Free chapter 路 Read without an account

Chapter 3&4

by @Mrs Alkali 路 SO DA HAWAYE!





馃挮SO DA HAWAYE 馃挮 

鉁嶏笍Mrs Alkali 

*Page 3-4*


WASHE GARI......


Gari ya waye a gidanmu cikin yanayi na daban. Ko'ina kaji muryoyin dangi da abokan arziki, kamshin abinci ya gauraye ko'ina. Yau ce ranar da kanwata Fatima zata tare a gidan mijinta bayan an d'aura musu aure. A matsayina na babbar yayarta, na tashi da wani irin farin ciki da kuma nauyin dake kaina na ganin komai ya tafi daidai.


Na fito cikin wani had'edden leshi da aka yi masa dinki na kece raini. Adon ya karbe ni, kowa ya ganni sai ya yaba, Dan ni kaina nasan kayan sun amshi jiki na. Na shiga dakin Umman mu domin duba yadda shirye-shirye suke, tafiya sai dai abin da na tarar ne ya so ya taba min zuciya, amma na dake na shanye.


A can gefe guda na dakin, na iske wasu daga cikin dangin mahaifinmu zaune da su da matar babanmu, Baba Ladi. Da shigata dakin, sai suka rage murya amma duddah haka naji abun da suke fa蓷i:

"Kunga dai yadda take wani rangwada, tana nuna ita ce babba, sai wani yau茩i take kamar wata sarauniyar kyawu," daya daga cikinsu ce ta fada tana watsa min hararan gefen ido. "Amma me amfanin hakan? Ga kanwarta nan yau zata tafi dakin mijin ta, ita kuma tana nan tana bin wani yaro wai shi Nazir. Ta rasa wanda zata bi sai wanda ya girme mata da kadan tare sukayi wasan kasa fa?"

Baba Ladi ta tare zancen da wani karkataccen murmushi, tana kara rura wutar:

"Ai dama abin ai abin kunya ne. Mace har ta kai munzalin aure amma ta tsaya tana wani wasan yara. In banda rashin kunya, ta yaya zata bari kanwarta ta riga ta fita daga gidan? Amma ai laifin uwar ne da take biye mata, dama chan ita ke goyon bayan shiriritar ta."


Duk abun da suke fad'a a kunne na, a Hankali Na kalli Umman mu, na ga yadda fiskan ta tayi da alama ita ma ta ji duk abin da suke fada. Zuciyata tace tafara tafasa, na so na tanka musu, amma sai na ga Umma ta girgiza min kai tana murmushin nan nata na manya. Ta cigaba da abin da take yi kamar ma bata ji komai ba.

Nima sai na saki nawa murmushin, na gyara daurin dankwalina. Na nuna musu cewa kalaman nasu ba zasu taba taba farin cikina ba. Na san waye Nazir a gareni, kuma na san lokacin Allah shi ne mafi kyau a garemu. Maimakon in yi fad'a dasu kamar yanda nayi niya , sai kawai na wuce gun Fatima domin taya ta shiri, yayin da su kuma suka cigaba da tauna bakin maganarsu.



Bayan na gama jure duk wani tsegumi na su Baba Ladi da ya'n uwan baban mu, hankalina duka na mayar da shi ga 茩anwata Fatima. Na shiga daki na iske ta zaune, kanta a 茩asa, da alama akoi wani abu dake damun ranta.


A matsayina na babbar yaya, ni na tsaya aka yi mata kwalliya ta 茩arshe. Na gyara mata mayafinta, na fesa mata turaruka masu da蓷in 茩amshi wa蓷anda na siyo mata su musamman sabi da auren. Koda na kalli fuskarta ta cikin madubi, sai na ga idanunta sun cika da 茩walla. Na dafa kafa蓷arta, na yi 茩o茩arin danne nawa kukan, na ce:

"Fatima, share hawayenki. Yau ce ranar farin cikinki. Allah zai albarkaci aurenki, kuma kullum muna nan tare da ke."


Muna cikin haka ne ,Can sai muka ji Karan motoci da kida dake tashi daga waje. Gidan ya cika da hayaniya sosai: "Amarya ta fito! Motoci sun zo!" Wannan sautin ya sa gaban mu faduwa nida Fatima. 拼an uwa da abokan arziki suka fara shiga motoci, ana ta sowa da murna.


Lokacin da aka fito da Fatima don kai ta wajen mahaifinmu da Umma don neman albarka, nan ne kuka ya 蓳alle. Fatima ta 茩an茩ame Umma tana kuka mai ban tausayi, tana cewa: "Umma, ba zan iya barinku ba. Umma, zan yi kewarku."

Umma ma kukan take yi, amma tana shafa kanta tana yi mata addu'a. Ni kaina, da na ga yadda Fatima take kuka, sai da hawaye suka zubo min. Na sani cewa daga yau, gidanmu ba zai sake kasancewa yadda yake ba tare da ita ba.


Haka Muka sanya ta a motar amarya, ni kuma na zauna kusa da ita dan kuwa tana ri茩e da hannu na a nata. Duk hanyar da muke bi, Fatima kanta yana kan kafa蓷ata, tana ta sauke ajiyar zuciya. Muna isowa kofar gidanta dake cikin unguwar GRA dake cikin garin GOMBE anguwa ne mai natsuwa, kasancewar sa unguwar masu hanu da shuni, haka muka shigar da ita, muka d'an sake gyara mata zaman dakin nata, duddah komai normal bakaramin kok'ari Baba 陌brahim yayi ba dan shine yayiwa Fatima kayan 蓷akin dan yace wa Baban mu shikam Fatima Diyar sa ce ya bar masa Abdul-Majeed, ba 茩aramin kyawu gidan fatima yayi ba kowa sai santin gidan yakeyi.

Kafin mu fito, daga cikin gidan na sake rungumarta. Cike da tausayin ta Na ganin yadda gidan yake sabon waje a gare ta. Na yi mata nasiha ta 茩arshe, a matsayina na yayar ta, sannan muka yi bankwana cikin kuka. Na fito daga gidan ina jin wani irin nauyi a zuciyata, amma kuma ina alfahari da cewa na sauke nauyin da yake kaina na babban yaya ,haka Motocin suka sake kwaso mu su ka dawo damu gida.


Bayan na dawo gida daga rakiyar Fatima, gidan ya yi min shiru, duk da har yanzu akwai ragowar mutane. Kukan da Fatima ta yi ya bar ni cikin wani yanayi na sanyin jiki da kewar ta, duk da cewa har yanzu ina cikin gidanmu. Na zauna a bakin gadona ina kallon hotunanta a wayata, sai kawai na ji kiran Nazir ya shigo waya ta domin kuwa nasan ringing tone d'in sa na Musamman ne.


Zuciyata ce ta buga da 茩arfi lokacin da na ga sunansa ya baiyana yana yawo a saman screen d'in wayata. A Hankali Na 蓷aga wayar, muryata a 蓷an dashe saboda kukan da na yi.

Cikin sanyin murya Nazir yace : "Haba masoyiyata, har yanzu kukan ne? Na san an kai amarya, amma ai murna ya kamata mu yi, ko?"

Ajiyar Zuciya na sauke kafin nace: "Nazir, kukan nata ne ya taba ni. Gidan ya yi min shiru sosai, jin nake kamar an cire wani bangare na jikina."

Ya yi shiru na 蓷an da茩i茩a, sannan ya sauke numfashi cikin murya mai cike da tausayi yace:

"Ina jin zafinki a zuciyata. Amma ki sani, kukan nan naki yana nuna irin girman zuciyarki ne da yadda kike son kowa naki. Fatima ta tafi gidanta cikin daraja, ke kuma kika nuna mata matsayinki na babbar yaya. Ki share hawayenki, don ba na son jin muryarki a haka."


Na 蓷anyi murmushi ka蓷an, na ce, "Na gode Nazir. Maganganunka ko yaushe magani ne a gare ni. Amma ka san abin da wasu danginmu suke fa蓷a kuwa?"

Sai ya yi dariya mai d'an sanyi, sannan ya ce:

"Bar su su fa蓷a, duk wanda yake magana a bayanki ai a bayanki yake. Ni ne nake ganin abin da ba su gani ba a tattare dake. Ke ce sarauniyar zuciyata, kuma ba da da蓷ewa ba, mu ma zamu taka wannan matsayin na su Fatima. Ki daina damun kanki da maganar mutane, kowa da tasa kaddarar."


Wadannan kalaman nasa sun sa na ji wani irin sanyi a zuciyata. Duk wani zafi da nake ji na maganganun su Baba Ladi, da duk wani kukan rabuwa da Fatima, sai na ji sun tafi. Muka cigaba da hira, yana sa ni dariya, yana gaya min yadda ya yi kewata duk da cewa yau ma mun hadu.

Muna gama wayar, na tashi na wanke fuskata, na ji wani sabon 茩arfin hali ya shige ni. Na sani muddin ina da Allah, kuma ina da Nazir, duk wata maganar mutane ba komai ba ce a gareni.



*** *** ****

Bayan tafiyar ya'n kawo Amarya, Fatima ta tsinci kanta a cikin wani yanayi na kewar gida da kuma ya'n uwan ta , Musamman ma Anty Huda, ga bedroom din yamata girma, sosai babban daki mai cike da sanyin A.C da 茩amshin turaren "Oud" mai tsada, irin wanda ake samu a masallatan Saudiyya. Tana zaune a gefen gado, kanta a 茩asa, tana saurarun bugun zuciyarta.

Can ta ji an turo 茩ofa cikin natsuwa. Abdul-Majeed ne ya shigo. Siffarsa ta nuna tsantsar nutsuwa da kwarjini:

 Dogon mutum ne, kyakkyawa mai kyakkyawar fuska da saje (beard) wanda aka gyara shi tsaf, irin na matasan da suka sha karatun addini a can birnin Saudiyya, farine na gasken gaske, ga wani gashin kansa bak'i mai sheki yana kwance luf-luf a saman kayinsa.

Yana sanye da wata farar jallabiya ta alfarma, wadda ta nuna za蓳in masu fa蓷a aji, dan kallo d'aya zaka mata kasan cewa ba kananun kud'ad'e aka kashe a wajen sayanta ba, sannan ya 蓷aura babban riga (Bisht) a kansa, wanda ya 茩ara fito da kamalarsa ta "Ustaz" mai mutunci da kamala.


A hankali yake Takunsa , har ya 茩araso kusa da ita. Ya zauna a gefen gadon, ya yi gyaran murya mai sanyi sannan ya ce, "Assalamu Alaikum, Ya Shariykata Hayati (Abokiyar rayuwata)."

Ganin tana kuka, kuma bata amsa masa bane yasa sai ya d'an matso kusa da ita, ya sanya hannunsa ya rungumeta (First Halal Hug). Rungumar ba ta sha'awa ce kawai ba, runguma ce ta kariya da nuna cewa yau ya zama gatanta. Ya sanya yatsunsa ya yaye mayafinta, a hankali ya kalli fuskarta da take cike da hawaye da kunya, ya ce:

"Fatima, fushin da kike yi ko kukan nan, duk suna da lada a wurin Allah domin nuna biyayya ga iyaye ne. Amma ina so ki sani, na da蓷e ina addu'ar samun mace ta gari, kuma Allah ya amsa mini ta hanyar za蓳in iyayenmu. Na yi na'am da ke tun ranar farko da aka ambata mini sunanki. Daga yau, ni ne Mahaifin ki, ni ne yayanki, kuma ni ne mijinki."


Kamar yadda ya tashi a kan ilimin addini, Abdul-Majeed bai bar komai ya wuce shi ba:

Haka Ya kama hannun Fatima cikin tausasawa, ya jagoranceta suka yi alwala. Suka gabatar da sallar nafila raka'a biyu. Bayan sun idar, ya sanya tafin hannunsa a saman goshinta, ya karanta addu'ar nan ta Sunnah: "Allahumma inni as鈥檃luka khayraha..." yana ro茩on Allah ya albarkaci aurensu.


Bayan sun gama, ya kawo madara da dabino da abinci. Ya fara gutsura mata dabino yana ba ta a baki. Fatima sai noke-noke take yi, tana jan yatsunta saboda tsananin kunya, tana jin yadda kwarjininsa yake ratsa ta. Shi kuma sai ya ri茩a yi mata murmushi yana cewa, "Wannan ma ibada ce Fatima, ki sani kowane loma da zan ba ki, muna da lada a ciki."


Haka yayi ta ciyar da ita sai da ya tabbatar da ta koshi, Bayan sun kammala cin abinci da addu'o'i, Abdul-Majeed ya cire babban rigarsa, ya rage sauran kayan jikinsa zuwa masu saukin kwanciya, dan shi mutum ne da baison takura Musamman idon ya zo kwanciya shiyasa most of time yafi ganewa da ya kwanta haka babu Riga a jikin sa, yau d'in ma sabi da ganin cewa ita d'in bakuwa ce a gare shi, shiyasa ya sanya rigan bacci marar nauyi, yayin da Fatima take zaune a gefen gadon, kanta a 茩asa, tana wasa da zoben hannunta saboda tsananin kunya.


Abdul-Majeed ya matso kusa da ita, ya zauna ta yadda gwiwowinsu ke gauraya da na juna. Ya kalli kyakkyawar fuskarta da har yanzu take cike da jin kunya, ya ce cikin muryarsa mai sanyi:

"Fatima, kin san Manzon Allah (SAW) ya ce: 'Mafi alherin cikinku shi ne wanda yake mafi alheri ga iyalinsa'. Burina shi ne in zama wannan mutumin a gare ki. Kada ki ji tsorona, kuma kada ki ji nauyina. Daga yau, ni ne suturarki, ke ma suturata ce kamar yadda Allah ya bayyana a cikin Alkur'ani."

Wannan kalaman nasa ya sa Fatima ta 蓷aga kai ta kalle shi a karon farko. Ta ga tsantsar gaskiya da 茩auna a idanunsa, wanda hakan ya sa ta 蓷anyi murmushi mai cike da jin kunya.


Abdul-Majeed bai tsaya nan ba, ya sanya hannunsa ya kamo nata, yana shafa tafin hannunta a hankali, yana gaya mata hadisan da suke 茩ara dan茩on soyayya a tsakanin ma'aurata:

A hankali Ya matso da fuskarsa kusa da tata, yadda take iya jin dumin sa numfashinsa mai d'auke da 茩amshin almiski. Kafin Ya ce mata, " Kallon da miji yake yi wa matarsa cikin 茩auna, Allah yana duban su duka da idon rahama."

Cikin nitsuwa Ya fara cire mata wasu daga cikin adon dake jikinta (irin su awarwaro da dankwali) cikin takatsantsan, kamar yadda ake kula da abu mai daraja. Duk abin da yake yi, yana yi ne cikin natsuwa, yana nuna mata cewa ita "茦auwarah" ce (wato rarrauniyar halitta mai daraja) kamar yadda Annabi (SAW) ya kira mata.


Lokacin da suka kwanta, ya juyo da ita gare shi, ya sanya kanta a kan kafa蓷arsa. Ya ri茩a rera mata wasu baituka na Larabci game da soyayya da kyawun mace ta gari. Fatima ta ji wani irin shau茩i yana ratsa ta, duk wani tsoro ya gushe, aka maye gurbinsa da wata irin nutsuwa da ba ta ta蓳a ji ba.

Ya sumbaci goshinta, sannan ya ra蓷a mata a kunne:

"Fatima, ke ce kyautar da Allah ya ba ni daga 茩asar Saudiyya har zuwa nan Nigeria. Zan kula da ke, zan so ki, kuma zan taya ki neman Aljanna."

A daren nan, Fatima ta fahimci cewa soyayyar "Ustaz" ta fi kowace soyayya da蓷i, domin tana ginuwa ne a kan tsoron Allah da girmama mace, kuma ta gane cewa ba miji kawai ta aura ba, ta aura bawan Allah wanda zai kaita zuwa ga Aljanna.



      Washe garin ranar, Hasken safiya ya fara haskaka ta cikin labulen dakin, yana bayyana yanayin dakin da har yanzu yake cike da natsuwar daren jiya. Fatima tana takure a gefen gado, kanta a binne cikin filo, sautin kuka maras sauti yana fita daga gare ta sakamakon radadin da take ji.

A hankali, Ustaz Abdulmajeed ya matso kusa da ita. 陌danunsa cike suke da wani irin kauna da tausayi wanda sai miji na kwarai ne yake yiwa matarsa irin sa.


Cike da nitsuwa Ya dora hannunsa akan kanta, yana shafa gashinta a hankali, sannan ya rada mata a kunnen ta:

"Kiyi shiru Humairatun-Nafsy (Haske kuma Farincikin Raina). Kukan nan naki yana sosa min zuciya. Ina so ki sani, daren jiya kin zama silar kammala rabin addini na. Allah ya miki albarka, ya saka miki da gidan Aljannah kamar yadda kika min biyayya kika zama tawa har abada."

"Daga yau, ba matata kawai kike ba, Fatima. Kin zama 'Amanar Allah' a hannuna. Na karbe ki a cikin zuciyata a matsayin sarauniyar da babu wadda zata taba zama kamarta. Ki daina kukan nan, domin kowane hawayen ki guda daya, nauyi yake min a cikin kirji na."


Ganin yadda ta gaza ko motsawa ne saboda nauyin da jikin ta yayi mata, yasa Ustaz Abdulmajeed bai tsaya wata-wata ba. Ya mike cikin natsuwa ya nufi bathroom, ya hada ruwa mai dumi wanda kamshinsa ya cika dakin.

Ya dawo gare ta, ya sanya hannunsa na dama ta karkashin wuyanta, na hagun kuma ta karkashin gwiwowinta, ya dauketa cak kamar jaririya. Fatima ta kura masa idanu, tana mamakin yadda mutumin da ta sani mai cike da kwarjini da ilimi ya koma mai tarairayarta haka daga daren jiya zuwa yau. Ta kasa magana, amma ta lafe a kirjinsa, tana shakar kamshin jikinsa wanda ya gauraye da na turaren dakin.

Yana takawa a hankali zuwa bathroom, d'in yana ci gaba da yi mata addu'o'in samun natsuwa da daukaka.

Bayan ya shiga da ita, cikin bathroom din Ustaz Abdulmajeed ya zaunar da ita a hankali a cikin bahon wanka (bathtub) , Ruwan dumin da ya hada yana fitar da tururi mai dadin 茩amshi.

Cikin nitsuwa ya fara taba jikinta ya na zuba mata ruwan dumin domin yana son ya gasa mata inda take jin zafin, nan take ya lura da yadda jikinta ya yi ja, wasu wuraren ma sun yi kalar shudi saboda rauni. A lokacin, ne Ustaz ya dakata na dakika kalilan, numfashinsa ya tsaya. Idanunsa suka cika da wani irin tausayi da nadama; bai taba tunanin cewa ya ji mata ciwo har haka ba.

 Bai ce uffan ba, amma sai ya rage karfin yanda yake danna jikin nata a cikin ruwan, ya koma shafa wurin kamar yana lallashin raunin. Ya sumbaci goshinta, sannan ya ci gaba da gasa mata jikin cikin natsuwa.

Fatima kam , duk da radadin da take ji, sai ta rintse idanun ta tana ciza lafiyayyen lebenta na kasa. Ba ta so ta nuna masa gazawarta ko ta sa shi jin nauyi a ransa, amma duk sanda ruwan dumin ya ratsa wurin da yake mata ciwo, sai ta kankame hannunsa. Shi kuma Ustaz, duk sanda ta yi hakan, sai ya kara matseta a jikinsa, yana hura mata iska mai dumi a kunnenta don ta ji sanyi.


Bayan ya gama yi mata wankan tsaf, ya nannade ta cikin babban tawul (bathrobe) mai laushi, ya daukota ya dawo da ita dakin da aka riga aka gyara.

Bai barta ta sa kaya da kanta ba. Ya zaunar da ita ya fara shafa mata mayukan sa masu dad'in 茩amshi.

Yayin da yake shafa mata mai, bai kalli, wani wuri daban ba sai cikin idanunta. Hannunsa yana yawo a jikinta cikin wani irin salo na girmamawa da yake nuna mallaka. Kowane taba jikinta da yake yi, yana yi ne cikin sanyi da nuna cewa "Ke tawa ce, kuma zan kare ki".

Bayan ya gama shafa mata mai sai Ya dauko mata wata lallausan riga ta alfarma (loose silk gown) ya sanya mata. Yayin da yake daure igiyar rigar, sai ya d'an tsaya na dan lokaci, ya dora kansa a kafadarta, yana shakar kamshinta, sannan ya rufe idanunsa鈥攚anda hakan ya nuna cewa duk duniya babu inda yake so ya kasance sai a kusa da ita.



Bayan ya gama shiryata tsaf, ya zauna a gefenta, ya sanya hannayensa biyu ya tallabo fuskarta, ya hada goshinsa da nata. Kamshin turaren jikinsa da na dumin jikinta suka gauraye a waje guda, ya rage muryarsa kasa-kasa yadda ita kadai zata iya jinsa, sannan ya rada mata:

"Humairatun-Nafsy... kiyi hakuri da radadin da na sanya ki. Amma ina so ki sani, daren jiya ba wai kawai na biya bukatar rayuwata ba ne, na mika dukkan ragamar rayuwata ne a hannunki. Ke ce mace ta farko da ta sa na ji cewa dukkan ilimin da na koya, ba zai taba nuna min yadda zan so ki ba, sai dai zuciyata ta koya min da kanta. Allah Ya sanya ki a matsayin rahamata a duniya da Aljannah."

"Daga yau, ciwonki nawa ne, farin cikinki nawa ne. Ba zan taba barin kukan bakin ciki ya ziyarci idanunki ba, muddin ina numfashi. Na gode da kika amince kika zama tawa."

Jin wadannan kalaman, wadanda suka fita daga zuciyar Ustaz Abdulmajeed cikin tsantsar gaskiya da kauna, sai Fatima ta ji wani irin sanyi yana bin kashin bayanta. Shau茩i da kunya suka ziyarci zuciyarta a lokaci guda.

Ba tare da ta shirya ba, sai ta ji idanunta sun fara cika da kwalla, amma ba na zafi ba, na tsantsar dadi. Cike da kunya, ta kasa kallon kwayar idanunsa, kawai sai ta sa hannayenta ta rufe fuskarta, ta tura kanta cikin faffadan kirjinsa ta lafe, tana shakar dumin jikinsa.

Ustaz Abdulmajeed ya sakar mata wani tattausan murmushi, ya sanya hannunsa ya rungumeta sosai a kirjinsa, yana jin yadda zuciyarta take bugawa da sauri-sauri. A wannan lokacin, Fatima ta tabbatar da cewa, ko da akwai radadi a jikin ta to tabbas, zuciyarta tana cikin murna da farin ciki mafi girma.

Ustaz Abdulmajeed ya mika hannu zai dauki wayarsa dake kan bedside drawer, fuskarsa cike da d'an damuwa yace. "Bari na kira family Dr. Ya turo Nurse , tazo ta duba mini jikinki, bana son wannan zafin ya dade," ya fada cikin muryar dake nuna lallai ba wasa yake ba.

Nan take Fatima ta zaro ido, fuskarta ta kara yin ja saboda tsananin zafin da takeji a 茦asan ta ga kuma kunya da ta mamaye ta. Ta yi saurin dafa hannunsa, muryarta tana rawa-rawa ta ce, "A'a, don Allah Ustaz... kar ka kira kowa. Kunya nake ji." Ganin ya tsaya yana kallonta ne ya sa ta kara cewa, "Idan ma lallai sai an duba ni, to Anty Huda nake so. Ita ma Nurse ce, kuma na fi sakewa da ita..." Ta fadi hakan ne yayin da idanunta suka cika da kwallar kewar Anty Huda, domin a yanzu take jin yadda rashin uwa ko yar'uwa yake da daci a lokacin da kake bukatar lallashin su.

Ustaz Abdulmajeed ya yi murmushi mai cike da fahimta, ya juyo gare ta ya ce, "Na'am, tunda ita kike so, hakan ma ya yi. Duk abinda zai sa ki ji natsuwa, shi ne nawa nima." Ya mika mata wayar tasa, "Kira ta yanzu, nima ina son lafiyarki."


Yayin da Fatima ta karbi wayar, tasa numbers d'in Anty Huda, nan take ta kirata, ringing d'aya ta dauka, ta fara magana da Anty Huda cikin shau茩i da kukan kewa, Ustaz Abdulmajeed ya koma gefe guda ya zuba mata ido, ganin yanda take magana da y芒r uwar tata.


A cikin zuciyarsa, ji yake kamar ya taba gajimare saboda dadi. Yana kallon yadda Fatima take murmushi tana goge hawaye, sai ya tsinci kansa da cewa "Alhamdulillah".


 A wannan lokacin, fuskokin iyayensa suka fado masa a rai. Ya ji wani irin kaunar iyayen nasa ta mamaye shi, domin su ne suka zaba masa ita, su ne suka zama silar wannan ni'imar. "Ya Ubangiji, Ka biya iyayena da gidan Aljannah, yadda suka sanya ni a wannan farin cikin," ya fada a cikin zuciyarsa yayin da yake kallon "Amanar" da suka bashi.



鉁嶏笍Mrs Al茩ali.

***.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.