Free chapter · Read without an account
Chapter Sixteen
CI GABAN LABARIN
Washegari misalin karfe goma na safe, Radiya tana zaune akan gadon da ta kwana. Hadimar Dr. Cara ta shigo hannunta ɗauke da dogon tray mai ɗauke da kayan karin kumallo.
Sai da ta risina ta gaishe ta, sannan ta ajiye ta fita.
A sanyaye ta ɗago ta kalli abincin tayi ajiyar zuciya, sannan ta miƙe ta shiga banɗaki tayi wanka ta fito ta jawo akwatunta domin ta sauya kaya.
Sannan daga bisani, ta zauna domin tayi breakfast, saboda tsananin yunwar da take addabarta, ta manta yaushe rabon da taci abinci.
Bayan ta kammala, ta zauna ita kaɗai tayi shuru tana nazarin rayuwa. Can daga bisani, wayarta ta faɗo mata a ranta. Da sauri ta ɗakko ta, ta kunna. Ba tare da ɓata lokaci ba, fara kiran layin Sadiq, domin taji jikin Abbas.
Bayan sun gaisa, tace masa:
"Ya jikin Yaya"
Ajiyar zuciya yayi, sannan yace:
"Da sauki za'a ce, tunda ba'a bari a ganshi. Yanzu na dawo daga immigration office tun safe suka kirani. Na karɓo komai, yanzu visa kawai muke jira."
Jinjina kanta tayi, sannan tace:
"Ka tafi office ɗin Dr. Lamir, ka kai masa komai, idan komai ya kammala yanzu sai mu tura kuɗin visa."
"Ba matsala."
Ya faɗa tare da miƙewa.
Bayan ya isa office ɗin Dr. Lamir, tare suka gudanar da komai. Cikin sauƙi suka siyi visa, bayan sun tura da duk wasu takardu da ake buƙata. Sannan suka ci gaba da jira har cuwa lokacin da komai zai kammala.
To da yake ta gaggawa ce, acikin awa 24 suka turo komai. A ranar Radiya tayi booking ɗin jirgi, ya kama ƙarfe biyu na rana zasu tashi daga garin Abuja zuwa Cairo.
Misalin sha biyu da rabi, jirginsu Abbas ya sauka a Abuja. Tun da suka taso daga Kano Radiya take airport tana jiransu.
Suna sauka da taimakon securities ɗin da suka rako ta, ta samu ta ga Sadiq, da kuma Abbas, wanda yake kwance akan gadon majinyata, hancinsa ɗauke da iskar oxygen, bai san wanda yake kansa ba.
Da sauri ta ƙarasa, ta kama gadon ta fashe da wani matsanancin kuka. Sannan daga bisani ta ƙanƙame shi, tana yi masa addu'ar Allah ya bashi lafiya.
Da ƙyar! Sadiq ya iya ɗago ta daga jikin gadon, a daidai lokacin da zasu wuce zuwa wajen immigration, sannan suka yi sallama.
Misalin ƙarfe biyu na rana jirginsu ya ɗaga zuwa birnin Cairo.
A daddafe ta dawo gida tana kuka, da ƙyar Dr. Cara ta iya rarrashinta.
Duk wannan al'amarin da ya faru a airport, Sultan da Sauban suna daga nesa suna hangota. Tayi matuƙar basu tausayi, hakan ya saka Sultan ya sake ɗaura aniyar kula da ita, da ƴan uwanta har zuwa ƙarshen rayuwarsa, kuma ya sani, ba zai taba gazawa ba.
Misalin ƙarfe takwas saura kaɗan na dare ta idar da sallar isha'i. Tana zaune akan carpet, tunanin duniya yayi mata yawa, cikin sanyayyiyar murya taji anyi sallama an shigo.
Tana ɗaga kanta suka yi arba da Sauban. A sanyaye ta amsa, sannan ya nemi waje a gefen gado ya zauna.
Bayan sun gaisa kenan, taji wayarta ta fara ringing. Da sauri ta ɗaga, whatsApp audio call ne ya shigo na Sadiq. Take ya fara yi mata albishir da cewar, sun sauka lafiya yanzu ba daɗewa a Cairo, suna kan hanyarsu ta zuwa asibiti.
Cike da murna da farin ciki ta masa, sannan daga bisani sukayi sallama da niyyar zata kira su idan sun isa, sannan ta kashe wayar.
A nutse ta ɗago ta kalli Sauban. Sai yanzu ta samu damar ƙare masa kallo. Tabbas ta yaba da kyawun hallita da tsarin jiki irin nasa, kana ganinsa kasan bai san wahala ba, sai jin daɗi.
Gyaran murya tayi, sannan tace:
"Duk saboda ɗan uwanka kake ta wannan kai komon?"
Murmushi yayi, sannan ya kalle ta yace:
"Kema saboda ɗan uwanki kika rabu da wanda kike so?"
Murmushin yaƙe tayi, sannan tace:
"Shi ɗin rayuwata ne, shine dalilin kasancewa ta a yadda nake a yanzu, bai taɓa gazawa ba akan al'amurana."
Ta ja dogon numfashi, sannan ta ci gaba da magana:
"Tun ina jaririya, bacci ne yake raba mu. Shi yake goya ni a bayansa, sai nayi bacci zai yi, sai naci abinci shima zai ci, in banci ba, bashi da kwanciyar hankali.
Idan bani da lafiya baya taɓa samun sukuni. A kaina ya rasa scholarship ɗin daya samu daga gwamnati zuwa ƙasar waje.
Saboda a lokacin na samu karaya a hannuna, babu irin maganin da ba'a yi ba, amma taƙi gyaruwa. Saboda ba zai iya tafiya ya barni ba, haka ya haƙura ya ɓata carrier ɗinsa saboda ni."
Take hawaye suka fara zubo mata. Sauban ya jinjina kansa cike da tausayawa.
"Na san kai baka san zafin talauci da wahala ba, amman mun sha wahala bayan mutuwar mahaifinmu. Da ƙyar muke iya samun abinda zamu ci.
A wannan lokacin Yayana bata cikinsa yake ba, ta nawa yake yi, duk yadda zaiyi sai ya nemo min abinda zanci, sai yayi, kuma mai kyau.
Yasha kwana da yunwa, amma ba zai taɓa barina na kwana da yunwa ba. Har zuwa lokacin da ya fara faɗi tashi, duk saboda ni yake yi neman kuɗi, har muka fi ƙarfin buƙatunmu.
Haka ya tsaya min tsayin daka nayi karatu, duk da ina gidan mijina bai taɓa gazawa ba. Sannan kake tunanin zan iya barinsa ya rasa rayuwarsa, bayan ina da yadda zanyi na taimaka masa?"
Ta ƙarasa maganar tana kallonsa.
Girgiza kansa yayi alamar a'a, sannan ya kalle ta yace:
"I understand what you feel Radiya, nasan zafin abinda kike ji. Amma abinda nake so ki fahimta shine, ba wai saboda mutum ya fito daga wealthy or influential background hakan ya na nufin bashi da matsala, ko kuma bai san zafin jarrabawa ba.
Ba haka bane, muma muna fuskantar tamu, may be ma tafi taku zafi. Babban misalin shine akan ɗan uwana, yana neman abinda kuɗi ba zai taɓa bashi ba, wannan shima nau'i ne na jarrabawa."
Jinjina kanta tayi, sannan ta share hawayen da suke zubo mata.
Ɗakin yayi shuru, zuciyoyinsu suna ta saƙe-saƙen al'amuran rayuwa.
Sannan ta sake katse shurun da cewar:
"Kace min ku twins ne. Shima kamar ka yake? Ina nufin...ku ɗin identical twins ne?"
Murmushi yayi, sannan ya kalle ta cike da tsokana yace:
"Kina son ganin ɗan uwana ne?"
"Yes, kuma gashi ko sunansa ban sani ba."
Ta faɗa a sigar tsokana.
Wayarsa ya zaro daga aljihunsa, sannan ya lalubo hoton Sauban ya miƙa mata.
Yana sanye da No. 1 uniform ɗin sa na kakin sojan sama.
Tana ganin hoton ta zaro idonta tare da kama bakinta cike da mamaki, sannan tace:
"Soja ne?"
"Yap! Squadron Leader Muhammadu Sultan, Nigerian Air Force."
Ya faɗa yana kallon ta.
"Wow!"
Abinda ta furta kenan fuskar ta cike da mamaki, sannan ta miƙawa Sauban wayar. Gabaɗaya hankalinta ya tafi akan uniform ɗin jikinsa, sam bata damu da ta ƙare masa kallo ba.
Cike da alamar tambaya ta kalli Sauban tace:
"Kaima sojan ne?"
Girgiza kansa yayi cike da murmushin jin daɗi, saboda ganin yadda ta fara sakin jiki dashi. Sannan yace:
"Kina so kiji labarinmu ne?"
Jinjina masa kai tayi alamar "Eh."
Tana murmushi, wanda hakan ya ƙara mata kyawu matuƙa.
Gyara zamansa ya sake yi, sannan ya fara magana:
"Tun bayan mutuwar mahaifinmu da ƴan watanni muka gama secoundry school. Muna kammalawa Sultan ya shiga aikin soja.
I can remember, the day we left home yana murna, sannan kuma yana damuwar rabuwa dani. Saboda Sultan yana matuƙar son aikin soja, amma kuma bashi da abinda yafi so a duniya sama da ni."
Sake gyara zamanta tayi, ta tarkata hankalinta kacokam akansa.
"Ranar da muka isa Air force base, tun daga gate Sultan ya ɗauki kayansa a kansa ya fara gudu, bai waiwayo ba, saboda kar zuciyarsa ta karaya, har zuwa lokacin da ya ɓacewa ganina.
Nayi kuka sosai, saboda ina tausayinsa, da tunanin wahalar da zai sha. Kin san aikin soja ba ruwansa da family background, gabaɗaya kowa ɗayane a wajen.
Haka na kwana ina kuka, naƙi jin rarrashin kowa, saboda shima na tabbatar haka zai kwana yanayi, saboda tunanina shine, idan ni nayi shuru, to shi waye zai rarrashe shi?
Wannan shine karo na farko da muka taɓa rabuwa da junanmu na tsawon lokaci.
Within one year suka ga exceptional competence ɗinsa a computer operations, sai suka yi sponsoring ɗin sa zuwa China domin ya karanta software engineering. Kin san a dokar aikin soja, duk matsayin mutum ko arziƙinsa, dole su zasu ɗauki nauyin karatunsa.
Bayan ya tafi nima na bishi, we studied together, na karanci international Relations.
After mun dawo nayi taking over family business ɗinmu. Uncle ɗinmu ne ya fara koya min komai before, then after, ya sakar min wasu manyan ɓangarorin da nake kula dasu, a wancan lokacin.
At the same year Sultan yayi aure..."
Da mamakinta ta kalle shi tace:
"Aure kuma, at which age?"
"Twenty Two."
Abinda Sauban ya furta kenan yana kallonta. Sannan yayi murmushi ganin yadda Radiya ta cika da mamaki, sannan yaci gaba:
"Sultan ya shiga aikin soja at 17, ya gama first degree at 22, the same year yayi aure. After one year hankalinsa ya tashi sosai saboda babu abinda Sultan yake so a duniya sama da haihuwa.
A wannan lokacin kuma matarsa Sarah ko ɓatan wata bata yi ba. Hakan ya saka suka fara zuwa asibiti for consultations, daga bisani aka tabbatar da ainahin matsalar Sultan."
Anan yaja dogon numfashi ya kalli Radiya yace:
"Ban taɓa shiga damuwa irin wannan ranar ba, amma da yake Sultan yana da dauriya da tawakkali, haka ya haƙura ya danne. Daga bisani muka fara shirye-shiryen yadda zamu fara binciken mu a sirrince, ba tare da kowa ya sani ba.
Bamu sani ba, Sarah ta fara neman magani a ɓoye, even though, ance mata lafiyarta ƙalau, but, tsakanin son da take yiwa Sultan ya saka bata yarda ba.
Haka ta gamu da wani likita ya bata wani sperm booster wanda ya zama silar ajalinta. Saboda a hankali ya lalata hantarta, a ƙarshe ta rasu, shekara biyu bayan aurensu."
Jinjina kanta Radiya tayi alamar tausayawa. Sannan Sauban ya sake yin ajiyar zuciya ya ci gaba:
"A lokacin damuwa ta sake yi mana yawa, ga ƙuruciya, Sultan ya shiga tsanani sosai, this led him to seek permission domin ya tafi Germany to persue his master's degree in Cyber Security.
Nima nayi applying muka tafi gabaɗaya. A wannan lokacin muka samu dama muka kwantar da hankalinmu.
After we returned, aka ƙara masa girma zuwa intelligence support/ICT operations. Saboda ƙwazonsa akan computer, har mamaki yake bawa hukumarsu.
So bayan nan, muka tafi Umra kafin mu dawo muka tarar Ammey ta yi mana aure.."
Nan fa ya fashe da dariya. Sannan ya kalli Radiya da take sauraronsa, fuskarta cike da mamaki ya bata labarin rikicin aurensu.
Bata san lokacin da itama ta fashe da dariya ba, don ta manta rabonta da yin dariya irin haka.
Sannan ta kalle shi tace:
"Wannan ɗan uwannaka ɗan drama ne."
"Haka yake idan baya son mace, shi fa bai taɓa cewa yana son mace ba."
Cike da mamaki ta kalle shi tace:
"Ya akayi yayi auren fari?"
Want the next chapter?
ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol