Free chapter · Read without an account
Chapter 6
06
Daki ta tashi ta shiga wayar ta a hannu ta kulle ƙofar ta ja labule ta kulle ko ina na ɗakin sannan ta shiga cikin banɗaki ta kira lambar wayar yayar ta ta. Bugu biyu ta daga wayar.
"Salamu alaikum..."
"Bar salamar nan Yaya kawai na fi son muyi wannan maganar ni da ke yau ba gobe ba."
"Ya akai yi? Ta samu kenan?"
"Na samu na shawo kan Babansu Mima a kan batun auren yaron nan Adnan da Zainabun mu."
"Kai haba don Allah da gaske kike ko wasa?"
"Haba! Zan miki wasa da wannan ne?"
"Kai amma Allah Ya yi miki albarka Fatima. Kin cika min burina wai ke ban san me ma yadda zan fasalta farincikina ba."
"Ba fa wai zuwa za ta yi ta zauna ba ne kin sani idanuwana a kan dukiyar yaron nan take tunda ni kin ba yaran nan nawa mata ne ba namiji a ciki ko guda ga shi yana da arziki yaron nan don ma yanzu ya soma Iskanci duk da haka ba zan bari ba so nake Zainab ta sa a ran ta zuwa tayi don aiki gidan Adnan ba wai soyayay mai tsayi ba kawai dai ta san yadda zata kwakwaso mana komai kawai a ci arziƙi tare a tsira tare."
"Na fahimta mana duk wannan karatun ai ni na koya muku shi ko kin manta da yadda na sa kika shiga gidan ki ka fitar da matar da ta aure shi tun yana faƙiri?"
"Ba sai an tono da matattu ba Yaya kawai a san yadda za ayi bakin su ya kulle ayi abin nan kin dai gane me nake nufi? Don uwar shi ba yadda za ta yi ba shi ma ɗan Iskan yaron ba yadda zai yi ba so nake a kulle bakin duk wanda zai hana lamarin nan."
"Sai ma kin faɗa min Fatima bayan na san halin kowa a'a ai sanya bai gan ni ba lokacin zuwa gun Malam ya zo."
"Yauwa yadda kuka yi sai ki gaya min na san yadda zan ɓullowa lamarin nima."
"Ba matsala sai na ji wayar ki."
Suka kashe wayar a tare .
Hajiya Suwaiba kuwa tana ajiye waya ta saki wani makirin dariya sannan ta gyara zama ta matse baki a cikin ranta kuwa cewa tayi "Wuyar ta Zainab bata shiga gidan ba amma in dai ta shiga sai yadda na tsara za ayi. Wacce wata Fatima? Yarinyar da ni na raine ta na kuma yi mata aure amma da ta tashi sai ta juya min baya ta nuna min miji da dukiya sun fi ni na zama kamar wata ƙanwar ta ita kuma yar sai yadda tayi dani nake bi har yarana ma suna jin haushina wannan ba ƙaramin dama ba ce Allah Ya kawo mata har ƙofar ɗaka ba kuma za ta yi amfani da wannan damar ta yi yadda take so har ta samo dukiyar ita da yar ta. Ba zata bari ta ci tudu biyu ba sam-sam ga dukiyar miji ga ta ɗan miji saboda haɗama da son zuciya bai yiwuwa." Murmushi ne kwance kan fuskar ta na hango wa kan ta nasara a gaba.
*
Meeting suka zauna don su tattauna kan matsalar da take ƙoƙarin tunkaro su. Mutane shiddan da ke zaune kewaye da wani teburi da aka zagaye da kujeru nayi ina sauraron su.
Mawaƙa ne ,amma ba irin mawaƙan da ake gani ba. Mawaƙa ne da suke gina wasu mawaƙan ta wata fuska ta daban ta hanyar iko ,barazana da kuma jini.Babban jagoran su Sarkin sauti ,ya jingina bayan sa da kujera yana jujuya zoben sa sannan yace "Adnan ya manta cewa mune muka fito da shi aka san shi. Muryar sa ta fara yin tsawo a gare mu sannan kuma ya daina bin layin da muka shimfiɗa masa."
Daga gefen dama wani mai suna Black Mic ya buga teburin da tafin hannunsa sannan yace "Mun hana dakatar da shi ya ƙi dakatuwa, mun ba shi aiki sai anje ya janye mun ja masa kunne amma ya ƙara samun kwarin guiwar raina mu."
Lil razor ya yi Murmushi na taƙaici idanuwnasa cike da mugunta da barazana sannan yace "Taurin kai ba laifi bane..sai dai in har taurin kan ya zama barazana ga iko. Kuma Balze ya fara zama barazana a gare mu." Shiru ya ratsa ɗakin na ɗan lokaci sai fitar numfarfashi kawai ake ji. Sarkin Sauti ya ɗora hannunsa a kan tebur sannan yace "Ba zamu kashe shi ba. Mutuwa tana sa jarumta. Muna son mu rusa shi a hankali."
"Ta yaya?" In ji Echo.
"Za mu fara da ɓata masa suna kamar yadda muka ɗauko hanya yanzu, za mu ƙirƙiro labarai a kan sa sannan za mu saka masoyan sa su juya mai baya su koma maƙiyansa. Zamu yi hanyar rufe masa ƙofofi ma'ana a daina jin sa a gidajen Radio,shows,da kuma wurin sponsers."
Black Mic ya yi dariya ƙasa-ƙasa sannan yace "Idan har muka kashe Muryar sa to ba makawa Adnan ya mutu murus."
"Idan kuma bai mutu ba fa?" Lil Razor ya faɗa.
Tambayar ta shiga kowannensu.
A fusace Echo yace "Sai mu tabbatar masa da cewa mawaƙa mafiya ba su yin barazana kawai suna iya aiwatarwa ma."
Sun rufe meeting da tunatarwa kan su cewa lokacin jarabawar Adnan ya zo."
*
Bayan sun gama wani show da abokan sa guda biyu ciki harda da Sahib amma Sahib bai sha komai ba ya na dai zaune yana charting a waya. A wancan lokacin ya na mu'amala da kayan maye sai dai ranar an yaudare shi ba tare da sanin sa ba aka sa masa maganin ƙarfin sha'awa kuma da wani dose na wata ƙwaya mai ƙarfi sosai.
Bayan sun gama sharholiyar su ne Sahib ya tashe shi da ƙyar suka ɗauki hanya sai dai tun kan su je ko ina ya ji ya kasa controlling ɗin kan sa da yanayin sa ya sa hannu ya dafe marar sa yadda take kawo masa danƙa take murɗa mai.
Hannun Sahib ya kama yace masa da ƙyar "Help me Sahib na shiga uku ban san me ya same ni ba ina jin wani iri this is not me."
Sahib ya faka a gefen titi ga duhu a arear da suke ba wani mutane tunda dare ma ya yi wajen ƙarfe ɗaya saura ne shiru wurin da suke. Ya kalli gaba da baya bai ga kowa ba ya rasa yadda zai yi kawai sai ya zaɓi ya fita ko zai sami chemist ya samo masa wani taimako don ya gane cewa akwai abinda aka ba wa Blaze a wurin wannan shagalin.
"Ka jira ni a nan Artist kar ka je ko ina."
Kai kawai ya gyaɗa masa cike da tashin hankali da ciwo. Sahib ya fita daga cikin motar da sauri ba tare da ya san inda za shi ba kawai yake cilla ƙafafuwan sa kawai. Fatan sa Allah Ya sa ya ci karo da wani shago.
Blaze kuwa marar sa ta kuma kai masa danƙa ya yi yar ƙara ya ɓalle murfin motar ya fita daga cikin motar har yana faduwa ƙasa saboda jikin sa babu ƙwari kwata-kwata da ƙyar yake iya motsi ma. Tunda ya zo duniya bai taɓa jin sa a irin wannan yanayin ba sai wannan lokacin cike da tashin hankali ya dafa jikin motar ya tashi tsaye amma ya kasa miƙewa gabaɗaya baya ma gani sosai saboda dama a buge yake ga wannan yanayin, ya dinga fitas da numfashi ya rasa ma me yake masa daɗi a duniyar gabaɗaya. Idanuwansa sai mannewa suke yi saboda baya gani sosai daga ɗan nesa ya ga kamar mace a tsaye tana kallon sa jikinta sai rawa yake yi duk da akwai duhu hasken farin wata bai hana shi ganin idanuwan ta ba. Bai taɓa ganin irin su ba ƙwayar idanuwan ta ba baƙi ba ne wani daban ne a hankali ta yo gaba kusa da shi sosai ta haɗe hannayen ta biyu tana neman taimakon sa amma ba ya jin abinda take faɗa sosai tuni shaiɗan ya raya masa ya afka mata kawai ya samar wa kan sa mafita ya bi umarnin zuciyarsa ya kai mata cafka ɗaya ya buɗe motar ya jefa ta ciki ya shiga ya kulle.........
Ɗakin aka buɗe aka shigo haka ya sa ya buɗe idanuwansa da suka yi ja saboda bacci ya sauke su a kan Ishak da Mima da Tasneem.
Tsaki ya yi a hankali yace "Me kenan?"
Ishak ya ɗan kama kunnen sa yace "Afuwa yaya bamu san bacci kake ba da ba za mu tashe ka ba."
Tsaki ya yi cike da jin haushin su bayan katse masa bacci har da mafarkin yarinyar da yake nema an katse masa ya kasa tuna komai a tare da ita na kamanni ko wani abu sai iya idanuwan ta da suke da wani irin sirri kalar su daban yake da na saura tsabar ma damuwa sai da ya yi bincike kan kalar idanuwan su ake kira da "Azure eyes kalar su rare ne ba kasafai ake samun su ba a cikin kaso 100% ma ba su wuce 5% ke da irin idanuwan ba. Blue ne amma kalar sararin samaniya kuma kamar na mai kuka kullum cikin moist amma a haka suke."
Mima tace "Yaya jikin Bro."
"Da sauƙi."
"Ba ka jin komai ko big bro?"
"Am ok Tasneem ya school ɗin?"
"Lafiya lau. Ai hankali na bai kwanta ba da na ji news ɗin abinda ya same ka faka-faka na taho na bar su."
"To ai yanzu kin gan ni am ok ,sai ki tattara ki koma kin san dai bana son wasa da karatu ko?"
Sai da ta ɗan zumɓuri bakin ta sannan tace "Haba Big Bro! Kar muyi haka da kai don Allah ka bari ko sati ɗaya ne nayi na ɗan ga dangi sai na tafi."
"No. Yau za ki koma. Ishak"
"Na'am Yaya?"
"Ka maida ta ko ka saka Ɗan bukarere ya maida ta."
Tuni ta dinga didira ƙafafuwan ta a ƙasa ita fa ba za ta je ko ina ba.
Ya ɗaga hannu yace "Zan mare ki."
Ta zumɓuri baki tace "To me nayi maka kuma ai dai zan koma ko?"
"Better."
"Dole a koma." Mima ta faɗa cike da tsokana.
Tasneem tace "Yaya ka ji ta ko?"
"Mima ba kya girma kullum tsonana kika iya."
"Bro ban mata komai ba fa kawai Autancin ne ya tashi ni ina ruwana da ita?"
"Ku tashi ku fita don Allah na warke na gode da dubiya."
Sarai sun san halin sa sum-sum suka tashi suka bar mai ɗakin. Suna fita ya koma ya kwanta abin sa.
Da gaske yana son ya gano wacce ce yarinyar da suka haɗu a wannan daren ,wadda ko ba a faɗa ba ya sani ya lalata mata rayuwa a yadda yake hasashe ma kamar ya kashe ta ne da nauyin sa. Ya saki numfashi a hankali ya yi tsaki ya juya ya buɗe idanuwansa zaman ya ƙi mai daɗi haka ma kwanciyar duk da kan sa yana masa ciwo kamar kan sa zai fashe haka ya cije ya sa fillo a bayan sa kawai ya jingina da shi. Yana kallo wayar sa na haske kuma ya ga kiran na Lil Razor ne tsaki ya yi ta juyar da fuskar wayar ya sa hannu ya dafe kan sa da hannu ɗaya.
Ɗakin aka kuma buɗewa aka shigo ciki. Yana ɗaga kan sa ya ga Abban sa ne da mamaki ya ɗan murza idanuwansa ganin da gaske Abban sa ne a gidan Mami a karo na farko.
"Abbbbbbbaaaaaa da gaske kai ne ka zo gidan Mami?" Ya tambaye shi da mamaki kwance a kan fuskar sa.
"My boy! Ai kai ne komai zan yi in dai a kan ka ne babu ja. Yau na karya alƙawarina na zo na gan ka ai lafiya ta fi komai."
"Abba na gode kuma na ji daɗin ganin ka."
Ya sa hannu ya dafa kafaɗar sa yana murmushi ya gyara zaman babbar rigarsa ya zauna a gefen sa yana murmushi Kuma hannun sa a kan kafaɗar sa yace "How are you feeling?"
"Am okey Abba na gode."
"Marin ka zan yi ka ƙara ce min wai ka gode baka da hankali?"
"Am sorry."
Hannunsa ya kama yace "To yaya kake ji ba wani ciwo dai ko?"
Ya sa hannu a ɓarin da yake sara masa yace "Nan ɓarin ne kawai yake min ciwo."
"Sai a hankali dana ka yi ta shan magani yadda suka gaya maka ka kuma kula da cin abinci."
"In sha Allah Abba."
"Da biyu na zo ma fa Adnan."
"Amma me ya faru Abba?"
"Aure nake so kayi."
Sai da ya yi freezing na kusan sakanni biyu kafin yace "Abba amma na zata mun gama wannan maganar bani da ra'ayin yin aure kwata-kwata i want my freedom."
"Kai dallah yi min shiru shashashan yaro wane ba za ka yi aure ba? Ban gane ba baka da lafiya ne ko kuma zallar iskanci ne?"
"Abba lafiya ta ƙalau kawai auren ne bani da intrest a kai."
"Saboda kana ganin kowanne aure irin nawa da na uwar ka ne ko?"
"Abba.." ya ja sunan sa da wani irin yanayi a kan fuskar sa.
"A'a gaskiya ne saboda kana min kallon mugun miji mara adalci wanda ya tsani uwar ka ko?"
"Abba ba haka bane kawai na tashi na ga yadda auren ku bai yi working ba ni bani da ƙarfin hali irin na ku. I can't take wannan hayaniyar da ake yi a ciki already ina cikin damuwa ban san add up."
"Adnan kai jini na ne , karaya ba nake bane , dole ne ka zama brave dole ne ka kasance mai ƙarfin hali da kuma mazantaka kamar ni dai tsayayyen namiji wanda mace bata isa ta taka shi ba."
"Abba wai kana nufin yadda kake yi wa su Mami ne tsayayyen namiji? Kana tare da ɗaya baka tare da ɗaya shi ne mazantaka?" Ya faɗa da ƙyar har muryar sa na cracking saboda ɓacin rai.
Abba yace "Ok! Tayi nasarar koya maka yadda zaka yi min rashin kunya ko? Ina yabon ka sallah ina alfahari da kai a cikin waɗanan mazan guda uku kai ka fita zakka ashe lalube a duhu nake? Ai shi kenan na gode tunda har babu wanda na isa da shi a cikin ku baku maida ni kowa ba saboda kun fi son uwar ku ta gama hure muku kunne a kaina ta ɓata muku tunanin ku a kaina tayi brain washing ɗin ku ba komai ni na sani da ace su Mima maza ne ba za su so su ga hawaye na ba saboda yadda suke tsananin ƙaunata da ganin girmana."
Sai da ya sauke numfashi ya saki ajiyar zuciya sannan ya ce "Abba zan yi shawara da Mani."
A fusace ya miƙe tsaye ya baza riga sannan yace "Ban yi lalacewar da zan bawa ɗa umarni yace sai ya yi shawara da uwarsa ba sannan zai yi yadda nake so ba ƙarya kake yi Wallahi ko da amincewar ka ko ba amincewar ka sai an yi nonsese boy kawai." Yana kaiwa nan ya fita daga cikin ɗakin gaba ɗaya.
Yana sauka ya ga Mami cikin kwalliya da ado kamar dai wadda take da miji a ranar. Ya kalle ta da kyau ya ji wani abu ya tsarga mata a rai ya ji yana son ya tanka mata yadda ya saba a lokutan baya amma sai ya buɗe baki sai ya ji kamar an tokare shi da wani abu mai nauyi a maƙogwaron sa sai ya ɓige da nuna ta da yatsa sannan yace "Na rantse miki da Allah ba ki isa ki raba ni da ɗana ba kuma yadda nake so haka za a yi ban yi lalacewar da zan zuba ido ki yanke hukunci na bi ba ba kowa bace ke aure ne zan yi wa Adnan kuma sai na mai da wadda nake so ba ki isa ki hana ba daga ke har shi ɗin."
