Free chapter · Read without an account
SARTSE A ZUCI....! Chapter 17
*SARTSE A ZUCI...!đź’”* *Arewabook@ayshadansabo*
*Paid book ****
©️ _Ayshat Ɗansabo Lemu_ ✍🏻
*Chapter 17*
A ɓangaren Zayd Abdallah kuwa time ɗin daya koma ɗakin baccinsa ransa a jagule yake sosai,don haka kai tsaye ya rage hasken fitillun bedroom ɗinsa yabar masu duhu ya wuce zuwa saman bed ya kwanta.Zuciyarsa da gangar jikinsa duka suna buƙatar jin ɗumin Hameedah da ni'imtaccen ƙamshinta a kusa dashi ne,yana buƙatar yayi wasanni da gangar jikinta koda ace bazai samu cikakkiyar gamsuwa ba.Ya lumshe idanunsa yana sake jin kansa na ɗaukar ɗumi,a nutse kuma ya buɗe idanun ya lalubo wayarsa dake soke a aljihun wandonsa ya kunna data domin hawa online ya duba ko yana da saƙonni ta mail.Bayan ya gama dubawa ne ya shiga whatsapp domin yin viewing status don ba kasafai ya fiya yin chat da friend's ɗinsa ba,sai dai kuma yana shiga yaga yadda saƙonni ke shigowa sai ya fara ragewa don haka a nutse ya fara bin chat ɗin yana dubawa har yazo kan lambar Najwa.Tamkar bazai buɗe saƙonta ba sai kuma ya buɗe zuciyarsa na kisima masa cewa yayi missing ɗinta,yana shiga ya tadda vedio ne ta aiko masa.Kuma daga time ɗin da yayi viewing vedio ɗin ne komi ya sake kwance masa ya shiga cikin azababben feeling,vedio ɗin jikinta naked ta aiko masa tana faman shafa ƙirjinta da wani irin salon daya motsa sha'awarsa ba kaɗan ba.Dama kuma gashi yana cikin yanayi sai abin ya haɗe masa ya sake rura wutar fitina a cikin zuciyarsa,ba tare da wani dogon tunani ba ya samu kansa da danna mata kira vedio call don yana da tabbacin cewa tana online.Kuma kamar yadda yayi zato hakan ne ya kasance domin ringing biyu kawai kiran yayi tayi receiving hoton kyakykyawar fuskarta ya bayyana a allon screen ɗinsa,kuma bai jira komi ba ya aike mata da zazzafar kiss ɗin daya tabbatar mata da cewa ya faɗa tarkonta domin ta tabbatar ya kalli vedio ɗin kuma shegiyar abar ta motsa masa.Ta saki lallausar murmushi tana wani taune harshenta da kashe masa idanu,shi kuma cikin sarƙewar harshe yake bata umurnin cire masa rigar baccin dake jikinta wanda ya bayyana surarta.Kuma ba tare da ɓata lokaci ba Najwa tayi masa yadda yake so,wani irin zafafan kisses yake aike mata ita kuma tana aiko masa da wani irin sautin nishi dake sake kunna wutar fitina a cikin zuciyarsa.Gabaki ɗaya sunyi nisa cikin aikawa juna dirty words dake tada ƙura ita kuma Hameedah ta murɗa handle ɗin ƙofar bedroom ɗinsa ta shiga,sam Yaya Zayd bai ji motsin shigowarta ba domin hankalinsa ya gama tafiya babu abinda kunnuwarsa ke jiyo masa sai sautin Najwa dake masa salo kala-kala da gangar jikinta yana sake rikicewa.Hannunsa guda yake wasa dashi akan jikinsa yana sake kunnuwa,don haka har Hameedah ta ida shigowa cikin ɗakin bai ji shigowarta ba.Ita kuma cikin duhun hasken ɗakin take hango yadda idanunsa ke kafe akan wayar dake riƙe a hannunsa guda,ga ɗaya hannun kuma naga muhallin data ɗauke idanunta daga wajen cikin sauri ƙirjinta na masifar bugawa sakamakon jiyo sautin muryar Najwa ƙasa-ƙasa.A hankali ta dinga takawa bugun ƙirjinta na sake ɗaukar rawa har ta isa bakin bed ɗin tayi tsaye nesa dashi kaɗan ta yadda za ta iya hango abinda ya ɗauke hankalinsa har ta shigo ba tare daya ankara ba,kuma a lokacin da idanunta sukai nasarar sauka a allon screen ɗinsa ne ta fasa ihun da yayi gaggawar maido da Zayd cikin hayyacinsa har ya fahimci cewa ta shigo cikin ɗakin.Sai dai duk yadda yayi saurin kife wayar da tashi zaune Hameedah ta riga taga fuska da jikin da hankalinsa ya ɗauku a kanta naked babu komi a jikinta domin ba iya rigan baccin daya buƙaci ta cire masa ta cire ba,tsirara tayi masa ta yadda tayi kwanciyar da zai dinga kallon komi yana sake shiga yanayi.Wani irin kuka ya sarƙe Hmaeedah ta juya da sassarfa domin barin masa ɗakin amma sai ya daka tsallen daya rigata isa bakin ƙofar,don haka koda ta iso bai bata kowani irin dama ba ya ɗauketa cak! Ya nufi saman bed ɗin da ita ya shimfiɗe.Kuma duk iya bore da magiyar da take masa akan kada ya taɓata ya barta ta fita bata son ganinsa Zayd bai ji ba,domin ƙarfi ya sanya ya sakar mata nauyinsa baki ɗaya ya kuma haɗe bakunansu waje guda ya fara aika mata da zafafan saƙonni a urunce.Duk irin kukan da Hmaeedah keyi masa bai saurareta ba ya cigaba da wasa da jikinta a zafafe,duk wani abu da zai sanya shi ya samu sauƙi shi kawai yake bai damu da kukanta da rashin maida martaninta ba.Sosai ya fara fita a cikin hayyacinsa ya fara ƙoƙarin wuce limit,hakan ya sanya ta ture hannuwansa dake ƙoƙarin rabata da wandon baccin jikinta tana sanar dashi a halin da take.Bai kuma saurara mata ba har saida ya cire wandon ya kuma tabbatar da abinda take faɗi sannan ya dakata daga yinƙurinsa,ya ƙanƙameta a ƙirjinsa yana jin yadda sautin kukanta ke sake hautsina kwanyarsa.Da ƙyar ya samu nasarar rage damuwarsa,ya margina gefe guda yana mai rintse idanunsa kunnuwansa na cigaba da jiyo sautin marayan kukan da Hameedah keyi zuciyarta cike da tashin hankali da jin matsanancin ɓacin ran dake zafafa ƙirjinta.Ahankali ta sauka daga saman bed ɗin ta shiga maida kayan jikinta tana yi tana kukan baƙin cikin halin da Yaya Zayd ya jefa kansa a ciki,gabaki ɗaya zuciyarta ta gama bata cewa ya riga ya faɗa tarkon neman mata domin bata yarda iya soyayyar shan sweet yake dasu ba.Fuskar Najwa da gangar jikinta data hango kawai ke sake yi mata gizo tana jin ƙirjinta na sake ɗaukar zafi,ko gabanta ba sosai take gani ba ta nufi ƙofar bedroom ɗin ta fice zuciyarta tamkar za ta rikito ƙasa haka take ji.Har ta ɗauki hanyar bedroom ɗinta sai kuma ta tuna tare da Anty Yaganah suke kwana kuma ba za ta so ta farka daga barci ta jita tana kuka ba,domin kuka sosai take so tayi ko zuciyarta za ta sami sauƙin abinda take jin zafinsa na babbaka ƙirjinta.Don haka kai tsaye tayi kwana ta nufi room ɗin da Amal ke kwana ta tura ƙofar ɗakin ta danna kanta ciki,kuma kamar yadda zuciyarta ta bata Amal ta jima dayin bacci sabida tashin dare hakan ya kasance domin a lulluɓe cikin duvet ta hangeta cikin dump light ɗin daya haske ɗakin kaɗan.Direct saman sofa ta nufa takai zaune tana mai fashewa da wani irin kuka mai cin rai,kuka take sosai wanda ita kanta bata san cewa sautinsa da ƙarfi yake fita ba har saida ta ji kamar Amal ta motsa.Kuma kafin ta iya rage ƙarfin sautin har Amal ta tashi zaune domin ita dama bata da nauyin bacci sosai,kuma a cikin duhun ƙaramin hasken ta hango Hameedah tallabe da kumatunta tana faman rusa kuka.A wani irin firgice ta sauka daga bed ɗin ta nufi wajenta tana tambayarta abinda ke faruwa,kuma a maimakon Hameedah ta baiwa Amal amsar tambayar sai kawai ta rungumeta tana sake rushewa da kuka.A cikin muryar kukan take kiran sunan Yaya Zayd,hakan yasa Amal riƙeta sosai a jikinta tana tambayarta mai ya samu Yaya Zayd ɗin? Still dai a maimakon amsa sai wani sabon kukan ya sake ƙwacewa Hameedah,Amal ta sake tambayarta baida lafiya ne? Nan ma shuru sai kuka.Wani tunani ya haska a cikin kan Amal sai tayi saurin yin ƙasa da muryarta tana faɗin,"Yaya Hameedah kuka bazai yi maganin komi ba just tell me abinda ke faruwa please!" Hameedah sai ta tsaida kukan tana faɗin,"Amal Yaya Zayd neman mata yake,na sake kamashi da ita suna ƙazantaccen vedio call,zuciyata zafi take Amal ina ji kamar ƙirjina zai buɗ....." Ta kasa ƙarisawa sabida kukan daya sake sarƙeta tana jan wani irin numfashi da ƙyar.Hankalin Amal ya tashi amma ko kaɗan batai mamakin jin abinda Hameedah ta faɗi ba,cike da zallar takaici da jin tsanarsa mai girma Amal ke faɗin,"Yaya Hameedah dole kiji koma miye domin babu abinda yakai ace kana kula da mijinka da tsare duk wani haƙƙinsa na aure amma kuma hankalinsa naga Matan waje,tabbas babu abinda yakai hakan baƙin ciki da takaici,bazan ɓoye miki ba Yaya Hameedah na tsani Yaya Zayd,na sake tsanarsa ne a ranar da idanuna sukai mummunar ganin da ban taɓa zato ko tsammani b...." Cikin sauri Amal ta tsaida kalamanta sakamakon tunawa da tayi da cewa Hameedah bata san komi ba,bata sanar da ita komi a wancan lokacin ba sabida gudun jefata cikin wani hali.Sai dai masu iya magana suka ce magana zarar bunu ce ta riga ta furta kalaman da suka sake tashin kan Yaya Hameedah,ta dubi Amal a hargitse tana tambayarta abinda ta gani wanda ya ƙara mata tsanarsa.Amal tayi shuru hawayen takaici na wanke idanunta domin babu abinda take hangowa sai surarsa a wancan lokacin,ta lumshe idanunta tana jin yadda Hameedah ke jijjigata tana tambayarta amma ta kasa buɗe baki tace komi.Da wani irin tsawa Hameedah ta girgiza kafaɗun Amal tana tambayarta ta sanar da ita abinda idanunta suka gane mata,cikin matuƙar sarewa tace,"Ko kema ya taɓa nemanki da lalata ne Amal ?" Tambayar yayi tsawa a tsakar kan Amal tare da masifar jijjiga zuciyarta.Ta buɗe idanunta cikin sauri ta dubi Hameedah dake kukan hawaye kashirɓan,cikin wani irin yanayi Amal ta shiga jijjiga kanta tana faɗin,"No! Yaya Hameedah,no!! Karki sake bari wannan tunanin yazo kanki please!" Hameedah tace a ƙagauce,"Amal idan har ba hakan bane to ki taimakeni ki sanar dani me kika sani game da Yaya Zayd wanda yasa kika tsanesa kike nesanta kanki dashi ko kaɗan bakwa gamaciji da juna?" Amal cikin raunin murya ta fayyacewa Yaya Hameedah abinda idanunta suka gane mata a ranar data dawo gida daga hospital domin yi mata girki.Ta rufe kalamanta da faɗin,"Na tsanesa Yaya Hameedah,kuma tun daga ranar kike bani tausayi domin nina san baki rageshi da komi ba,kina son shi don haka ki ɗaura ɗamarar yin yaƙi da matan banza,na rufe komi ne sabida a lokacin kina cikin halin da komi zai iya faruwa idan kika ji wannan fasadin daya aikata a cikin gidan aurenki,wannan dalilin yasa ko ganinsa bana son yi domin ina takaicin in buɗe idanuna inga irin yadda kuke tarairayar juna amma shi hakan bai taɓa sawa ya kasa haɗa jikinsa da wasu matan ba bayan ke,kiyi haƙuri ki masa addu'a nina san a irin soyayyar da zuciyarki ke masa ko kinji zafinsa zuwa wani lokaci kaɗan zai miki daɗin bakin da za ki sake manta komi Yaya Hameedah." Amal ta ƙare kalamanta tana jin wani irin ɗaci a cikin zuciyarta domin a cikin idanun Hameedah take sake hango gaskiyar dukkanin kalaman data furta mata domin ba tun yau ta fahimci irin zazzafar makauniyar soyayyar da Yaya Hameedah kema Yaya Zayd ɗin ba.Gani tayi Hameedah ta jinjina kanta tana kai hannu ta share hawayen da suka kasa tsaya mata,kuma ga tsananin mamakin Amal kalaman da suka fito daga bakin Yaya Hameedah bana tsanar mijinta bane kalamai ne na roƙo da magiya akan ta cigaba da rufe wannan sirrin data sani.Cikin rauni da sanyin murya ta riƙo hannun Amal ta damƙe a cikin nata tana cigaba da faɗin,"Amal ina so ki rife sirrin mijina kada ki taɓa bari Iyayenmu suji irin ta'asar da yake aikatawa,idan kikai mini hakan tabbas ko bayan raina zan cigaba da yin alfahari dake,idan har banyi tsawancin rayuwa ba ina fata ki riƙe mini Abdallah kada ki taɓa bari yayi maraicin rashina,nasan kin tsani Yaya Zayd amma ina so a kullum kika ji tsanarsa ki tuna cewa ƴar Uwarki Hameedah tana sonsa,da soyayyarsa aka halicci zuciyata kuma da sonsa za a zare numfashina,Amal Zayd na da wani ɓangare na kyawawan halayensa dani kaɗai nasani,hakan yasa soyayyarsa ta zame mini SARTSE A ZUCI mai wuyar cirewa." Yaya Hameedah ta ƙarisa furta kalaman hawayenta na cigaba da zuba suna ɗiga a saman hannun Amal Taheer dake jin tasirin kalaman da Yaya Hameedah ta furta suna ratsa kwanyarta da zama daram a cikin kanta.Ta ɗaga manyan idanunta ta sauke a saman fuskar Yaya Hameedah tana mata albishir da cewa ko bata roƙeta ba babu wanda zai ji wannan sirrin daga bakinta,don haka ta kwantar da hankalinta kuma za ta tayata da addu'a akan Allah ya shiryesa tunda tana sonshi.Daga ƙarshe ta roƙi Yaya Hameedah akan kada ta sake ambato mata kalmar mutuwa domin zuciyarta ta girgiza da jin hakan,tace da ita koda ranta Abdallah ɗanta ne kuma za ta kula dashi.A lokacin wani irin murmushi mai sanyi taga Yaya Hameedah tayi kafin ta sake damƙe hannunta a cikin na Amal tana cigaba da sanar da ita dukkanin abinda idanu da kunnuwarta suka taɓa gani ko jiye mata akan alaƙar Yaya Zayd ɗin da wasu matan,domin ba za ta iya gane cewa da mace ɗaya kaɗai yake wannan harkar ba.Amal ta dinga kwantar mata da hankali tare da bata shawarar yadda za ta cigaba da kula dashi da yin yaƙi da matan banzan dake neman hana mata nutsuwa a cikin gidan aurenta,daga ƙarshe Amal ta share mata hawayenta tare da bata shawarar kada tace masa komi kota nemi jin wani abu daga bakinsa ta cigaba kawai da tarairayarsa da sauke haƙƙinsa dake kanta.Sukai ma juna saida safe bayan Hameedah ta miƙe domin komawa room ɗinta sakamakon kukan Abdallah da suka jiyo,Hameedah na fita daga ɗakin Amal ta tallabe kanta tana jin tausayin Yaya Hameedah mai girma na sake mamaye zuciyarta.Bata taɓa tunanin girman soyayyar da Yaya Hameedah kewa Yaya Zayd ɗin yakai hakan ba sai yau,don haka tana ji a cikin zuciyarta cewa dole ta sassauta tsanarsa da take ji a cikin zuciyarta kada watarana Yaya Hameedah ta fara ganin aibun rashin ƙaunar da takewa mijinta kuma Yayansu gaba ɗaya da basu da tamkarsa tunda ko babu aure tsakaninsa da Yaya Hameedah tasirin jini mai ƙarfi ya riga ya ratsa a tsakaninsu.Ta jima bacci bai ɗauketa a wannan daren ba saida time ɗin data saba tashi sallar dare yayi,don haka direct toilet ta nufa ta ɗaura alwala ta fito ta fara jera nafilfilinta.Kuma koda taje sujadarta ta ƙarshe ta zuba kirari da yabo tare da fara roƙon a amsa buƙatu da addu'o'inta sai ta samu kanta da roƙawa Yaya Zayd ɗin shiriya,ta kuma roƙawa Yaya Hameedah ƙarfin zuciya da haƙuri akan dukkanin halin ƙuncin da zuciyarta za ta cigaba da shiga ciki domin matuƙar ba a shiryar dashi ya daina bibiyan mata ba tabbas Yayarta ba za ta daina shiga cikin ƙuncin zuciya ba.Sai ƙarfe huɗu ta samu ta kwanta kuma hakan ya janyo mata makara tashi sallar asuba,ƙarfe shida saura ta farka tayi gaggawar ɗauro alwala tazo ta bada farali tayi zaman yin azkar kafin ta koma bacci.Shi kuma a ɓangaren Zayd Abdallah kwana yayi yana tunanin da wasu kalamai zai iya kare kansa a wajen Hameedah? Har garin Allah ya waye zuciyarsa ta kasa samun nutsuwa game da yadda Hameedah ta kamashi yana aikata haramci alhali ita ta kawo kanta wajensa ne domin ta faranta masa.Tausayinta ya dinga rarike zuciyarsa,ƙarfe 9:30am yayi wanka ya kintsa kansa cikin ƙananun kaya ya fice zuwa ɓangaren Hameedah domin duba lafiyarsu ita da baby Abdallah.Kuma yana sanya kansa cikin falon da Amal ya fara cin karo ta kammala shirya dining tana shirin barin wajen,kallo ɗaya sukaiwa juna suka ɗauke kawunansu bayan Amal ta jefa masa wannan kallon daya tsana.Muryarta a cinkushe ta gaidashi tare da nuna masa dining ɗin da hannu alamun abincin breakfast ɗinsa ne ta gama shiryawa,kuma daga hakan ta wucesa ta nufi room ɗinta domin zuwa tayi wanka.Zayd ya kasa motsawa daga inda yayi tsaye yana kallonta har saida ta ɓacewa ganinsa,ya taka a nutse ya nufi bedroom ɗin Hameedah yana shirin shiga Anty Yaganah ta buɗe ƙofar ta fito.Suka gaisa ta bashi hanya ya shige ita kuma ta ƙarisa ficewa hannunta riƙe da kayan abincin da Yaya Hameedah ta gama yin breakfast,yana sanya kansa a cikin ɗakin fitinannen ƙamshin daya kama komi na cikinsa ya shiga karaɗe hancinsa idanunsa suka sauka akan Hameedah data sha wanka ta haɗe cikin wani voile lace mai azabar kyau.Tayi masa kyau ba kaɗan ba jiki da fuskarta duka wani irin glowing suke na zallar hutu da gyaran da fatarta ke amsa,ya ɗauke idanunsa daga kanta yana sake raina kansa a gabanta domin ji yayi duk nadama ta gama dabaibaye shi.........✍🏻