Free chapter · Read without an account
Page 6
by Pending amarya · IMAM ZAID
***
IMAM ZAID 🔬🥼
Pending Amarya ce🎭
JAJIRTATTU WRITERS ASSO………………✍️
The Odogwu Writer ✍️
Chapter2: THE HEIR HAS ARRIVED 🙌🏻
An Empty barrel makes the loudest noise 🙌🏻🎭
IMAM ZAID 🔬🥼🧪
Paid book ne.
At a low fee za ku samu 500 naira kacal.
***😢
Opay Farida Aliyu Ibrahim
shaidar biya via what’s app🙌🏻
***
Pending Amarya 006
Not edited
The Lord that lifted me up will never let me down 😢🥰🙏🏻
Saurin daukanta Jalal ya yi dan tun lokacin da ta fadi Sabila ke durkushe a wajen ta na ta malala kuka.
Saurin janyeta Jamal ya yi sannan suka kinkimi Fattumahr suka yi hospital da ita.
Dadah kam ta kasa zaune ta kasa tsaye daga karshe dai ta bi bayan su zuwa hospital din ita da Sabila da har sannan taƙi ta daina kuka.
12Am Aminu Kano Teaching hospital.
Sai karfe sha biyu na dare sannan Fattumah ta haife cikin dake jikinta, inda Allah ma ya ceceta ba dry labour ta yi ba.
Bayan an gyara ita da Babyn aka kawo ma Jalal shi, Wanda a lokaci daya ya masa duk abin da musulumci ta tanadar sannan ya ma sa huduba da suna ZAID amma za a dinga ce masa IMAM, ya ci sunan mahaifinsu sannan babban limami Wanda ke jan kowacce sallah a kowani hali ya tsinci kansa a ciki.
A wancan lokacin a zamanin Mahaifinsu ya yi tashe sosai, mahaifinsa haifaffen dan Tanzania a yayin da mahaifiyyarsa ta kasance yar kasar Oman 🇴🇲.
Mahaifinsa ya shahara wajen muslumtar da mutane iri iri, a wannan dalilin ne Allah ya sanya ya hadu da kakar su Jamal har suka dawo Tanzania suka haifi da suka sanya masa ZAID, shi da kannensa biyu mata wayanda suma suna cikin family house na yanzun, wannan kenan.
Kukan da jaririn keyi ne ya sanya Dadah dake zaune cikin corridor tashi a firgice, daga dan baccin da ya dauketa.
Ganin jariri a hannun Jalal shi ya kara firgitata tare da tashi tsaye daga zaunen da take ta na kallon kyakkyawan jaririn.
“Marhaban Ya ZAIDU nah mijina abin alfahari na.” kara rushewa ya yi da kuka, sannan ta amshe shi ta na rarrashinsa.
Sai da ta yi kwanaki hudu a hospital din sannan aka sallamesu suka dawo gida inda yan uwa da abokan arziki suka yita tururuwa zuwa ganin jaririn.
Kan kace kwabo har an fara shirye shiryen taron suna.
“Ke Sabila ina kika je ne da tun dazu iyayenku ke ta jiranki?.” Dadah ta fada a dan tsawace.
Kallon Jamal da suka shigo tare ta yi sannan ta yi yake ta ce “A’a ban san sun zo bane Dadah.” Ta fada a sanyaye dan wani kalar Shan kamshi Dadar ta tsiro mata da shi kwanan nan.
“Toh maza kije ki gaida su ki dawo ki min kitso gashi na duk ya tuje.” Dadah ta fada tare da zama a kan kujerar palon.
Tabe bakinsa Jamal ya yi tare da zama a kan kujerar dake kusa da ita.
“Ba kaje wajen yayan naka bane yau?.” Ta fada tare da basar da kallon da yake mata dan ta san halin Jamal kila haushin tsawan da ta yiwa Sabila yake ji.
“Naje bangarensa ki min fada?, kice na take sharudan ki?.” Ya fada tare da kara fuskewa.
“Kaji da shi, Nifa Matar nan taka zarginta nake yanzu.”
“Wani kalar zargi?, Nifa Maama ba za ki sanya min ido a cikin lamarin aure na kamar yadda kika saka ma Yaya ba, wannan Sabila take ita kuma waccan Fatimah take, wallahi da a US kike da tuni an dade da kamaki.” Ya fada tare da fara shirin barin falon.
“Toh Jamal tun da kai rayuwar turai ka yi sai ka sa polisawan Nigeria su kama ni, Ronald Reagan shugaban Amurka.” Ta fada tare da tashi ita ma ta yi hanyan hanyan dakinta.
Tabe bakinsa ya kara yi sannan ya yi hanyar part din Yayan nasa.
Zaune ya tarar dasu suna hira gabadaya, Aunty Maryam na rike da ZAID ta na shafa masa Vaseline, ita kuma Sabila na zaune ta na aikin duba kayan fitar sunan da aka kawo dazun.
Karasa shigowa ya yi ya kara gaida AMMUH, sannan ya wuce ya nufi side din da yafi tunanin yayansa yake.
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya har ranar suna ya yi, sunan da ba’a taba yin kalarsa a familyn Swahili ba, sunan da a tarihi ba a taba kashe naira kalar sa ba.
Shema dasu Shamsiyya da Habashiyya Sakinat kam group suka hada nakin fita taron sunan, dan kam har aka watse kafarsu bai taka duk wani waje da aka kiyadda shi saboda taron ba.
An yi suna mai rai da lafiya anci an sha, mutane da dama sun so creating problems Allah bai basu saa ba.
Facalolinta da na Dadah da kannen mahaifinsu Jalal kam kamar bakin ciki ya kashe su, dan Sam suma ko kadan ba sa son Fattumah, tun zuwanta cikin family din.
“Iklima Kina ganin dai komai na familyn nan gaba yake karayi, dan ni dai kam dole na koma wajen mutumin nan, ban taba tunanin yaron nan zai kai har suna da bayan suna ba tare da ya koma inda ya fito ba.” Inji cewar wadda ke zaune cikin shigarta na wani kamla hannayenta da wuyanta da kunnenta sanye cikin gold.
Wadda aka Kira da Iklima ce ta tabe bakinta tare da fadin “ Nifa Yaya Abu janye kaina zan yi daga lamarin Y’ayan Zaidu, dan Kina ji Kina gani indai malaman nan ne tass za su cinye mana kudadenmu na dan abinda shegen ya bar mana daga gadon da iyayenmu suka bar mana.” Iklima ta fada tare da mikewa zaune daga kwancen da take.
“ZAIDU?, ZAIDU, ba zai ga annabi bafa Iklima, kalar fake soyayyar da ya nuna mana, dan sa ma ya auri Habashiyya yak’i ya yi fatali da tayin da na masa yaje ya auri shegiyyar bahaushiyyar nan.”
“Ai kin ga Rakibu dake gasurkumin munafuki ne, a ta biyun yar sa Sakinat ya basa bai yi shawara da mu da muke y’an uwan mahaifinsa na jini ba.”
“kuma yake kokarin bayar da Shema ga Jamal, ki kiyayi dan Adam Iklima.” Yaya Abu ta fada with soo much seriousness.
****
“Haba Rukayya , mai kuke yi haka ne?, kuna fad’a da juna ku kun bar yara a tsakani, mai sa ba kwa min adalci ne?.” Babban mutumin da ya shigo cikin madaidaicin gidan bulon da babu filesta, sai a dakuna uku dake jere ya fada tare da janye wani dan karamin yaro dake tsakanin wajen da suke damben.
Kallo daya za ka musu ka gane kishiyoyi ne.
Ganin ba su da niyar sakin junan nasu ne ya sanya shi dage labulen da ya lullube turakar nasu tare da dauko wata dorina ya nufi inda suke ta dambe kamar Allah ya aiko su.
Wadda a ka Kira da Rukayya ce a dazun ta yi saurin sakin abokiyar zaman nata sannan ta shige turakar ta tare da banko kofar karfen dake jikin bulo din dakinta.
Ita ma dayar dauke danta ta yi tare da nufar Malam dake tsaye ta masa sannu da zuwa sannan ta wuce dakinta.
Shi ma biyo bayanta ya yi tare da zama a kan kasan sumintin da aka shinfida masa abin sallah.
“Yanzu ke ma Suwaiba biye mata za kiyi kullum kuna ihu makota na jin ku?, idan ita ta zama babban banza sai ki biye mata ku zama?.” Malam ya fadi hakan tare da kara hasken fitilar kwan aci bal bal dake gabansa.
“Yi hakuri ranka shi dade, ba zaa kara ba da yardar Allah.” Suwaiba ta fadi hakan cikin zazzakar miryarta tare da tura masa kwanon farau farau a gabansa.
“Allah ya min arziki Suwaiba ku huta da kunna itace.”
“Amin Malam.” Ta fada a takaice.
“Alhaji dan k’wara ma tun jiya ya min magana, Akan wai idan zan sai da gona ta na siyar masa, amma ni wallahi tsoron siyar masa nake ji Suwaiba?.”
“Tsoro kuma Malam?, kudin da ya ce zai siyi gonar babu yawa ne?.”
“Eh toh Suwaiba, da yawa sosai wallahi, dan ni na zaci ko zai min tayin wulakanci ya ce min Naira biyar ko zuwa naira hamsin, amma naira dari ya ce min zai siya kin ga kuwa har ya ishe ni na shiga kasuwar kwari ko kurmi na fara siye da siyarwar nan, dan har zuciyata bana jin dadin ganinku a wahala ga bala’in ku da yake bani tsoro.”Malam ya yi maganar a sanyaye.
“Ba zamu kara ba Malam, amma a ganina ka siyar, zan hada maka da saitin daham dina ka siyar ka hada da nawa filin ma san a kalla za a samu kusan dari biyar, ka ga zai isheka wasu ababen.” Ta fada tare da shigewa kuryar daki, ta na mai bar masa runfar domin dauko set din Daham dinta.
*****
Har ZAID ya yi three months kullum cikin nuna masa kauna iyayensa suke, barimma Fattumah da take jin sa har cikin ranta.
ZAID ya kasance yaro mara son hayaniyya, kusan kullum a wajen Dadah yake yini, small Mum dinsa ta gidan kam kullum ya na manne a bayanta kamar magnet.
Bangaren Jalal kam tun haihuwar ZAID kamar hanyoyin saan sa ne suka kara budewa, dan kullum cikin samun karbuwa ake a komai nasu na companies har ma da factories.
“Aunty wai yaushe zamu je gidan Yaya Shattimah?, kuma kin ga Aunty Sharifa ba tada lafiya.” Sabila ta fada a sanyaye.
“Aunty information, sai ki shirya mu tafi.” Ta fada tare da zare bakin ZAID da ga abincin da take basa.
Sai wajen yamma sannan suka dawo daga gidan Yaya Shattimah.
Da daddare ma gabadaya mutanen gidan na zaune suna dinner babu babba babu yaro gabadaya an hadu Ana cin abinci.
Daya daga cikin facalolin Dadah ce ta budi baki tare da fadin “Amina yaushe ne Jalal ya miki maganar bude companyn da su Sagiru za su rike a hannunsu? Dan kin ga next month zasu dawo daga karatun.” Matar ta fada tare da kallon sauran facalolinta.
“Ga ku gashi sai ya fada muku yaushe zai yi hakan.” Dadah ta fada tare da tashi ta nufi dakinta.
“Na tsani mutum mai pride da yawa dubi yadda ta wani bar mutane suna cikin mata magana.” Dayar facalarta ta fadi hakan tare da mikewa ta bar wajen.
Haka rayuwa ta ci gaba da dadi babu dadi har ZAID ya yi shekara daya, tafiya yake cikin rashin kwarewa a cikin falon mahaifiyyar tasa ya na tafe ya na kiran sunan Pa….pa, Pa……aaa.
Ya na cikin gwarancinsa aka bude kofar dakin da sauri ya juya ya kalli kofar a firgice sannan ya yi saurin juyawa da jikinsa gabadaya ya na murmushi ganin mahaifinsa ne hade da ihu.
Karasowa Jalal ya yi tare da daukansa, sannan ya yi hanyar bedroom dinta, fitowarta kenan daga bathroom jikinta daure da towel, bayan wuyanta na dauke da wani karamin kumfa.
“Cutie wanka kike?.”
“Yeah, amma gashi na fito.”
“Toh ai kuwa kin taimaki Jalal da d’ansa, how about going out d’in?.”
“Ina zamu je hope dai ba gidan zoo ba ko?.” Ta fada a sanyaye.
“A’a gidan makama zamu je Hajjaju, ki yi sauri ki shirya, dauko min kayan IMAM na sanya masa, su Jamal are done.” Ya fada tare da amsar kayan da take mika masa.
“Sabila ba zata zauna ba kuwa Jalal?.”
“Why?.”
“Toh kana gani dai duk wani ciki idan ta yi zubewa yake kuma sai ta fice da shi ta na langwabe langwabe?.”
“A’a dan Allah karki hanata, Ki bar ta kila idan ta ga mutane ta sake.”
Ba ta sake masa magana ba ta gama shiryawa, suka wuce compound da Jamal da Sabila ke tsaye a jikin motar Jalal kirar _Range Rover Classic_ Wanda ko a wancan time din kudinsa ya kai almost 500k, dan wannan motar a wancan time din is a very luxurious car is not for y’ay’an Malam Shehu.(😂🙌🏻Yawwa).
🥰🙌🏻
Like and share fi sabilillahi ❤️🥰🙏🏻
> IMAM ZAID ONLY ON PENDING AMARYA’S BOOK CORNER EXTRAORDINARY EVERYDAY 🥰
~///Soft Noorah///~
> PENDING AMARYA😘
> FARIDATOOL NOOR🥰🙌🏻
> THE ODOGWU WRITER ✍️
*** account number
Farida Aliyu Ibrahim
Opay
IMAM ZAID PAID BOOK NE🙌🏻
Ku yi hkr data na ne ya kare kuma naje gidan kitso😌💕🙏🏻
Wslm sis gashi nan