Free chapter · Read without an account
59
by ZAHRAA · Bayan Murmushi
Wasa wasa Aminci sosai ya shiga tskanin farhana da qawayenta ,taje gidansu suzo gidanta Yau Akwai tattaunawa na asiri tsakanin Farhana da kawayenta. Suna zaune, Farhana tana kallon sararin samaniya ta taga, ta sauke ajiyar zuciya.
"Kinsan me Hailey? Burina na gaske shi ne in zama Pilot. Tun ina yarinya nake mafarkin tuka jirgi, amma mijina baya so. Shi a ganinsa aikin yana da hatsari kuma zan yi nisa da gida," Farhana ta fada muryarta cike da rauni.
Hailey ta kalli dan ta, kevin wanda yake wasa a carpet da twins sannan ta kalli Farhana. "Farhana, life is too short to live someone else's dream. Idan har kina so, zamu taimaka miki."
Isabella ta gyara zaman gilashinta, "Gaskiya ne. Kiyi karatun nan a boye mana! Kinsan kudin karatun pilot yana da tsada, amma akwai scholarships da kuma tsare-tsare na rance da zamu iya bincika miki. Idan kika kammala digirinki na yanzu koyan karatun tuki jirgi zata zo miki cikin sauki."
Farhana ta zaro ido, "A boye? Ta yaya zan yi karatun tuka jirgi ba tare da AK ya sani ba?"
"Zaki iya fara karatun ka'idoji (Ground School) ta yanar gizo," Hailey ta bayyana mata. "Sannan lokacin da kika fara tashi na gwaji (flight hours), zamu ce masa kina wani bincike ne na daban ko kuma kina tare da mu. Kafin ku dawo daga Najeriya nan da watanni kadan, zamu riga mun nemo miki makarantar da zaki fara a boye."
Farhana ta ji gabanta ya fadi, amma kuma zuciyarta ta buga saboda murna. "Kun tabbata hakan zai yiwu?"
"Tabbas!" Isabella ta fada tana rike hannunta. "Mun zama kawayenki, kuma burinki namu ne."
Daga karshe, Farhana ta kalli karamin yaron hailey dake ta faman wasa da kafar Khalil. "Isabella, Kevin yana da kyau sosae. Nagode da kuka zama kawaye na a lokacin da nake neman hauka."
Hailey ta yi murmushi, "Kevin ma yana son Sultana da Khalil. Kinga yadda yake basu kulawa? Zai zama babban yayan su a nan Boston."
AK ya dawo gida, ya tarar da su Isabella sun tafi. Ya iske Farhana tana ta faman duba laptop dinta cikin hanzari.
"Wifey, kun sha hira Yau sosae? Me kike dubawa haka?" AK ya tambaya yana ajiye rigarsa.
Farhana ta rufe saitin binciken da take yi na Flight Schools da sauri, ta maida na Thesis dinta. "Ina ta faman gama rubutu na ne Honey. Isabella ta taya ni da wasu bayanai sosae."
AK ya rungume ta, "Ina alfahari da ke Farhana. Nan da wata daya kacal graduation dinki, sannan mu nufi Najeriya. Ina son komai ya tafi daidai."
Farhana ta boye fuskarta a kirjin sa. Tana jin dadi, amma kuma tana jin tsoron sirrin dake tsakaninta da su Hailey. A ranta tana tunanin: "Honey, ina son ka, amma kuma ina son in tashi a sararin samaniya. InshaAllah zan tabbatar da burina ba tare da na rusa gidan mu ba."a haka Haka sai da Ak ya ja farhana har zuwa shekara daya basu tafi najeriya ba ,inda su Isabella ke debe mata kewa Alhamduillah ,tayi Kiba ta farfado miss Elizabeth ma Tana mata taimakon ta a gefe ,farhana ta kara kyau .yara Dama tuni suka yaye kansu
Yayin da kwanakin graduation suke kusatowa, Farhana ta zama tana da ayyuka biyu: Karatun International Relations da safe, da kuma binciken yadda zata zama Pilot a asirce da daddare lokacin da AK yake barci.
Ranar yaye dalibai (Graduation Day) ta zo da wani irin sanyi mai dadi a garin Boston. Jami'ar ta cika da dalibai sanye da bakaken rigunan digiri (Gowns). Farhana ta fito radau, fuskarta shake da annuri, sanye da riga da wando na alfarma a karkashin babban rigar digirin nata.
AK yana gefe rike da Khalil, yayin da Brianna take taya su rike Sultana. Isabella da Hailey ma sun hallara domin taya kawarsu murna.
