Free chapter · Read without an account
SARTSE A ZUCI...! Chapter 15
*SARTSE A ZUCI!đź’”*
*Arewabook@ayshadansabo*
*Paid book ****
©️ _Ayshat Ɗansabo Lemu_ ✍🏻
*Chapter 15*
Kamar yadda yayi promise a washegari yayi sallama da Hameedah ya wuce Abuja yabi flight zuwa Borno,kuma bai bar gidan ba saida ya sake jaddadawa Babah Gaje akan ta kula masa da Hameedah sosai.Kuma Babah Gajen da gaske ta kula da ita ɗin domin yini suka yi tare da Hameedah tana kula da ita hatta girki ita tayi musu a ranar,a washegarin ranar Ya Zayd ya biyo su Daddy ya dawo aka bar Amal da Momy su sai anyi sadakan bakwai za su juyo.Kwana biyu Zayd ya ƙara ya wuce Lagos domin ana buƙatarsa a wajen aiki da gaggawa,hakan ya sake jefa Hameedah cikin kaɗaici ga cikin jikinta da duk ta ƙosa su rabu lafiya dashi.Acan Maiduguri kuwa Amal har suka kwana biyu zuciyarta ta kasa sakewa,abinda ya faru tsakanin Najwa da Yaya Zayd ya kasa barin kwanyarta ta huta.Tausayin ƴar Uwarta Hameedah take ji sosai tare da ji mata tsoron kada yaje garin bin matan banza ya kwaso musu wata cutar kamar yadda tasha jin ana faɗi,zuciyar Amal bata taɓa kawo cewa sau ɗaya kaɗai Ya Zayd Abdallah ya taɓa shiga jikin wata ƴa mace ba bayan Hameedah.Daga Momy har Anty Mamah kafin su wuce sun sakata a gaba da tambayarta ko lafiya domin sun fahimci bayan mutuwar Hajiya Babba daya bigeta akwai wata damuwa da take ɓoyewa a zuci,amma sai ta sanar dasu cewa babu abinda ke damunta alhinin mutuwar ne kawai.Kuma duk da hakan Momy bata yarda ba bayan wucewar su Anty Mamah saida ta sake sanya Amal a gaba da tambaya amma ta tabbatar mata da cewa babu abinda ke damunta,gudun kada Momy tayi ta tambayarta yasa ta saki ranta a kwanaki biyun da suka biyo baya har tana iya yin Vedio call da Aman Kurfi dake can ƙasar Egypt suna jinyar Doctor Kurfi.Kuma a cikin vedio call ɗin da suke yi Amal ke sake fahimtar halin damuwar da Aman ke ciki akan jinyar Mahaifinsa Doctor Shehu Kurfi domin ya shaida mata cewa jikin nasa kwana biyu ya matsa masa ana shirin yi masa aiki ne a mafitsararsa da jijiyoyin suka tottoshe idan zaiyi fitsari gabaki ɗaya sai ya tada hankalinsu da ihun azaba,sosai Amal ta tausaya ta kuma yi addu'ar samun nasara idan har aikin zai kawo sauƙi ga matsanancin yanayin da Abban Aman ɗin ke ciki.Yaya Hameedah ma kullum sai sun yi vedio call da Amal tana faɗi mata duk ta ƙosa su dawo domin bata jin daɗin zama daga ita sai Babah Gaje,ita kuma Amal gabaki ɗaya ta tsani ta koma gidan Yaya Zayd duk da cewa tasan ya koma bakin aikinsa.Sai dai kuma duk yadda take gujewa komawa gidan saida Momy ta jaddada mata cewa gidan Hameedah za ta koma,kuma koda suka biyo flight ya saukesu a Abuja washegarin ranar da akai bakwai Habu driver ɗin Yaya Hameedah shine yaje daga Kaduna ya ɗakkosu zuwa gidan Yaya Zayd ɗin.Momy tayi kwana ɗaya kafin Yaya Sulaiman yazo su wuce Zaria a washegari,har kuka Amal tayi a ɓoye domin taso Momy ta amince su tafi Zaria tare amma sai Yaya Hameedah ta dinga roƙonta akan tayi haƙuri tayi zamanta kada ayi haihuwar babu ita tunda saura kwanaki suka rage ta shiga watan da EDD ɗinta zai cika.Kuma cikin kwanaki goma da Amal tayi zaman jira Allah kaɗai yasan irin dauriyar da tayi da bata sanar da Yaya Hameedah abinda idanunta suka gane mata game da mijinta ba,domin lokuta da dama idan suna zaune ya kira wayar Hameedah taji yadda take zuba masa shagwaɓa da soyayya sai taji Yaya Hameedah na bata tausayi matuƙa.Ana gobe EDD ɗin zai cika Yaya Zayd ya iso Kaduna da daddare domin jirgin da ya biyo six ya sauka,gashi babu halin hawa train motar haya ya biyo dole ya iso Kaduna domin baiyi dabarar kiran Habu yaje ya ɗakkosa daga Abuja ba.Time ɗin daya iso ya tadda Amal tare da Hameedah zaune a cikin falo suna hira,Hameedah ta yunƙura za ta tashi yayi saurin ƙarisowa ya maidata zaune yana kissing forehead ɗinta yake tambayarta lafiyarta ita da unborn ɗinsa.Amal ganin hakan ya sanya tayi saurin tashi domin wucewa room bayan ta gaidashi ciki-ciki tana jifansa da kallo mai cike da tsana,kuma sosai tasirin kallon ke ƙona zuciyar Yaya Zayd yana sake jin cewa yayi nadamar barin Najwa ta jima a cikin gidansa har tayi tasirin rinjayar ra'ayinsa.Ko a yau kafin barowarsa Lagos yaga saƙon ban haƙurinta akan rashin ɗaga call ɗinta daya daina yi,kuma shima Suraj tun daga ranar da abin ya faru ya kirashi yana bashi haƙuri akan ya yafewa Najwa ba laifinta bane Allah ne ya ƙaddara Amal za ta kamasu tare.Har Amal ta wuce ya kasa ɗauke idanunsa daga bin bayanta da kallo zuciyarsa na saƙa masa abubuwa da yawa,domin tabbas yasan a yadda ta gaggaya masa kalamai har da furta masa kalmar tsanarsa ƙarara to wannan shurun da tayi bata tona asirinsa a wajen Hameedah ba akwai abinda take shiryawa domin yasan halin darunta da kafiyarta tun tana ƙarama.Kissing ɗin yatsun hannunsa da Hameedah tayi shi ya maidosa cikin hayyacinsa ya riƙeta suka nufi side ɗinsa domin a gajiye yake sosai,kuma ya taho da tarin buƙata amma kuma baya jin Hameedah za ta iya dashi yadda yaga tana narkesa masa.Kuma kamar yadda yayi zato koda ya fara nuna mata maitarsa saita dakatar dashi tana masa complain da cewa maranta ke ciwo,haka ya danne feeling ɗinsa ta taimaka masa ya shirya kafin su fito zuwa falonsa taje kawo masa fruit da black tea da ragowar roasted chicken da Amal tayi musu ɗazu.Cikin dare ciwon naƙuda ya taso Hameedah ta fara masa kukan ciwon baya,ƙarfe uku saura yaje ya bugawa Amal ƙofa wacce ke zaune bisa kan sallaya a lokacin tana addu'a bayan ta idar da nafilfilin da tayi.Tunda taji bugun ƙofar kuma gabanta ya faɗi tunaninta ya bata cewa Yaya Hameedah babu lafiya,cikin sauri ta isa ta buɗe ƙofar tana kallon yadda Yaya Zayd ya zubo mata idanu ganinta da dogon hijab har ƙasa ya sanya shi bata umurnin biyosa yana sanar da ita cewa asibiti za su ta ɗakko jakan kayan haihuwa da suka shirya.Suna isa asibitin aka duba Hameedah Likitan ya tabbatar musu da cewa haihuwa ce,Yaya Zayd ya barsu da Amal ya koma gida tunda Likita tace dashi Hameedah za ta iya kaiwa safe bata haihu bama.Koda ya koma gida ya kasa rintsawa,yana taso ya kira Momy ya sanar da ita amma kuma baya son ɗaga musu hankali.Yana idar da sallar asuba ya ɗauki hanyar komawa asibitin,kuma koda ya isa ya tadda Amal saita sanar dashi cewa har yanzu dai babu wani labari amma Likitan tace nan zuwa 7am suke sakaran za ta iya haihuwa.Kuma kamar yadda Likitar ta faɗi bakwai da ƴan wasu mintoci Hameedah ta sankato santalelen jaririnta mai kama da ita tamkar kwabo da kwabo,duhun fatar Babansa kaɗai ya ɗakko sai tsayin domin tun yana jinjiri dogo ne dashi tubarkallah.Kukan daya dinga canyarawa tun fitowarsa duniya ya fara yiwa su Amal albishir ɗin cewa ta sauka,kuma koda Nurse ɗin ta fito domin yi musu albishir ta basu tabbacin cewa daga Uwar har Jinjirin lafiya lau suke da zaran an kammala kintsasu za a fito musu da jararin.Yaya Zayd ya zube a ƙasa yayi sujudar nuna godiyarsa ga Allah,Amal farin ciki ya cika zuciyarta na cewar ta sami ɗa.Tsabagen farin ciki duk sai Yaya Zayd ya ruɗe yama manta da batun kiransu Momy burinsa kawai yaga Hameedah da babynsa,Amal ce ta kira line ɗin Anty Mamah ta fara yi musu albishir da haihuwar Hameedah.Kuma da yake Anty Mamah ita keda Daddy Amal na jiyo time ɗin data saki guɗa muryar Dad na tambayarta ko guɗar ta mece ce? Latse kiran tayi tabar Amal na sakin murmushi kafin ta mayar da akalar kiran zuwa ga line ɗin Momy.Bugu biyu Momy ta ɗaga wayar tana tambayar Amal me suka samu domin tunda taga kiranta a daidai wannan time ɗin tasan cewa Hameedah ce ta haihu,kuma koda Amal ta sanar da ita cewa Namiji aka samu buɗan bakin Momy kawai sai cewa tayi,"Allah shi raya mana little Abdallah da imani." Mamaki ya rufe Amal da jin ƙarfi hali irin na Momy daga faɗan haihuwa har ta raɗawa Yaro suna,sai dai kuma abinda bata sani ba shine tuni Momy da shalelen nata Zayd suka gama yanke shawarar idan Hameedah Namiji ta haifa to sunan Abbah Abdallah zaici,idan kuma mace ce sai dai a raɗa mata suna Asiya duk da cewa Yaya Zayd ɗin ya tubure cewa idan mace ce Aysha ce ba Asiya ba.Kuma a lokacin da aka fito musu da Jaririn Yaya Zayd ya ɗaukeshi yayi masa huɗuba,sai kawai Amal ta jiyo wannan miskilar muryar tasa yana faɗin cewa,"Allah ya rayaka little Abdallah yasa ka gaji kyawawan halayen mai sunan."Jin sunan da shima ya kira jinjirin nasa dashi ya bata tabbacin cewa dama can sunyi shawara da Momy kenan shiyasa itama ana cewa Namiji aka samu ta kirashi da suna Abdallah.Hannu Amal ta miƙa masa alamun ya bata jaririn amma sai ya sake rungume Yaron yana jifanta da wani mugun kallo,sai ta shagwaɓe fuskarta tare da narkar da murya ta fara masa magiyar son ganin babyn.Ya zuba mata idanu lokacin Yarintarta na dawo masa tar a cikin kansa domin haka take kwantar da kai idan tana son ai mata wani abu,harara ya dalla mata kafin ya miƙa mata Yaron ta amsa hannunta har rawa yake.Wani irin farin ciki take ji na cika zuciyarta ƙaunar Yaron na keta jinin jikinta yana shiga,kamannin Yaron da Yaya Hameedah ya dinga baiwa Amal mamaki duhun fatar kawai ya ɗakko na Yaya Zayd ɗin.Ganin yadda Amal ke kallon jinjirin tana satan kallonsa ya sanya Yaya Zayd sake haɗe face ɗinsa,ana cewa an kai Hameedah ɗakin hutu suka rankaya domin dama a ƙagauce yake da son ganin lafiyar matarsa.Kuma lokacin da suka shiga suka hango Yaya Hameedah a kwance shine ya fara isa bakin bed ɗin ya rungumeta yana fara mata ɓarin kalamai,Amal tayi tsaye sake da baki tana kallon tsagwaron duniyanci da rashin kunya a wajen Yaya Zayd.Gabaki ɗaya nunawa yayi tamkar baisan cewa tare da Amal suka shigo ɗakin ba,ita kuma Yaya Hameedah ta lafe a jikinsa da alamu ita Kanta ta manta da Amal na cikin ɗakin.Ita kuma Amal da zuciyarta ya gama ɓaci sai ta ja ƙwafa tana isa bakin bed ɗin ta lallaɓa ta aje babyn a gefe guda,kuma a lokacin Hameedah tayi saurin ɗagowa ta kalli fuskar Amal data hadeshi tana jifansu da harara.Yaya Zayd dake kallonsu ya danne dariyar dake son ƙwace masa yana mamakin ƙarfin hali irin na Amal Taheer,ita ko Hameedah murmushi ta sakar mata tana barin jikin Yaya Zayd ɗin ta koma ta jingina da jikin bed ɗin tana amsa sannu da jikin da Amal ta fara yi mata.Kuma bayan Hameedah ta gama amsa sannun sai Amal ta juya domin barin musu ɗakin bayan ta duƙa ta sumbaci bouncing baby ɗin da soyayyarsa ya gama cika zuciyarta farat ɗaya,tana fita ta kunna data ta hau online ta fara yima Aman Kurfi albishir da cewa sun samu baby boy.Kuma cikin sa a yana online sai kawai ya kirata vedio call,suka jima suna magana bayan ta tambayi jikin Abbansu yace da sauƙi gobe za a yi aikin da ya faɗi mata cewa za a yi ɗin.Tayi fatan nasara tana sanar dashi cewa za ta turo masa pic's ɗin baby idan ta ɗauka,bata sauka daga online ɗin ba duk saida tabi su Zulaiha da friend's ɗin Hameedah da take da lambarsu ta sanar dasu haihuwar.Ta kira Anty Falmata da Anty Salma suma ta sanar dasu tana sake jin kewar rashin Hajiya Babba na cika zuciyarta,tasan da tana raye itace mutum ta uku da za ta fara kira ta sanar da ita haihuwar Hameedah.Cikin sanyin jiki ta kira line ɗin Baba Aminu Mahaifin Momy ta sanar dashi haihuwar Hameedah,Dattijon ya nuna farin cikinsa tare da addu'ar samuwar ɗorewar lafiya ga Hameedah da babyn.Har ta manta bata kira Anty Yagana ba sai ta kirata ta sanar da ita,ta shiga nuna farin cikinta tare da sanar da Amal cewa zuwa jibi tana nan tafe dama alƙawari ne tsakaninta da Hameedah cewa itace za ta yi mata zaman jego.Zuwa ƙarfe goma da rabi na safe motar dake ɗauke dasu Anty Mamah ya iso cikin asibitin,Nuhu driver ne ya kawosu domin Yaya Sulaiman ya tafi Abuja a daren jiya.Amal ce ta fito tayi musu jagora zuwa ɗakin da Hameedah da baby suke bayan sun rungume juna ita da Anty Mamah da Jamcy,cike da farin ciki Jameelah ke sanar da Amal cewa ta ƙosa taga da wa baby yayi kama Uwan ko Uban gashi dukkansu naji da kyawu.Suna isa Jameelah tayi ido biyu da babyn ta saki hailala tana jinjina buwayar Ubangiji,kyawun Jaririn da tsananin kammaninsa da Hameedah ya rikita zuciyarta.Soyayyar Yaron ya cika zuciyarta da ƙyar ta iya miƙawa Anty Mamah babyn,Anty Mamah ta amshi Abdallah itama tana jinjina buwayar Ubangiji domin Allah yayi halitta a wajen.Ta tofe Yaro da addu'a tayi ma Uwa fatan samun lafiyar shayarwa,suna nan zaune suna santin kyawun baby Yaya Zayd ya shigo ɗakin hannunsa riƙe da ledan maganin da aka rubutawa Yaya Hameedah.Suka gaisa da Anty Mamah cikin sakin fuska bakinsa ya kasa rufuwa sai murmushin farin ciki kawai ke haskawa a saman kyakykyawar fuskarsa,ba a basu sallama ba sai wajen la'asar tukunna.Kuma da yake Anty Mamah tazo kenan har sai anyi suna Jameelah kaɗai ce bayan ta idar da sallah suka juya Zaria ita da Nuhu driver,Amal ta bata saƙon cewa ta miƙa mata gaisuwa wajen Momy ta kuma sanar da ita cewa idan bata zo taga baby zuwa gobe ba sunyi fishi da ita......✍🏻