Free chapter · Read without an account

Page 15

by AISHA YUSUF HANWA · Gaba Kura

Gaba kura.



   Aisha Yusuf


Page 15


Basu daɗe ba suka yi masu sallama suka wuce. Anan ne Inna Hauwa ta yi musu bayanin yadda suka yi da su. 
 
"Yau dai muna ganin ikon marabbuka, dama kuma su o'o haka ake nema shiyasa kika kasa zama wuri ɗaya jin kun tsinci dami a kala to Adai ƙara bincikawa domin abun ya fara fita a musulunci" Cewar Jamila zuciya cinkushe da wani baƙinciki da hassada. 

"A a Jamila ai mu gaba ta kaimu gobarar titi Jos,  A murnan Amara mu kam, yanzu me muke zaman yi tunda abunda muka zo yi an fasa ai kawai mu sungumi kayan mu koma da su alabasshi mu da muka rako mu ɗiba abunda muke so a ciki kayan katakon kuma a ajiyewa ɗaya daga cikin ƙaññanta kunga an huta koda lokacin na su ya yi Yaya ba shi da haufi".


 "Tabɗijam lallai Allah ya yi wa wasu arziƙin ƙarfin hali wato ku ɗiba ko tunda ance maku sauran abincin da kuka gama lodawa a cikin ku ne ko? To babu wannan maganar hakkin yarinya ce kuma sai mun jera shi ko ba yawa, ya zamana dai za ta ɗaga ido ta kalle su ta yi kuma alfaharin daga gidansu aka samar da su. Ga ɗakin can mu tashi yamma na yi".

"Ai sai dai ke da ƴar taki ku miƙe ai mu da kika ganmu nan ba inda za mu motsa tunda mugun abu ne cinkushe a zuciyarku to ku jera muna jiranku amma mu dai kam ba cas ba as ehe, har kina da bakin faɗa mana magana to ko ita ƴar uwar taki bata isa ba ballantana ke karan kaɗa miya"

Inna Hauwa ta zaburo za ta maida mata da magana Munari ta riƙe mata hannu "Inna ki yi haƙuri mutanen nan har yanzu basu tafi ba suna nan a harabar gidan kada mu bar ma Amina abun magana a dangi dan Allah" Ba tace komai ba suka juya suka nufi ɗakin dan fara kakkaɓe shi.

"Dan Uwarki ni da baki ce na yi haƙurin ba to ba ki ga na mutu ba ƴar banza me kama da maburgin kaɗi" Kyakyacewa Jamila ta yi da dariya tana nuno Munari, ita kuwa kamar ba da ita ake yi ba tunda idan da sabo ta rigada ta saba da halin su.


 A gurguje suka kammala jeren ganin la'asar ta yi nan da nan da biyar ta yi sai dai ka ji kiran sallar magariba. Kamar yadda suka ce suna zaune ba su motsa  ba har suka gama aikin tas suna kallon su.

Sun kafa gado suka saka katifa da mashinfiɗi kujeru dai babu gurin su saboda haka suka roƙi masu motar su maida masu cikin motar tunda su ne za su maida su gida. 

Komai ya yi cas a talauce babu wanda zai kalli ɗakin ya raina masu. Sai da suka gama sannan su Jamila suka shiga ɗakin tsabar hassada idanunta har wani yaji yaji ta ji yana yi duk yadda ta so ɓoye baƙincikinta ya gagara sai da ta furta "Allah Ya sa dai ba ɗan ƙarya bane mutumin nan domin jikina yana bani ba shi da gaskiya, idan kana da gaskiya meye na wani ɓoye asalinka?, Uhm bari na yi shiru kar ace baƙinciki nake yi".

"Na nawa kuma! Ai sai dai kar a kuma"Inna Hauwa ta katse ta.

Ƙarfe biyar suka baro garin suka kamo hanyar likoro kowa cikin shi cike da labarin bayarwa, musamman Jamila da wani kuka ke yunƙuro mata take maida shi tun a cikin gidan, so take sai ta dangana da uwar ɗakin Innayo sannan za ta dage ta shaƙi abunta ko nauyin dake zuciyarta ya ragu.


Ana shiga cikin gari Inna Hauwa ta roƙi direban akan zai kai mata ragowar kayan gidanta ne, shi kuwa tunda an cika masa aljihun shi da sulalla ya ce "Babu matsala". "Bamu gane ba" cewar Guggonsu da Jamila har suna haɗa baki.

Aka ce shiru ma amsa ne; to shi ta musu, hasalima ko kallon gefen da suke bata yi ba, ta dai riga da ta rantse kayan nan sun bar cin shi, kuma ta san indai suka koma da shi to ya tashi a na yar uwarta wannan makirar 
matar gidan za ta san yadda ta yi suka koma hannunta, to gara ko me za'ayi ayi amma kayan ba za su koma ba.


***

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.