Free chapter · Read without an account
SARTSE A ZUCI.....! Chapter 24
*SARTSE A ZUCI...!đź’”* Arewabook@ayshadansabo
Paid book ***
©️ Ayshat Ɗansabo Lemu ✍🏻
Last Free Pages
Chapter 24
Tunda Amal ta doshi ƙofar shiga falon Daddy taji gabanta na tsananta bugu,ta doka sallama cikin siririyar muryarta da tun rasuwar Ya Hameedah ya sake yin sanyi domin gabaki ɗaya karsashinta da komi nata ya ragu.Daga ciki ta jiyo muryar Daddy na bata izinin shiga,kuma koda ta shiga shi kaɗai ta samu a zaune daga ƙasan carpet yana siffing ruwan black tea da Anty Mamah ta gama haɗa masa ta fice,don haka Amal na shiga saita isa kusa da Daddy takai zaune zuwa ƙasa tana gaidashi.Ya ɗaga kansa ya zuba mata idanu yana sake jin tausayinta dana ɗan dake goye a bayanta na sake karya zuciyarsa,"Amal zauna da kyau mana,magana za mu yi mai muhimmanci don haka ina buƙatar nutsuwarki a tare dani." Daddy ya furta hakan idanunsa akan Amal wacce ta gyara zamanta sosai tana ɗaga hijab ɗinta domin buɗe fuskar Abdallah da bacci ya ɗaukesa,a nutse ta furta,"To Daddy ina saurarenka." Daddy ya aje cup ɗin black tea ɗinsa da saura kaɗan ya shanye ya sake gyara zamansa yana fuskantarta sosai,cikin nutsuwa ya kirayi sunanta,"Amal." Sai ta ɗaga kanta ta dubesa tana sake jin ƙirjinta na bugawa da ƙarfin gaske.Bai kuma jira ta amsa ba ya ɗaura da faɗin,"Amal a yau nazo miki da wani al'amari mai girman gaske,kuma ina fata ba za ki watsa mini ƙasa a idanuna ba wajen bijiremini domin nasan daga ke har ƴar Uwarki baku taɓa saɓa mini ba,Yayanki Zayd yazo mini da buƙatar ki maye masa gurbin ƴar Uwarki."Ya ɗan dakata yana kallon yadda Amal tayi saurin ɗago fuskarta a firgice ta dubesa idanunta na warowa waje,alamun tsoro da ɗinbin firgici ya haska a cikin idanunta.Daddy yayi tamkar bai fahimci tsoro da razanin da kalamansa suka jefata a ciki ba ya cigaba da faɗin,"Kece zaɓin da mukai masa domin ki maye masa gurbin ƴar Uwarki daya rasa,mun yanke shawarar cewa nan da sati uku masu zuwa za mu ɗaura miki aure da ɗan Uwanki kuma Yayanki Zayd domin kece kaɗai za mu wanke mu bashi zukatanmu basu yi kukan cewa Abdallah zai iya tasowa ya fuskanci wani abu wai shi maraicin rashin Uwa ba,don haka ina so kiyi haƙuri ki sadaukar da soyayyar da kike wa shi wancan Aman ɗin domin Zayd ya fishi buƙatarki a yanzu,ina fata za ki je kiyi nazari ki kuma duba ɗanki Abdallah domin abin alfahari ne ya taso ya rayu a tare daku ke da Mahaifinsa a matsayin Iyayensa,ki tashi kije kiyi addu'a kinji ko?" Daddy ya kai ƙarshen kalamansa yana jiyo sautin kukan da Amal ke rerawa ahankali,kuma bata iya furta koda kalma guda ba ta miƙe tana jin yadda hajijiya ke neman ɗibarta ya zubar dasu ita da Abadallah dake goye a bayanta.Mutuwar ƴar Uwarta ya dawo mata sabo fil a cikin zuciyarta,taku ɗaya ana biyu tayi taji ƙafafunta suna lanƙwashewa.Hakan yasa tayi saurin dafe kujerar dake kusa da ita tana sake ɓallewa da kuka mai ban tausayi,Daddy dake kallonta yana jin tausayinta na kekketa zuciyarsa sai yayi saurin ɗaga waya ya kira Anty Mamah.Kuma ba a ɗauki lokaci ba sai gata ta shigo ya bata umurnin ta kama Amal ta kaita ɗakinta,daga haka ya miƙe ya nufi bedroom ɗinsa yana jiyo sautin kukan da Amal ta sake rushewa dashi tana sanar da Anty Mamah cewa ta shiga uku.Haka Anty Mamah ta kama hannunta suka fito daga ɓangaren Daddy zuwa nata,ta raka Amal har zuwa ɗakin baccinta tana rarrashinta da dukkanin kalaman da za su tausasa zuciyarta amma Amal kuka kawai take tana nanata kalmar ta shiga uku inama mutuwa ita ta ɗauka ba Yaya Hameedah ba.Tausayinta ya kassara zuciyar Anty Mamah ta fice daga ɗakin domin zuwa tayi magana da Daddy,ta sanar dashi cewa hukuncin da suke neman yankewa tamkar ƙwaruwa ne a wajen Amal ɗin tunda zuciyarta na da wanda take so suka kuma yi alƙawarin yin aure da juna.Kuma lokacin data samu Daddy da wannan maganar ne ya tabbatar mata da cewa babu wanda ya isa ya tada wannan alƙawarin daya ɗaukarwa Zayd Abdallah na cewa ya bashi Amal domin ta maye masa gurbin Hameedah,don haka gara taje ta tayasu rarrashin Amal ɗin ta kuma nuna mata muhimmancin yima Iyaye biyayya.A can ɓangaren Amal kuwa tun tana kuka da sambatu har hawayenta suka ƙafe,kukan ya tsaya cak sai wani irin ajiyar zuciya da take saukewa.Daren ranar gabaki ɗaya bata iya rintsawa ba domin duk yadda ta motsa kalaman Daddy ne ke hautsina kwanyarta tana ji inama ba ta kawo iyanzu ba,domin koda wasa bata taɓa hasaso cewa Daddy zai iya tunkaranta da makamancin irin kalaman daya furta mata a yau ba.Babu abinda take lissafawa a cikin kanta irin yadda za ta rayu ba tare da Aman Kurfi a cikin duniyarta ba,domin bata taɓa hasaso cewa za ta iya kallon wani ɗa namiji ba sai gashi ana mata zancen ta auri Namijin da take jin tsanarsa kullum ƙaruwa ma yake a cikin zuciyarta.A tunaninta idan ta koma ta roƙi Daddy ta kuma sanar dashi cewa Aman Kurfi nanan a cikin rayuwarta zai ji tausayinta ya kuma janye kalamansa,hakan yasa tana tashi da safe ta gama hidimar Abdallah ta je ta samu Daddy domin gayar dashi ta kuma roƙeshi akan yayi mata rai ya janye kalamansa na cewa ya baiwa Yaya Zayd ita domin ta maye masa gurbin Yaya Hameedah.Kuma cikin rashin sa a tana isa ta tadda Yaya Zayd ɗin har ma da Mummy duka a ɓangaren Daddyn alamun sun shigo gaidashi ne ko kuma shi ya nemesu domin yin magana dasu oho,duk da hakan bayan ta gayar dashi sai ta isa ta kama ƙafafunsa tana masa magiya akan ya ji tausayinta ya canza buƙatar da yake dashi a gareta amma ba za ta iya kallon Yaya Zayd a matsayin mijin aurenta alhali ya rayu da Yayarta da suka fito ciki guda ba.Yaya Zayd a lokacin yana zaune yana sauraren yadda Amal ke kuka tana ma Daddy magiya amma gabaki ɗaya yaƙi saurarenta,daga ƙarshema sai ya sake jaddada mata cewa matuƙar shi ya haifeta kuma ya isa da ita to shikam ya gama magana babu abinda zai sauya.Da tsananin firgici ta juya wajen Mummy ta riƙe ƙafafunta tana roƙonta ta sanar da Daddy cewa Aman Kurfi shine zaɓinta,amma sai ta ji Mummy ta buɗe bakinta tana rarrashinta da cewa Yayanta yafi Aman buƙatarta don haka matuƙar albarkarsu da amincewarsu take nema to tayi haƙuri ta amshi Yaya Zayd a matsayin zaɓin da ƙaddara tayi mata domin ta maye gurbin ƴar Uwarta.Mummy ta sake furta kalaman da suka sanya Amal fasa ihu har tana birgima a tsakar falon Daddy tsabar firgici da shiga tashin hankalin da kalaman Mummy suka jefata a ciki,domin cewa tayi,"Amal idan har ba za ki amince da buƙatar mu ba to ina baki tabbacin cewa ba za ki cigaba da rayuwa da Abadallah ba,domin Ubansa bazai amince ɗansa ya rayu a gidan waninsa ba don haka saiki fara shirin rasa Abdallah bayan kin rasa Hameedah."Waɗannan kalaman ne kuma sukai masifar ɗaga hankalinta domin furta kalmar rabuwa tsakaninta da Yaron da bata san ma ta yadda za ta iya kwatanta yadda take jinsa a dukkanin jikinta ba,tamkar ana gaya mata kalmar rabuwa da numfashinta ne baki ɗaya.Yaya Zayd ɗin ne kuma ya fara rarrashinta a lokacin da take ihu da birgimar cewa babu mai rabata da Abdallah domin kuwa a gabansu Yaya Hameedah ta sake tabbatar musu da cewa ta bata shi,jin muryarsa kaɗai a tsakar kanta ya cigaba da ninka tsanarsa a cikin zuciyarta har bata san time ɗin data fice a guje daga ɓangaren Daddy ta koma ɓangaren Anty Mamah tana ji tamkar za ta yi hauka ba.Da ƙyar Anty Mamah ta rarrasheta ta tsaida kukan da take,ta kuma kama Abdallah da dama wajen Anty Maman ta barshi ta rungumeshi tana jin wani sabon sonsa da tashin hankalin yadda za ta rayu babu shi na sake hargitsa duniyarta baki ɗaya.Tana tsaka da wannan tashin hankalin ne kuma sukai waya da Aman ya sanar da ita cewa a washegari zai diro ƙasar,kuma wannan albishir ɗin da yayi mata shiya sake jefa rayuwarta cikin tashin hankalin da bata san yadda za ta misaltashi ba.Don haka suna aje wayar mutum na farko data kira ta sanar dashi halin da take ciki shine Yaya Sulaiman,a lokacin yana Lagos bashi a Kaduna.Tana kuka ta sanar dashi yadda sukai da Daddy da Momy tana roƙon ya taimaketa ya fahimtar dasu cewa ba za ta taɓa iya rayuwa da Yaya Zayd a matsayin miji ba.Kuma daga yanayin yadda taji yana amsa maganarta ta gane cewa shima lamarin ya dokesa,domin sam basu riga sun tattauna batun da Daddy ko Mummy ba.Tausayin Amal sosai ya kamashi domin shi shaida ne akan irin soyayyar da suke wa juna ita da Aman Kurfi,kuma shima har cikin zuciyarsa ya yaba da Aman da dukkanin nagartarsa kuma bazai taɓa jin daɗi ace sun rabu da juna ba.Sai dai baiyi gaggawar nuna mata rauninsa ba domin baisan me ƙaddara ta tanadar ma rayuwar Amal ɗin a gaba ba,don haka ya rarrasheta akan cewa tayi haƙuri za su tattauna batun idan ya dawo sati guda kawai zaiyi ya dawo daga Lagos ɗin.Kuma bayan sun aje wayar sai ta kasa haƙuri ta kira Jameelah ta fashe mata da kuka tana sanar da ita irin hukuncin da Daddy ke shirin yankewa