Mami ta mike tsaye jin ya ambaci aure.
"Aure za ka yi wa waye?"
"Adnan ko ban isa bane?"
"Ka isa amma nima ina da isa yadda kake da ita."
"Isar ki ɗin banza da wofi kin isa ki mai auren ne? Ni ne nan uban sa ko kin manta da uba ake ado ba rigar aro ba? Ko kin taɓa ganin inda aka je uwa ta ɗaura aure, ko ta nemi aure?"
"Ba a taɓa ba kuma ba za a taɓa ba amma dole nima sai in tayi min sannan zan yadda."
"Zan ga ranar da za ki yi hankali kuwa. Kuma zan nuna miki iko daga shi har ke dole ne ku fuskanci hukunci." Yana kai wa nan ya sa kai ya yi gaba.
Mami kuwa ta soma magana da karfi don ya ji. "Ai Wallahi sai Allah Ya tambaye ka hakkin mu yadda ka cuce ni ba zan yadda ka cuci yarana ba. Ba zan yadda ka lalata musu rayuwa ba sai na kai ƙarar ka wurin Allah."
Yaya Deeni ne ya yi saurin kamo ta ya tsayar da ita yana bata haƙuri.
"Mami don Allah kiyi shiru kiyi haƙuri don Allah ki daina damun kan ki akan wasu abubuwan."
"Kana jin abinda ya faɗa ko? To Wallahi zai aikata kuma na san shirin matar sa ne ita ce ta kitsa masa don a zo a lalata rayuwar ɗana kuma ba zan laminta ba tayi kaɗan tayi tsararo."
Adnan daga sama yace "Mami...." Sai kuma ya yi shiru. Mami ta kalli saman benen tayi saurin share hawayen ta tace "Koma ka kwanta Adnan ba abinda ya faru."
"Mami na ji komai kuma na san me ya faru da ni ya fara maganar amma na fi son ki kwantar da hankalin ki kin sani ina son ki kuma ina son Abba babu wanda dan iya saɓawa a cikin ku zan auri wadda yake so kema ki kawo wadda kike so zan aura in sha Allah na raba faɗan."
Yana kaiwa nan ya juya ya koma ciki. Mami za ta yi magana Yaya Deeni ya girgiza mata kai ya zaunar da ita akan kujera hawayen ta sun kasa tsayawa.
"Shamsu ban san me yasa mahaifin ku ya ke nuna min ƙiyayya ba, ban san me nayi masa da zafi ba, kullum sai na tambayi kaina laifin da nayi masa amma har yau na kasa ganewa me nayi masa? Ni ban yi magana akan auren cin amanar da aka yi min ba sai su ne zasu uzurra wa rayuwa ta? Na gaji wannan karon ba zan laminta ba."
Tana gama faɗa ta shige na ta ɗakin. Shamsu ya kalli saman bene ya kalli ɓarin ɗakin Mami. Ya sauke ajiyar zuciya ya juya ya koma ya zauna a one seater ya zauna. Duk yadda yake da ƙiyayya da mahaifinsa to fa a gun Adnan Abban nasu ba ya taɓuwa kuma shi ba ya iya yi masa musu wannan kowa ya sani. Abba da Adnan ba sa rabuwa. A iya shekarun da suka yi a rabe basu kuma taka ƙafafuwan sa cikin gidan Abba ba amma Adnan ku san a can ma ya taso tare da Abban a kan wani dalili da babu wanda ya sani daga shi sai Allah kawai. A sati kullum yana zuwa gun Abba sau huɗu kuma akwai sabo sosai a tsakanin su fiye da kowa shi in ta shi ne ma zai iya sauya sunan uba amma bai isa ba saboda Mami ma ta hana kuma bata taɓa zaunar da su ta ɓata Abba a gaban su ba kullum fadi take fadan ta Abba tsakanin su ne babu ruwan su amma ko da yaushe Abba yana son ya ɗaga yatsa a kan Mami ya ɗora mata laifi akan komai wanda hakan baya musu daɗi.