Free chapter · Read without an account

Chapter 9

by Ummulkhairi Sani Panisau · ADNAN (The Artist)

ADNAN
Ummulkhair Sani Panisau 
(Khairatup)
Vote @wattpad khairi_muhd.
@Arewabooks khairatup01.

                      09
Abubakar ya bi bayansa suka shiga cikin gida,ya sunkuyar da kansa kafin ya shiga cikin falon.Falon na da ɗan girma kaɗan,yana da tsafta da tsari sun bayyana a falon.Kujerun roba ne a ciki masu ruwan ƙasa an jera su a gefe,a tsakiyar ɗakin akwai ƙafamin tebur da aka shimfiɗa farin zani a kai. A bangon ɗakin hoton ka'aba ne a manne,sai kalandar bankin arewa ta shekarar 1996.
Abubakar ya tsaya a ƙofar falon.Bismillah..."Baba ya faɗa da murya mai cike da nutsuwa. "Shigo mana ka zauna." Abubakar ya taka ciki a hankali,ya zauna gefen kujera a ƙasa."Sunan ka fa?"
"Sunana Abubakar Muhammad Sanda,ranka ya daɗe."
"Ummina tace min kai ɗin Malaminsu ne a FGC da suka gama shin me ya kawo ka?"
"Baba ba da yaudara na zo ba,kuma ba wasa na zo yi ba, na zo ne dan neman izinin fara zuwa wurin Fatima saboda ina son mu ƙulla alaƙa da ita ta auratayya ta zama na har abada." Sai kuma ya yi shiru. Baba ya gyaɗa kansa yace "Shin sana'ar me kake yi?"
"A yanzu haka ina da shago a kasuwa ina saida kayan gini ne sannan ina zuwa aikin gwamnati ma'aikacin banki ne ni,ina aiki da bankin nan na Union Bank."
Baba yace "Ma sha Allah! Shi kenan na baka izinin fara ganin Ummina."
Kamar ya daka tsalle haka ya ji sai ya dake saboda Baba ya sunkuyar da kan shi ƙasa bakinsa ya kasa rufuwa don daɗi da walwala. Baba ya tashi ya fita daga ɗan ƙaramin ɗakin wanda yake a matsayin wani ɗan falo haka na baƙin Baba.
Kai-tsaye ɗakin Inna ya shiga ya yi mata bayanin zuwan Abubakar da kuma bayanin ya ba shi izinin ya dinga zuwa ɗan Zariya ne kuma ya san mahaifinsa yana jin ana maganar sa ɗan kasuwa ne gidansu gida ne na tarbiya ya yarje masa. Inna ta dinga hamdala ta ajiye linkin da yake yi ta shiga ɗakin Fatima. Ta tarar da Fatima a kwance a kan gado hannunta da littafi tana karantawa.
"Tashi Fatima ki je falon baƙin Baban ki kina da baƙo Babanki ya yarje masa ya dinga zuwa wurin ki don Allah ki kula ki kuma nutsu banda rawar kai bana son rawar kai."
A hankali ta amsa da "In sha Allahu Inna zan yi yadda kika ce."
"Allah Ya miki albarka Fatima."
"Amin." Ta amsa haɗe da yafa mayafi ta fita.
*
   Da kwanon sha a hannunta ta shiga ciki ta ajiye masa ruwan kanta a ƙasa ta kasa ɗaga kanta ta kalle shi saboda tsananin kunya da rashin sanin me zata yi. Da ya gaji ya ja kwanon ruwan ya sha ya ajiye yana murmushi yace "Haba Fatiman Baba ki ɗago mana ki kalli cikin idanuna Wallahi Kewar ki suke ki bani haɗin kai na gwada miki yadda kike a cikin ruhi da gangar jikina."
Fatima ta sa mayafi ta kulle fuskarta tana kallon ƙasa Allah Ya sani bata taɓa zama sa saurayi ba sai yau kunya take ji kunyar Abubakar take ji sosai saboda malaminsu ne."
Haka dai ya yi ta zancen shi,shi kaɗai kunya ta hana Fatima magana sam. Ya tashi tsaye ya zaro sabuwar Nira 100 daga cikin aljihunsa ya ajiye mata a kusa da ƙafarta. A lokacin ji tayi kamar ya ajiye mata rabin zuciyarsa ne. Ya fita waje tana ji yana sallama da su Baba ya gaishe da Inna ma.
Ta fita daga cikin ɗakin ta miƙa ma Inna kuɗin.Inna ta karɓa da mamaki tace "Ka ga Alhaji Naira 100 ya bata."
Baba yace "Ki adana ta."
Fatima dai tayi shigewar ta ɗaki ta bar su a tsakar gida.
Baba da Inna a shekarar da ta wuce sun je sun sauke farali a Makka haƙoransa akwai haƙoran makkah na Inna mai gold ɗin nan na Baba Kuwa wannan na silban ne. In suka yi magana ana gani. Ita ma ya mata alaƙawari yace "Da kasuwa ta yi albarka yadda ake so zai kai ta ita ma." Tayi murmushi kawai tana fatan Allah Ya ba shi iko.
Soyayyar Fatima Sani da Mr.Abu ta soma sauya salo bayan wasu satittuka.A lokacin babu waya a gidansu ko wata landline,ba sa yawan magana da juna sai dai aiken wasiƙa haka.
Kamar yau ya zo zance wajen ta. Da littafi a hannunsa ya buɗe tsakiyar ya zaro wata farar takarda sai ƙamashi take fitarwa.
Tun kan ya bata takardar ta ji gabanta ya faɗi. Ya miƙa mata takardar yana murmushi yace "Ba zama zan yi ba sauri nake yi zan yi tafiya ne zanje Legas saro wasu kaya sai an kwana biyu zan dawo ki amshi wannan takardar soyayyar ki karanta kina tunawa da ni." 
Fatima ta amshi takardar tana murmushi ya hau kan mashin ɗinsa ya burga ya yi gaba. Ta dinga juya takardar amma bata buɗe ba saboda bata son ko Inna ta gani. 
Sai bayan ta gama kowanne aiki da daddare kan ta kwanta ta ɗauko wannan takardar a hankali.
Rubutunsa ta shafa sai ta ga kamar zanawa aka yi. Ta warware takardar ta soma karantawa.
Duk lokacin da na zo gidanku,ina komawa gida da murmushi.Idan kika ɗago kai kika kalle ni da idanunki a wannan lokacin kina kashe ni sau ba adadi,kallon ki kaɗai ke wadatar da ni na wuni cikin nishaɗi,son ki nake cike da mutunci da niyyar aure. Ki riƙe wannan wasiƙar kamar yadda riƙe da sunanki a zuciyata.Tana gama karantawa ta rungume takardar a ƙirjin ta,ta sake karantawa sau biyu ,sau uku, sau huɗu sau ba adadi tana maimaitawa saboda abin ya burge ta. Ta sunne kanta a ƙasan filo tana dariya.
Bayan sati biyu ta rubuta masa wasiƙa ta ajiye ta adana saboda tana son ta maida masa martani ta yarda yanzu tana son Malam Abubakar. An kwana biyu kafin ya zo. Ya yi mata ƙiba a fuska sosai ga bashi takarda da zai koma. Bayan ya je gida ya karanta wasiƙar.
"Malam Abubakar na karanta wasiƙar ka. Na ji daɗinta kuma fiye da yadda zan iya faɗa a baki.Amma ka sani,ina jin tsoro.Ba na son a taɓa mini mutuncina ko martaba ta,bana kuma son a taɓa mutuncin ka,idan soyayyar nan da gaske ce kake yin fa ka riƙe ni da daraja."
Tun daga wanann ranar wasiƙa ta zama hanyar gadar soyayar su saboda Fatima ta fi sakin baki a wasiƙa fiye da fili. 
Watarana Abubakar ya je studio don ayi masa hoto ya bawa masoyiyarsa Fatima. A wancan lokacin hoto ba abu ne mai sauƙi ba sai an je studio an zauna a gaban bango mai zane sai a ɗauka a wanke a baka.
Fatima Sale bata nan aka soma wannan bidirin ta tafi Kano gidan yan'uwansu. Akwai wata ƙawar ta Hafsa Sama'ila ita ta raka ta hoto gidan hoto. Ta ci kwalliya cikin sabuwar atamfa ruwan shuɗi ,ta zauna a kujerar roba. Mai ɗaukar hoto yana bata umarni yace "ki ɗanyi murmushi." Ta yi murmushi mai sanyi zuciyarta cike da ƙauna da begen Abubakar. Bayan sati guda hoto ya fito ba ta ba shi kai tsaye ba sai da ta saka hoton a cikin hoton.
_"Wannan kyautar bazata ce ga masoyin da ba zan iya mantawa ba a rayuwata. Domin ka daina kewa ko bege na ,ya saka na ɗaukar maka wanann hoton na baka._
Hoton ya zame ya sa hannu ya ɗauka ya kalla bakinsa ya kasa rufuwa kallon hoton yake yi kamar wani abu mai tsarki.Ya adana hoton a cikin wani littafi da yake ƙauna.
Daga wannan lokacin soyayyarsu ta ƙara zurfi.Ba su taɓa rungume juna ba,ba su taɓa riƙe hannun junansu ba,amma wasiƙunsu sun ɗauke musu komai suna cikin rayuwar su wani zubin ma ya kan yi yawo da wadda ya fi so a cikin aljihunsa,hoton Fatima kuwa yana kusa da zuciyarsa. 
Fatima na kwance ta ɗauko hotunsa da ya aika mata ta kalla da kyau tana murmushi ta shafa sanye yake cikin shadda hannunsa a cikin aljihu ,yana kallon kyamara kamar yana kallon ta ita kaɗai. Soyayar baya babu hayaniya amma akwai jira,akwai hoto,akwai wasiƙu, akwai,zuciya mai kyau da son bautawa masoya akwai haƙuri da juriya.
*

Ranar tayi sanyi bata da zafi. Fatima na zaune a tsakar gida tana tankaɗen garin tuwo. Inna bata nan taje suna maƙota. Aka yi sallama aka shigo ko ba a faɗa ba ta san Fatima Sale ce. Muryarta ta cika gidan.
"Ah! Lale marhabin Fatiti ikon Allah kin ɓace ɓat."
Fatima ta zauna a kan tabarma tana murmushi tace "Jiya na dawo daga Kano ke na ji daɗin Kano garin ya yi fa yanzu ma don ba yadda zan yi ne yasa na dawo."
"Eh sannu uwar son yawo ya hanya?"
"Hanya alhamdu laillai,gajiya kuma ta bi jiki.Yaya Suwaiba ce zasu tafi Potachort aiki shi ne na dawo Baba ya hana a tafi da ni."
"Allah sarki.Sannu fa."
"Yauwa."
"Kin samu labari?"
"Labarin me?"
"An kawo kuɗin aure na."
Fatima ta tashi da kyau tace "Me kika ce?"
"An kawo kudin aurena an sa bikin ma."
"Waye don Allah , yaushe aka haɗu ina ina ?"
"Satin da ya wuce aka kawo."
"Subahanallahi! Wa ya kawo?"
"Mr.Abu."
Sunan ya sauka a cikin kunnenta kamar kururwar iblis kamar kuma bata ji daidai ba tace "Wa kika ce?"
"Mr.Abubakar."
"Ɗan bautar ƙasa?"
"Shi."
Cikin ranta ta ji wani abu ya soki ƙirjinta tunani ta soma "Malam Abubakar mai kuɗi,mai matsayi,ma'aikacin banki kuma ɗan kasuwa... Fatima ta girgiza kafaɗar ta sai tayi fit tace "Wallahi na rasa inda zan saka kaina don murna Fatima ina taya ki farin ciki gaskiya.Allah Ya sanya alkairi! Allah Ya baku zaman lafiya da juna."
Fatima tayi dariya kawai.
Cikin zuciyar Fatima Sale kuwa kamar tayi bindiga ,kamar wuta ta kama haka take ji ta ayyana a ranta anya ba zata shiga ta fita ta hana Malam Abubakar kawo kuɗin auren nan ba don ta jima tana son shi kawai sai yace Fatima Sani yake so bayan duk wannan wahalar sai dai a fili bata nuna komai ba.
Fatima ta durfafi zuwa gidansu Fatima Sani kullum tana hanyar gidan don kawai ta ga zuwan Mr.Abu amma Allah bai taɓa haɗasu ba.
Yanzu ma suna zaune suna hira Fatima ta gyara zama tace "Wai Ummi kin tabbata Malam bai taɓa soyayya da wata yar ajin mu ba ko wata siniyar mu ba? Kin san fa malamai...."
Fatima tace "Hmm! Ke ma kin san ai za a so shi kuma ko ya yi dasu baya ne yanzu nice yake so ba su ba na yarda da shi ai zuciyar namiji don son mace aka yi ta." Ta ƙi bari kalaman Fatima su yi tasiri a cikin zuciyar ta. Ta sani idan ta biye wa ance-ance tabbas ƙwayar shakku z ta fara shuka a ranta. Tana tuna lokacin da Malam Abubakar ya kawo kuɗin auren ta cike da alfahari da yadda mahaifin ta ya yi farin ciki da yadda Inna ta dinga jera hamdala tana sanar da maƙota da abokan arziƙi,sai ta kulle ƙofar duk wani zargi a ranta.
Fatima Sale kuwa kamar tayi hauka kishin Fatima na cin ta a rai idanunta sai rawa suke yi sai tambayar kanta take yi "Me yasa ba zai ce ita yake so ba? Me yasa har yau ba mai zuwa gun ta da niyyar aure? Daga wannan lokacin da ranar ta sa a ranta ba zata bari ayi auren Abubakar da Fatima ba.
*
"Ka nemo aure daga babban gida kam ka kyauta Allah Ya yi maka albarka banda shaidar arziƙi babu abinda yarinyar nan Ummi ke samu na ji daɗi sosai Abubakar fatana kar ka bani kunya ka riƙe amana ka kula da kyau duk wasu kalle-kalle da neman magana da kake yi ka sauke su Abubakar ba na son wannan tara yan'matan tuni na gaya maka yau ma zan maimaita maka."
Kansa a ƙasa ya shafa ƙeyarsa yace "In sha Allahu Abba ba zaka same ni da ɓata maka ba ina son Ummi sosai Wallahi."
"To ai na ga alama tunda ga shi ka sayar da kunyar a gabana kake faɗa kana son Ummi."
Abubakar ya yi dariya ya miƙe tsaye ya shiga cikin gidan ,Abba ya bi bayansa da kallo yana gyaɗa kai fatansa hanyar shiriyarsa ce ta zo don baya son wannan tarin yan'matan da yake da su don ranan yana zaune a tsakar gida wasu mata suka zo wai ganin Mr.Abu abin dai bai basa daɗi ba shi yasa da ya ji labarin yana son ya yi aure ya shige masa gaba.
Dama shi Abubakar mutun ne mai farinjinin yan'mata sosai, ba kuma ya son wargi zai kalallame mace ya ɗaureta ta yadda ba zata iya fita daga cikin ƙaunar sa ba ya sa ta a shingen sa ya yi mata dabaibayi kuma ya zo ya bar ta da ciwon rai. Sai Allah Ya sa masa ƙaunar Fatima Sani a ransa kamar me duk wata mace ya bata red card baya kula su. Mahaifiyarsa ta rasu su biyu rak ta haifa da shi da ƙanwarsa. A gidan sai matan baban shi su uku ris su talatin ne yaran babansu dai duk yan boko yan kwalisa ana wa gidansu lakabi da gidan farare don a cikin gidan kam Ma sha Allah! Allah Ya basu fari Adda Zainab da Hamma Sharif ne ma masu ɗan duhu a cikinsu sai dai cikinsu shi Abubakar ɗin ne tabarkallah in ka kalle shi sai ka sake kallon shi.
Matar baban shi Iya Zulai ta juyo tace "Ka ga angon kwanaki kaɗan lale."
Ya yi murmushi ya tsugunna yace "Hajiya Iya ikon Allah tauraruwa mai haska zuciyar Abba."
Ta kama haɓa tace "Kai kam wayewar ka tafi ta kowa a gidan nan ni za ka sa a gaba kana wa shaƙiyanci?"
"Tuba nake Hajajju."
Daga cikin madafi kuwa Hajiya Iyye uwargidan Abba kenan ta fito hannunta riƙe da fulas ɗin abinci da alamu Abban za a kaiwa ɗaki.
"Barka da yanzun Hajiya."
Ta ɗan kalle shi ta taɓe baki tace "Barka." Bata tsaya ba ta shige ciki. Shi ma bai bi ta kanta ba inda sabo ya saba don ya sani ba son sa take ba.
Sama ya haura ya shiga cikin ɗakinsa. Ya cire kaya ya zauna daga shi sai singileti ya kwanta yana kallon sama. Ya sani yana son Fatima sosai kuma ba zai iya barin ta ba tana da kunya,tana da aji,ta na da sanyi da ladabi da biyayya wanda su suka sake sawa ya ji baya kamar ta a duniyarsa.
An soma shirye-shiryen bikin suna zaune a ƙofar gida, kan tabarma. Iskar maraice na kaɗawa a hankali , ƙamshin ƙasa na tashi ya haɗe da warin daddawa da ke tashi na girki.Abuhakar ya jingina da bango,yana sauraron hirar da ake cike da nutsuwa,yayin da Isma'il abokinsa na kud da kud ,ke ta jujjuya carbi a yatsunsa yana murmushi. Fatima ta sunkuyar da kai tana wasa da yatsunta. Fatima Saleh ta matsa kusa da Fatima tace "Yanzu me aka yanke ina ga iya kamun ya wadatar ko?"
"Uhm." Tace kawai bata mayar mata da amsa ba.
Isma'il yace "Ai duk za ayi bikin Sarki ne fa da sarauniya."
Suka yi dariya duka Abubakar yace "Baiwar Allah ce Kamu kawai zasu yi da yinin biki yadda dai al'ada ta tanadar."
Abubakar ya basu kudi don lalle da siyo zanin anko. Abubakar da Isma'il suka miƙe zasu tafi ya tsaya ya kalle ta yace "Ko ba komai ina son bikinmu ya kasance abin kwatsnce da tunawa,aure mai sauƙi mai albarka." Suka rabu suna raha.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol