Free chapter · Read without an account

Chapter 5

by Ummulkhairi Sani Panisau · ADNAN (The Artist)


5

Tafiya suke suna hira har suka isa unguwar da Hussai ke aiki. Babban gida ne wanda ya amsa sunan sa gida tunda suka nufi gidan ta hangame baki tana kallon ikon Allah ba yau ta fara ganin gidaje ba amma wannan kam ya burge ya matuƙa kuma ya sa ta zama yar ƙauyen ƙarfi da yaji. Ta kama hannun Hussai tace "Ke wannan wane irin gida ne kamar na yan yankan kai."
"Dallah can Malama kina da rainin wayau, me wani abin rikicewa a wannan gidan."
"Ke Hussai Allah Ya basu a nan mu ma Allah Ya bamu a can ke wannan ai ita ce aljannar duniya." 
Hussaina tayi dariya tace "Wallahi kar ki bada ni a gidan nan in mun shiga."
"To na ji muje. Na ga kina ta min wulaƙanci ne."
Ta ja hannunta tace "Muje."
A bakin gate suka fara tsayawa sannan Hussai ta buga ƙofar. Ba'a ɗauki lokaci ba aka buɗe ƙaramin gate ɗin aka fito maigadi ne da uniform ɗin shi fari da wando ash. 
"Malam ka buɗe mana ƙofar ko?"
"Ke Hajiya bata nan."
Sai da dalla mai harara sannan tace "Sau nawa na zo aikin Hajiyar bata nan kuma nake yi na tafi ko ta zo ta same ni? Yau wani sabon fi'ili kake ji da shi ko me?"
"Ban sani ba mara kunya matse bakina sai na gaya miki uwata."
"A'a gardi da kai ai ban haife ka ba can da yawar ka kawai ka matasa min na shiga nayi aikina na fita ban san damu.
Ya ƙi basu hanya suka yi ta cacar baki a nan. Wani ne ya fito yace "Bar su mana Habu su wuce tayi aikin ta kawai ta tafi."
"Don dai ka yi magana ne amma yau da na nuna mata ƙaryar rashin kunya Wallahi."
"Mu nunawa juna dai." Ta faɗa tana hararar sa suka shige ciki. Tana ji yana cewa abokin aikinsa "Ka gani ko? Ka na gani yarinyar nan tana min rashin kunya da ka bar ni na mare ta in ya so in ga me za ta yi."
"Haba Habu yaushe zaka dinga cacar baki da yara ƙananu? Ba girman ka bane."
Ya yi ƙwafa sannan yace "Ai shi kenan."
Suna shiga ciki Lamrat ta kasa ɓoye mamakin ta na ganin wannan hamshaƙin gidan. Kamar ba za a mutu ba. Da ƙyar Hussaina ta janye ta suka shiga kitchen suka yi wanke-wanke tare suka yi shara suka share ko ina cikin awannin gidan ya sake yin ƙal ya yi haske sosai. A cikin fridge Lamrat ta ga kayan fruits ai kuwa ba ta yi ƙasa a guiwa ba ta sa hannu ta ɗiba ta soma ci da ta ga Hussai bata ganin ta kuwa ta ɗebi apple guda uku ta ɓoye. Da an bar ta ma har kallo tayi niyan yi sai dai bata iya amfani da su ba.

Mami ta shigo cikin falon ta samu gu ta zauna a kan kujerar a gajiye bayan ta kuma su Shamsudeen ne suka shigo su ma.

Hussai ce ta fito da tray a hannun ta da ruwa a kai da cups ta ajiye a kan tebur ta tsugunna tace "Barka da zuwa Hajiya Mami."
Mami tayi Murmushi tace "Yauwa barkan mu. Yaya mutan gidan?"
"Suna lafiya lau Hajiya."
Lamrat daga kitchen ta dinge leƙe ta ga Mami fara tas da ita kyakyawa sai matar ta burge ta. 
Shamsudeen da Ishak suka zauna su ma. Hussai ta ba su ruwan suma suka sha. 
Ta tashi ta koma kitchen.
Ishak yace "Mami amma dai wanan ba ta mana girki ko?"
"A'a bata yi iya gyaran gida kawai take yi."
"Ah! Har na tsorata na kusan fara jin amai."
Mami tayi Murmushi kawai bata ce musu komai ba kawai ta ɗauke kai don ta gaji iya fargabar da ta ji ma tsakanin jiya da yau sun cinye ta.
Hussai ta koma kitchen ɗin tace "Kin ga Lamrat mu bi ta ƙofar baya kar Hajiya Mami ta gan ki."
Sai da ta yi satare sannan tace 'Ban gane kar ta gan ni ba kamar wata mai mugun kama ko mai mugun hali."
"A'a ba haka nake nufi ba fa gani nayi bata san na zo da ke ba."
"To na gane wato kar ta gan ni ta yi min abin alkairi ko?"
Hussai ba mafaɗaciya ba ce sai ta bata haƙuri kawai fa ja hannun ta suka fito tare.
Ishak da ke kallon ƙofar kitchen ɗin ya hango su amma abin da ya fara ɗauke mai hankali a tare da su shi ne idanuwan Lamrat da suka yi wani haske su ba blue ba su ba golden ba ba normal colour ɗin eyes na mutane ba haka ya sa yace "Subahanallahi Mami wace wannan haka?"
Mami ta ɗan buɗe idanuwanta da suke a rufe da tace "Ishak yaya aka yi ne?"
"Mami kallo idanun yarinyar nan mutum ce kuwa?"
Sai a lokacin Mami ta kalli Hussai da Lamrat a bakin kitchen sun yi tsuru-tsuru da idanuwa kamar ance sun yi sata.
Mami ta gyara zama tace "Hussaina wacce ce wannan a bayan ki?"
"Hajiya Mami....yi haƙuri kawata ce na zo da ita aiki take nema shi ne nace ta tsaya na gama sai mu shiga maƙota mu nemo."
Lamrat ya ɓuya a bayan Hussai saboda yadda yan falon suka yi mata kwarjini. Musamman ma mazan da suke kallon ta kamar sun ga sabon abu.
Mami tace "Fito na gan ki."
Lamrat ta ƙi fitowa ta ƙanƙanme rigar Hussai daga baya Hussai kuwa sai janyo hannunta take yi tana son ta juyo da ita amma ta kasa janyo ta. Sai da Mami tace "Kar ki ji tsoron komai mu ma mutane ne kamar ki ,ki fito na gan ki ai ba laifi kika yi min ba."
A hankali Lamrat ta fito da kan ta idanuwanta Mami ta fara gani sun mata wani dau ba ta taɓa ganin irin idan ba kuma ba ta ja da ikon Allah wannan ma ɗaya daga cikin hallitar Allah subhanahu wata'ala ce. A hankali tace "Fatabarakallahu-Ahsanul khaliƙin."
Da hannu ta yafito Lamrat alamar ta zo inda take. Lamrat kamar mai koyon tafiya ta matsa kusa da inda Mami take duk bakin ta da iya Shegen ta yau ji tayi komai ya ɗauke mata kamar ma bata san ya ake yin magana ba. A gaban Mami ta tsugunna tace "Na..mm Hajiya..ban yi komai ba."
"Na sani ya sunan ki?"
"Lamrat Ado Bala"
"A ina kike da zama?"
"Idi Araba"
"Unguwa ɗaya da Hussaina kenan?"
"Eh." Ta faɗa tare da gyaɗa kai.
"Aikin me kika iya?"
"Na iya shara da wanke-wanke har wanki ma ina yi na kuma iya tuyar awara da ƙosai da doya na iya dafa wake da shinkafa." Da ta faɗi wanke da shinkafa sai aka yi sa'a Ishak ya kalli haƙoran ta bai san lokacin da ya miƙe tsaye ba ya yi waje da gudu saboda yadda zuciyarsa ke tashi. Mami ta bi bayansa da kallo Shamsudeen kuwa ne ze yi in ba dariya ba. Mami dai bata kula su ba tayi Murmushi tace "A'a banda girki ina da mai yi min girki sai dai ko wankin da ban ruwa ma fulawa ki kamawa Hussaina wasu ayyukan haka."
Da sauri Lamrat ta kamo ƙafar Mami tace "Zan iya Wallahi zan iya."
Mami ta janye ƙafar ta tace "Amma za mu yi faɗa da ke in har ba kya tsafta."
"Yau ma nayi wanka Hajiya." Ta faɗa da sauri.
Mami tace "Ba iya wanka ba har da tsaftar haƙora da jiki nake nufi da kayan sawa kin ga in ba iya gyarawa yarana maza zasu sa na Kore ki."
Da sauri tace"Wayyo yaran Mami don Allah kar ku sa a Kore ni ina da bukatar aikin Wallahi ina yin wanka kun ga ma yau sai da muka yi faɗa da Atika na riga ta shiga banɗaki."
Shamsudeen dai Murmushi ya yi ya ɗauke kai ya ci gaba da danna waya. A ransa kuwa cewa ya yi akwai dirama lallai wai ya za ayi idan Blaze ya zo ya ga wannan harigidon a gidansu."
"Mami are you serious?" Shamsudeen ya tambaye ta yana kallon ta.
"To wai ina wasa da ku ne?"
"Allah Ya huci zuciyar ki Mami. But..." Ta ɗaga masa hannu ya sa hannu a kan leɓɓen sa ya koma ya kwanta a kan kujerar yana danna wayar sa.
Mami ya kalle su tace "Kin ji me nace miki ko? Bana son ƙazanta sam-sam in har kina son ki shirya da ni ki siyo brush da macline kina wanke bakin ki sannan kullum sai kin yi wanka."
Da sauri ta ɗaga kai tace "Na ji Hajiya zan yi Wallahi amma dai ban da kuɗin siyan brush da macline ɗin ba."
Hajiya ta janyo jakar ta da ta ajiye a gefe ta zaro dubu biyu ta bata. Ta washe baki tana godiya. Suna fita daga gidan Hussai tace "Kai lallai kin taki sa'a Hajiya ta baki aiki a yadda kike to sai ki shiga hankalin ki wannan haukan da kike yi ki daina sai kin nutsu dole kin san su masu kuɗi ba sa san wannan haukan dole ne ki zama mai aji tsafta dai ba sai na sake gaya miki ba tunda dai kin ji ta gaya miki da kanta. To maza muje ki sayi macline ɗin da brush ɗin har sabulun wanka zamu siya.''
"Na ji Hajiya uwar iya uwar tsari."
Suka tafi shago suka sayi komai.
Tun kan ta shiga cikin gidan ta soma jin hanyaniya a tsakar gidan tuni ta kyañe fuska tace "Wannan gida namu shi ake kira buji house kullum a masifa ake kamar ba yan gida ɗaya ba."
Ciki ta shiga da baƙar Leda a hannun ta. A tsaye ta ga yan gidan sun yi cirko-cirko suna kallon Habiba da Atika cakume da kwalar juna suna kokawa. Bata ce musu ƙala ba ta shige ɗakin su.
Ko zama bata yi ba aka ɗaga labulen ɗakin. Koda ta juya Umma ce ta leƙo.
"Sannu da zuwa mai gida don ubanki tun safe kika sa ƙafa kika bar gidan nan baki dawo ba sai yanzu uban waye ya zai yi miki aikin?"
Sai da ta ɗan yamutsa fuska sannan tace "Umma aikin me zan yi tsakani da Allah? Na ga dai bana ma gidan bare a ce na ci wani abun ko na ɓata wani abun duk ga mutane a gidan sai ni?"
Umma tace "Iye! Sannu fitsarara mara kunya to yau sai na koya miki hankali in kin ga na bar ki to kin yi aikin nan ne in kuma taurin kan da kika saba za ki yi min ne to yau ina miki albishir da cewa uban naki baya nan ya tafi aiki sai an kwana biyu zai dawo daka ki zan in yi manɗo da ke ba wanda zai san me ya same ki a gidan nan."
Jin Baba baya nan ya sa ta kama kan ta tayi gum da bakin ta. Tashi tayi tana zumɓurar baki tace "Ai ina zuwa ki je ko?"
Umman ta sauke labulen ta koma.
Kayanta ta fara cirowa daga cikin bakon ta saka apple din nan da macline da brush da sabulu a ciki ta maida kayan sannan ta zuge ta fita daga ɗakin.
Sai da ta bi tsakar gidan da kallo sannan ta ɗauki tsintsiya ta soma sharar sama-sama ta soma tattara kwanukan ta wanke su ta ajiye a nan bakin kicin bata koma ba aka ce ta zo ta yi miyar tuwo Atika kuma zasu tuƙa tuwon haka dai suka yi aikin kadaran-kadahan. Suna tsaka da yi ƙanin su Isa ya shigo da gudu yana hakki yace ga wasu can suna dukan Sahabi. Habawa tuni suka tafi yuuuuu suka yi wajen su ka ga an mai rubdugu kusan matasa huɗu a kan sa shi kaɗai. Bata san yadda aka yi ba sai gani tayi ta ɗauki wani ƙaton dutse ta jefa wa ɗaya cikin sa'a kuwa ta same shi a ƙeye nan da nan wurin ya fashe ya soma jini ya zabga wani uban ihu kamar ba shi ke dukan wani ba. Suka juya sauran su ga waye da wannan aikin sai suka ga Lamrat.
Habiba da Atiƙa da wani ƙanin su Isma'il da Shehuwa suka yi kan su suma da duwatsu suka shigar wa dan'uwansu. Dama yan gidan Baba Ado Bala sun saba a tsakanin su kamar suna ganin hanjin junansu amma idan wani zai taɓa su to tabbas za a ga aikin gayya don taɓa ɗaya ka ga dozen ne taken su. 
Da ƙyar aka raba faɗan nan sai da aka ce za a kawo yan'sanda tukunna sannan suka koma ciki da Sahabi.
Umma sai mita take yi ba zata yarda ba sai ta kai ƙara ba wanda ya kula ta dai da ta gaji tayi shiru tana tsaki.
*
 Kwanaki biyu ya yi a asibiti aka ba su sallama. Gidan Mami aka wuce da shi duk da Abba bai so haka ba amma ba yadda ya iya wannan karon.

Ɗakin sa an riga an gyara masa shi tsaf sai ƙamshi yake yi. Wannan aikin Mami ne bata bari kowa ya shigar mai saboda baya so ana shigar masa ɗaki duk da ba kasafai yake zama a gidan ba ma amma in dai yana nan ba mai shiga Sabgar sa sai Mamin sa kawai.
Yanzun ma ta gyara masa ko ina da kan ta Allah Ya sani tana son Adnan sosai ba ta sani ba ko dan shi ba a wurin ta ya taso ba bai shaƙu da ita ba kamar sauran. Hannun sa ya sa ya taɓa na ta hannun yace "Mami tunanin me kike yi?"
"Ba komai ba abinda yake maka ciwo dai ko?"
"Ba komai Mami komai lafiya lau."
"Alhamdu Lillahi. Allah Ya kiyaye na gaba."
"Amin-Amin. Ka dinga kula Adnan duniyar nan fa yanzu ta zama abinda ta zama ba kowa ake yarda da shi ba kuma ba kowa ake taimaka ba yanzu dai ga shi an yi amfani da kyawawan hallayen ka an illata ka yanzu da ace Allah be kawo wannan baiwar Allahr ba Hajiya Khadija ai da yanzu muna zaman makoki ni dai na soke maka fita kai kaɗai tunda dai Allah Ya rufa maka asiri kuɗin nan kana da su ,masu tsaron na ka ma akwai ka daina fita ba su bana son Sabgar faɗuwar gaba Adnan ka kiyaye."
Kai ya gyaɗa mata yace "In sha Allah Mami zan kiyaye kuyi haƙuri ina cikin wani ƙadami ne wanda nake son ku taya ni da addu'a na fita daga ciki ,Mami bana jindaɗin komai , rayuwata bata yi mini daɗi ,ban san me yake damuna ba akwai abinda na aikata amma na kasa tuna ga wa na aikata amma abin na damuna ya tsaya mini a rai Mami ina buƙatar addu'ar."
Hannu ta sa tana shafa masa kai tace "Adnan Allah gafurur rahim ne ka roƙe shi gafara zai yafe maka kai ma ka koma ga Allah ka daina duk wasu abubuwa da Allah baya so Adnan ka dawo cikin hayyacin ka i want my old son."
"Mami Allah baya yafe hakkin wani."
"Ka nemi yafiyar wanda ka zalunta in sha Allah za su yafe maka."
"Mami ko da kuwa wanda na yiwa laifin baya duniya?"
Sai Mami ta yi shiru gabanta ya buga ya bada dum ya rasa me yake yi mata daɗi ta rasa me za ta ce masa kuma kawai sai ta ƙaƙalo murmushi tace "Ka yi ta istigifari Adnan. Sannan ka soma shiri ka nemi mata ka yi aure ka yi settling wataƙila in ka samu abokiyar rayuwa ka samu salama da sauƙi a ran ka."
"Mami wanne aure? No bana son nayi aure."
"Ai kuwa za ka yi Adnan aure ba babu fashi in dai kana da rai kana numfashi sai ka yi shi. Ba a zauna a haka ba yaro."
"Mami Ya Deen ma ba ki ce ya yi ba sai ni?"
"Ya Deen ya fika hankali ai bana jin komai a kan sa saboda nutsuwar shi."
"Mami kamar fa kina nufin ni ban da nutsuwa ne?"
"To ku san haka nake nufi."
"Innallillhi wa inna illahir rajii'un Mami...."
Mami tayi dariya ta tashi daga kan gadon tace "Zan maka abinci na aiko maka da shi ka huta yanzu sannan ban ce ka yi ta kiraye-kiraye ko amsa waya ba rest."
Da ka ya amsa mata ya koma ya kishingiɗa da baya. "It's been a while da muka yi hira da Mami haka. Ashe dai tana sona." Ya faɗa a fili.
Murmushi ya yi ya lumshe idanuwansa bayan fitar Mami daga cikin ɗakin. Matar da ta taimaka masa da ta zo suyi sallama ɗasu yake ta tunani ya kasa cire kammanin ta a cikin idanuwansa like kamar ya taɓa ganin ta in ma bai taɓa ganin ta ba ya san wani ko wata mai kama da ita sosai yana tsaka da tunanin ne ma maganin ya fara yin aiki a kan sa bacci ya ɗauke shi.

*

"Alhaji na jima ina gaya maka gaskiya amma ba ka yarda ko kuma tsoron uwar sa kake ji ne ni ban sani ba amma abin ya yi yawa kamar sa hannu ko baki?" Mama ta faɗa tana kallon ƙasa tana marairaice murya.
Alhaji ya gyara zaman sa yace "Ba tsoro bane ai in ita ban isa da ita ba shi na isa da shi tunda ni na haife shi ɗana ne kuma ni ne uban sa ya ma isa na faɗa ya ƙi yi? Ai ban haifi wannan ɗan ba sai dai ɗan ya sake uba."
"Ato ya kamata dai ka nuna musu hakan wannan karon. Ni dai duk abinda za ka yi ni me mara maka baya ba ce a dukkanin wani hukunci da za ka yanke."
"Amma a wurin ki wa kike so a ba shi ayi abin nan a rufawa kai asiri ba tare da an ji kunya ba."
"Ga yara nan yan mata da yawa a dangi kawai ja ce ga wadda za a zaɓo masa."
"A'a ni da ba kallon su nake ba ya za ayi na sani? A'a ki je ki zaɓa mai ke ko a dangin ki ne ma."
"To ai dai ka san yaron nan baya jin magana ga shaye-sheye ya na fama da shi kar na zo ne na lallaɓa iyayen yarinya a zo a watsa min kasa a ido ya ce bai san magana ba."
"Haba ke kuma bana son irin haka, ko kina nufin Adnan zai ja da ni ne ko hukunci na? Ko ke ba shaida ba ce kan yadda yake min biyayya ba?"
"A'a Allah Ya huci zuciyar ka Yallaɓai tuba nake ayi min afuwa ban san hakan zai ɓata maka rai ba tuba nake."
"Gaskiya bana so ki je kiyi duk abinda ya dace ki zo min da bayani auren gata ma zan yi masa bana buƙatar komai na sa."
"Alhamdu Lillahi wannan abun kam ya yi ma sha Allah! Na ji daɗin hakan akwai yar Yaya Suwaiba dama da ta gama makaranta sai na sa ayi Sabgar nan ta alkairi da arziki da su. Ka san ta ai yarinyar da ke zuwa nan hutu kafin ta koma makaranta Zainab ba sai ayi abin gida ba kawai tuwo na maina ba?"
"Duk yadda kika yi da ni bani da matsala na yarda na kuma gamsu da zaɓin ki Adnan ai ɗan ki ne."
"Wallahi ina son ka Yallabai saboda yadda ka bani muhimmanci a rayuwar ka kuma ka yarda da ni a lamuran ka ba gode! Na gode! Allah Ya bar mu tare har a aljanna ,Allah kuma Ya ƙara bani ikon yi maka biyayya."
"Amin matata Amin. Ai yadda kike yi mini in dai aljanna ce na ɗage ƙafata kin wuce ."
Suka sa dariya gaba ɗayan su a tare. Ya shige ciki. Ta koma ta kwanta a kan kujera tana dariya mai cike da nishaɗi.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol