Free chapter · Read without an account
Page 5
by Pending amarya · IMAM ZAID
***
IMAM ZAID 🔬🥼
Pending Amarya ce🎭
JAJIRTATTU WRITERS ASSO………………✍️
The Odogwu Writer ✍️
Chapter1: THE BEGINNING 🙌🏻
An Empty barrel makes the loudest noise 🙌🏻🎭
IMAM ZAID 🔬🥼🧪
Paid book ne.
At a low fee za ku samu 500 naira kacal.
***😢
Opay Farida Aliyu Ibrahim
shaidar biya via what’s app🙌🏻
***
If you have Allah, you have everything🥰🙌🏻🙏🏻
Pending Amarya 005🥰
Not edited 😩
Bangaren su Dadah kuwa ko Sakinat ta samu ciki sai ya bi ta makwarara, abin duk ba a cewa komai.
Kuma har yau ko da wasa Jalal bai sanar da su cikin dake jikin Fattumah ba, kuma suma basu damu su ji inda take ba.
Tun safiyar ranar ta tashi da dauki Wanda ba ta san dalilin sa ba, ko da yayar tata da matar yayansu suka tambayeta, sai ta nuna musu babu komai kawai canjin yanayi ne ya sameta.
Tun safiyar ranar suka yi waya da Jamal ya sanar da ita yaje ya samu Uncle dinsu Qanin mahaifinsu Wanda suke kiransa da uncle Raqib, kuma ya tabbatar masa zasu je su tambaya masa ita, zai aika danginsu na can Zanzibar da suje su tambaya ma Jamal Sabila, kuma Sam uncle din bai sanar ma Dadah halin da ake ciki ba.
Haka ta ci gaba da walwalarta har yamma ya yi can gida suka Kira Yaya Shattimah suka sanar masa.
Zaune suke a falo suna cin abinci, ban da karar spoon babu abin da yake tashi a area din.
Yaya Shattimah ne ya yi Breaking silence din da fadin “ Auta kema kin isa aure kenan da za ki aika kanin mijin yayar ki can wajen su Appah a tambaya musu aurenki.?” Shiru ta yi ba ta ce komai ba sai ma jujjuya spoon din hannunta da take yi.
Kallon ta kawai Fattumah ta yi sannan ta dauke kai ta ci gaba da cin abincin ta.
Ko da suka shiga daki kallonta Fattumah ta yi tare da fadin “ Sabila mai sa ba ki fadamin ba?.” Ta yi maganar tare da jin tausayin kanwar tata dan ta tabbatar ba lallai bane ba a yarda a can gida duba da yadda Dadah ke gasa ta.
landline din dakin su ne ya dauki kara hakan ya sanya ta saurin yin direction din hade da pick call din tun da line din Jamal ne.
Kara wayar ta yi a kunne hade da yin sallama, murya a sanyaye ya ce “Mu yi hakuri da junan mu hakan nan Allah ya zaba mana Sabila.” Ya yi maganar a sanyaye.
“What do you mean Jamal.?” Ta fada trying not to cry.
“ kin san Uncle Raqib shi ne mahaifin Shema?.”
“ Yeah, na sani.”
“And kin san Shema ita ce wadda Dadah suka zaba min, then da muka hadu dake na ce musu na fasa aurenta?.”
“ Talk mana, ka fadi komai a lokaci daya na san halin da zuciyata take ciki Jamal.” Ta fada idanunta na zubda kwalla.
Ban da kallo babu abin da Fattumah ke bin ta da shi.
Har ta gama wayar ta yi ruf da ciki babu abin da Fattumah ta fada mata, sai da ta tsagaita kukan sannan ta kalli Sabila tare da fadin “Da za ki daina wannan kukan naki dan ba auransa zan bari kiyi ba, in ban da rashin hankali Kina ganin kalar halin da nake fuskanta a wajen mahaifiyyarsu amma kina son shigowa cikin gidan da babu komai sai zallar bakin ciki da ɓacin rai Wanda ban san ranar dainawarsa ba, kuma still Sabila Kina son kiyi joining journey din dake cike da duhu da fargaba?.”
“Toh Aunty ba kaddarar kowa da ban ba?, kika sani shigowa ta ya zame miki sassauci daga wajen mahaifiyyar ta su.”
“Toh ai shikenan, duk abin da ya biyo baya ni Kar ki saki ko da wasa ki kira ni, tun da ke Idan an fada miki ba ji kike ba.”
“Aunty fa ke da bakin ki kike cewa kaddarar kowa da ban, toh shi Jamal din miye aibun sa?.” Ta karashe maganar tare da mika ma Fattumah ragowar ruwan da ta sha dazu ta ajiye.
“ Ko na fada miki ba ji za ki yi ba , Allah ya tabbatar da alheri.”
“Amin Aunty, ko ke fa?.”
Yammacin ranar☺️
Karfe shida na yamma a kofar gidan Yaya Shattimah ya musu da shi da yayansa, Jikinsu sanye yake da shadda na alfarma dinkin dake tafe da zamanin sa.
A kofar gate din gidan suka yi parking sannan suka iso cikin main compound din gidan.
Entrance din suka nufa tare da knocking a hankali, within 2 minutes dan gidan Aunty Sharifa Samir (matar Yaya Shattimah sunan ta Sharifa) ya zo ya bude musu door din.
Sai da ya gaida su sannan ya wuce dakinsu Timmy ya sanar da ita su Uncle Jalal na parlour.
Wani dogon hijab kawai Fattumah ta ja tare da kallon Sabila dake kwance ta na baccin yamma fuskarta duk hawaye.
Kauda kanta kawai ta yi gefe tare da karasa sanya hijab dinta sannan ta wuce cikin falon da duk suna zaune cikin kayan su na alfarma.
Sai da ta gaisa da Jamal sannan ta gaisa da Jalal Wanda tun fitowarta yake kallonta.
Wani kalar kyau ya ga ta kara yi masa, Saurin dauke kanta ta yi tare da nufar kitchen dake dining area.
fridge ta bude tare da dauko musu Eva water da lemon 7up na kwalba, tare da daura shi a faranti ta nufo inda suke zaune da shi.
Da kyar da sidin goshi suka sha ruwan da lemun sannan suka ajiye mata kayan marmarin da suka siyo mata a hanya.
Da Jamal din ma bai ga Sabila ba bai tambayi yayarta kuma ta na ina ba har suka gaisa da Aunty Sharifa dake ta tsokanar Jamal da angon gobe.
Sai da safe suka mata ita da Aunty Sharifa sannan suka fice daga cikin gidan.
“Ina Sabilar?.” Aunty Sharifa ta tambayi Fattumah.
“Bacci take Aunty, shiyasa ban tasheta ba.
“Kin ji wai bikinta sati mai zuwa aka sanya?.” In ji cewar Aunty Sharifa.
“Sati mai zuwa kuma Aunty?, ni fa sam bana son auren nan nata da Jamal, kema dai kin san abin da nake fuskanta a wajen Mamansu amma Sabila taki ganewa.”
Fattumah ta fada ranta a dan bace.
“Ki taya ta da Addua kawai, kema lokacin naki ai Muktar a ka so baki kika ce ke Jalal kike so.”
“Amma ay Aunty wannan maganar ya riga da ya wuce tun da kusan shekaru 10 ake magana a yanzu.
“Haka ita ma natan zai zo ya wuce, kuma Appah ya ce ranar da zaa kai ta dakinta kema za ki koma gidan mijinki.”
“Gidan mijina kuma Aunty?.”
“Kwarai kuwa Timmy, jibi za a kawo lefen nata, sai ki san yadda za ki fuskanci dangin mijin naki.”
“Allah ya kai mu Aunty, ki bama Samir ya kawo min madarar shanun nan na dazu dan Allah Aunty.”
“Ay tuni na baiwa Sabila ta afke shi, sai dai na kira yayanku ya taho da wani madarar shanun sai na miki hadi na musamman.”
“Toh na gode Aunty sai da safe.”
After 2 days.
A yau aka kawo lefen Sabila akwatuna 4 sai kit karami da aka kawo mai dauke da Qurani da carbi.
Tun da safe da suka yi waya da Jamal ba su kara waya ba sai da masu kawo kayan Amaryar suka tafi, Sabila ta sha kuka ganin da gaske auren za ta yi sannan ta tsagaita kukan.
bayan ranar kam da kwana hudu ta kasance jumaah, Ana sauko wa daga masallaci aka daura aurenta a bisa sadaki naira dubu biyar cash.
Da yamma kuwa after magrib a ka nufi dakin mijinta da ita, iya danginsu da suke nan kadai ne suka hallari bikin Sabilar, dan su Ammuh da Appah ba su samu jirgi ba.
Ko da aka kawo Sabilar ba ta wani shiga dangi ba direct part dinta ta wuce dan ba ta son kowa ya yi noticing cikin jikinta da har ya fara girma, yake a watan shi na shida.
Sai da aka fara kai Sabila part din Dadah sannan aka kaita bangarenta.
Sabila is just 15 years old young lady, ta na son yayarta sosai duk da ba ta da Wayo sosai aka yi auren Fattumahr dan Fattumah ta girmeta da 7 years.
Bayan an haifeta da kwana biyu mahaifiyyarta ta ta rasu, shi ne rainonta da komai na ta ya koma wajen Mahaifiyyar Fattumah.
Fattumah ita ce auta a dakinsu, Yaya Shattimah shi ne dan fari sai Aunty Maryama dake aure a can Tanzania, sai Said sai Fattumahr da kuma Sabila da ake karawa a matsayin auta.
Dadah da sauran dangin sun amsheta da hannu bibbiyu kamar yadda a ka yiwa yayarta a zuwansu na farko, an ci an sha sannan kowa ya watse.
Sai da Fattumah ta yi sati daya curr sannan Dadah da mutanen dangi suka lura da cikin jikinta, sun sha mamaki mara misaltuwa, barimma Sakinat da abin ya sanya ta kuka kamar ranta zai fita.
Jalal kam tamkar ya maida ta cikinsa dan nuna kulawa, abin da bai yi ma Sakinar ba lokacin da take da cikin yan biyunta.
Hakan ba karamin harzuka ta ya kara yi ba, su Shema da sauran cousins dinta kuwa idan ban da zuga ta babu abin da suke yi idan sun zo bangarenta.
Yau ma kamar kullum bayan ya gama hada mata breakfast dinta, fita ya yi aikinsa tare da jawo mata kofar ya kulle mata.
Bai zarce ko ina ba sai bangaren mahaifiyyarsa, zaune ya ganta a kan kujerar falonta Sabila na mata tsifa, sai da suka gama gaisawa da Sabilar sannan ta silale ta koma part din yayarta.
A zaune ta sameta a kan gado ta na breakfast, cikinta ya fito sosai Wanda da alama ya kai almost wata 7 da wanzuwarsa.
“Aunty.” Sabila ta kirata a sanyaye.
Dago kanta ta yi tare da sauke idanunta a kan her beloved kanwarta sannan ta ce “Naam.”
“Aunty wai Dadah ke tambayar idan akwai abin da za ki ci a lunch afara hada miki tun yanzu.” Ta yi maganar tare da amsar Mug din da yayarta ke bata.
“ Ba na jin yunwa.” Ta bama Sabila amsa a takaice.
“ Kai Aunty, wallahi son ki take yanzu sosai.”
“Son jikarta ko jikanta dai ba ni ba, tashi ki tafi bangarenki bana son surutun banza.” Ta fada tare da gyara kwanciyyarta.
Haka rayuwa ta ci gaba Dadah na iya bakin kokarinta a wajen Fattumah, ya yin da Ita ma Sabila ke dauke da ciki mai kimanin watanni biyu.
Gadan gadan Fattumah ta shiga cikin watan hahihuwarta, kullum cikin fita excercise suke ita da Jalal dake kara macewa a kanta.
Sakinat kam ko ga maciji ta daina yi da Dadah, ganin yadda take kula da Fattumah day in day out, hakan ba Karamin bata mata rai yake ba, dan ko tambayarta Dadah ta yi sai ta yaba mata magana.
Tun safiyar ranar ta ta tashi da ciwon baya da kuma ciwon jiki, Sabila na ta fama da kanta saboda laulayi da ya tiso ta a gaba.
Zuwa Yammancin ranar nakuda ta yi mata babban kamu, dan yau ma tun safe ake ta sadakan zagayowar rasuwar mahaifinsu Jalal din duk ba su samu zama ba.
Tun ta na iya cijewa har ta fara yarfa hannu.
Sakinat ce ta fara lura da rashin sakewarta, kallonta ta yi ta dauke kai tare da cigaba da abin da suke yi ita dasu Shema.
Saurin ajiye butar da take mika ma wasu almajirai na sadakar ranar ta yi saurin yi hade da dafe mararta da bayanta dake yi mata wani kalar zafi.
Jin wani ruwa na bin kafarta ne ya sanyata saurin kwala wani kalar ihu Wanda hakan ya janyo attention din family din zuwa wajenta.
Shigowarsu kenan cikin gidan shi da Jamal da kuma Dadah sun dawo daga gidan marayun marigayi.
Ganin dandazon mutanen dake wajen, da alamun an kewaye wani Abu a wajen.
Saurin faka motar suka yi tare da saukowa suka nufi wajen da mutanen suke, ganin sun iso wajen ne ya sanya mutanen gidan buɗa musu wajen domin su ga abin da yake faruwa.
Saurin daukanta Jalal ya yi dan tun lokacin da ta fadi Sabila ke durkushe a wajen ta na ta malala kuka.
Saurin janyeta Jamal ya yi sannan suka kinkimi Fattumahr suka yi hospital da ita.
Dadah kam ta kasa zaune ta kasa tsaye daga karshe dai ta bi bayan su zuwa hospital din ita da Sabila da har sannan taƙi ta daina kuka.
12Am Aminu Kano Teaching hospital…..,.
Sai mun hadu on Monday in shaa Allah 🥰🙌🏻
Like and share fi sabilillahi ❤️🥰🙏🏻
> IMAM ZAID ONLY ON PENDING AMARYA’S BOOK CORNER EXTRAORDINARY EVERYDAY 🥰
~///Soft Noorah///~
> PENDING AMARYA😘
> FARIDATOOL NOOR🥰🙌🏻
> THE ODOGWU WRITER ✍️