rayuwarsu ita da masoyinta Aman Kurfi,itama Jameelah ba ƙaramin shock ta shiga ba domin koda wasa bata taɓa hasaso cewa za a ce Amal ɗin ta maye gurbin ƴar Uwarta ba duba da cewa ansan akwai alaƙar soyayya tsakaninta da Aman Kurfi kuma Daddy da kansa ya bashi izinin zuwa zance.Amma itama kamar yadda Yaya Sulaiman ya rarrashi Amal haka itama ta rarrasheta akan cewa tayi haƙuri,idan ta fito lactures a washegarin ranar za ta wuto gidan domin suyi magana.Kuma kamar yadda tayi mata alƙawari a washegarin ranar ta iso gidan Daddy misalin biyu da rabi na rana,kuma koda suka ƙule a cikin ɗaki taga yadda Amal ta fice daga cikin hayyacinta sai tausayinta ya sake kama Jameelah.Ta shiga yi mata nasiha tana bata baki akan tayi haƙuri ta sanya a addu'a a gaba,domin shi kaɗai ne magani tunda basu san abinda ƙaddara ta tanadar ba.Suka haɗu ita da Anty Mamah suka dinga kwantar da hankalin Amal tare da bata shawarwarin da suke ganin za su amfaneta,sai ƙarfe biyar Jameelah tabar gidan kuma ko awa ɗaya da tafiya bata yi ba Aman ya kira Amal ya sanar da ita cewa gashi a Abuja ya sauka zai kamo hanyar Zaria komin dare.Kuma a washegarin ranar da safe ya kirata vedio call domin tun jiya da yake kiranta taƙi bari suyi vedio call sabida bata so yaga halin da take ciki bare ya tuhumeta,babu yadda ta iya haka ta ɗaga vedio call ɗin lokacin tana rungume da Abdallah a jikinta.Suna haɗa idanu da juna ta cikin wayar taji zuciyarta ta sake karyewa sai kawai ta sakin masa kukan data kasa riƙewa,hankalinsa yayi masifar tashi ya fara tuhumarta akan ta sanar dashi abinda ke faruwa amma Amal ta kasa magana sai kuka.Koda ya sanar da ita cewa zaizo gidan zuwa yamma sai ta dakatar dashi cikin rishin kuka,tana roƙonsa kada yazo za ta sanar dashi dukkanin abinda ke faruwa ta chat.Kuma suna aje wayar ta shiga account ɗinsa ta zayyane masa dukkanin abinda ke faruwa,time ɗin data ga ya karanta saƙon amma baiyi reply ba sai hankalinta ya sake tashi.Ta kira wayarsa taji a kashe sai hankalinta ya sake riɓanya tashi,a gigice taje ta sanar da Anty Mamah halin da take ciki domin ita kaɗai take iya tunkara da matsalarta sabida yadda Mummy tayi masifar ɗauke mata kai tare da tabbatar mata da cewa tana bayan Daddy itama Zayd shine zaɓinta ba Aman Kurfi ba.Sosai Anty Mamah tausayin Amal ke ɗawainiya da ita,ta rasa ta yadda za ta iya shawo kan Daddy ya fahimci cewa raba wannan soyayyar dake tsakanin Amal da Aman ba abu ne mai sauƙi ba amma Daddy ya kasa bata dama bare har ya fahimceta.Burinsa kawai yaga cewa sun cinma burinsu wajen mallakawa Zayd Amal domin ta maye masa gurbin matarsa daya rasa,ba tare da cewa sunyi la'akari da halin da ita Amal ɗin za ta iya shiga ciki ba tunda tun farko ba jituwa suke da juna ba.Tun daga ranar Aman bai sake neman Amal ba sabida yana can cikin matsanancin tashin hankalin da bazai misaltu ba,shiyasa ma ya kashe wayarsa domin yana fata time ɗin da zai sake kunnata yaga cewa mafarki yake ba Amal ce ta turo masa saƙon cewa wai za a bada ita ga Yayanta Zayd domin ta maye masa gurbin ƴar Uwarta Hameedah ba.Kuma wannan rashin jin daga garesa shi ya sake dagula dukkanin lissafin Amal Taheer,ta sake fita a cikin hayyacinta tana ji tamkar a ɗauke numfashinta.Ta sake zabgewa ta fita daga cikin nutsuwarta,duk dare bata iya bacci daga kuka sai tunani da yin Sallah tana addu'ar Allah ya kawo mata mafita amma kuma ta kasa ji a cikin zuciyarta cewa za ta iya yin biyayyar amsar mutumin da take jin tsanarsa a cikin zuciyarta.Mutumin da take masa kallon fasiƙi wanda take da tabbacin cewa ƴar Uwarta ta Mutu da baƙin cikin irin fasiƙancin da yake aikatawa,taya za ta rayu dashi alhali tafi kowa sanin sirrinsa da irin ɓarnar da yake aikatawa? Kullum waɗannan tambayoyin ne suke cika kanta har ta ji cewa ko duniya za su taru a kanta zai yi wahala ta iya sadaukar da soyayyar Aman Kurfi ta amshi jininta wanda ko kaɗan bata jinsa a cikin zuciyarta sabida munanan ɗabi'unsa da basu yi mata ba.Kuma kullum tana gayawa kanta cewa suma su Daddyn dake tausayinsa don basu san asalin waye shi bane,da tabbas ba za su yi sha'awar sake wanketa su bashi ita bayan rasa Hameedah ba.Amma ta riga ta yiwa Yaya Hameedah alƙawarin cewa ba za ta taɓa fallasa sirrin mijinta ba ko bayan ranta,matuƙar ba Ubangiji ne da kansa ya bayyana musu asalin waye Yaya Zayd ɗin suka gano irin ɓarnar da yake aikatawa da kansu ba.Kwanaki uku Aman Kurfi ya ɗauka bai nemeta ba,sai safiyar yau ɗin da yake roƙonta akan ta sameshi a gidan Abbah da yake matsayin mallakinsa a yanzu domin suga juna.Kuma babu abinda ke bata tsoro irin yadda a kullum taje gaida Daddy yake sake jaddada mata cewa yana kan bakansa na cewa zuwa Sati uku masu zuwa zai maye wa Yaya Zayd gurbin ƴar Uwarta da ita,bai taɓa nuna jin tausayinta ko ya tuna cewa tana da nata zaɓin ba burinsa kawai ta amshi buƙatarsa ta kuma yi masa biyayya wajen ganin burinsu ya cika shi da Mummy.Kullum Yaya Zayd kaɗai suke tausayi da riritawa,abinda ke sake janyo masa tsana a cikin zuciyarta kuma basu taɓa magana gaba da gaba dashi akan lamarin ba sai yau ɗin daya kirata zuwa ɓangaren swimming pool ya faɗi kalaman da suka sake riɓanya tsanarsa a cikin zuciyarta.Sai kuma gashi Anty Mamah ta sake furta mata kalaman da suka sake tayar da hankalinta na cewa wai Yaya Zayd ɗin da kansa ne ya roƙi alfarmar a bashi aurenta guiwa bibiyu,lamarin da ya sake jefata cikin halin ɗimuwa da shiga tashin hankalin da bazai misaltu ba.Ta kuma haƙiƙance cewa yana da manufa ne na yin hakan,domin a ganinta yafi kowa sanin cewa ita da shi ba za su taɓa zama a inuwar aure har a samu daidaito a tsakaninsu ba domin tun asali zuciyarta bata rayu da ƙaunarsa kamar yadda take ƙaunar ɗan Uwansa Yaya Sulaiman ba.
To masu karatu anan na kawo ƙarshen free page's Na wannan labari,don haka yanzu ne za mu shiga cikin asalin labarin SARTSE A ZUCI......
CIGABAN LABARI