-nas (nurses) ɗin asibitin da suke ta shiri don goge jariran da ruwan ɗumi da auduga. Nene ta harari ɗaya daga cikinsu.

"Ke Maryam, gaya wa waɗannan matan su janye hannunsu daga jikin yaran nan . Wane irin wanka ne wannan na shafa ruwa kamar ana goge tebur? Ni zan musu wanka da kaina!"

Farhana ta zaro ido, "Nene, a nan asibitin  su suke yi wa jarirai komai."

"Haba Maryam! Yaran naki ne  fa!Idan ban musu wanka na gaskiya ba, yaya kashinsu zai yi Kwari ? Abdulkadir, gaya musu su ba ni ruwan zafi na gaske , in nuna musu yadda ake wankan Matazu!"

AK ya yi dariya ya dafa kafaɗar Nene. "Nene, kiyi haƙuri. Idan mun koma gida Chestnut Hill, sai ki musu duk yadda kike so. A nan dokar asibiti ce."

Nene ta taɓe baki, "Toh, maza mu koma gidan, domin wannan goge-gogen da suke musu ba zai sa yara su yi ƙarfi ba. Kuma maza kace su kawo min kazar nan ta jiya, ina jin yunwa."


Bayan kwanaki uku, aka sallami Farhana. Suna isa gida, Brianna ta fito tana kuka tana murna. Sameena ta rinka ɗaukar bidiyon jariran tana sa wa a status: "The Boston Twins are home!"

Nene ta shiga kitchen ta ɗora ruwan zafi a babban tukunya (tukunyar da ta gano a gidan). "Yauwa! Yanzu za a yi wankan gaskiya. Maryam, maza kawo min su, in nuna miki aikin tsohuwa!"

Farhana ta kwanta a kan gado, tana kallon Nene tana shirya kayan wankan jarirain Ta ji wani irin daɗi. Duk da CS ɗin dake mata ciwo, ta san cewa tana da kariya—Nene a gefe guda, tagwaye a gefe guda, kuma AK a tsakiya.


Brianna ta tsaya tana kallon yadda Nene take zage damtse. Nene ta karɓi jaririn namijin, ta fara masa wankan gaske—irin wankan nan na murza ƙashi da goge kunne da hanci. Jariran suka rinka tsandara kuka, Brianna ta kusa kiran "911" saboda tsoron yadda Nene take juyasu.

"Nene, karki ji musu ciwo!" Farhana ta faɗa cikin fargaba.

"Yi min shiru Maryam! Ke ma haka aka miki kika yi ƙwari. Dubi yadda suke kuka, ai numfashin su ne yake buɗuwa," Nene ta faɗa tana dariya.


Falon Chestnut Hill ya cika da koke-koken jarirai da kuma ƙanshin magungunan gargajiya na Nene. Wayar Farhana ba ta huta ba; tun daga asibiti har zuwa dawowa gida, kiran murna yake ta shigowa.

Abdulkarim da Halima sun kira bidiyo suna ta murna, Fadila ma ta yi murna sosai da samun twins niece and Nephew .group ɗin Besties ya rude, kowa yana sa hoton jariran da Sameena ta rinka turawa ta wayar farhana suna kiran kansu "Anties din Massachusetts ."

Abun mamaki sai Bayan kwana 3  Hanadi ta kira. Muryarta ta nuna dacin kishi, amma ta daure ta ce, "Farhana sannu, Allah ya raya su." Farhana ta amsa ta a takaice, ta san ba don Allah Hanadi ta kira ba.

Daga ƙasar Italy kuwa, Anti Nafeesah ta kira tana ta murna, tayi alƙawarin aiko da kayan sanyi na musamman daga Milan. Daddy (Mahaifin AK) shi ma ya kira, muryarsa cike da alfahari, yana yi wa jikokin nasa addu'a.


Duk da wannan murnar, Farhana tana ta duba wayarta ko za ta ga sunan Mummy, Yaya Safiyya, ko Yaya Ramla. Amma shiru kaƙe ji babu sako bare kira. Ko da AK ya gaya musu a waya, basu nemi su ji muryar uwar jariran ba.

Farhana tana zaune a bakin gado, Nene tana taya ta gyara zaman jaririn namijin. Ta sauke ajiyar zuciya, "Nene, wai me na yi wa Mummy da zafi haka? Ko don na haifi tagwaye ne hakan ya ƙara ɓata mata rai?"

Nene ta taɓe baki, ta gyara wa jaririn towel . "Ke Maryam, rabu da su. Kiyayya idan ta shiga zuciya makanta take yi. Ba haka suka so ba , Allah ya nuna musu ikon sa a nan Amurka. Karki sanya damuwarsu a ranki, kinsan kina da hawam jini kuma yaran nan suna bukatar natsuwar ki."


AK ya shigo ɗakin, ya sami Nene ta gama wankan, tagwayen sun yi bacci luff  saboda dumin ruwa. Ya zauna kusa da Farhana, ya nuna mata pics din da akayi wa twins tin suna hospital .

"Wifey, mako mai zuwa zamu yi radin suna. Ko da yake baza mu yi taro babba ba saboda sanyi,gashi ba wasu mutane muka sani a garin ba amma inshaAllah zamu yi grand birthday dinsu a Nigeria .

Farhana ta kalle shi, Honey, ina so a sanya wa namijin sunan Abbi (Ibrahim), macen kuma a sanya mata sunan Diddi (rukayya). 

AK ya yi murmushi, ay tin  da kika haife su  na samu masu sunan su abbi.sosai farhana tayi mamakin karar da Ak ya mata fatan Allah ya raya mata Ibrahim Abdulkadir tambuwal da rukayya Abdulkadir tambuwal 



Ranar radin sunan tagwayen Boston ta waye cikin wani irin sanyi mai ratsa kashi, amma a cikin gidan Chestnut Hill, dumi da kamshin turaren wuta na "Oud" da na girkin Nene ya gauraye ko'ina.

Although Ak yayi Oder abinci daga restaurants kala Kala .

Bayan sallar asuba, AK ya sanar wa nene da sameena da sunayen da suka sawa twins Namijin ya ci sunan Ibrahim (Abbi),zaa  kirasa da Khalil. Macen kuma ta ci suna Rukayya (Diddi), ana kiranta Sultana.

Nene na jin sunayen iyayen Farhana ne aka sanya, ta saki guda tana gyara daurin zaninta. "Iyye ! Ibrahim da Rukayya! Lallai Maryam kin kyauta, kin girmama iyayen ki .Abdulkadir, Allah ya raya Khalil da Sultana, Allah ya sa su zama Kamar kai ,a hankali farhana ta furta ba ameen ba.


Wajen karfe biyu na rana, baki suka fara isowa. Farhana ta fito cikin wani hadadden leshi mai launin Cream and Gold Wanda ta taho dashi tun tana amarya bata sami damar sawa ba kanta ya sha daurin dankwali na alfarma. Duk da nishin CS da take yi kyan da Yau  ya zarce misali.

Abokan AK na kusa sun hallara; Dr. da matarsa, sai kuma Jamal da Chole wadanda suka dawo daga tafiyar kasuwancinsu. Brianna tana ta faman rarraba ababen sha da snacks na zamani, yayin da Nene take raba tata kazar da ta sha daddawa da citta.

Daga karshe sai ga makwabtansu, tsofaffi Mrs. and Mr. Henderson. Sun zo rike da hannun juna, fuskarsu dauke da murmushi da manyan kyaututtuka na jariran.


Nene tana zaune a falo, ta zuba wa Mrs. Henderson ido. Ganin yadda tsohon nan Mr. Henderson yake ririta matarsa, yana ja mata kujera sannan ya zauna yana shafa hannunta a fili, ya sanya Nene ta taba Farhana da gwiwar hannu.

"Ke Maryam, duba can! Wadancan tsofaffin (The Hendersons) me suke yi haka? Dubi tsohuwar can, duk ta

Yamushe  amma tana wani lumshe ido mijinta yana shafa mata hannu kamar amarya. Su basu da kunya ne a kasar nan?"

Farhana ta yi dariya kasa-kasa, "Nene, soyayya ce mana. A nan koda ka tsufa, matarka ita ce abokiyar rayuwarka ta har abada."

Nene ta tabe baki tana mamaki, "Ikon Allah! To amma dubi tsohuwar, har da wani jan baki (lipstick). Mu a Matazu ai idan ka kai wannan shekarun, ko kallon mijin baka yi bare wani shafar hannu. Amma gaskiya turawan nan sun iya rainon so, dubi yadda tsohon yake kallonta kamar yau ya aure ta."


. Farhana ta  dauki hoton tagwayen a hannun AK, ta dora a status dinta da rubutu: "Khalil & Sultana: My world, my strength. Named after the best parents, abbi and diddi 

A can Najeriya, Hanadi tana ganin hoton tsofaffin Henderson da matan abokan AK a gidan ga mayan rich tycoons sunzo ta ji kishi ya turnuke ta. Ganin Farhana ta zama uwar gidan Amurka tana karbar baki manya, ya sanya ta jin cewa daukakar Farhana tana neman zarce tata.

Mummy ma tana Jin labarin  sunayen iyayen Farhana aka sa, ta Kara kullarta farhana 


Bayan an gama cin abincin , Mr. da Mrs. Henderson suka tashi domin yin bankwana. Mr. Henderson ya sanya wa matarsa jacket dinta, sannan ya sumbaci tafin hannunta yana yi mata murmushi.

Nene ta kasa jurewa, ta taso daga inda take zaune ta nufi wurinsu, fuskarta dauke da mamaki. Ta kalli Farhana, "Maryam, gaya musu su dakata! Ina so in tambayi tsohuwar nan wani asiri   take amfani da shi."

Kowa a falon ya yi tsit basa Jin me nene ta fada dai .Farhana ta dan ji kunya, ta tambayi Nene, "Nene, me zaki tambaye ta?"

Nene ta nuna Mrs. Henderson da yatsa, "Gaya mata nace, shakarta  nawa? Kuma meyasa har yanzu mijinta yake ririta ta haka? Ko akwai wani maganin daka-da-fura da take sha ne? Kalle ta yadda take wani kyalli kamar amaryar bana."

Farhana ta dan yi gyaran murya ta fassara wa Mrs. Henderson tambayar Nene cikin sigar wasa: "My grandmother is admiring your beautiful relationship and wondering how you keep the spark alive at this age."

Mrs. Henderson ta bushe da dariya, ta kama hannun Nene cikin kauna. "Tell her it's just love, patience, and always being each other's best friend."

Farhana ta fassara wa Nene. Nene ta taɓe baki, ta waigo wurin AK. "Abdulkadir, ka ji ko? Wai soyayya da hakuri. Amma gaskiya kam, tsohuwar nan ta iya zama da miji. Maryam, kema kiyi koyi da ita, ki rinka ririta Abdulkadir ko kya samu rance idan kin tsufa."

Duka falon aka fashe da dariya da aka fassara masu abinda nene tace .har su Jamal da Chole. Mr. Henderson ya mika wa Nene hannu don su gaisa, Nene ta ja baya da sauri tana yarfa hannu.

"A'a! Dakata tsoho! ba a taba min hannu haka kawai. Sai dai idan gaisuwa ce ta baki."

AK ya kusan faduwa daga kan kujera saboda dariya. Daga karshe tsofaffin suka tafi suna ta yabon "Strong African Grandmother."


Bayan baki sun tafi, Jamal da Chole sun ajiye wa Farhana dankareriyar kyauta ta dala dubu biyar ($5,000) a matsayin barka da suna. Dr. da matarsa kuma suka kawo hadaddun kayan jarirai na Designer.

Amma babban abin farin cikin shi ne kiran da Diddi da Abbi suka yi ta bidiyo.

"Abbi, ga Khalil dinka nan," Farhana ta fada tana nuna masa jaririn namijin.

Abbi ya share hawayen murna, "Nagode Maryama. Allah ya raya su. Allah ya miki albarka 

Diddi ma taji dadin ganin mai sunanta 

Gabadaya yan gidansu farhana sunji dadin wanan karar .

Daren ranar, bayan gidan ya yi tsit, AK ya shigo dakin ya sami Farhana tana kallon tagwayen. Ya rungume ta ta baya, "Wifey, Thank you for Khalil and Sultana."

Farhana ta lumshe ido, tana jin dumin AK da kuma natsuwar cewa yanzu ne asalin rayuwarta ta "Bayan Murmushi"ya fara.



Authors note ✍️


Shin “Zuciyarku  ta shirya da abinda ke zuwa nan gaba … akwai wani sirri  da zai sauya rayuwar kowa 💔”

Wa Ina farooq ne?

Nusaiba fa?mai shirun ta yake nufi ?

Auren precious da Hamma sajid yana yiwuwa kuwa ?

Mai fateeha take boyewa ne game da rayuwarta?

Lastly Wanene AK?

Ku cigaba da bibiya dan warware muku zare da abawa 

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol