Free chapter 路 Read without an account

Chapter 39

by Fatima Rufa'i Nasidi 路 AYSAM

(The grief of losing my whole) 40 day's later. Kwanaki sun shude anfara maganar wata ayaudin Alh Alhassan Abu Jandal yacika kwanaki arba'in da rasuwa garden din yayi tsit adaren rnr gidan jikake yi kmr anyi yasa bayan kwashe kwanaki kusan arba'in ana xaman makoki after sadakan arba'in muhsin ganin mutane sunsamu guri basuda niyyar tafiya yasanya yanade carpet yace yasallami kowa da kowa su xasu koma rayuwarsu , adaren yaune kuma alqali da barr jarma suka qaraso gidan danbatun rabon gado wannan yasanya duk wani meruwa da tsaki cikin gadon Alh Yahalarci gurin, barr ne yay gyaran murya yana fadin "toh da bismillah xamu fara amma wani hanxari bagudu ba someone is missing here," muhsin ne kekallon sauran yan uwansa nagurin yana fadin "kowa yananan xaka iya farawa," turo glass din sa gaban hanci yay yana fadin "nooo,banga baby girl ba," muhsin dan dafa kansa yay kafin yace "I'm sorry barr nixan wakilci dimple daga yanxun kasan bata cikin state din daxata iya fitowa ba,i think she need a real psychiatrist,she has lost herself completely," anwar cikin jin haushin furucin dan uwannasa akan dimple yake fadin "no she's OK, she'll definitely be ok, kasan menene yake sata feeling ok amma duk da halin datake ciki kamasa katanga daga zuwa gareta batawa kowa magana batacin abinci kullum se tea bata bude dakinta kullum akulle bata kuka bata dariya and the last time she spoke she open up to sameer kasanda haka ko, so kake taqara yunqurin commiting sui....." "shut up" cewar muhsin yana daka masa tsawa,yamiqe yana kallonsu duka yana cigaba da mgn i thought munriga mungama wnn mgnr duka taxama fast ba sameer ba dimple acikin gidannan idan kuma naji wani yaqara kiran koda sunansa ransa xeyi mummunan baci, anwar miqewa yay yana wancakalar da kujerar gefensa yay gaba yana huci yanaji muhsin na kwala masa kira yadawo yay masa banxa. ahaka daixaman yatashi sbd rashin halartar dimple da anwar abubuwa dayawa sunfaru bayan dimple tayi yunqurin committing suicide seda tai satittika a hospital bayan tasake yunqurin yanke jijiyar hannuwanta da temakon sameer da anwar suka kamata takasa aikata hakan sbd maganganun sameer din dasukai tasiri aruhinta, "kina tinanin inkika kashe kanki popsy xetaba alfahari dake a rnr gobe qiyama xaki fitone atutar asararru wanda basuda cikakken imanin yarda da qaddara, dimple Allah ne yarubuta hakan arayuwarki kidena abu kmr wacca bata xuwa makarantar islamiyya kinsan idan kika kashe kanki wuta xaki tafi dimple kuma popsy baxeso kiyi mummunan qarsheba irin haka, dimple idan kikatafi yaxanyi da rayuwata i cannot live without you," yafada mata yana xubda kwalla, "toh sameer yaxanyi yatafi bayan yamun alqawarin baxe taba tafiya yabarni ba why did he live so early nibansan yajja xanfara rayuwa batareda popsy ba, shine rayuwata sameer shine komai nawa shine jinin jikina da numfashina,idan ina shaqar oxygen natina popsy bayanan sena ringa feeling suffocating,sameer yatafi yatafi" taqarasa tana kifa kanta agadon asibitin batareda taxubar da kwalla kodaya ba nan yacigaba da lallabata har tasamu tafara kuka metsuma xuciya tayi kuka mexafi wanda shine xaman lpynta wnn kuka datai yabata peace of mind, tundaga wnn lokacin tadena mgn dakowa se sameer shikansa se yayi mata goma iya kacinta uhm,ko un-un,hakan yasa yaxage kullum yana hanyar xuwa hospital gurinta muhsin bece musu komai ba kuma behanashi ganinta ba harse rnr da Alh dikko da mal sufyan sukaxo yimusu ta'axiyya rnr da mal sufyan yay danasanin xuwansu Abuja, ummi ce takira muhsin takanas duk da bawani shirin arziqi sukeba, taqulla masa cewar idan yasake yasakarwa iyayen sameer fuska ayaudin xasu dauka kmr har yau da mgnr auren tanason shida muhassin already tayiwa sooraj mgn shima daman bason abin yakeba suyiwa iyayen sameer tarbar wulaqanci suyi musu rashin arxiqin dasuka ga dama, kallonta yay yana fadin "ke meye kuma hadinki da iyayensa daxakice muci masa mutunci," kallonsa tai tana fadin "banason aurennan duk da shima Arsal din bawani qaunar hadin nakeba gara ta aureshi akan taqare acikin xuri ar matsiyata," agurin yamiqe yana barinta besanar da kudrat komai ba lokacin datake sanar masa xuwan iyayen sameer din yasan idan tasan mesuke shiryawa tabbas xata sakashi agaba da wa'azi ga sabuwar rigima data koya don taga yana nannan da ita idan har tanason abu toh dole yayi ko yanaso ko bayaso tanada influence akansa yanxun sosai sbd wani gurbi daya bata namusamman acikin zuciyarsa. Alh Dikko da mahaifin sameer sunqaraso gidan ana tsakiyar makokin, muhsin naxaune tareda baffanshi sooraj suna hirar kasuwancin, sameer na asibiti gun Aysha besan wainar da ake toyawa ba bisa jagorancin Samar wanda yarakosu har gidan suka qarasa Alh dikko yana washe baki ana gaggaisawa da jama'ar gurin daman shi mahaifin sameer miskiline ajin farko wanda beshiga harkar da babu ruwanshi, Alh dikko ketambayar ina yaran nasa suke sudin surukan Alh ne, ababban parlour da muhsin yake aka rakasu,muhsin yayi musu wani kallon sheqeqe lokacin dasuka qaraso sunai masa ta'aziyyar addu'oin dasukaima popsy kadai ya answer ciki ciki, muhassin kam ko sauraronsu beba yacigaba da danna wayar sa, Alh dikko ke kallon muhsin cikin dan yaqe da kallon banxan da yake masa yake tambayar "ina yarinyar take Allah sarki arakamu gurinta muyi mata ta'axiyya mudin iyayen sameer ne," muhsin yadago yana fadin "and so," Alh dikko dabaya daukar wulaqanci ko kadan ahankali yake controlling temper dinsa tun shigowarsa yafahimci yaran sam basu dakko dattaku da kyawawan halaye irin na mahaifinsu ba ko dakallon wulaqanci dasuke binsu dasu, Alh dikko cikin kakkausar murya yake sake maimaita "mudin iyayen sameer ne wanda xe auri aysha,wnn mahaifinsa ne mal sufyan nikuma amininsa ne," wani killer smile muhsin yasaki yana kallonsu yamiqe tsaye yana fadin " malan naxata manya sunfi yara hangen nesa koh,ashe bahaka bane duka rashin kunyarku da rashin tinaninku irin nasa sak, ku kalli fadin gidannan kaf ai ina tinanin ko maid din tatake wa dimple goge goge tafi qarfin danku mara kunya yakalla yace yanaso ballantana har ku kwaso qafa kuxo waiku ta axiyyar suruki," muhassin yadora da "dude wai bakasan shidaman talaka bashida kunya ba,idan kunshanye popsy yayarda da shirmenku mudin munfi qarfin maytar fulani wllh," anwar dasauri yaqaraso yana fadin "ya muhsin meye haka muhassin harda kai" wani kallo muhsin yawatsa masa yana fadin "get out of my side before nai losing temper dina kuma kai gaggawar cemusu subarmin parlor kafin parlor nayadauki qaxamin stink dinsu," mal sufyan ne yafara miqewa Alh dikko da kaf rayuwarsa ba ataba cin xarafinsa kmr yauba qamewa yay axaunen dayake dan cikinsa kefada masa wadannan mugwayen kalaman, irin wnn yaguda tun farko sedai bayan haduwarsu da Alh xuciyarsa takwanta yayi tinanin komai xexoda sauqi tunda har mahaifinta yasan darajar mutane ashe yaransa basu gajeshi ba, miqar dashi mal sufyan yay don yasan xuciya irin ta aminin nasa yanxun idan basu fita ba xa'a iyayin batacciya, sunkai daf da bakin qofa sooraj kefadin "wait" basu jiyo ba sedai suntsaya chak takowa yay yaqaraso yana facing dinsu kudi yaxaro a aljihunsa naira dubu dari uku yajefo kan fuskarsu yana fadin "kudin xancen da kuka kawowa Alh ne dubu dari harda riba duk munbaku bama buqatarsu kunaji kuma daga yau karmu sake ganin qafar ku acikin gidannan,mum raba auren baxamu bayarba shi darajar wanda kukeci yatafi" Alh dikko ne yajuyo xefara masifa da sauri mahaifin sameer yajanyeshi suka fice daga parlour sukabar kudin xube nan, yana huci suka fita yana fadin "fillo dakabarni nafada masu wacca xata kwana tanai musu ciwo arziqi haukane koshi AJ haka sukaga yana yi marasa kirkin yara,kmr jira suke daman, Suji ance babu idon bawan Allah,ai shikenan yarinyar nan ko huril aini ce muma danmu baxeyi aure cikin gidan rashin tarbiyya haka ba," Samar ne yadauke su, mal sufyan yake tambayar sa 'ina sameer din?" yace " ai yanacan asibiti ayshan ce bata da lpy yana tareda ita," cikin baqincikin abinda akamusu Alh dikko kefadin "kaji ko sunmaida shi dan aikinsu ma memusu jinyar ya shikuma sunyiwa nasa iyayen rashin arxiqi muje sena cimasa mutunci idan da halima sena tasashi gaba munkoma tare," imperial suka nufa duka shi mal sufyan takaici ma yahanashi magana tsabar jin xafi kuma yaquduri aniyar raba dansa dawadannan yaran tunda dai wanda yariga yahada yarasu kuma yaga basa mutunta mgnrsa ko hukuncin da yayanke. VIP ward aka nufa dasu dake gurin sunsan Samar sosai kusan kullum shiyake xuwa yakai lilly ko yadawo da ita gurin kakalla kace wani babban hotel ne tsabar tsaruwa duk da ba awani cika masa kyale kyaleba amma gurine me tsari na ajin farko awaje suka tarar dasu lilly sunyi jigum jigum kowacce kakalleta tayi dan wiya kaika rantse kace suma jinyar suke, samar ne yay introducing din su matsayin iyayen sameer suka gaishesu cikeda mutunci da mutuntawa bayan sun tambayi yame jiki, meenah ta answer da "da sauqi alhmdlh," alh ne kefadin "ina sameer din" lilly tace "yana ciki tare da ita," cikin dan jin nauyi yake fadin "akira musu shi xasu wuce" dan jim lilly tai don tayi tinanin sunxo su duba aysha ne sumata ta'axiyya,lilly tace "naxata ko xa'ai muku iso ne ciki baba itama ayshan idonta biyu ne" yace "ok ba matsala" yana kallon mahaifin sameer dayay masa alama da bakomai,shiga tai jim kadan se ga sameer nan yafito shikansa yarame sosai se tsayi ga fuskarsa tayi wani mugun haske idanuwansa sun kumbura alamun rashin samun barci ishashshe,gaisheda iyayen nasa yay yana me musu iso da su shigo ciki ahankali suka tura dakin tana kwance lilly tadan yafa mata babban veil akanta fuskarta kmr jaririya tayi wani irin smooth bakin yabushe duk takode, qoqarin miqewa tafara yi lokacin data hango sunqarasa shigowa dakyar tatashi xaune yajja taga sameer nagaida manya yasanya itama take qoqarin tsugunnawa ta gaishesu Alh dikko tausayin qaramar yarinyar yakamashi lallai dole alh yaqaunace ta ita kadai kejin mutuwarsa wadancan daman kmr jira suke, yana tina maganganun mahaifinta lokacin dayake basu ita, sosai xuciyarsa takaraya da kudurin tafiya da sameer din ayau, Alh dikko kefadin "sannu aysha base kin duqaba keda kefama dajikin ki tashi kixauna kinji aysha," cikin sanyin muryar da ayaune lilly tafarajin tayi mgn tunbayan mutuwar take fadin "ina yinin ku,ya hanya" akanta aqasa,mal sufyan kansa yarinyar ya qara yaba da hankalida nutsuwarta da alama itace tayo halin mahaifinnasu sede kash itadin macece bata isa ta aurar da kanta ba, ansa gaisuwar nata sukai suna tambayarta yajiki dakuma qarin haquri lumshe ido tai hawaye na bin kuncinta tace "da sauqi alhmdlh," Alh dikko kefadin "Kidena kuka yarnan Allah yajiqansa,Allah yasa ya huta yasanya shi cikin rahmarsa,kiqara haquri kinji ayshatou komai me wuce ne" jinjina kai tai tana jin dadin adduar dasuke yima popsy, sameer nagefen ta zaune karo nafarko daya qarajin alfahari da xaban ayshan matsayin abokiyar rayuwarsa aduniya ba abinda yafiso da qauna irin mahaifansa wnn girma data basu taqara siye xuciyansa, hawayene suka cigaba da gangarowa daga idanunta tana rufesu gaba daya, mal sufyan yace "muxamu wuce koh," lilly tace " baba har xaku wuce," Alh dikko yace "toh yaxa ayi yannan yamma nagabatowa kuma bakwana xamuyi ba," tace "toh baba mungode Allah yasaka da alheri" ya amsa da bakomai,juyawa sukai karo nafarko aysha tasakarma Alh dikko murmushi tana musu fatan isa lpy, wani irin dadi sameer yaji yamamaye shi yajuya yabi bayansu don rakasu harbakin qofa mal sufyan ne yatambayi yaushene xa'a sallami ayshan daga hospital yasanar dashi cikin satinnan in Allah yayarda, yace "sameer rnr da aka sallamota kaxo gida ina nemanka," jim yadanyi donshi inso samunsa yakasance tare da ita har seta soma dawowa rayuwarta ta dede amma bayajja xa'ai yay musu da mgnr baffan nasa" da toh ya answer masa basu sanar dashi wulaqancin dasu muhsin suka musu ba haka suka kamo hanyar dawowa kano. Adaren rnr sameer naxaune gefen aysha ta kashingida tana kallonsa,yaxauna kan stool din gefen gadon riqe da novel yana karanta mata tana sauraronsa duk aqoqarinsa nasata tamanta da halin da take ciki, Wuthering height yake karantamata yasan it's one of her favorite's although s he's not very fan of fiction work's, don yafaranta mata yake karatun kuma tana jin dadin effort dinsa akanta domin dabadan sameer dasu lilly ba batasan ya rayuwarta xata kasanceba yaya anwar ne kadai cikin ahalinta kexuwa duk dare yadubata amma ummi tunda tafarfado sau daya tak taganta taxo shima da qawayenta su haj salma dubata daganan bata qara ganinsu ba ballantana yaya muhsin ko muhassin,hudallah cema ke xuwa jefi jefi. hudallah ce tashigo dakin dauke da murmushi afuskarta hannunta riqe da favorite's orchids din dimple taqaraso tana rungume dimple ajikinta xata bata air kiss tadan kauce tana basarwa this day's haka suke keeping cool relationship atsakanin su bagaba bahantara hudallah kewani mugun shige mata itakuma daman can ba agabanta takeba balle ace, dan basar da yarfin da dimple tai mata tai tana fadin "kace little sis tafara samun lpy,ga favorite rose dinki nakawo miki,get well" Qarda tai tana ajje flower gefen gadon, "hudallah tadorada "haka nakeso Allah yaqara qarfin jiki," sameer ne ya ansa mata da " ameen" yana sake tambayar ta qarin haquri kallonsa tai kafin tace "da muhsin AJ fa mukaxo yana waje" yace "kaje kasameshi" dan jim yay kafin yace "yayan aysha kuwa" tajinjina kai alamun eh, kallon aysha yay yaga itama takalleshi ahankali yamiqe yana fadin "love bari naje naga lpy ko,I'll come back for you," dan kwabe bakitai alamun shagwaba tana kallonsa yaje yatsugunna gefenta yana fadin "menene kuma?are you OK,ko karnaje" girgixa kai tai alamin a ah yace "speak pls, you always tell me you don't like body language, I also don't like one,I want word's" dan smiling kawai tai wanda shikadai ya iya shedashi sbd qasa qasa tayi shi cikin sanyi da rashin kwarin jiki taxauna, "please come back soon, don't live me here all alone," yace "don't worry Aysh, yanxun xandawo and your not alone hudallah will stay here with you ko?" yafada yana kallonta duk da talurada wani mugun attitudes da sameer din kebata kwana kinnan tun fadawa dimple mgnr rashin lpyr popsy tsaki taja qasa qasa, kafin afili tace "of cause darling I'll always be here for you" ko kallonta dimple batai ba har sameer yamiqe yafice daga dakin, Acikin motar sa yasameshi yabude murfin motar Ferrari 296, yaxiro qafa daya yana danna waya, seda yaxo daf dashi duk da tun tahowarsa yaganshi yabasar, Shima sameer din dake sarkin misqilanci qarasowa yay gefen motar yacake domin sam jininsa dana yaya muhsin be haduba haka kawai domin da badan yaci darajar kasancewarsa dan uwan dimple ba daba abinda xesa ya answer wnn kiran ciki ciki yake fadin "barka da yammaci," muhsin yadago yana kallon sameer tundaga sama har qasa kafin yadanyi smiling jijidakan yaron na matuqar burgesa da bashi mamaki yafahimci baya qaunar raini ko kadan daya fuskanci shi muhsin dan wulaqanci ne duk abinda xe hadashi dashi kaffa kaffa yake dashi, fitowa yay amotar gaba daya yana jingina jikin bayanta yarasa gane meyasa bayason kallon cikin shudayan idanuwan wnn yaron wani irin kwarjini suke masa dako wani abu yay niyyar fada mara dadi yana kallon wadannan idanun na sameer se yaji shakka, dakewa yay ganin idon sameer aqasa yake daya dago, "kai iyayenka basu fada maka saqon dana basu su baka ba," Yatambaya,dan kallon muhsin yay alamar iyayena Kuma yace "eh iyayen ka kake kallo na kmr wani sa anka,mara kunya," yarasa shi wace rashin kunya yay wa muhsin da akullum yake kiransa dahakan, muhsin ne yadora "da alama aikena beqaraso kunnuwanka ba ko qila basu da xuciya ne,kwada yayyu" axabure sameer yadago yanajin farucin da muhsin keyi game da iyayen shi yace "eh nafada marasa xuciya ainayi tinanin adaren yau zasu juya dakai kano sekuma naga saqona bexo ba daman ance xuwa da kai yafi saqo koh,toh naxo nai maka mugun gargadi kmr yajja naiwa iyayenka kan kafita daga sabgar aisha salin alin kagama ta karatunka kakoma garinku idan ba hakaba, I'll destroy you" sameer rintse ido yay kawai daman tun farkon ganinsa da muhsin yasan cewar baya qaunar shi amma shiwana irin mara tausayi ne daxece yarabu da aysha awannan gabar lokacin datake buqatarsa fiyeda komai arayuwarta, muhsin cikin quluwa da shirun sameer din yake fadin "nagayawa matsiyatan iyayenka mgnr datafi wnn xafi adaxun nasa an mayar musu da kudin aurensu duk da sunqi karba although nasan ana buqata daman quri akai aka bayar toh munmaida maku harda riba,aysha ba matar ka bace tunda taxo duniya nasan cewan fate ya hada sunanta dana Arsal,he's good for her matsayinsu yadaidaita kaikuma tafi qarfinka don haka if you have some dignity left" idan kafita daga hospital dinnan karka sake dawowa ba cinmutunci daya masane yay masa ciwo ba furucin nagaya ma matsiyatan iyayen mgnr datafi wnn ce tatsaya masa aqirji yasan halin baffa sarai bayason wulaqanci shiyasa yake rayuwarsa baruwansa dakowa cikin amincin Allah, balle kuma Alh dikko daya gama sanin yajja yake jida kansa bawanda ya isa yaketa shi be ramaba yau shiyayi sanadin kawo baffa gurin da xa amasa wulaqanci idan har bebar gaban muhsin ba toh tabbasa se ya iya xubar masa da haqoransa nagaba idan ba ai sa a ba duk qimar dayake bashi tarigada taxube cikin qanqanin lokaci, baffa kenan shiru yay masa kawai koh shine nemansa dayake yi, tabbas baxe juri hakan ba da baya da baya yasoma tafiya yana barin gurin muhsin da yajuya yacigaba da mgnr beyi aune ba yana juyowa yanemi sameer yarasa tsaki yaja yana fadin "yagudu kenan yakasa jurewa" ya murmushi,wayarsa yaciri yana danna number Arsal tana ta ringing se can yadaga yana fadin "muhsin" cikin sassanyar murya yace " hey dude yane wai duk mutuwarce har yanxun bata sake kaba ko xaman makoki baka xo anyi dakai ba" yace "dude yanxun haka Ina NYC abubuwa dayawa sun dagule mun ankama kayayyaki na a border sun tsareni anan baxan fita daga garinba harse sungama bincike, dude shune akaimun wllh wata biyu dasuka wuce suka fara targeting kawai nashigo suyi ram dani ga kudaden gurina daxan yi dan hasafi asakarmun duk sunqare" yace "Eyyerh Arsal, sorry kaji kaima meya kaika fita a Nigeria awannan yanayin aida baka komaba kasha badai suyi arresting dinka bako," yace "yah basuyi ba kawai dai garine baxan bariba konan da Nevada fa barasu bari na leqaba," yace "dude karka damu aikai nawane akwai kaya aqasa masu nauyi nagaske" yace "kai kace Allah" yace "ina fada maka,kasan yajja xakai kawai kasiye xuciyar dimple sharar datake gefenta duk natattare naxuba a bola kuma baxata qara dawowa kusa da ita ba,dude old man yabar kaya masu inganci baqarya xamu fantama" yace "dude I love you shiyasa nake matuqar sonka" yace " karka damu kayi wuf da ita kawai kasan nayi approaching lawyer kan rabon gado yacemun it will at least take a year gurin tattara dukiyoyin popsy duka guri daya musamman na overseas, dude nakusan xama billionaire kafara mun biyayya" yace "ah ni waneni tun tuni ma," dariya yay yana soma komawa cikin hospital, "kmr nawa kake buqata" yatambaya yace "it's much fa almost 500m USD" Tsaki muhsin yay yana fadin, "iyasu kenan,I'll transfer it yanxun kyauta ba bashi ba tukuicin kulada ni lokacin danake gidanka a NYC," chakawa Arsal yay daga daya bangaren yana fadin "nikuma I promise you I'll continue taking care of you,idan natashi dawowa xandawo maka da the strongest marijuana ever," "no,no,no" muhsin yafada daga nasa bangaren "dude I don't do drug's any more baby tahana" cikin kaduwa da tashin hankali, yake fadin "wace babyn wai wnn qaxamar yarinyar," cikin dan jin xafin mgnr tasa yake fadin "pls arsal is all in the fast matatace fa yanxun uwar yayana maman babies dina,I thought kaima kanaso nai quitting harkar koh?" cikin dan rudewa Arsal ke tambayar muhsin "did you suddenly fall for her?," dan smiling yay yana jingina da qofar dakin da aka kwantar da aysha ya lumshe ido yana fadin "dude she's good to me,she's all I got right now I just don't know how ?when?where? i just fell head over heels for kudrat bansan meyasa ba," fargabar Arsal qara ruwa tai jin furucin muhsin lallai dole hudallah tasani seda muradinsu najuya qwaqwalwar sa yake daf dacika kudrat na neman wargaxa musu shiri basason muhsin yataba nutsuwa yadawo cikakken mutum basa qaunar hakan har abada, jan numfashi arsal yay yana fadin "that's good to here nixan koma office sena jika koh," "toh" ya answer masa dashi yana fadin "I got your account number daman,' dakin yatura yashiga yana fadin "my little sis big brother is here" dimple data dan kwanta tana jiran dawowar sameer dasauri tadago tana kallonsa sekuma takoma don tayi tinanin sameer dinne, yace "sannu koh" yana shafa kanta "we are going home tomorrow nasan kingaji xasu sallameki seki qarasa warkewa acan duka" dube dube tafara yi adakin,hudallah da tun bayan shigowar muhsin ta ajje wayar tana kallon indayake,kafin tace "a ah ina kuma sameer din yake wani mugun kallo yabita dashi yana fadin "ai a aljihuna nake yawo dashi ko," aysha ce takafe su biyun da ido batareda takawo komai aranta ba takoma takwanta tasa aranta qila yanxu xeje yadawo, ahaka tanajin firan muhsin da hudallah har barci me nauyi yadauketa sakamakon allurar bacci da likitan yasake mata. sameer dasauri yaqarasa hostel yana qara danna number baffa tana ta ringing be dagaba duk yajja xaai he has to sort all this things tabbas dole yasan kalaman daxeyi amfani dasu gurin bawa su baffa haquri indai har yanason ganin daidai arayuwarsa shikuma batun rabuwa da aysha yasan baxe taba iyawaba koda muhsin xesa wuqa yasoma yagar naman jikinta, itafa amana ce agareshi ayanxun data rasa popsy mesuke so tareda itane dasuke yunqurin tarwatsa mata farincikinta, harhada kayansa ya somayi daren rnr kwana yay ko rintsawa beyiba yana saqa da warwaran abinda kuma xebiyo baya bayan bijerawa mgnr koma waye ba yaya muhsin kadaiba akan mgnr rabuwa da aysha. Ahankali tabude idonta tun tana ganin dishi dishi har ganinta me haske yasauka akan kyakkyawar doguwar fuskarsa me tsananin haske, murmushi yake mata taqureshi da ido tana kallon kyawawan features din fuskarsa, "good morning" yafada yana miqo mata mug din coffee dake hannunsa smiling tai kadan kafin tamiqe tana soma tafiya don daman bawani mgnr arziqi take yiba, yace " Aysh ina kuma xakije yanadan tabe fuska" irin yajja take masa juyowa tai takalleshi asanyaye take fadin "I want to brush my teeth," smiling yasake yi yana fadin "inxo nataya ki?" kafada tamaqe yadan sosa kai yana fadin "dakin bari nayi miki ai," girgixa kai tai tashige bathroom tana dan murmushi, yana xaune har tafito ta sameshi anan takalleshi da dan mamaki tana kallon jakar goyon da ya ajje gefen gado me dan girma, yana gani tana kallon jakar yasan neman ba asi take yace "I'm sorry banfada miki ba xandanje gidane,na jima banjeba i need to sort something's," yamutsa fuska tai kafin tasoma hawaye,yace "please aysha kidena kuka inkina kukannan xuciyata xafi takeyi, kibari pls," tace "kaima tafiya xakai kabarni kamar yajja popsy,yatafi,sameer mutuwa xanyi" dasauri yarufe bakinta da tafin hannunsa ahankali kafin yace "baxaki mutuba aysha please stop it,shima popsy lokacin sane yay kuma Allah yarubuta lokacin tafiyarsa xeyi Aysh dina baxamu mutuba in sha Allah har se randa Allah yarubuta lokacinmu yayi kinji," tace "toh nidai sameer karka tafi kabarni," yace "xandawo in sha Allah it's very important ne dolene dabe xama dole ba ba abinda xesa natafi nabarki,kodai nasaki a pocket dina mutafi tare" girgixa kai tai tana dan chuckling softly,handkerchief yaciro yana goge mata hawayenta kafin yace "I'm thinking of name daxansawa brand din shagonmu babe,mexamu sa" turo baki tai tana fadin "nima bansani," cikin raha yake fadin "shall I use our secret code AYSAM if you permit" danxaro ido tai tana fadin "what?noway,it's my name ninaqi," yace "please please" kmr yaron dake roqon abashi sweet,sosai yajja sameer yakoma kwanakinnan ke burgeta duk da shi alallai so yake yadawoda ita rayuwartata baya wacca tasan har abada baxata qarayin kwatan kwacin taba sbd babu popsy cikin ta, "OK,OK nayarda" tafada tana sipping coffee din miqewa yay yana rataya jakarsa ahankali yake fadin "I'll miss you so much Aysh," lumshe idonta kawai tai tanajin kmr kada yatafi yabarta tana bude idonta taga fuskarsa daf da tata harta na iya jin hucin numfashinsa idanuwanta suka fifito waje, tana kallonsa cikin sanyi kmr rada yake fadin "I love you," kalmar wani irin mugun tasiri take dashi acikin gangar jikinta da ruhinta tana kallo yafara ja dabaya yana daga mata hannu yana murmushi har ya isa daf daqofa yamurda yafice, ahankali tasauke numfashi tana komawa xata kwanta kewarsa nasoma mamaye zuciyarta, qit taji anbude qofar tadago sameer ne yaleqo dakansa dakin yana fadin "did you already started missing me AYSAM" sosai lamarin nasa nayanxun kebata mamaki da qayatar da ita sweet side dinsa se qara fitowa yake,tace "SAAAAAAM," Yace "OK OK,tunda baxaki fadamun ba xanfadama kaina da kaina,bye Sam I'll miss you too i love you y" aqarasa yana blowing kiss to her. sosai tasoma murmushi har yafice tanayi. wnn kenan kwanaki nata shudawa sessions din makaranta seqara nisawa yake cikin sameer da aysha bawanda yake xuwa makaranta tun tafiyarsa kano bata sake koda mgn awaya dashiba tun abun baya damunta har yasoma taxama wata irin muguwar introvert kullum tana cikin daki bata mgn dakowa harta cin abinci se Gabby da anwar sun sata agaba take samu taci wata irin rayuwa taqunci tatsinci kanta aciki seta shiga daki tawuni tana kuka rana daya tatashi tashirya tafita taje bangaren popsy takwaso duk wani hoto nasa tasassaka adakin ta setaita kalla tana mgn da hotan se kaimata mgn goma ko kallonka baxatai ba tamayar dakanta bebiya kuma kurma wata biyun kenan yanxun darasuwar popsy, amma lamarin aysha kullm sake lalacewa yakeyi sunfara waya da sameer sosai ayanxun shine kedan debe mata kewar wanda tafahimci shi yanada matsala yaqi sakin jiki yafada mata se kewaye kewaye yakeyi duk wani kasona aysha nagado daxarar anfitar hannun Muhsin take shiga amatsayinsa na guardian dinta, kmr yajja sukai tsammani dukiyar ta tasamma fin qarfin tinaninsu duk da will din dayay metsawo akan yan uwansa dayay umarnin abasu wani kaso ga hudallah ma, sannan yaroqi alfarmar yayansa su cigaba dakula masa da gidauniyar sa takulada marayu da yan gudun hijrah, sosai abin yabaasu mamaki irin sadaqatujjariya da AJ keyi da dukiyarsa, duk cikinsu bawanda besamu maxajen kudade ba ga kadarori me tarin yawa wanda akasarin su bawanda yakai darajar company din da yabama dimple wnn company yatsone musu ido nagaske hakan yasa muhsin yatattara komai tareda shedar alqali harsetayi aure komai nata xekoma hannunta mijinta yacigaba da kulawa dashi,kowa yay na'am da wnn mgnr. *** ***

Don't forget to Comment Share And Vote. [25/05, 15:29] Fatima Rufa'i Nasidi馃馃挍鉂わ笍: AYSAM Its Fatoums Passion's Love,passion,betrayal,romance,hatred and power between two different world's. Quote of the day It's hard to trust someone who always lied. It's hard to love someone who made you cry. It's hard to care when you want to die. It's hard to believe when you have no pride. It's hard to forgive when you already tried. It's hard to be happy when there are tears in my eyes.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.