Free chapter · Read without an account
THE BEGINNING
by Pending amarya · IMAM ZAID
IMAM ZAID🕌📿🔬
Pending Amarya ce 🔥♐️
Marubuciyyar👇🏻
*Beyound Heartbreak 💔
*The Regret
*Gold digger’s
And Now IMAM ZAID……..🔥🔥🔥
JAJIRTATTU WRITERS……….✍️
#paid book @500❤️🤭
Bismillahir Rahmanir Rahim
Typing 💬……..IMAM🔬📿💕🫶🏻
This novel is lovingly dedicated to my late parents😘
Ya Rabbi ka jikan iyayena ka gafarta musu, ka sa Aljannah ta zama makomar su.
To every soul reading this book, I humbly ask that you say a prayer for my late parents.
May Allah forgive them, have mercy on them, and grant them Jannatul Firdaus.
Allah ya shige mana gaba Ameen 🥹🤝
Copyright ©️
Wannan Littafin na IMAM ZAID mallakar Pending Amarya CE, ban yarda a wallafa min shi a kowani kafofin sada zuminta ba tare da izini na ba.
This is a work of fiction.
Any resemblance to real persons, living or dead, is purely coincidental.
:::::::::::::::::::::::::::::::::::
Allah does not burden a soul beyond that it can bear.💕🫶🏻🥹
THE ODOGWU WRITER ✍💪
Firstly let me start with menene rashin haihuwa a zamanin iyayenmu.?
A lokacin da iyayenmu suke yammatanci har suka zamto matan Aure, rashin haihuwa ya zamto abin tsangwama a garesu ko da kuwa matsalar ba daga garesu bane.
Sun sha tsangwama sosai daga mutane mabanbanta, ba ga danginsu ba, baga kuma daga mutanen dake na jikinsu ba.
kuma galibi Ana jingina shi ne ga mace ko da ba ita ce da matsalar ba, wasun su sun fuskanci raini, zargi, koma a kare musu da kishiya ba tare da an binciki gaskiyar Al amarin ba.
Duk da haka wasu daga cikin iyayenmu sun yi hakuri, sun jure, kuma suka tsaya tsayin daka a kan imaninsu.
Allah ka tsare imanin mu, ka kare mu daga sharrin zuciya, sannan ka bawa iyayenmu wayanda har yau ya ba su haihu ba haihuwa mai albarka.
Tabbas iyayenmu sun sha wahala a wajen dangin miji 😭😭😭.
IMAM ZAID🕌📿🔬
:::::::::::::::::::::::::::::::::::
Allah does not burden a soul beyond that it can bear.💕🫶🏻🥹
Another Bismillah🫶🏻
Bismillahir Rahmanir Rahim 🥰
Chapter one: The beginning 🔦
Pending Amarya 001❤️
1980🎥📸
Abduljalal Zaid Swahili, Babban dan kasuwa ne a ƙasar mu ta Nigeria, shi dan ƙasar Tanzania, amma anan Nigeria aka haifesa.
Mahaifiyyarsa ƴar ƙasar Somali ce, a taƙaice dai shi ba Nigerian bane.
Matarsa ɗaya shekararsu na uku kenan da aure amma ko ɓarin wata bata taɓa ba.
Sunan matarsa Fatima ƴar Nigeria ce amma iyayenta mazauna Tanzania ne.
“Buh Abdul Jalal don’t you think kuɗin da muke kashewa a hospital akan neman haihuwar nan ya yi yawa, I’m fed up with all this, wollah.” Kyakkyawar matashiyyar buduwar da bazata wuce 15s ɗinta ba ta faɗa tare da shigewa jikin wanda ta kira da Abdul Jalal.
“Oh noo Fatima, stop wasting your precious tears, duk wannan abu mai wucewa ne, koda kuwa dukiyata gabaɗaya zai ƙare a shirye nake domin na sadaukar a sanadin samun lafiyarki, for now let’s try this native Doctor, ƙila a dace.” Ya yi maganar tare da goge hawayenta da lallausan palms ɗinsa, haɗe da ɗaura kanta a kafaɗarsa.
Babu jimawa bacci mai nauyi ya kwasheta ba tare da ta shirya masa ba.
Washegari da sassafe har suka gama breakfast ba ta ce da shi komai ba, shi ma kuma bai damu da rashin maganar nata ba.
Breaking silent ɗin ya yi tare da faɗin “If you’re done let me know, Sai mu kama hanyar gidan Dadah, daga nan ne zamu wuce can wajen Mutumin da ta yi min introducing some weeks ago.” Ya na gama faďan haka ya ďauki brief case ďinsa tare da key ɗin motarsa ƙirar Mercedes Benz W 123, sabuwa fil brown color.
Ba ta ce da shi komai ba ta ďauki wani mayafin dogon rigar jikinta tare da barin cikin ďakin na su.
A parking space ta same sa a zaune cikin motarsa ya yi balance ya na jiran firowarta.
Walking slowly ta karaso ta shige gaban motar ba tare da ta kallesa ba.
shiru ne ya ratsa motar na wani lokaci, sannan a hankali ya kai lallausan hannunsa ya kamo nata.
Ajiyar zuciya ta sauke tare da kai dubanta garesa, langwaɓar da kansa ya yi wanda hakan ya bata damar fashewa da kukan da tun ɗazu take ɓoyewa, dan ita kaɗai ta san mai zata tarar a gidan Dadah, uwar mijinta kenan.
“Fatima.” Ya kira sunanta a sanyaye, ɗago kanta ta yi tare ɗaura daradaran idanuwanta a kansa sannan ta ce “Naam.”
“I’ve told you several times ki daina shedding precious tears ɗin ki , Allahn da ya ƙaddara mana hakan, shi zai cire mana wannan damuwar, pls stop all this, ban san ki da karaya to this extent ba.” Ya ƙarashe maganar tare da yin horn a babban estate ɗin da yake unguwar Hotoro.
Gida ne mai kyau ma shaa Allah, wanda ke ɗauke da parts da dama, wanda da dukkan alamu sun nuna Family house ne.
Motoci ne parke a parking lot ɗin na alfarma kalar wanda ake ya yi a wancan zamanin, dan sai wane da wane kan iya hawan motocin a wancan lokacin.
Wani kalar bugu taji ƙirjinta na yi sakamakon ganin compound ɗin da suka iso, sauka yayi daga motar wanda ita ma hakan ya bata warrant ɗin sauka tare da bin bayansa ta na mai karanto wasu addu’o’i a cikin zuciyarta.
Part ɗin da yake a farko shi ya nufa, ita ma ta na biye da shi a baya. Sosai gidan ya haɗu daidai da zamaninsa.
Wata mata ce Zaune a kan lafiyayyan sofan dake falon, cikin shiga na alfarma.
Cikin takunsa na isa ya ƙarasa shigowa cikin living room ɗin ita ma ta na biye da shi kamar jela a bayansa.
“Good morning Maama.” ya gaisheta a ladabce, “Morning son, how was your night?.” Ta karashe maganar tare da shafa kan ɗan nata.
“Splendid Maa.” Ya fada tare da tashi daga tsugunnen da yake.
“Ita kuma matar taka ban kai ta gaida ni ba kenan, any ways ba yau farau ba, kuma taimakon da zan yi ba dan ita zan yi ba, gaisuwarta ba zai rage ni da alkhairan da Allah ya yi niyan zai bani ba.” Ta ƙarashe maganar tare da rataye Mama’s bag ɗinta.
Kallonsa ya kai ga Fatima da ta durƙusa a kan gwiwoyinta wanda alamu sun basa ta na shirin gaisheta ne ta fara masifa, shi ya rasa dalilin tsanar da Maama ta yi ma Fatima.
“Idan ba zaku je ba i should take my leave dan akwai inda zanje sannan na tsaya biye ma kai da matarka.” Muryar mahaifiyyarsa ya dawo da shi daga tunanin da yake.
Tashi ya yi tare da bin bayan mahaifiyyarsa da har ta bar cikin falon.
Jiki a saɓule itama ta bi bayansa, a gaban motar suka tarar da Dadah ta yi balance ta na jiran fitowarsu.
Ita dai Fatima ba ta ce komai ba ta shige bayan motar sannan ya mata key suka bar compound ɗin.
Cikin motar ma haka Dadah ta yi ta faɗa wai ta na mutsu2 da yawa, babu yadda ta iya sai dai ta yi shiru ta mai da hankalinta wajen kallon window.
Tafiyar awanni wajen shida suka yi, sannan suka iso wani ɗan ƙauye wanda ba ta san ina ne bama.
Wani ɗan hut Dadah ta shige ba tare da ta juyo ta kalle su ba, bayan wani ɗan lokaci Dadah ta musu alamun da su shigo, a hankali ya kamo hannunta ba tare da ya kalleta ba suka shiga cikin hut dake cike da ganyayyaki na magani kala kala, wani clay pot mutumin ya ɗauko sannan ya musu prescribing yadda za su yi da maganin sannan ya musu fatan alheri suka kamo hanyan dawowa gida.
Har gida suka ajiye Dadah sannan suka dawo gida.
Direct ya wuce kitchen ɗinsu bayan sun dawo gidan tare da ɗaura clay pot ɗin a kan gas sannan ya zuba ruwa daidai litre da aka ce masa.
After some minutes ya fito daga kitchen ɗin da wani mug a hannunsa ya miƙa mata maganin.
“Honey, is it bitter?.” Ta tambayesa tare da ajiye wani Novel ɗin da take karantawa a hannun chair ɗin falon.
“Babu ɗaci just a little kuma ba sosai ba.”
“Are you sure?.” Ta faɗa a sanyaye.
“Yeah I am, ko ba ki yarda da ni ba ne yanxu?.” Ya yi maganar tare da zama a kusa da ita.
“Nooo, why wouldn’t I trust you, wacece ni da ba zan yarda da kai ba?, you must be joking Abdul Jalal.” Ta faɗa tare da fara sipping maganin ta na ɗan ya mutse fuska.
“Yarinyar nan kin fa raina ni, Do you want me to warned you again?.” Ya yi maganar tare da janyota jikinsa.
Months later.❤️
Yau ma kamar kullum, zaune take a study room, hankalinta gabaɗaya ya raja’a akan chatting ɗin da take yi, ƙaramar fitilar desk lamp ce kawai ke bawa ɗakin haske.
Kan desk ɗin wani fax machine ne a kai wanda alamu sun nuna shi ne na’urar dake taimaka mata wajen chatting ɗin nata.
Na’ura ce wadda babu mai amfani da shi sai masu kuɗi na wancan zamanin.
Rubutu take a nutse fuskarta na ɗauke da murmushi, sannan ta ajiye bic ɗin hannunta tare da tura A4 paper ɗin da ta rubuta masa message ɗin cikin Fax machine ɗin dake kan desk, haɗe da tallaɓo chicks ɗinta tana kallon Fax machine ɗin.
Ƙara kallon abin da ta rubuta masa ta yi “I miss you… but I won’t tell you how much.”
Ko da ta kara karantawa wani kunya ne ya ƙara kamata sannan ta barsa ya shige cikin machine ɗin gabaɗaya.(mai abin kunya anan 🤣 in ban da lamarin yan 199s😂🙏🏻🙌🏻)
Jingina ta yi da kujerar ɗakin ta na mai lumshe manyan sexy eyes ɗinta.
Cikin mintuna biyu a hankali paper ya sauko daga cikin Fax machine ɗin, wanda hakan ya sanyata saurin ɗago da kanta jin ƙarar da machine ɗin yake yi, yage paper din ta yi tun kafin ya yi landing.
“What are you doing to me Fatimah?, Now I can’t even concentrate.”
Murmushi ta yi tare da lumshe idanuwanta na wani lokaci wani kalar sanyi na ratsa zuciyarta, sannan ta sake rubuta masa “Maybe you should come home and find out.”
Ta na gama rubutawan ta tura masa, ta na Jin wani kalar kunya na Lulluɓeta, sannan ta bar study room ɗin dan ta ɗan kimtsa jikinta, dan ta san indai Abdul Jalal ne ya na hanyan dawowa.
After some minutes taji tsayuwar motarsa, ba ta yi mamaki ba dan ita kanta ta san sai ya dawo gida in dai yaga text ɗinta.
Haka rayuwarta ta cigaba a gidan Jalal da daɗi babu daɗi ta kan yi hakuri da cin fuskar da mahaifiyyarsa kan yi mata.
Dan daga ƙarshe ma ce masa ta yi su bar apartment ɗinsu su dawo family estate inda kowa yake zaune da iyalansa, he didn’t complained to his Mom,He had no other option than to move into the estate with his precious wife, gidan dake cike da facaloli, different characters……
This is just the beginning 🥰🙏🏻
- Like and share fi sabilillahi 🥹🙏🏻🙌🏻