Free chapter · Read without an account

Chapter 3

by Pending amarya · IMAM ZAID

***



IMAM ZAID 🔬🥼





Pending Amarya ce🎭




JAJIRTATTU WRITERS ASSO………………✍️



The Odogwu Writer ✍️ 

Chapter1: THE BEGINNING 🙌🏻



An Empty barrel makes the loudest noise 🙌🏻🎭



IMAM ZAID 🔬🥼🧪

Paid book ne.
At a low fee za ku samu 500 naira kacal.

*** 
Opay Farida Aliyu Ibrahim.
 Shaidar biya via what’s app👇🏻

***.

FREE 
     PAGES 
             BABU YAWA 
                           PAY ON TIME 😢🙌🏻


And whoever relies upon Allah 💕 then He is sufficient for him.🥹🙌🏻


Pending Amarya 003🎭


Yatsine fuska ta yi sosai dan ganin Sakinat da ta yi ya sanyata koshi at once.

“I’m full Jalal, kai nake jira.” Ta karashe maganar tare da dauke kanta daga kallon da Dadah ke mata.


“Ina za ka kaita, Munafuki.” In ji cewar Dadah da ta ajiye glass cup din 5alive din da take sipping.


“Unguwa zan kai ta, Ta so mu tafi.” Ya karashe maganar da kallon Fatimah tare da fara barin wajen.

“Ba za ka kaita ba, ga Sakinat nan tun jiya take fama da Zazzabi, in dai har za ka kai waccan mai kama da Lucifer din, toh sai dai ka hada da Sakinat ka ajiyeta hospital a mata check up then Sai ku bar duniyar idan shi za ku bari.”


“Okay Maa, ta yi sauri ta fito because ina da wajen zuwa.” Daga haka ya damki hannunta suka fita daga gidan.


Cikin 5 minutes Sakinat ta fito da similar shiga kalar na Fattumah, dan in dai competition ne idan ka sameta just shout loud Hallelujah.


Atsaye Sakinat ta tsaya a bakin kofar motar ta na jiran Fatimah ta sauko daga gaban motar ta hau.

“Ke dallah malama get in.” Ya fada tare da daure fuskarsa ta mau.

“ Yaya she’s sitting in my seat, tell her ta koma baya.”  Sakinat ta fada ita ma fuska a daure.

Warming motar ya fara yi tare da fadin “ It’s like ba kya son zuwa in da aka ce za ki je din.” Ganin da gaske tayar da motar zai yi hakan ya sanya ta Saurin shige wa bayan motar kamar ta fasa ihu.



Ko da suka iso hospital din ba su fi minti 30 suna jiranta ba ta fito da wani farin takarda a hannunta, fuskarta dauke da zallar murmushi ta karaso wajensa ta kofar side dinsa. 
Amsar takardar da take miko masa ya yi daga hannunta tare da fara karantawa a hankali.
Dago da kansa ya yi ya kalleta sannan ya kara kallon takardar.

Murmushi ya sakar mata mai kyau, so yake ya nuna farincikinsa amma tuna da wacce suke tare ya sanya sa danne hakan  tare da fadin “Congratulations, get in side.”  Hararar Fattumah ta yi tare da kallon back sit din sannan ta shige cikin motar.



Tafiya yake da dan gudu a kan titin, motar shiru babu mai yin magana sai karar wucewar motoci dake tashi.

Sakinat ce ta yi breaking silence din da fadin “After all the ups and downs ni ce wadda za ta bawa Jalal heir a family na mu, da aurena ka yi tun tuni da yanzu muna da yara fiye da shida.” Sakinat ta yi maganar ta na kure Fattumah da kallo da kuma wani kalar murmushi.


A hankali ta juyo da kanta tare da sauke manyan idanunta a kan Sakinat sannan ta ce “ Congratulations.” Sannan ta dauke kanta wasu kwallar na sauko mata sannan ta yi sauri ta goge.

Parking ya yi a kofar gate din gidansu ba tare da ya juyo ba ya ce “Out.” 

“Wacce daga cikinmu.?” Sakinat ta fada a kufule.

“Kar ki saka na maimaita kaina da ranar nan?.”

“Duk dai a kan mai shanyayyan mahaifa ake mun wannan korar it’s all right.” Ta fada tare da ficewa a motar.


Sai da ya ja tsaki sannan ya figi car dinsa ya bar wajen.


Sakinat kam sai da ta bar saman kwaltan dake shinfide a street dinsu ta je ta bulbula ƙasa a kafarta sannan ta wuce ciki, kuma ba ta zarce part din kowa ba sai na Dadah.



“Shi ne kika sakar mata baki kike kuka ko?, ke ba ki yarda ba mai sanyin hali, na sha fada miki duk wanda ya taka ki ki taka shi, and you’re taking my words for granted ko?, dan Allah gobe ta miki ki tsaya zubda kwalla ki ga yadda zan miki.”

Kara fashewa ta yi da kuka, ta jingine kanta da sit  ta ci gaba da yi.


Bai kalleta ba sannan bai ce da ita bari ba, har suka karasa gidan Ya Shattimah.


Sai da ya parker motar sannan ya juyo da kansa ya kalleta.


“Dan Allah karki damu kanki, bayan isha zan zo mu koma gidan kin ji?.”

“Toh amma Jalal ka dade ka na son yara, Buh you’re not happy about the pregnancy why?.” Ta fada a sanyaye tare da kallon cikin idanunsa.
Sai da ya furzar da iska daga bakinsa sannan ya ce “I don’t want you to feel bad, Fatimah, idan na nuna farinciki na kin shiga uku a family na, amma idan ma yaran ne nafi son ki haifa min su, and I’m very sure watarana za ki haifa min yara ma su albarka , in shaa Allah, ki fawwalawa Allah komai shi kuma zai shiga cikin lamarinki kin ji uwar y’ay’ana?.” Ya fada tare da shafa kan nata.

Gyada masa kai kurum ta yi sannan ta bude motar a hankali ta sauka ta  na masa waving da hannu.


Walking slowly ta karasa shiga cikin compound din, a hankali ta fara knock kofar entrance din har wata kaykkyawar mata wadda ba za ta wuce 20yrs ba ta bude mata kofar fuskarta dauke da murmushi dan ganin wadda ke gabanta.


“Nyeee Timmy sai yau kika tuna da mu kenan?.”


Cikin sassanyar muryarta ta ce “ Ba haka bane Aunty abubuwan ne suka dan yi yawa.”

“ Ba laifi shigo mana , kika tsaya a kofa Kina koro min jawabi Auta.” 


karasa shigowa ta yi babban living room din tare da ajiye jakarta a kan daya daga cikin kujerun da suke a falon.

“ Yanzun nan yayanku ya fita, ko minti goma bai yi ba wallahi, bari na zubo miki abinci, ko kin yi breakfast?.”

Auntyn ta fada tare da mika mata yaron da tun shigowarta yake mika mata hannu.

Amsar sa ta yi daga hannunta sannan ta ce “ Wallahi Aunty ban ci komai ba tun jiya, Maman nan ta sa kullum cikin cin fuska, ni wallahi na gaji.” Ta karashe maganar idanunta na zubda wasu sabbin hawayen.


“Dukan ki ta sake yi ne?.” Inji cewar Aunty.
“A’a Aunty, tun ranar da suka dake ni ita da Sakinat da ya saki Sakinar har yau ba ta sake yin wannan gangancin ba, kawai dai ko kusantata ba ta barinsa ya yi cikin dadin rai, jiya ma haka tai ta bubbuga mana kofa bayan mun kebe.” Ta yi maganar tare da goge hawayenta.


“Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, Fatimah wannan wani banzan family kika kai kanki ciki marasa addini?, Anya wannan auren za a ci gaba shi haka kuwa.?”

“Toh amma ayy Aunty ina son sa.”

“Za ki biye ma soyayya ne ki lalace da kuruciyyar ki da gatan ki?, bari yayanku ya dawo ko can gida ne Kya je ki dan huta ki dawo, rashin mutumcin is too much. laɓe take muku kenan ayy, ita haka uwar mijinta ta yi mata?, ko bayan su Jalal din wasu ta sake haifa in ban da rashin sanin kaddara kalar na wasu  kabilar larabawa .”

“Aunty fa yanzu Sakinat ciki gareta.” Ta karashe maganar tare da sake rushewa da wani sabon kuka.

“Toh sai mai?, Allahn da ya bata zai baki, ko Jalal din shi ma canza miki ya yi?,  ki ci gaba da adua,a komai mai wucewa ne ayy, yanzu ci abinci kije ki kwanta kafin Yayan ya dawo tun da na san sai dare zai zo daukan ki ko?.”


Da toh ta amsa ma Matar yayan nata sannan ta fara cin abincin a hankali.


Ko da ta gama cin abincin kwanciyyarta ta yi a dakinta dake gidan har yaran Auntyn suka dawo daga school.


Yammancin ranar 🥰🙏🏻


Around karfe shida yaya Shattimah ya dawo gidan hannun shi rike da ledoji, fuskarsa sake ya amsawa kanwar ta sa gaisuwar da take miko masa.

“Nyee Timmy kece yau a gidanmu?.” 
“Eh wallahi Yaya, ya hanya?.” 
“Lafiya lau Auta, ya mai gidan naki da sauran mutanen gidan.”
“Lafiya lau Yaya, kowa Alhamdulillah.”
“Ma shaa Allah.” Haka suka ci gaba da hira har Jalal ya zo daukanta.
Bai jima da zuwa ba suka bar gidan zuwa can estate dinsu.

Shigar su gidan ke da wuya Dadah ta kama Jalal da fada har a ka samu nasarar marin Fattumah.

Tun daga ranar sunanta a estate din ya koma juya, babu mai ganin girmanta ko darajarta, ko yara ta aika babu mai je mata, tun daga ranar ma rayuwarta ya zama upside down, sai dai taurin zuciyarta ya sanya ta sam ba ta bar kanta a kasa kowa ya taka ta ba.


Haka rayuwa ta ci gaba har cikin Sakinat ya isa haihuwa babu wani canji da ta samu a wajen uwar mijinta sai ma worst da abubuwan suka yi, dan a yanzu ko falo ba ta fita iyakarta dakinta, sai ta tabbatar kowa ya shige part dinsa sannan za ta fito daukan abin cin ta .


Kuma duk wadannan dramas din ba ta taba fadawa Jalal ba.

Kamar kullum yadda ta sa bawa kanta, hakan ce ta kasance bayan ta ji daukewar kafafu a downstairs.

Fito wa ta yi ta na waige waige har ta buge mutum wadda ba ta san da shigowarta falon ba.


Wani kalar ihu Sakinat ta kwala daidai karfinta tare da daukan hannun Fattumah ta daura shi a saman wuyanta, tare da fara kiciniyya da hannunta kamar ta na shirin kwace kanta ne daga wajen Fattumah.

Yadda Fattumah ta yi shock a tsaye sai ka rantse da gaske shake wuyan Sakinat ta yi .

Daidai fitowar Dadah wanda akan idanunta Sakinat ke ihun neman taimako da sauran mutanen gidan dan around 12 na dare ne, kuma Sakinat ta riga da ta gane time din fitowar Fatimah ne shiyasa ta fito ita ma.


Dai dai nan Jalal ya shigo cikin Falon, dan ya na can bangaren Dad dinsa da ya zama part dinsa a gidan yanzu.

“Toh ga Annobar da ka auro ta shake uwar yaranka, tun dazu ake yi da ita ta sake ta ki saki.” Dadah ta fada tare da komawa gefe ta na kallon sauran Jamaar gidan.

“Fattumah what the heck are you doing to her?.” Fadar hakan da yayi shi ya bama Sakinat daman sulalewa a kasa tare da sakin ihu.
Dan sosai ta bugu dan duk a tunaninta Jalal zai tare ta.


Nan da nan wani kalar azababben nakuda ya kamata, wan da babu jira gaba daya aka yi hospital da ita a ka bar Fattumah a tsaye.


Ta ma rasa mai za ta yi, haka kurum ta koma dakinta ba tare da ta dauko abincin nata ba dan ko yunwar ta dauke at once.


Har yamman washegarin daren da abin da ya faru babu wani feedback game da halin da Sakinat take ciki, kuma babu wanda ta isa ta tambaya.



Jingine take da kan gadon dakinta fuskarta dauke da busasshen hawayen da bata san ranar dainawarsa ba, fuskarta ya yi laasar Duk saboda kuka, dan ko rintsawa ba ta samu ta yi ba.


“Fattumah.” Ta ji saukar muryarsa a sanyaye kamar ko da yaushe, ɗago kanta ta yi wanda hakan ya sanya idanunsu hadewa cikin na juna, wanda hakan ya ƙara karyar da zuciyarta ta ƙara fashewa da wani sabon kukan.



“Toh yanzu mai ye na kukan?, wani ya bata miki rai ne?.” Ya yi maganar tare da dan kwanto da kanta a kan kafadar sa.

“Toh ba kaine ka min tsawa ba, kuma gashi babu wani feedback a hospital din da kuka kai cousin din ku, and wallahi babu abin da na mata, a kasari ma ni zan je kitchen daukan abincin da zan ci ne.” Ta yi maganar wani hawayen na sauka a idanunta…..

Mu hadu a gobe In shaa Allah 😢🙌🏻

Like, share comment 🥹🙌🏻
Karku canza nima ba zan canza muku ba 😂😂😢

> IMAM ZAID ONLY ON PENDING AMARYA’S BOOK CORNER EXTRAORDINARY EVERYDAY 🥰


*///Soft Noorah///*

> PENDING AMARYA😘 

> FARIDATOOL NOOR🥰🙌🏻

 _THE ODOGWU WRITER_✍️

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol