Free chapter · Read without an account
57
57⌨️💬
Zee ta shafe kusan awa guda tana kuka bayan Farhana ta kashe mata waya. Ta kasa yarda cewa Farhanar da suka yi rayuwa ta mutunci da ita ita ce ta daka mata wannan tsawar. Cikin zafin rai da kuma tausayin ƙawar tata, ta latsa lambar Diddi (zee tana da number diddi tun bikin farhana ta amsa suna gaisawa time to time )
Diddi tana zaune a tsakar gida tana gyara wasu ganyayyaki, ta ɗaga wayar fuskarta ɗauke da murmushi. "asalamu Alaikum zainab ashe ana tuna tsoffi? Ya kuke, ya karatu?"
Zee ta sauke ajiyar zuciya, muryarta a murtuke. "Diddi, lafiya lau muke. Dama na kira ne in tambaye ku, ko kuna jin daga Farhana kwanan nan?"
Diddi ta gyara zama, gabanta ya faɗi. "Farhana? Ai rabo na da muryarta tun satin da su Nene suka taho. Shi Abdulkadir ɗin ma idan ya kira, sai ya ce tana barci ko tana karatu. Me ya faru Zainab ?wani ya faru ne da Maryam din ne ?
Zee ta fashe da kuka, "Diddi, wallahi Farhana ba ta da lafiya. Ƴazu nan muka yi waya, ta daka min tsawa, tana kuka kamar ranta zai fita. Ta ce kowa maƙiyinta ne, ta ce tana rainon tagwaye ita kaɗai, karatu ya yi mata yawa, kuma Abdulkadir ba shi da lokacinta sam."
Diddi ta saki ganyen hannunta, "Ikon Allah! Maryama ce take faɗar haka? Amma Abdulkadir ya gaya mana komai yana tafiya daidai, har da Nanny ya ɗauko mata."
"Diddi, Nanny ba miji ba ne," Zee ta faɗa cikin dacin rai. "Farhana tana cikin wani hali da Turawa suke kira Postpartum Depression. Tana buƙatar ku. Idan ba a yi hankali ba, yarinyar nan za ta iya haukacewa ko ta yi wa kanta wani abun. Shekarunta nawa Diddi? Ashirin kacal fa! Amma an bar ta da nauyin da ya fi ƙarfinta a ƙasar sanyi."
Hankalin Diddi ya tashi
Diddi ta kasa zaune, ta kasa tsaye. "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un! Ashe halin da take ciki kenan muna nan muna murna? Zainab nagode da kika gaya min. Zan kira Abbi yanzu mu ga abin da za a yi."
Bayan sun gama waya, Diddi ta kira Abbi a ofis. Ta gaya masa komai daki-daki. Shima Abbi hankalinsa ya tashi sosae, ya rasa dalilin da yasa AK yake ɓoye musu gaskiyar lamarin.
A can Boston kuwa, Farhana tana kwance a duhu, idonta biyu. AK ya dawo gida, amma maimakon ya shigo ɗakin ya lallashe ta, sai ya wuce ɗakin baƙi ya kwanta. Maganar "Lamido" dake fita daga bakin Farhana tana yi masa ciwo dole yayi bincike .
Farhana ta kunna wayarta na daƙiƙa biyar, ta ga missed calls ɗin Diddi da na Abbi. Ta sake kashe wayar ta kifa kanta a matashin kai.
"Diddi... Abbi... ba zan iya muku magana ba. Ba zan iya gaya muku cewa na gaza ba," ta faɗa a zuciyarta.
Washegari da asubanci, wayar AK ta ɗauki ruri. Ganin sunan Abbi ya sa shi tashi da sauri ya ɗaga.
"Hello Abbi, barka da asuba," AK ya faɗa yana sosa ƙeya.
Muryar Abbi ta fito a dake, babu wasa. "Abdulkadir, yaya kake barin Maryama tana wahala ita kadai a can ba tare da ka gaya mana ba? Me ya sa kake barin ta ita kaɗai da nauyin tagwaye da karatu alhalin kana da damar zama da ita? Idan har ba za ka iya kula da ita ba, maza ka shirya mata tsummanta ta dawo abuja!" Dan na Baka auren yata bashi ke nuna bana sonta ba .
AK ya girgiza,ya rasa wa ya kai wa Abbi wannan rahoton. "Abbi, ba haka ba ne... ina ƙoƙari ne..."
"Bana son jin wani bayani," Abbi ya katse shi. "Ina son in yi magana da ita yanzu, kuma ina so ka gaya min gaskiya, me yake faruwa tsakanin ku?"
AK ya kalli kofar ɗakin Farhana, ya san cewa yanzu asirin rashin kula dake tsakaninsu ya gama tonuwa.
AK ya shigo dakin rike da wayar, fuskarsa dauke da wani irin yanayi na bacin rai da kuma fargaba. Ya mika wa Farhana wayar yana kallon cikin kwayar idonta. "Abbi ne, yana son magana da ke."
Farhana ta karbi wayar, hannunta yana rawa. Tana jin muryar Abbi, wani daci ya taso mata, ta tuna irin lallashin da yake mata lubge .
"Hello Abbi..." Muryarta ta fara rawa, nan take ta fashe da kuka. Kuka take yi na fitar rai, kukan da ya sa Abbi jin kamar ana zare masa rai a can Najeriya.
"Maryama! Yi shiru kiyi magana. Me Abdulkadir yake miki? Gaya min gaskiya, ko ya daina kula daku ne? Zainab ta gaya mana halin da kike ciki."
Farhana ta share hawayenta da sauri, ta kalli AK wanda yake tsaye yana jiran jin abin da zata ce. Ta san idan ta fadi gaskiyar cewa AK yana watsar da ita , Abbi zai iya sa a dawo da ita gida yanzu. Amma sai ta daure, ta haidi zuciyarta.
"A'a Abbi... ba komai. Kawai na gaji ne. Rainon tagwaye biyu a nan bashi da sauki, ga karatun final year ya matsa min. AK yana kokari sosae, shi ma aikin ne ya masa yawa... amma he’s trying he’s best .
Abbi ya ja numfashi, "Maryama, karki boye min komai saboda biyayya. Idan akwai matsala gaya min."
"Babu komai Abbi, gajiya ce kawai. InshaAllah zan ji sauki, muna nan muna shirin dawowa gida nan da watanni uku."sosai abbi ya kwantar wa da farhana hakankali .
Bayan sun gama wayar, Farhana ta mika wa AK wayarsa ba tare da ta kalle shi ba. Ta koma ta kwanta, ta juya masa baya.
AK ya dade tsaye a tsakar dakin. Ya ji dadi yadda Farhana ta kare shi a wurin Abbi
"Wifey..." ya kira sunanta a hankali.
Farhana ba ta juyo ba, "Kaje ofis dinka Ak Karka tsaya bata lokaci a kaina, kasan aiki ne a gabanka."
AK ya ji zancen ya soke shi fiye da dukan tsiya. "Na san fushi kike yi, amma ai kinyi magana da Abbi yanzu. Me yasa baki fada masa gaskiyar ba?"
Farhana ta juyo, idonta ya yi jawur. "Saboda ni ba Hanadi bace. Kuma bana son in sanya Abbi cikin damuwa alhalin ba zai iya yin komai daga Najeriya ba. Amma ka sani, duk abin da nake boyewa a raina ne, ba wai don baka kyauta ba ne."raayina ne
"
Ranar AK ya kasa gudanar da aikin kirki. Maganar "Lamido" dake fita daga bakin Farhana da kuma kukan da take yi a boye sun sa shi fara zargin wani abu. Ya kira wani abokinsa dake zaria a asirce.
"Malam Bello, akwai wani bincike nake so kamin a boye. Ina so ka gano min ko akwai wani da ake kira Lamido a rayuwar Maryam tun kafin mu yi aure, musamman lokacin da take makaranta."
AK ya lumshe ido bayan ya kashe wayar. Wani sashi na zuciyarsa yana gaya masa cewa Farhana tana son sa, amma wani sashin kuma yana gaya masa cewa akwai wani mutum da take tunawa a lokacin da ta shiga damuwa.
Mummy ta samu labarin cewa Abbi ya buga wa AK waya ya yi masa fada. Dan Bayan Sun gama waya abbi ya kira daddy ya fada masa Akan Ak ya Kara kula da farhana .’mummy ta Kira ramla
"Kin ji ko? Har sun fara kai karar Abdulkadir wurin uban Maryam. Wai yanzu yarinyar nan ta zama abin tausayi a Boston.
Ramla ta yi dariyar mugunta, "Mummy, ai naji dadin hakan ko banza yanzu Ak yasan hanadi ce matar rufin asirin sa ,tunda bata taba Kai karar sa ba .
A ranar Adda Sabrina ta Kira farhana kiri kiri farhana taki dauka
Yayyenta maza gaba daya ma bata dauki kiran su ba,dan kowa lefinsa take gani ,da Sun dage ay bazaa mata aure da kananan shekarunta taba ,taga message dinsu fateeha da precious inda ta amsa masu sama sama
Kiran didddi kawai ta amsa inda sukayi magana for almost 30 min diddi na mata Addua diddi ta cigaba da bata shawara Akan yadda zata tafiyar fada raino da gidanta baki daya .
Haka dai aka cigaba da tafiya ba wani canji kuma a hakan farhana ke karatu Ak ya qara zama very distance ,inda hanadi ta nema zasu zo Hutu da yara ,Ak yace matarsa is not in the right conditions ta Bari shi da farhana zasu zo Nigeria ,Neman magana yasa hanadi ta turawa farhana text message
Naji labarin kin Haukace Subhallahi take it easy on your self farhana ,and lastly Ramin karya……
Kala farhana bata cewa hanadi ba from the text .
Wani lokacin sai Briana ta tunawa farhana cewa batayi wanka ba ,ta dafa abinci ta bata da kanta dan Kamar mutum mutumi take wani a times .
Yau gidan ya farka da sabon yanayi. Brianna ta kasa jure ganin yadda Farhana ta zama tamkar inuwar kanta. Sultana tana da rigima, kukan nan nata mai sautin gaske ya isa ya hana mutum barci mako guda.
"Mrs. Farhana, please," Brianna ta faɗa tana mika mata tawul. "Go and take a long, hot shower. Relax. Emily and I have the babies. Just for an hour, go out and get some fresh air. You need it."
Bayan Farhana ta yi wanka, ta ji sauƙin jikinta kaɗan. Ta saka wani dogon riga na sanyi mai launin toka (grey sweater dress) da baƙar riga mai kauri. Ta ɗauki makullin motarta, ta fara tuƙi a titunan Chestnut Hill ba tare da takamaiman inda za ta ba, har sai da ta ci karo da wani ɗan ƙaramin Coffee Shop mai suna "The Quiet Bean".
Ta zauna a wani tebur dake gefen taga, tana kallon kankara dake narkewa a waje. Ta yi lula cikin duniyar tunani, har ba ta lura lokacin da wasu mata biyu Turawa suka ƙaraso teburin nata ba.
"Hi! Is this seat taken?" Wata fara kyakkyawa mai suna Isabella tambaya cikin fara'a. Ɗayar kuma, mai suna hailey tana riƙe da kofin Latte.
Farhana ta firgita, ta gyara zama. "Oh, no. Please sit."
Matan biyu suka zauna, suna ta hirarrakinsu kafin su lura da Farhana dake kallon baby monitor dake ajiye a gefen kofin Coffee ɗinta.
"New mother?" Isabella ta tambaya tana murmushi, tana nuna baby monitor ɗin.
Farhana ta ɗan yi murmushin yaƙe, "Yes. Twins, actually. 4 months old."
Hailey ta zaro ido cikin juyayi, "Twins! Oh boy, you're a superhero! I have one, and he's driving me crazy. How are you holding up?"
Wani abu game da yadda matan nan biyu suka kalle ta da tausayi da kuma girmamawa ya sanya Farhana sakin jiki. Ta tsinci kanta tana amsa musu hira, koda yake sama-sama ne.
"I'm tired," Farhana ta faɗa a gaskiya. "I'm in my final year of university, and my husband is always at work. It feels... overwhelming."
Isabella ta jinjina kai, "Postpartum is real, honey. We've been there. Hailey used to cry in her closet every night when her son was born. Don't feel guilty for being tired. You're just 20? You're doing amazing."
Hailey ta matso kusa, "Listen, we meet here every Tuesday. If you ever feel like the walls are closing in on you, just come over. No babies, no husband-talk, just coffee and us."(Muna Haduwa duk ranar laraba a nan ,idan kika ji Kamar kofa ta rufe miki kizo ,ba yara ,ba miji ,kawai Shan coffee da mu)
A karon farko cikin wata hudu Farhana ta ji an fahimci damuwarta ba tare da an yi mata shari'a ba. Ta yi musu bayanin karatun ta na International Relations (cos ta canza course )su kuma suka gaya mata ayyukansu; Isabella lauya ce, Hailey kuma mai tsara gidaje (Interior Designer).
Sun yi ta ba ta dariya game da rigimar yara, har Farhana ta kusan mancewa da damuwar AK da ofis ɗinsa.
"Thank you, Isabella and Hailey Farhana ta faɗa lokacin da za ta tafi. "Inda suka yi hugging dinta daya Bayan daya .I really needed this."