Bayan an gama taro, aka kira sunan Maryam Ibrahim matazu (Farhana) a matsayin daya daga cikin dalibai da suka yi nasara a fannin International Relations. AK ya ji wani irin alfahari, ya san kokarin da Farhana ta yi na hada rainon tagwaye da karatu.
Bayan an watse, su Isabella suka ja Farhana gefe zuwa wani dan lungu na jami'ar, inda AK ba zai gan su ba. Hailey ta fito da wani babban envelope mai dauke da tambarin wata fitacciyar makarantar tuka jirgi (Flight School) dake kusa da Boston.
"Farhana, wannan ne kyautar mu ta Graduation gareki," Hailey ta fada tana mika mata envelope din.
Farhana ta bude takardun, idonta ya zaro. Asali ne na Admission Letter da kuma shaidar biyan kudin matakin farko na karatun Pilot (Ground School enrollment). Sunyi nasarar samar mata da wannan damar ta hanyar wani tallafi na mata (Women in Aviation Grant) da suka nema mata a boye.
"Isabella... Hailey..." Farhana ta fara magana amma muryarta ta dashe. Ta fashe da wani irin kuka mai cin rai, ta rungume su duka biyun. "Ban taba tunanin zan samu mutanen da zasu fahimci mafarki na haka ba. Nagode sosae!"
"Kiyi shiru Farhana," Isabella ta shafa bayanta. "Mun san zaku tafi Najeriya nan da kwanaki biyar. Amma ki sani, wannan takardar tana jiran ki. Idan kun dawo daga hutu, zaki fara karatun nan a boye. Zamu taya ki boye wa Abdulkadir har sai ranar da kika zama Pilot sannan ya gani."
Farhana ta goge hawayenta, ta boye takardun a karkashin rigar digirinta. "InshaAllah, zan fara wannan tafiyar. Ba zan taba mantawa da ku ba."
Bayan kwanaki hudu, gidan Chestnut Hill ya cika da akwatuna. Farhana tana ta faman shirya kayan tagwaye, Khalil da Sultana wadanda yanzu suka kara girma da wayo.
AK ya shigo dakin, ya ga Farhana tana kallon taga. "Wifey, kin shirya? Gobe zamu nufi Najeriya. Abbi ya kira, ya ce tuni an fara shirye-shiryen tarbar mu an Abuja."a space of time din nan mummy tsinewa Ak ne kawai batayi ba Akan rashin zuwan sa ,hanadi tayi kuka tayi korafi inda yace idan ta sake masa maganar zuwa a bakin aurenta .
Mummy ta Kira farhana inda tace
Maryam nina Haifa Abdulkadir kiri kiri kin Hana sa zuwa wajena ,ba komai na bar miki shi
Kema ga yaro nan kin Haifa inshaAllah sai an miki abinda kika sa aka mun,kafin farhana tayi magana dif mummy ta kashe waya,me yasa baa mata Adalci ne ?Ak din da ba dadin sa take ji ba?Ak din ya sa ta kusa Haukacewa?
Ita ta isa ta Hana ko tashi shi Abu ne?mummy bata kira ta mata barkar yara ba sai kiran yin Allah ya isa
Firgit muryar Ak ta dawo da farhana daga tunaninta
Farhana ta juyo tana murmushi, "Na shirya Honey. Ina kewar su Diddi sosae. Amma kuma zanyi missing dinsu Isabella."
AK ya dan taba kuncinta, "Karki damu, watanni biyu ne zamu yi mu dawo. Kuma kinsan me? Na yi murna sosae da kika gama karatun nan. Gashi Kin dawo hayyacinki .da ace lokacin da kika so mu tafi ne ay su diddi baza su gane Kiba
Farhana ta gyada kai, ta tuna yadda ta koma yar 40 years lokacin Alhamduillah zuwan su Isabella ya kawo sau yi sosai a rayuwar ta mutane rahma ne.
Washegari, suka nufi filin jirgin sama na Logan International Airport. Su Isabella da Hailey sun zo har bakin kofa don yi musu bankwana. Isabella ta rungume Farhana, ta rada mata a kunne: "Remember, the sky is waiting for you."
Suna shiga cikin jirgin, Farhana ta tsinci kanta tana kallon matukin jirgin (Pilot) dake shiga dakin iko (Cockpit). Ta kalli hannunsa, ta kalli kayan jikinsa, sannan ta kalli AK dake kokarin sanya wa Sultana bel din zama.
Wani irin kwarin gwiwa ya ziyarci zuciyarta. Ta san cewa wannan dawowar Najeriya, ba dawowa bace ta hutu kawai, dawowa ce ta shirin fara sabuwar rayuwa.
Filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja ya cika da jama’a, amma ɓangaren masu isowa daga ƙasashen waje ya fi kowane wuri
Yan gidansu farhana duk Sun hallara Wanda Ak ne ya tsara hakan dan faranta wa farhana rai
Diddi tana sanye da wani babban leshi, fuskarta shake da farin ciki da fargaba, tana ta rarraba idanu ko za ta hango ‘yarta.
Lokacin da aka buɗe kofa, sai ga AK ya fito yana tura trolley, sanye da riga mai sanyi da wando na zamani. A bayansa kuwa, Farhana ce ta fito, riƙe da hannun Khalil wanda yake ta taku yana ƙoƙarin tafiya da kansa,sultana tana kafadar babanta dama ita daddys girl
ce
Wani irin kukan murna ne ya baƙanci filin jirgin. Diddi ta rugo da gudu, ta rungume Farhana tana kuka, Farhana ma ta fash dadi.
"Maryama! Maryama ta! Kin dawo? Dubi yadda kika yi kyau, dubi jikinki yadda ya washe," Diddi ta faɗa tana shafa fuskar Farhana.
maryama kinyi kyaun gani sosae. Fatarta ta yi wani irin sheƙi na Turai, ta yi kiba kaɗan wadda ta ƙara mata kwarjini da haiba. yanzu Farhana ta zama cikakkiyar mace, , kuma mai ilimi.
Abbi ya ƙaraso cikin takunsa na dattaku, ya karɓi Khalil (Lamido) yana murmushi. "Ibrahim... kalli kamaninsa da Abdulkadir. Allah ya raya mana ku."
Bayan an gama murnar ganawa a filin jirgi, ayarin motocin dangi suka nufi unguwar Asokoro, inda babban gidan AK yake. Farhana tana kallon titunan Abuja ta taga, tana jin wani irin sanyi a ranta. Ko da suka isa kofar gidan, danginta su Abbi da Diddi suka tsaya a nan, suka yi mata bankwana tare da addu'ar fatan alheri, suka bar Sameena kadai domin ta taya ta wasu ayyukan na dan lokaci.
Suna tsaye a harabar gidan, Farhana riƙe da Khalil tana ƙoƙarin daidaita tsaiwar sa ,samena rike da sultana intisaar sai kokarin daukar Khalil take yayinda kausar ta kurawa sultana ido cike da kauna .a gefe daya Hanadi tana kuka sosai a ƙirjin AK, tana gunƙuni tamkar wadda aka yi wa mutuwa.
Maimakon AK ya nuna rarrashin na mutunci a matsayinsa na miji dake tsaka-tsaki, sai ya ƙara matse Hanadi a jikinsa, yana shafa bayanta da gashin kanta a gaban idanun Farhana. Ya manta cewa Farhana ma baƙuwar gida ce, ya manta cewa yanzu suka sauka daga jirgi.
"Haba Hanadi, kiyi shiru mana. Na dawo, kuma ba zan sake tafiya in barki ba," AK ya faɗa muryarsa na rawa da shauƙi.
Hanadi ta ɗago fuskarta dake shake da hawaye, ta kalli AK cikin ido. "Darling na yi kewarka. Kalli yadda na rame, kalli yadda gidan nan ya yi min Baki saboda rashinka."
AK ya duƙo, ya sumbaci goshin Hanadi a gaban Farhana, sannan ya raɗa mata maganar da ta soki zuciyar Farhana kamar kibiya: "Baby, tonight is going to be special. I really miss you, and I promise to make it up to you tonight."
Farhana ta ji wani irin jiri yana neman ɗibarta. Kalmar "Baby" da "Special Tonight" sun daki kunnenta. Wannan shi ne mijin da a Boston yake gaya mata babu wadda yake gani sai ita? Wannan shi ne mijin da yake rantsuwar cewa ita ce tauraruwar sa?
AK ya juyo ya kalli Farhana, fuskarsa babu alamun kunya ko nauyi. "Farhana, maza ki shiga ciki ki huta. Na san yaran nan sun gaji. Bari in shigar da Hanadi ciki, tana bukatar kulawa ta yanzu."
Bai jira amsar Farhana ba, ya sa hannunsa a kafaɗar Hanadi, suka nufi ɓangarenta suna magana ƙasa-ƙasa, suka bar Farhana tsaye a tsakar gida da yaranta da akwatunanta.
Farhana ta shiga ɓangarenta da ƙyar, ƙafafunta suna mata nauyi. Ta zauna a kan kujera, ta kasa magana. Sameena ta ƙaraso da sauri ta karɓi Khalil dake kuka.
"Adda Farhana, kiyi haƙuri. Abin da yaya AK ya yi bai kyauta ba, amma..."
"Sameena, karki ce komai," Farhana ta katse ta, muryarta a dashe. "Na gani da idona. Na gani yadda soyayyar Boston take ta yaudara ce. A can, ni ce kadai matarsa saboda babu wata. A nan kuma, ni 'yar kallo ce."
Ta tuna kiran Mummy , ta tuna tsinuwar da aka yi mata, sannan ga wannan wulakancin na AK. Ta ji zuciyarta ta yi tauri kamar ƙarfe.
Ta miƙe, ta nufi akwatinta. Ta buɗe ta ciro takardun Pilot ɗin nan. Ta kalle su, sannan ta goge hawayen dake ƙoƙarin fita.
"AK, ka je wurin Hanadinka. Ka yi duk abin da kake so ka yi yau," ta faɗa a zuciyarta. "Amma ka sani, wannan takardar ita ce gatana. Daga yau, ba zan sake kuka a kanka ba. Zan rinka kallon sararin samaniya ne kawai, domin can ne natsuwa ta take."
AK ya tura kofar dakin Hanadi ya murda makullinsa, . Kamshin turaren Oud da Khumra mai ratsa jiki ya tarye shi, dakin ya gauraye da sanyin AC da dumin fitilu masu launin ja da rabe-rabe.
Hanadi tana zaune a bakin gado, sanye da wata kyakkyawar rigar barci ta siliki (silk) kalar ja wadda ta bayyana kyan surarta da fatarta mai santsi. Tana ganinsa, ta mike a hankali, idanunta cike da sha’awa da kukan shagwaba.
"Darling ..." ta kira sunansa cikin sanyin murya.
AK bai tsaya wata-wata ba, ya karaso ya janyo ta cikin jikinsa. Ya tura hannunsa cikin gashinta, ya dago fuskarta yana kallon cikin idonta. "Na yi kewarki, Hanadi. Na yi kewar komai na jikinki."
Ya duƙo ya fara sumbatarta a wuyanta, yana jin yadda fatarta take kamshi da laushi. Hanadi ta saki wani nishi mai sauti, ta rungume shi sosae, hannunta yana yawo a faffadan kirjin sa. AK ya ji wani irin dumi yana ratsa shi, ya mance da gajiya, ya mance da Boston, ya mance da komai.
Ya dauke ta cak ya dora ta a kan gado, ya biyo bayanta yana rarraba mata sumbata a ko’ina na jikinta. Hanadi ta fara kokarin cire masa riga, tana jin yadda bugun zuciyarsa yake karuwa. "Karka sake tafiya ka barni," ta fada muryarta na rawa yayin da AK yake nutsawa cikin dumin jikinta.
"Ba zan tafi ba, baby. Yau naki ne ni kadai," AK ya amsa yayin da yake rage kayan jikinsa.
Dakin ya cika da gunƙuni da kiran sunan juna. AK ya nuna mata irin kewar da ya yi mata ta hanyar nuna matsanancin shauki da kwarewa. Ya rinka wasa da ita tamkar sabuwar amarya, yana sa ta jin cewa babu wata mace a duniya bayanta. Hanadi ta mika wuya ga kowane bukatar sa, tana kukan dadi da kuma farincikin cewa ta dawo da martabarta a matsayinta na uwar gida.
A wannan daren, AK ya narkar da duk wani kishin dake zuciyar Hanadi da dumin jikinsa, yayin da ita kuma ta tabbatar masa da cewa ba ta da sa'a a wurin rarrashin miji.
Farin cikin dake fuskar Hanadi bayan komai ya lafa ba zai misaltu ba. Tana kwance a kirjin AK, tana jin bugun zuciyarsa yayin da yake barci mai nauyi. Ta shafa gashin kirjin sa, ta yi murmushin nasara.
"Ko da zata tafi da kai karshen duniya, a nan ne matattararka," ta rada a hankali.
Ta san cewa Farhana tana can bangarenta tana kuka ko tana tunanina , amma hakan bai dame ta ba. Babban burinta shi ne ta sa AK ya mance da "Maryama" koda na wasu kwanaki ne, kuma wannan daren ya tabbatar mata da cewa tana da sauran karfin ikon sa a hannunta.
this is just the beginning of the ending
zuwan su farhana Nigeria zai
zama silar tunuwar wani sirri