Free chapter · Read without an account

3

by Maimoon Abdallah · BANI DA HUJJAH!

🌺BANI DA HUJJAH!!🌺 

3. 

Zuciyarsa a dagule, fuskarsa a haɗe ya fito daga sashen mahaifinnasa, yana kokarin ficewa daga ɓangaren gabaɗaya suka kusa cin karo da mummy ya matsa baya a hankali ya bata hanya ganin shiga zata yi wajen Daddy, a taƙaice ya gaishe ta shima ciki ciki

 â€śina wuni” ko kallonsa bata yi ba ta shige ciki abinta ya bita da side eye kafin ya buÉ—e Ć™ofar shima ya fice a gidan, ba tare da kallen kallen komai ba ya buÉ—e motarsa ya shiga ciki ya tayar aka buÉ—e masa gate É—in Cds. Umar wazeer turaki ya fice yana driving gently, a gaban gate É—in barr Ameena wazeer turaki yayi horn ba tareda ya ko kalli opposite house É—in da shi kuma aka rubutu DR Ameenu Wazeer turaki ba, aka buÉ—e masa gate É—in ya shiga yayi parking yana kallon motar AMEEN dake parking space É—in which means yana gida as expected. Bai samu kowa a palourn ba sai sanyin ac da Ć™amshin turaren wuta mai daÉ—i nan ma, stairs ya nufa kanshi tsaye yana jujjuya key É—in hannunsa. 

“Aryaan?” Dakatawa yayi tare da juyowa yana kallon Mami da fitowarta kenan daga kitchen, ta ɗan buɗa ido tana kallonsa tace

 â€śashe dai kai É—inne hamshaĆ™i” É—an murmushi yayi kaÉ—an ya fasa haurawa ya dawo palourn ya zauna a kujera yana sake Ć™irĆ™iro murmushi

 â€śina wuni Mami” 

“Da ban wuni ba zaga ganni ne aryaan?” Shiru yayi kawai dan ya san dama dole sai tayi ranting in dai ta gansa, rabonsa da gidan ya kwana biyu tayi mita har ta gaji. 

“Yau kuma Allah yayi ka tuna mu kenan Aryaan, yanzu abinda kake yi ya kyautu kenan? Yaro É—an gata amma ka mayar da kanka kamar maraya?” Ta faÉ—a tana zagayowa ta zauna a kujerar da ke facing É—inshi tana ta kallonsa keenly, Nan ma bai ce mata komai ba sai murmushi kawai da yayi, ta sauĆ™e ajiyar zuciya  a hankali tace 

“To Allah ya kyauta, ya kake toh? How have u been?” Sai a sannan ya amsa da 

“Alhamdulillah Mami” 

“Are u sure?” GyaÉ—a mata kai yayi, tace 

“Toh Allah yayi albarka, ya tsare gabanku da bayanku, ya baku abinda kuke nema duniya wa lahira, a cigaba da hakuri a kuma cigaba da yayyafawa zuciya ruwan sanyi, zama lafiya da kowa ya fi zama É—an sarki, komai lokaci ne da shi haka zaka ga watarana kamar ba’a yi ba” 

“Amin Mami” ya amsa yana jinginar da kansa da kujera, miƙewa tayi tana kallonsa tace

 â€śAMEEN É—in ai yana sama kaje bari nima in duba girki ya kusa gamuwa ma  su lailerh zasu kawo muku” gyaÉ—a mata kai kawai yayi bashi da niyyar tashi, ta miĆ™e ta wuce kitchen, 10 minutes later ta kuma fitowa, da mamaki take kallonsa ganin har sannan yana zaune a wajen yana danna wayarsa, hakan yasa bata kulashi ba ta wuce sama dan kiran Ameen É—in da kanta, tare suka sauĆ™o da wani matashin saurayi kyakkyawa wanda zasu yi sa’o’i da Aryaan sai dai ya fi Aryaan hasken fata da glasses a idanunsa dressed casual, ya kalli Ammi bayan ya sauĆ™o cikin palourn yace 

“Ammi where is he?” Ammi ta Ć™araso cikin palourn tana kallonsa tace 

“Ji iskanci! Anan fa na barsa shine ya kama hanya ya wuce bai ce min zai wuce ba? Kuma fa har abinci nace ya jira amma shine ya wuce ya tafi abinsa koh? Kirawo min shi kace nace ya dawo yanzu ya zo yaci abinci”. Ameen ya É—an sauĆ™e ajiyar zuciya yana zama a kujera yace 

“Ki Ć™yaleshi kawai tunda ya tafi ba juyowa zaiyi ba kin sani” zama tayi itama a kusa da shi tace 

“Al’ameen me ke damun É—an uwanka ne?” Ya buÉ—a mata hannu alamun bai sani ba shima yana murmushi, 

“Ya zaka ce min baka sani ba, bayan ure closer to him than anyone” 

“Allah Ammi ban sani ba, but bari na watsa ruwa inje gida in same sa inji if there’s anything i should know” gyaÉ—a masa kai tayi tace 

“Idan ya faÉ—a maka pls ka zo ka faÉ—a min” 

“Okay Mami” ya faɗa yana miƙewa ya wuce sama murmushi kwance a fuskarsa

“Lailerh ta kawo maka abinci yanzu?” 

“Ah ah idan na dawo zanci” 

“Toh” ta faɗa tana kallonsa har ya haura kafin ta wuce kitchen dan duba abinda su lailerh da siyama ke yi.

Yana driving yayi dialing lambarsa yana ajiye wayar a gefensa bayan yayi connecting da speaker É—in motar, sai da kiran ya kusa yankewa kafin ya É—aga, Al’ameen yayi gyaran murya yace 

“Malam kana ina ne?”  

“Why?” 

“Ban sani ba! Kana gida ko baka gida?” 

“Bana gida!” 

“Kana ina?” 

“Doesnt concern u!”  Murmushi Ameen yayi kawai ya katse kiran yana nufan gidan nashi bayan ya kalli agogo Ć™arfe 10 saura. 

BuÉ—e masa gate mai gadi yayi bayan yayi horn once, ya shiga yayi parking a kusa da motar Aryaan dake space kafin ya fito ya nufi cikin gidan,  ba tare da knocking ba ya tura Ć™ofar palourn ya shiga ciki yana kallon ko ina, ganin baya ciki ya gyara glasses É—in idanunsa ya nufi hanyar sama da takalmansa, motsi da yaji a kitchen ya sa ya dawo da baya ya nufi kitchen É—in, a bakin Ć™ofa ya tsaya ya harÉ—e hannu a Ć™irji yana kallonsa, yana tsaye a jikin counter da singlet baĆ™a a jikinsa against fair skin É—insa, yayi pairing É—inshi da three quarter iya guiwarsa dat looks loose, Al’ameen ya kalli plate É—in scrambled egg dake plate da toasted bread guda biyu a gefe, black tea da yake haÉ—a ma kanshi a lokacin ya kalla kafin yace 

“Yaushe ka koyi girki bawan Allah” ko kallonsa baiyi ba, barin jikin Ć™ofan yayi ya nufe shi yana faÉ—in 

“WulaĆ™anci ne bana so, sai in juya in koma in da na fito, da ina da zuciya ma wallahi ba zaka ganni a nan ba, ko da yake Mami ce tace na zo ka je kana acting weird a gida kuma before in sauĆ™o ka wani wuce ka tafi, idan ka san baka so in zo waya ce ka zo gidanmu nemana?” 

“Says who kai naje nema?” Ameen ya hararesa yace 

“To me kaje yi?” Sai da ya ajiye cup É—in a gefen tray É—in kafin yace 

“Mami naje gaisarwa” Al’ameen yayi wani dariya da ya sa Aryaan kallonsa yace 

“Ko ba gaishe da Mami ba, u that i know É—in koh? Kai dai faÉ—i me ya kaika kawai, amma kafinnan haÉ—a black tea É—in da ni banci abinci ba na fito” ko kulasa baiyi ba ya É—auki tray É—in ya fita a kitchen É—in, Ameen ya Ć™arasa ya É—auki well cleaned cup da spoon ya biyo bayansa yana faÉ—in 

“Wannan É—in zai ishemu ne?” Bai kulasa ba ya ajiye tray É—in akan dinning, tun kafin ya zauna Ameen ya ja kujera ya zauna tare da É—aukar toasted bread guda É—aya ya bar masa É—aya, ya saka spoon ya É—ibi scrambled egg É—in ya kai baki, zama kawai shima yayi ya É—auki É—ayan bread É—in ya soma ci, Al’ameen ya É—auki cup É—in black tea É—in ya zuba a cup É—insa ya raba musu daidai da daidai, kafin ya tura masa nasa gabansa, komai bai ce masa ba ya ja ya fara sha yana É—an danna wayarsa fuskarsa a haÉ—e, sai da suka conye duka kafin ya miĆ™e ya koma cikin palour ya zauna yana danna wayarsa, kwashe kayan Al’ameen yayi ya kai kitchen ya ajiye a sink ya buÉ—e fridge ya É—auko bottled water guda biyu ya fito da su a hannunsa, jefa masa É—aya yayi ya cafe shi kuma ya Ć™araso yana shan É—aya, ya zauna a wani kujeran daban ba wanda Aryaan ke kai ba yana cigaba da shan ruwan, sai da ya gama sha ya ajiye sauran a center table kafin ya kalli Aryaan dake buÉ—e ruwan hannunsa a lokacin zai sha, yace  

“What happened bro? Tell me mana why are u acting all up haka?” Aryaan ya rufe ruwan ya ajiye tare da É—an dafe kansa, hakan yasa Ameen putting serious face ya miĆ™e ya dawo kujeran da yake zaune yace 

“Me ya faru É—an uwa?” Ajiyar zuciya ya sauĆ™e a hankali ya É—ago ya kalli Ameen da idanunsa da suka É—an yi ja yace 

“I’m tired Ameen! Please tell me miye nayi ma Daddy?” 

“What happened?” Ameen ya tambaya sounding concerned! Duk abinda ya faru ya kwashe ya faɗa masa from zuwan su uncle Ameenu zuwa zuwanshi gidan, Al’ameen ya sauƙe ajiyar zuciya yana kallonsa har ya kai aya kafin ya dafa kafaɗarsa yace

“Calm down bro! Yanzu iya wannan abinne ya saka ka É—aga hankalinka haka? Har ya nuna a face É—inka cewa ure tensed? Haba aryaan” wani mugun kallo Aryaan ya masa yana Ć™wace kafaÉ—arsa yace 

“Bangane iya wannan abin ba, shey u no comprehend abinda nace maka? Cewa fa nayi Dad and his brothers so suke in kawo mata nan da two months, how is this possible Ameen? Meyasa sai ni kaÉ—ai suka gani? What happen to u and hamza and the others? Kai da hamza da kuka girmeni ba’a ce ku kawo mata in so so so time ba sai ni?”  Al’ameen ya gumtse dariyarsa yana kallonsa yace 

“Wato yanzu ka yarda mun girmeka da yake zancen is not in ur favour, what happened to watanni ba girma bane? Kuma da kake zancen mu ba’a ce mu kawo mata ba, kai ai ka san dalilin da ya sa suka ce ka kawo mata, baka jin magana Aryaan, i’ll be so happy wallahi idan ma kayi auren ko wasu abubuwanka zasu saitu” Ganin yadda ya haÉ—e rai ya sa Ameen ya É—an bubbuga kafaÉ—arsa yace 

“Sorry bro, ka kwantar da hankalinka za fa ka samu mata nan da wata 2” jingina kansa yayi a jikin kujera yana kallonsa yace 

“I was thinking about Aneela…” tun kafin ya kai Ć™arshe Al’ameen ya haÉ—e rai tare da hararansa yace 

“Over my dead body ne zaka auri yarinyar nan, kai tsakaninka da Allah idan aka barka sai ka auri yarinyarnan? Sai kace ma yaranka wace irin uwa ka zaÉ“a musu kenan?” Kallonsa kawai Aryaan yake baice komai ba, Al’ameen ya É—auko wayarsa dake ringing ganin Mami yace 

“Mami ce, let me come and get going home”  

“Spend the night here mana” ya faÉ—a yana kallonsa, É—an shiru yayi sai kuma ya É—aga wayan yana sauraren Mami tare da kallon Aryaan da ya lumshe idanunsa, can yace 

“Eh Mami, ill spend the night here gobe zamu shigo tare da shi” shiru yayi sai kuma ya amsa da 

“Amin” daga haka ya katse wayar yana kallonsa yace 

“Duk ta damu ta É—auka wani babban abu ke damunka” 

“Okay yanzu Ć™arami ne ke damuna kenan” 

“Eh mana daÉ—i ne yayi maka yawa, ni ace in fito da matar a gani mana da tuni na kai an wuce wajen” 

“To yanzu ma idan ka kai ai ba zasu Ć™i yi maka ba” ya faÉ—a yana miĆ™ewa 

“Ah ah barsu dai su tambayeni first ni ai ina da wacce nake so, jira kawai nake a tambayeni in gabatar da ita gaban kowa da kowa, ba irinka bane ni da kake tunanin auren mace irin zaleena sunanta ko aleena….” 

“Aneeela..” suka tsinkawo muryarta daga bakin Ć™ofa, duk suka É—aga kai suna kallonta, idanunta cike taf da hawaye take kallonsu hannunta rike da jakarta sai wayarta a É—aya hannun tana sanye da  tshirt mai maÉ“allai fara da blue jeans, attachment É—inta ya xubo har gadon bayanta, sai siririn É—ankwali da ta É—aura a kai as usual. 

Kallo É—aya Al’ameen ya mata ya haÉ—e rai tare da miĆ™ewa da nufin haurawa sama yana mamakin irin rashin kamun kanta, yo rashin kamun kai mana idan ba haka mai zai kawo mace da ta san darajar kanta gidan mijin da ba nata ba da wannan daren? Halinta disgust him, Ko da yake its not entirely her fault har da na mai gayya mai aikin dan shi ya bata daman haka shi yayi welcoming É—inta a gidansa anytime idan ba haka ba ai bazata zo ba, wani takaici ya takure shi a wuya ya ja tsaki tare da É—aukan wayarsa zai wuce sama, ajiye jakar tayi ta Ć™araso palourn tare da shan gaban Ameen tana kallon cikin idanunsa tace 

“Al’ameen miye na taÉ“a yi maka a rayuwarnan da ka tsane ni? Baka Ć™aunata baka Ć™aunar gani na tare da farincikin rayuwata, mai nayi maka da zafi har haka da kake ikirarin over your dead body ya aureni”  wani kallo yake mata irin na malama na miki kama da wanda kika zo wajensa ne, kamar bazai kulata ba sai kuma yace 

“I’m glad uve been eavesdropping tun É—azu kuma kinji duk abinda nace, aryaan bazai taÉ“a auren mace irinki ba God forbid”  juyawa tayi ta kalli Aryaan dake kallonsu kansa a kishingiÉ—e da kujera, kafin ta juyo ta bawa Ameen amsa ya raÉ“ata ya wuce sama abinsa, ta bishi da kallon tsana kafin ta juyo ta dawo kujerar da Aryaan ke zaune tace 

“Love ka ji abinda yake faÉ—a koh? Pls dont listen to him, ure my life ka sani”  miĆ™ewa yayi shima zai wuce sama tayi saurin kamo hannunsa ya juyo yana kallonta, ganin yanda take kallonsa idonta cike da hawaye ya sa ya janyo ta jikinsa yana kallon face É—inta ya sa finger É—inshi yana share mata hawayen dake kumatunta, Ć™asa Ć™asa yace 

“Go home zamuyi magana later okay?” Ta gyaÉ—a masa kai tana kallonsa, ya sake ta ya ja da baya yana kallonta da guntun murmushi akan fuskarsa, Ć™arasawa tayi ta É—auki jakarta har ta buÉ—e Ć™ofa ta sake juyowa ta kalleshi, kashe mata ido É—aya yayi, tayi murmushi tana share hawayenta ta fice tare da jan Ć™ofar, yana juyawa ya ga Al’ameen a tsaye a jikin stairs ya harÉ—e hannu yana kallonsa, suna haÉ—a ido ya haÉ—e rai, kallonsa kawai Ameen keyi har ya zo zai wuce kafin ya ja tsaki da ya tabbatar yaji ransa a É“ace ya furta 

 â€śkayi asara” ko kulashi bai yi murmushi kwance a fuskarsa ya wuce sama, juyawa yayi ya bi bayansa saman ransa a mugun É“ace. 


#Banidahujjah
#Maimoon
***

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.