Free chapter · Read without an account

THE BEGINNING page 2

by Pending amarya · IMAM ZAID

***


IMAM ZAID 🔬🥼





Pending Amarya ce🎭




JAJIRTATTU WRITERS ASSO………………✍️



The Odogwu Writer ✍️ 

Chapter1: THE BEGINNING 🙌🏻



An Empty barrel makes loudest noise 🙌🏻🎭



IMAM ZAID 🔬🥼🧪

Paid book ne.
At a low fee za ku samu 500 naira kacal.

*** 
Opay Farida Aliyu Ibrahim.
 Shaidar biya via what’s app👇🏻

***.


Indeed, Allah does not wrong the people at all, but it is the people who are wronging themselves.🫩🥺❤️

Pending Amarya 002🙌🏻
Not edited 🙌🏻

Dan daga ƙarshe ma ce masa ta yi su bar apartment ɗinsu su dawo family estate inda kowa yake zaune da iyalansa, he didn’t complained to his Mom,He had no other option than to move into the estate with his precious wife, gidan dake cike da facaloli, different characters.




1983🫩😘



wasa wasa yau shekara shidda da aurensu amma har yanzu shiru kake ji ko  ɓarin wata Fattumah ba ta taɓa yi ba.




Kullum cikin kuka take, kullum addua take koda sau ɗaya ne Allah ya nuna mata gudan jininta a duniya.



A cikin 3yrs ɗinnan Jalal ya biya mata kuɗin saudi fiye da sau shida. 
Hakannan ta fawwalawa Allah komai, dan babu ranar da zata zo ta wuce batare da Dadah ta ci mata mutumci ba.


Abin baƙin cikin ma har Aure Dadah ta sa ya ƙara da cousin ɗinsa a zuwanta na saudi na karshe.



“Kin ga Sakina, Abdul Jalal ba ya son heavy food in dai ya yi tafiya mai nisa, it’s better ki yi masa ko spaghetti ne a kan tuwon Semon da kika haɗa masa.” Fatima dake sanye da wani jeans trousers da kuma wani baķin riga mai net wanda ya lafe a flat tummy ɗinta ta faɗa ta na kallon kishiyarta mai suna Sakinat.


Ɗago da kanta Sakinat ta yi tare da dalla ma Fattumah harara sannan ta fice daga cikin kitchen ɗin.



After some minutes sai gata ta dawo tare da Dadah.


“This should be the first and the last warning da zan miki a kan kitchen ɗinnan da kuma Sakinat, stay away from her, ina ruwanki idan ma abincin yarabawa ta dafa masa karewar heavy food, ko siraran kafafuwan nan naki na kara gani a kitchen dinnan, wallahi sai kin bar gidan nan, Sakinat zo ki ci gaba da abin da kike yi, ke kuma zo ki fice tun da ba gidan ubanki bane ba.” Dadah ta karashe maganar ta na haki.


Jiki a sanyaye Fattumah ta fice a kitchen din , struggling to hold back her tears.




After some hours ta ji tsayuwar motarsa a compound din gidan, jiki ba kwari ta shige toilet tare da wanko fuskarta sannan ta dawo cikin ɗakinta.



Zaune take a bakin madubi, jikinta na sanye da kayan baccinta wanda suke mata kyau sosai red color, skin dinta dake glowing ta kurawa idanu sannan ta yi sauri ta miķe daga gaban madubin sakamakon shigowan da ta ji an yi.


Sanye yake cikin kayan bacci wanda suka dan kama jikinsa sannan suka fito da samartakansa, ƙarasa shigowa ɗakin nata ya yi cikin isa da taƙama sannan ya ƙaraso ya zauna kusa da ita kamar zai mai da ta cikinsa.


Saurin matsawa ta yi baya dan yadda ya matso sosai yadda ka san wanda zai sumbace ta.


“Why didn’t you come for  dinner?, and why   do you look upset?, wani ya miki wani abu ne Cutie?.” Ya yi maganar tare da janyota jikinsa.

Murmushin yaķe ta yi tare da shafa gemunsa da ya gaji da haduwa, sannan ta yi peaking dinsa a kumatu.


“Kawai so nake naje gida na ga Appah, na daɗe ban jeba.” Ta karashe maganar a sanyaye.


“Shi ne kika ɗagawa mijinki hankali?, babu kuɗi a landline da za ki kira ?.” Ya yi maganar ya na mai ɗan shingiɗewa akan gadon nasu, ya na mai saƙalo da hannayensa ƙugunta ya na ɗan shafawa a hankali.


“Stop it manaaa.” Ta yi maganar tare da turo bakinta, hakan da ta yi kam ba ƙaramin kunna shi ta yi ba.


Hungrily ya fara bata wani kalan french kiss wanda hakan ya sanya kwakwalwarsu gabaɗaya birkicewa at ones.


Cikin wani kalar kasalalliyyar murya ta ce “ AbdulJalal, ba ni ce da kai ba yau, Please don’t do this to me.” Ta karashe maganar tare da rike hannunsa da yake kokarin rabata da kayan jikinta.


“Please let me in, da sauran kwana daya naki ai kafin na ta fi.” Ya yi maganar da wata irin disassiyar murya.



“Buh Jalal……..” bai bar ta ta karasa ba ya ci gaba da aikinsa.



Wani kalar kwankwasa musu ƙofa da aka yi shi ya yi sanadiyyar ɗagata da ya yi  a birkice.

Countinuesly a ka ci gaba da knocking din non stop.


Saurin saka kayansa ya yi tare da wucewa bakin ƙofar ɗakin ya na faɗin “ Waye?.”

“Uwarka ce .” Dadah ta fada daga can wajen.

“Maama, mai ya faru?, hope all is well?.”


“Za ka ci uwarka idan baka fito daga ɗakin nan ba tun da bana gyatumar ka bane, kaje ka na wasting ƙarfin ka a unnecessary waje, wajen da ba zai bani jiƙa ba.” Dadah ta faɗa cike da ɗacin rai.



“Maama what’s all this?.” 

“Jalal, come on buɗe ƙofar ka daki wacca ta kawo ka duniya saboda bahaushiyya, wallahi idan ba ka  buɗe ƙofar nan ba tsaff za ka yi dana sanin haifarka da na yi.”



Buɗe kofar ya yi a sanyaye tare da ɗaure fuskarsa sannan ya riƙe handle ɗin ƙofar yaƙi kuma barin jikin ƙofar.



“Wallahi Jalal you better respect yourself, babu kai babu kwanciyya da ita har sai na yarje maka ka kusance ta, babu kai babu ita, idan har ka kusance ta kuma bada izinina ba ban yafe maka ba har abada.”

“Kamar ya?, ban gane ba, mata ta ce fa Maama.”


“Are you questioning me?, saboda ka san dadin aure?, it’s all right, Sakinat wuce  muje, Kar ya zo ya same ki a dakin ki ya kwanta a wajen juyaa.” Dadah ta fada angrily.

Jiki a sanyaye ya karaso ya dawo cikin dakin ta na zaune ta cusa kanta cikin gwiwowinta ta na kuka.

“I’m sorry Fattumah, Please don’t take her words personal, Dan Allah kiyi hakuri.” Ya fada tare da durkusawa a kan gwiwoyinsa.



“I shouldn’t take her words personal ka ce?, ni ka nema min visa na tafi gidanmu ba zan iya ba, na fasa auren.” Ta yi maganar tare da janyo wani dan trolly ta fara zuba kayanta.


“Fattumah…….” Saurin tare numfashinsa ta yi tare da faɗin “Not now please, na ri ga da na gaji da kalar cin kashin  da Maama ke min, at least ba a kaina bafa farau, kuma Allah shi ke bada haihuwa ba mutum ba.” Ta karashe maganar tare da kara fashewa da wani Sabon kukan mai cin rai.


Saurin dawowa ya yi kusa da ita tare da tallafo face dinta tare da fadin “ Please, Fatima yi hakuri da halin Maa, she will change one day, I’m giving you my words, Kar ki saka Duk wasu abubuwan da take miki a zuciyarki please Fatuh.” Ya yi maganar tare da daura goshinsa akan  nata wasu hawaye na zuba a idanun kowannensu.


A ranar dai a dakin nata ya kwana bai bar Dakin kamar yadda mahaifiyyarsa ta Umarcesa ba.



Washegari da safe bata yi gigin shiga kitchen hada hannu da su domin breakfast ba kamar yadda ta saba, shi ma kuma bai mata dole a kan ta fita din ba.

Shirye yake sosai a cikin shigarsa na yau da kullum na zuwa aiki, lallausan gashin kansa wanda ya ci gyara ya gaji sai sheki yake yi.

“Good morning Hajjaju.” Abdul Jalal ya fada tare da sakar mata peak a goshi .



“Morning Jalal.” Ta amsa masa da zallar murmushi a face dinta.

“Soo tell me, how was your night?.” Ya yi maganar tare da dan kanne mata ido 

Rungumesa ta yi tsam jikinta tare da fadin “ Alhamdulillah, Please Jalal zan je gidan Yaya Shattimah, if you don’t mind?.” Ta karashe maganar tare da dan zamewa a jikinsa.


Ya san Sarai so take ta kaucewa cin zarafin Dadah na yau hakan ya sa bai hanata ba ya ce da ita ta shirya ta jira shi a Dinning room.



Ta rasa ma murna za ta yi, ko kuka dan ita dinning din bata son gani balle mutanen dinning din.

Jiki a sanyaye ta shige toilet tare da yin wanka ta shirya cikin wani wando da riga hade da sanya wani after dress a kan shigar nata, dan babu laifi yar wanka ce.


Shigar ya mata kyau sosai, wani flat shoes baki ta saka tare da rataye wani dan jaka mai gashi- gashi, sannan ta fito babban falon gidan dake cike da jammaan gidan Ana ta breakfast.


Shigowarta falon ya sa gabadaya mutanen dinning din suka yo da idanu kanta, ban da Sakinat da ta kalleta ta yatsine fuska.


A hankali ta zagayo inda yake tare da jan empty chair din kusa da shi ta zauna.

Kura mata idanu ya yi na wasu seconds sannan ya dau empty plate ya fara zuba mata abincin.

Yatsine fuska ta yi sosai dan ganin Sakinat da ta yi ya sanya ta koshi at once.

“I’m full Jalal, kai nake jira.” Ta karashe maganar tare da dauke kanta daga kallon da Dadah ke mata……..


This is just the beginning ❤️🥰

Pending Amarya for you ❤️😘



The lion does not turn around when a small dog barks❤️🥰

Sai mun hadu gobe in shaa Allah 🥹🙌🏻

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol