Free chapter · Read without an account
60
by ZAHRAA · Bayan Murmushi
farahana tashi da asuba, idanunta sun yi luhu-luhu. Ta ji shirun dake gidan, ta san inda AK yake. Ta yi wanka, ta gyara yara, sannan ta fita kitchen dan ganin mai sameena da Ruth suke na breakfast .
Ba ta dade da fita ba, sai ta ga AK ya fito daga bangaren Hanadi, sanye da wata doguwar riga, fuskarsa cike da annurin daren da ya gabata. Ya ganta, ya tsaya yana sosa koya, ya kasa hada ido da ita.
"Ina kwana, wifey ya fada a sanyaye.
Farhana ta kalle shi, ta ga wani hickey (tambarin sumbata) a wuyansa wanda Hanadi ta tabbatar ta bar masa don ya bata wa Farhana rai. Farhana ta yi murmushin takaici, ta kauda kai.
"Lafiya kalau. Allah ya ba da sa'a," ta amsa, sannan ta wuce ta bar shi nan tsaye, tana jin wani irin kwarin gwiwa na cewa: Idan jikin sa naki ne, rayuwar sa kuma tana hannuna.
A week later
Tun sassafe gidan Asokoro ya cika da hayaniya da kamshin girke-girke na alfarma. AK ya bai wa Farhana maƙudan kuɗaɗe dan grand birthday din twins ,inda ya ce mata ta tsara komai yadda take so, domin wannan ranar ta tagwayensa ce. Farhana ta nuna bajinta; ta tsara komai cikin natsuwa, amma kuma tana tafiyar da komai cikin nuna ko-o-ho ga AK.
AK ya kula da yadda Farhana ta zama sanyi-sanyi da shi (very cold). Idan ya matso kusa da ita, sai ta ba shi sarari. A ransa ya ƙudurta cewa idan suka koma Massachusetts, zai yi amfani da lokacin can ya sake gyara dangantakarsu.
Hanadi tana gefe guda, tana ta ƙoƙarin tsokanar Farhana. Duk da cewa Hanadi ba ta kishin tagwayen, domin ta san AK yana son yaranta kuma ba maganar gado ko kudi, din iyayenta Sun bar mata gadon da ba su kausar ba harta yaran farhana sai Sun mora,her only problem shine Ak yafi son yaranta
"Maman twins kinyi ƙoƙari wajen taron nan. Naso ace haka kika maida hankali Wajan gyara tsakaninki da papa ,dan har yanzu naga da ragowar kishin ruwan da kika dade Kina starving dinsa.Hanadi ta faɗa tana murmushin mugunta.
Farhana ta kalli Hanadi, sannan ta yi murmushi mai cike da sirri . "Hanadi, ki kwantar da hankalinki. Idan mijin ne ma gaba ɗaya kike so, ki ɗauke shi. Ni yaran nan sune gaba na, kuma kin ga yau ana murnar birthday dinsu su ne. Kina iya ci gaba da jin daɗin darenki da shi, ni ba ruwana."
Farhana ta juya ta bar Hanadi nan tsaye baki buɗe. Hanadi ta ji wani iri; ta saba ganin Farhana tana kishi, amma wannan sabuwar Farhana ta fi ƙarfin tunaninta.
Yaya Safiyya sun iso. Sun shigo bangaren Farhana ne kawai don su ga kiba da kyaun da ake cewa tayi Suna ganin Farhana ta fito cikin wani tsadadden leshi, sai suka ji kishi ya turnuke su.
"Lallai Maryama, ashe dadin USA ya shige ki haka?" Yaya Ramla ta fada tana yatsina fuska. "Mun jin labarin cewa ma kin kusa haukacewa a can, ashe duk karya ne?"
Farhana ta kalle su, ta tuna cewa har yau ba su taba yi mata barkar haihuwa ba. "Lafiya ta kalau Yaya Ramla. Watakila wadanda kuka ji labarin a gunsu ne suka kusa haukacewar."
Ta kyale su ta ci gaba da kula da baki. Abin mamaki, Kausar (diyar Hanadi) ta kusan tarewa a bangaren Farhana. Tana son Sultana sosae, ba ta yarda kowa ya dauke ta sai ita. Wannan haduwar jini tsakanin yaran ya ba kowa mamaki, har ma Hanadi no hard feelings from her side
Chan saiga fateeha abun ya farhana mamaki Ashe surprising dinta zatayi don ko da safe sunyi waya tace bazata sami zuwa ba ,already precious da Halima da Adda Sabrina da su ake ta shirye shirye (precious ma Tana abuja ta gama Abu )inda ko wacce ta kawo wa twins birthday gift na alfarma .
Lokacin yanke Cake ya yi. Aka fito da wasu manyan akwatunan kyaututtuka na twins ,kyautar ta girgiza kowa .Zee ta turo hadaddun kyautuka daga inda take, suma su Abbi da Diddi ba a bar su a baya ba.
Su Yaya Ramla suna can gefe suna gunƙuni. "Lallai Abdulkadir ya kashe kuɗi. Dubi yadda aka zuba abinci da drinks na Turai talawakan dangin farhana sai raba ido suke .Wato ma ba za ta kawo mana yaran mu gani ba?"yayi Safiyya ta tambaya cike da mamakin farhana
Hanadi ma ta ba twins gift inda taba Khalil kyautar fili a kaduna ,sultana kuma saitin gold .kyautar da taba kowa mamaki sosai Ak yaji hanadi ta kara samun matsayi a zuciyarsa
Kausar tana can manne da Sultana, . Hakan ya ba mutane sosae sha'awa ganin yadda yaran kishiyoyin suka shaku, yayin da iyayensu kowa yake jan nasa igiyar.
Daddare bayan taro ya lafa, gidan ya rage daga dangi sai abokan arziki. AK ya iske Farhana a ɗaki tana ƙoƙarin cire wa yara kaya. Ya matso kusa da ita.
"Wifey, taro ya yi kyau sosae. Na gode," ya faɗa yana ƙoƙarin kamo hannunta.
Farhana ta zare hannunta cikin dabara. "Ba komai Honey. Yara sun ji daɗi, hakan ya isa."
AK ya ji zafi, ya gane cewa daren nan ma ba zai samu kanta ba. Ya san cewa yanzu Hanadi tana jiran sa a ɓangarenta, kuma ya san cewa duk yadda ya nuna wa Hanadi soyayya, zuciyarsa tana ga Farhana. Bai sani ba cewa Farhana ba tashi take ba tana neman lokacin da jirginta zai ɗaga ta bar duk wannan hayaniyar ta ƙasa.
Bayan farhana ta sa yara bacci ta koma guest room inda precious da fateeha suke ,Yau zasuyi hirar Yaushe gamo
Wai ni farhana Yaushe rabonki da nusaiba ne? Fateeha ta tambaya tana shafa serum a face dinta
Uhmm gaskiya an kwana biyu dan na goge number ta ,kuma naga Kamar tayi left a group
Well Muna dan chatting dai tunda muka gama Abu ta zama distance Nima naja gefe fateeha ta amsa a sanyaye
Ay ni zan fada maku distance kiri kiri ni da zainab mun kusa zama tarihi ,tun sanda na Sami matsalar nan Massachusetts nayi nayi friendship dinmu yaki dawowa na hakura ,na tura mata invitation din birthday tace Tana Lagos ,kuma naga Kamar ba lokaci Hutu bane ya kamata ace tana school.
Nifa Kamar Nafa zainab a wuse 2 jiya Ina kokarin karasawa ta shige cikin crowd precious ta fada Tana kure su da ido .
Gaskiya ba ita kika gani ba,dan zainab bata da wata alaka da abuja maybe dai kammani ne.
Farhana ta fada in a dismissive way,suka cigaba da hirarsu
Chan sai wayar farhana tayi kara unknown number
Kije garden din gidanki zaki ga hanadi da partner dinta ,ras gaban farhana ya fadi,ita tunda take bata taba shiga garden din gidan ba sai da birthday din yaran nan,garden ne babba daya amsa sunansa yaji flowers masu kyaun gani ,babes kuzo muje garden Yau Ina ga dubun nusaiba zai cika kunga text message din daka min
Gidan yayi tsit amma da fitilu walwal .cikin sanda suka karasa inda suka fara jiyo magana kasa kasa ,Wai hanadi Kina nufin dan Mijinku yafi dokin ki shimfida shikenan Kin chi wasa?kin manta wahalar da kika sha fiye da shekara bai zo ya ganki ba?to wallahi kika bari suka Koma usa tare sai kinyi shekara biyar biki gansa ba ,dan ni Nasan irin asirin da diddi take aika wa farhana dan nice ma yar aikenta amma sabida alakata dake idan ta bani replace nakeyi .dan haka mu cigaba daga inda muka tsaya tun farko. jikin farhana rawa ya fara inda precious ta dalle su da flash din wayarta dan garden din bashi da Haske sosai ,ZAINAB gaba dayan su suka kira sunanta a tare