Free chapter · Read without an account

11

by Pending amarya · IMAM ZAID

IMAM ZAID 🔬🥼





Pending Amarya ce🎭




JAJIRTATTU WRITERS ASSO………………✍️



The Odogwu Writer ✍️ 

Chapter4: THE PRESENT IS CALLING…….. 🥹



An Empty barrel makes the loudest noise 🙌🏻🎭



IMAM ZAID 🔬🥼🧪

Paid book ne.
At a low fee za ku samu 500 naira kacal.

***😢

Opay Farida Aliyu Ibrahim 
shaidar biya via what’s app🙌🏻
***



️


Pending Amarya 11
Paid pages 🥰
Not edited 





Cikin baccinta haka nan kurum taji kamar Ana kiran sunanta, a hankali ta bude idanunta tare da maida dan kwalinta da ya sullibe mata ta yi hanyar kofa ta na bin sunan nata, misalin karfe biyun dare ne gidan ya yi shiru, sai kukan tsuntsaye da magunan Imamu dake tashi da karfi, karnukan masu gadin estate suma na nasu ihun, a hankali ta yi ta bin sunan nata har ta bar cikin estate din baki daya da katon cikinta…….✍️

FATUMMAH 😩🫩🥹

_____*****______

Tafiya take da tukeken cikinta, she has nowhere to go, ba ta ma san inda ta nufa ba ita dai kawai zuciyarta da kwakwalwarta na ingizata na ta ci gaba da tafiya.

har yinin ranar ya wuce ba ta daina tafiya ba sannan kuma ba ta tsaya ba.

It was very late at night, when dogs barked helplessly at night, Jin wannan kukan karnukan shi ya firgitata tare da nufar wani dan babban gida da yake farkon street din da ta shigo.


All her life she haven’t suffered to this extent in her whole lifetime, sai a lokacin wani kalar hawaye suka zubo mata, she couldn’t even speak or recall anything about herself.

Yadda garin ya yi shiru hakan ya sanyata gane cewa dare ne ya tsala sosai ba na wasa ba, fashewa ta kuma yi da kuka forcing her brain ya tuna mata abu daya nata buh she couldn’t.


kiran sallahn asuba ne ya tasheta daga baccin da ya kwasheta na wucin gadi, jikinta gabadaya kaikayi yake mata na cizon da sauraye suka yi mata.

Jin an bude gate din da take jingine  ya sanyata saurin tashi a firgice tare da komawa baya, shima kansa Alhajin gidan da ya fito sai da ya firgita ya koma cikin gida sannan ya dake ya yi ta maza ya fito wajen.


Kallonta ya yi ganin ita ma kallonsa take kuma kamar sabuwar Mahaukaciyya ce ya sanya shi saurin barin wajen tare da wucewa masallaci hannunsa cikin na dansa gudun Kar ta fasa musu kai.


Sai wajen 6am na safe sannan ya fito daga masjid din hannunsa rike da Ahmad, ganin ta na zaune a kofar gidan ba ta motsa ba ya sa shi zuwa wajen da take zaunen.

“Baiwar Allah.” Ya fada ba tare da ya kusanci kofar gidan nashi ba, shi dai Ahmad kallonta kawai yake.

Bakinta na nauyi ta dago da kanta a hankali ta na kallon sa tare da fadin “Naam.” 
“Lafiya kike zaune haka?, mai ya faru?.” Ya tambayeta.

“Babu komai hutawa nake.” Ta fada a takaice tare da jinginar  da kanta a bangon gidan.

“Ina za kije?.” Ya kara jefo mata wata tambayar.

“Ni ma ban sani ba.” Ta fada a sanyaye hawaye na fita a idanunta, dan ta san dole da akwai daga inda ta fito Amma ta manta.
“Ya sunanki?.” Ya kara jefanta da wani tambayar.
“Ban san miye sunana ba shima.” Ta fada a sanyaye.
“Toh daga Ina kike?.”
“Nima kawai gani na na yi ina tafiya.” Ta fada masa ta na mai ci gaba da zamanta.

Wucewa ya yi ciki tare da barinta a wajen dan gani yake ko setup aka yi masa.

Hada hada ake a cikin gidan na daura girki da ma wasu gyare gyaren babban falon, Umma da har ta gama dama kunun gyada ta ajiye a dinning ce ta juyo ta kalli Alhaji ganin ya shigo cikin gidan nasa jikinsa duk babu wata walwala.

“Alhaji mai ya faru?, ka shigo babu walwala kamar kullum?.” Ta fada tare da ajiye kular da ta zubo alala a cikinsa tare da dan dafe cikinta.

Furzar da iska ya yi daga bakinsa sannan ya fada mata duk abin da yake faruwa na ganin matar dake zaune a kofar gida da ya yi.

“Amma Alhaji ba ka ganin mu taimaka mata?, akan ta fada hannun wasu azzaluman?, dan wannan duk yadda a kayi asiri ne a kayi mata.” Ta fada idanunta na kawo ruwa dan har ga Allah ta na da mugun Jin tausayin dan Adam a rayuwarta.

“A taimaka mata da mai?, da kudi ko da uwar mai?, ke fa Suwaiba shishigin ki haushi yake bani, ba ki taba ganin mutum ba kawai ki wani ce a taimaka masa?, ni ki bani kumallona ma na shige dakina da yarana Kar suyi mugun gani idan nan za ku kawota.” Mama ta fada tare da mikewa ta na kama hannun yaranta da suka kai kusan 6 yrs old.


Ba ta ko bi ta kan Mama ba ta fice daga cikin gidan, kamar yadda ya fada mata kuwa ta na zaune hannunta na rike da wani dutse ta na ta jifa da shi a cikin fararen duwatsun dake malale a kofar gidan.


Umma ba ta mata magana ba ta mika ma Matar dake zaune hannu, sai da ta dago ta kalleta sannan babu musu ta mika mata hannun.

Kafafunta duk sun farfashe, bakinta duk a bushe kamar dai kishin ruwa take ji, zaunar da ita ta yi a falon gidan tare da dauko mata ruwa mai sanyin gaske ta kafa a baki, sai da ta shanyesa tass sannan ta dago da kanta tare da yi mata murmushi.

Ita ma Umma murmushi ta mayar mata sannan ta zubo mata abinci ta fara ci a haukace.


_____****_____



Ya na tashi da asuba dakin Maminsa ya nufa domin tashin ta, amma wayam ya tarar da bata ciki, kofar toilet ya nufa tare da kwankwasawa a tunaninsa ko ta na ciki, ya kai kusan 5 mins ya na knocking sannan ya bude ya ga wayam ba ta ciki.

Hankalinsa bai kara tashi ba sai da ya ga har 7 babu Maminsa babu dalilinta, a million ya nufi side din Amminsa, ta na zaune ta na duba wasu takardun assignment din Zayn, ganin ya shigo mata a birkice ne ya sanyata ajiye assignment din tare da kallonsa da sauri hade da fadin “Mai ya faru?, wani ya biyoka da gudu ne?.”

Fashewa ya yi da kuka tare da fadin “Ammi I’m searching for Mami since morning, har yanzu ban ganta ba.” Ya karashe maganar tare da matsowa kusa da Amminsa.

“What are you saying Imam?, mai hakan ke nufi?, kuma kaje part din Dadah?.”

“Mami ai ba kullum take zuwa part din Dadah ba Ammi.”

“ Ka kwantar da hankalinka mana Imamun Mami, ya kake ta kuka kamar Mamin yarinya ce?.”

“Tom na yi shiru.”

Haka shi da ita da Zayn suka rankata side din Dadah Amma babu Mami babu dalilinta sai ma bakar magana da suka kwaso daga wajen Dadahr akan Mamin.


Jin wannan labarin ba karamin girgiza family din Swahili da na su Mamin ya yi ba, dan Appahnta ma cewa ya yi bai yarda ba sai sun nemo masa yar sa dan dama tun da can ba sonta suke ba.


Shi Jalal kasa tantacewa wa ma ake nufi ya yi, dan birkita kwakwalwarsa da akayi.


WASA WASA gabadaya rainon Zaid ya koma wajen Amminsa amma still kullum cikin  zuwa side din Maminsa yake ko Allah zai sa ya ganta ko da akarkashin gado ne. (🫩😭 Wanda suka tasa uwa su kadai ne za su ji ciwon da Imam ke ji).😭

Kullum zai zo ya zauna a position din da tafi son zama a falon ya yi ta kuka ko ya dauki picture din ta ya na kalla ya na mata magana.


Haka shekaru suka yi ta wucewa har ya gama secondary school aka nema masa makaranta a can kasar turai, amma still bai gajiya da kallon hoton Maminsa, kullum cikin yawo yake da komai da ya danganci na Maminsa.


Estate dinsu na Hotoro kam tun ya na 200L aka gina musu sabo suka koma can Wanda yafi wannan komai, dan har yan aiki a ka saka musu, kuma komai kafin ayi shi sai an shawarci Sakinat dan ita ke da mulkin gida.


Ya na 300L Zayn ya na 100L, idan sun dawo Hutu ma shi bai cika zama a wancan new estate din ba he  always prefer the old one because of his childhood memories, kuma dakin Maminsa will always be his comfort zone, dan ko lokacin da za a kwashe kayan estate din ayi sadaka da su cewa ya yi a bar masa na side din Maminsa babu yadda aka iya aka bar masa dan ba shiga harkar kowa yake ba a gidan, da kyar da karfin addua sannan ya daina kwanciyya a estate din nasu na da, shi ma sai da Papansa ya kusa marinsa sannan ya yarda ya fara zuwa can sabon estate din nasu tsilli tsilli, amma sai da ya kafa musu sharuda suka yarda.

Bangaren Sakinat kam duk yadda ta so raba Imam da mahaifinsa abun yaci tura, saima kamar kara masa soyayyarsa ake Duk da ya mance mahaifiyyar yaron…..



 After 20 years da batan Fattumah.🥰













Toh sai yadda hali ya yi a gobe kuma 😂🙌🏻🫩




 🥰🙌🏻
Like and share fi sabilillahi ❤️🥰🙏🏻




> IMAM ZAID ONLY ON PENDING AMARYA’S BOOK CORNER EXTRAORDINARY EVERYDAY 🥰


~///Soft Noorah///~
  

> PENDING AMARYA😘 

> FARIDATOOL NOOR🥰🙌🏻

> THE ODOGWU WRITER ✍️ 


Your favorite troublemaker, Noor 😌


Free pages sun kusa karewa 🥹
Sai da kuka dauki alkawarin like da share da comment fa?🥹😭😭😭

Amma babu komai 😢
Komai lokaci ne 🫩😌
Lokaci na nan zuwa da zaku dinga nema na kamar nama 🫩😌 In shaa Allah 😏❤️

Idan an ga type error ku gyara a wajen karatu, dan yau wayata ta dau zafi over🥹😭




# Hidden secret 
#Love
#Truelife story
#Drama
#Imam Zaid 
#Pending Amarya
#paid book 500
#like#comment # share
#Arewapen
Not edited Goodnight bacci nake ji 🥺🤣😭

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol