Free chapter · Read without an account

Chapter 45

by Fatima Rufa'i Nasidi · AYSAM

(Married couple) Moon ce keta kici kicin jera breakfast din baffa data gama hadawa a dan madaidaicin tray din silver, ammi tashigo kitchen din tana tambayar ta kota gama ta ansa da eh yanxun xata kawo tace mata ta ajje xatakai masa daki taje tacewa sameer yafito yaja musu ruwa arijiya tun kafin rana tagama kwallewa, da toh kawai ta ansa mata batareda ta motsa daga inda takeba,tace "baxaki wuce ba koh ninaje da kaina" dan jim tai tana tsoron kada ammin tagane sameer din baya dakinsa ahankali tanufi dakin tana waiwayan ammi har tatura qofar tashige haka kawai ammi taji bata yarda da zuru zurun da idon Moon yay ba, aranta tace "badai yarinyar nan ce takwana adaki tareda shiba" dasauri tadire tray din data dauka tafito afusace tanufi dakin sameer tabanka qofar amma ga mamakin ta moon tagani taxuba tagumi tana kallon qofa tadan firgita ganin ammin, kallon dakin tai tsaf kafin tace "ina sameer yake? qasa Moon tai dakanta tana girgixa kai tace "ina yaje da sassafennan ina tambayar ki kinmin shiru" dan girgixa kai tai alamun bata saniba takasa hada ido da ammin, ammi cikeda takaici take fadin "ina waccan yarinyar" wacca tasan aysha take nufi badai daukarta yay suka fice da sassafennan ba, fita tai takoma parlor tana dauko wayarta no din sameer tasoma dialing can tajiyota tana ringing daga can dakin Moon cikin mamaki ammi tabi sautin wayar ahankali tatura qofar dakin Moon din suna tsakiyar qatifar manne jikin juna barci sukeyi hankalinsu kwance ya maqalqaleta sekace yaro meqiwa da akarabashi da mamarsa akadawo dashi. suman tsaye tai tana kallonsu kafin tajuya tafita da dan sauri, moon dake parlor yarfar da hannunta kawai take tsabar tsoran fadan ammi tana fitowa suka hada ido tabata wani dirty look kafin tace " xanyi maganin ki tunda hardake ake hada baki a munafunceni algunguma kawai," dif tai don tasan ammi xata iya kwarfeta anan idan tatanka mata koda uffan, cikin fada take fadin "wllh sena yi maganinki daga kehar shi sameer din kun rainani ban isa nafadi mgn agidannan kubita ba ko sbd ga sa'arku kuma wllh nadawo naganshi adakinnan daga kehar shi sena gyarawa xama" taqarasa tana ficewa a parlor dakanta tasoma jan ruwa arijiya tanayi tana masifa ita kadai, moon kam da gudu taqarasa dakin badai tashiga cikiba daga bayan labule take fadin "hamma,hamma,hamma katashi ammi ce taxo" cikin barci sameer yajiyo muryar moon din ahankali yabude idonsa kallonsa yasauka akan kyakkyarwar babu face din aysha hannunta saqale jikinshi barci takeyi da alama yay mata dadi dan jim yay kafin yaqarajin sautin moon din tana fadin "Hamma dagaske nake wllh, ammi taxo" adan firgice yamiqe duk da haka seda yasamu nutsuwar janye hannunta daga bayanshi ahankali gudun kada yatasheta don yalura tanada nauyin barci miqewa yay yana kallon agogo it's almost 10 in the morning. fitowa yay sukaci karo da moon yay mata nuni da suje parlor karsu tasheta batai masa musu ba suka fito parlor tare tana zayyana masa abinda yafaru dafe kai yay kunyar mahaifiyarsa naqara mamayeshi meyasa yakasa haqurine yabi abinda tace, yatabbata yanxun ranta yakai qololuwar baci xatai tinanin wani abun daban wanda shi tsakani da Allah bashi yakaishi gareta ba Kawai yanason yaringa jinta akusa dashi shidin ba mahaukaci bane daxe kusanci aysha acikin gidansu ai abun da kunya, ahankali ya leqa tsakar gidan ya hangeta tana ta share gurin da ruwa yataru, dasauri yakoma ganin kmr taganshi, "fito" yajiyo muryarta tana fada "baxaka fitoba koni saina shigo ciki" ahankali yabude labulen yafito tsakar gidan yana durqusawa harqasa yana gaisheta banxa tai masa kafin tace "yaushe xaka koma makaranta," dan jim yay kafin yace "uhm ammi kafin dai jarrabawar xamu koma duka," cikin hade rai take furta "xadai kakoma itakuma ai karatu yaqare mata tunda tarigada tayi aure koh,anan nakeso kabarta gurina," adan firgice yadago yana kallonta yace "amma ammi nata karatun fa itama xatai jarrabawar," tace "kunsan dahakan kukaje kukai aure batai jarrabawar ba toh kasani saidai taxabi abu daya ko aure ko karatu baxan laminci rayuwar kafircinnan ba wai mace da aure taringa gantalin makaranta daga kai har ita saidai kuxaba," "injiwa" cewar baffa daya shigo gidan yafita xaman karatun safe dayakewa su Alh dikko, dagowa tai duk da gabanta yafadi tana fadin "injini mana yallabai," girgixa kai yay yana mamakin rigima irinta walijam yace "toh ban amince ba jibi jibinnan xasu koma Abuja Kuma tare don haka kar naqara jin makamanciyar maganar nan tafito daga bakinki walijam," cikin fada ammi kefadin "toh kunada gurin ajjeta kenan ban amince taxauna a cikin makaranta ba batare dashi ba mekukece masa hostel kome ban yardaba" dan murmushi baffa yay irinnasu namanya kafin yace "wayace miki basuda inda xasu xauna albishirinki Alh yakama musu hayar gida acan natsawan shekara guda harsu kammala duk abinda xasuyi sudawo," sakin bakitai tama rasa mexatace yace "nasan xakiyi mamaki tunjiyan da akai abun nasanar dashi yace shitasa gudummawa auren ga sameer kenan abokinsane yake harkar real estate din qananan gidaje ne na yanmakaranta yanuna min awaya," "toh madalla" kawai tace tawuce ciki fuuuu kmr meshirin tada iska. kallon baffannasa yay yana fadin "baffa yaushe akai hakan" yace "yace babban mutum baxan taba bari kaxauna anan ba matarka xata takura walijam bata qaunarta kuma karka damu kaji babban mutum munmaka mewiyar ai ita raya sunnah ce sekaje kaima Alh godiya ko xuwa anjima ne, nayi nayi dashi yabarni nabiya kudin hayar yaqi qarshedai da kyar yabari nabiya rabi yabiya rabi fatana dai karnaji karna gani kaxauna lpy dayar mutane kasandai abinda yan uwanta sukace,kuma karka bari walijam tai tasiri arayuwar aurenka bance kasabama mahaifiyarka ba kawai dai kabita ahankali ku rabu lpy" godiya sameer yay masa tareda alqawarin in sha Allah baxe basu kunya ba miqewa yay yawuce yay wanka yashirya har lokacin aysha nabarci seda xefita yaleqa gurinsu sbd fitar da ammi tai xuwa gidan Alh dikko gurin matarsa. ganin tana barci yasanya yacewa moon karta tadata kawai banisa xeyiba inta farka tatabbatar tayi break tashirya xata rakashi anguwa, fitarsa kenan tafarka taje tai wanka tafito Moon taimata hadin breakfast mekyau takawo mata, taci sosai balefi kafin tashirya cikin riga da wandon plazo tagyara gashinta tamaida shi style din ponytail tasaka headband akanta tayi kyau matuqa duk da fuskarta datai fyau bako makeup akai lotions din da moon ke amfani dasu tai applying before tai settling down taje shopping nata kayan. bayan sungama ne akai kiran sallah suka wuce sukai sannan Moon tace xata shi ga kitchen tai girkin rana cikeda xumudi aysha tace xata tayata Moon batace komaiba ganin tamatsa yasa suka shiga kitchen tare, fira sukeyi sosai aysha ganin ammi batanan ga Moon kuma sejanta jikinta take yasanya tasake sunata fira harda dariya, Lilly takira wayar moon sungaisa da dukkansu kafin sukatse da alqawarin indai basu dawo imperial weekend ba su xasu xo, a kitchen Moon ke girki aysha ta isheta da tambayoyi kala kala duk abinda tataba seta tambaye ta sunan sa tuntana answering tana murmushi hartaxo tana fadin "dan Allah sis dimple kitemaka kiyi shiru ki kalla kawai kindameni," dariya taringa mata tana tagirki amma taji dadi sosai kasancewar ayshan atare da ita sbd tadade tana fama da kadaici idan har hudallah da sameer basa gidan bata tareda kowa komai ita kadai takeyi duk da talura ayshan bata iya komai agirki ba amman tana matuqar jindadin firan dasuke tare. atsakar gida tasaka kujera taxauna tana tambayar Moon wai yaushe sameer xedawo ne, itafa kewansa takeyi takirashi tace masa matarsa tana jiransa yadawo moon sedariya take mata domin talura qawa ayshan ke yi da ita ba surukaba se tsokanarta take tana yaba kwalliyarnan datai wai in yaya yagani xaucewa xeyi tsintsiya moon tadakko xatai sharar parlor aysha takarba tana fadin "bari naje nasharo miki," tace "xaki iya" ta jinjina kai tana kallon tsintsiyar tana murmushi, "toh" Moon tace tabata tashiga ciki tama rasa gane tayajja xata fara sharowa tatsaya kmr wacca Akasa wani babban aiki, sallamar sameer taji yasanya tai hamdala tana fitowa dagudu tsakar gidan, murmushi take masa shima murmushin yay mata da wata polythene bag ahannunsa, bude mata hannuwansa yay alamar taxo tatako da gudunta tafada qirjinshi tana fadin "shine katafi kabarni ko" cikeda shagwaba,shafa kanta yay yana fadin "bakece kiketa barci ba kuma banason natashe ki,yakwanan baqunta," dagowa tai tana fadin "it's nice" yace "fadi dai gaskiya," dan jujjuyawa tai tana dan fara ido tana fadin "dagaske nake yi," sosai abinda tai ayanxun yaburgeshi abubuwa dayawa takammasa wanda yasan ita kanta batasan tasirin dayake acikin kwakwalwarsa ba dakyar ya iya fuxgo numfashinsa yana kallon tsintsiyar hannunta yana fadin "mekuma xakiyi da ita" cikin rada take fadin "shara" tana smiling danxaro ido yay yana fadin "shara kuma,sharafa xaki iyane wayasaki," turo Lip's tai cikin shagwaba take fadin " nine nasa kaina da kaina" moon,moon yasoma kira fitowa tai a kitchen tana fadin hamma gani tun shigowarsa batai gangancin fitowa ba ganin daga shihar ayshan ba ta ido garesu ba gara tarufama kanta asiri taxauna aciki,yace " kekisa aysh shara koh," hararar wasa ta watsa masa tana fadin "ninace maka haka xakai mata fadan ko," Moon tace "garadai kifada masa matarnan taka batajin mgn seda nace tabarshi tabarshi taqi gashinan kinja xexo yadagan hankali" dariya aysha tai tana mamakin fadan sako da sako dake tsakanin Moon din da sameer duk irin abinda xasuyima juna basa iya gaba da juna ko yaya setaji itama tana kewar kasancewa danata yan uwan duk da bawata jituwar arziqi garesu ba amma still tana matuqar son kayanta, sameer taji yakarbe tsintsiyar yana furta "kawo nayi muje ciki," Moon dariya tai tana fadin "garadai katayata don naga kmr sharar wiya tai mata," harara ya galla mata yanajan hannun ayshan sukai ciki Moon tagigirxa kai takoma kitchen tacigaba da abinda takeyi jin sunyi tsit har tagama girki tasan cewar ba iya sharar akeyiba ambi wani layin kuma na daban. Cikin babban parlor ba abinda kakeji sai buge bigen glasses da ake fasawa da kayan amfani tassssss kakeji anwanchakalar da wani tsadadden vase aqasa, dagowa tai ahankali tana kallon cikin idanuwansa dasukai jajir kmr wuta tsaki taja kafin taqarasa taxauna adan space din kujeran dabe bata ba cikin parlor,bata dena kallonsa ba,yace "what? tace "what? what? kai xantambaya what is wrong with you? kasan dollar nawa nakashe kuwa gurin siyan wadannan kayayyakin nawa daka fasamin," muhsin jan tsaki yay yana fadin "ke akan tsadar kayama kike complaining ni halin da yake ciki nafi damuwa akai" Arsal bi yay takan glasses din dayafasa yana tattakawa da bear foot dinsa aiko se jini bawanda yay qoqarin stopping dinsa cikin hudallah da muhsin da muhassin dake parlor, saida yaga qafar naneman dena aiki yasa yatsugunna agurin yana hawaye kmr wani qaramin yaro, "Bravo" hudallah tafada aranta tana yaba acting skills din arsal, muhsin ne yataso yaqarasa yana rungumeshi, "kamanta da ita kawai you'll get someone wacca tafita,you can even go out with hudallah idan hakan xe sanyaya maka ranka," cikin kuka yake fadin "banason kowa se ita i want her,I need her baxan taba jurar rashinta arayuwata ba, muhsin Idan har bansamu dimple ba xan rasa raina," muhassin ne cikin daga murya yake fadin "har nawa wancan banxan yaron yake nayi dana sanin qinbin ku gombe,musa adakko shi a aikashi inda baxe taba dawowa ba mana let's just get rid of him for good," dasauri hudallah tasoma girgixa kai tana fadin "a'ah ya muhassin ba xancen kisan kai acikin plan dinmu,if we kill him mekenan mukai munji tsoron tasirinsa arayuwar aysha kenan ita xamu sanya tai killing dinsa,I'll make her break his whole life daxe gwammaci mutuwa akan rayuwa" muhsin cikin tsawa yake fadin "tayaya kenan kullum haka kike cewa kinada control over both of them kwana nawa da auren yanxun may be ma they already consummate,kisani idan har wani abu yashiga tsakaninsu kinci amanar Arsal kinsan dahaka koh, ba abinda xaki iya koh xuwa gidan dasuka tare a wuse2 kin kasa don haka kibarmu mukashe shi kawai," hudallah murmushi tai tana fadin "sameer fa qaramin alhaki ne meye xekaiku datti da hannayenki gurin ganin bayansa already shi mara darajane badai suna Abuja Yanxun haka ba,inada plan kuma I'm hundred percent sure cewan xeyi aiki" Arsal cikin shashsheqar kuka yake fadin "what's your plan? tace " kuxo kuji" duka su ukun suka qarasa inda take suka gwarakai takai minti goma tana kitsa musu abinda xa'ai before kowa yadago da murmushi asaman fuskarsa banda muhsin, yace "what if the plan doesn't work? tace "I'm sure it will work" tana miqo hannunta tace "deal" hannuwansu suka daura saman nata suna fadin "deal." Rayuwa tun ana qirga kwanaki har akasoma qirga satittika da watanni abubuwa dayawa sunfaru sun shude mutuwar popsy auren sameer da aysha dawowarsu abuja, yau takasance rana me mahimmanci ga duk wani senior student dake imperial school ranace wacca xasu fara xana jarrabawar su ta IGCSE sosai student din suka duqufa gurin karatu kowa yana fatan yafito da sakamako mekyau wanda xesa iyayensa alfahari haka take ta bangaren couples dinmu, sameer ne kwance saman madaidaicin bed din dake dakin nasu barci yake me dadin gaske tashigo dakin sanye da uniform dinta bata dora top dinba tana parlor tana jiran yafarka yagoge mata kugu tariqe ganin tun tashinsa datai ko motsawa beyiba dagudu tahau kan bed din tana jijjiga shi "baby wake up we are getting late is already time," "uhmmmmm" yafada yana qara sanja position bude bakitai irin mamakinnan kafin tasoma tickling stomach dinsa, "aysh stop,aysh pls" yafara fadi cikin thick morning voice dinsa dake mata matuqar dadi, "a'ah naqi nabari harseka tashi" tafada tana cigaba daimai dariya yasoma yi har yabude idonsa yana fadin " I surrender,xantashi xantashi" yafada yana daga hannuwansa duka biyu alamun yayi surrender dariya tai tana miqewa tace "good boy," step biyu tai yafixgota tafado jikinsa tana fadin "ouccch baby xamuyi latti fa," dan squeezing face dinsa yay yana fadin " who care's, shine last night kikai barci kika barni koh,inata surutu ashe,toh nima sena rama," yafada yana smooching neckline dinta numfashi tasauke tana fadin "pls baby kaga inada aiki a lab before exam, sophomore students are still under me," kallon agogo yay yana fadin "we still have 30 minutes we can make love before time din yacika," xaro ido tai tana fadin "laaaaaah nadaura ruwan tea kada yaqone tun daxun xanje nakashe yasan sarai bawani ruwan tea din data daura duk xille xille ne,yace "Bad lier,fine in yaqone we will eat outside," tace "baby kamanta munyi budget no spending too much money on useless things atsakiyar month muke fa," yace "nasani but one meal ai ba abinda xema budget ko" yaqarasa yana qoqarin balle mata bottle's din jikin farar shirt din jikinta ganin dagaske yake kuma tasan idan yafara maybe masu manta daxuwa makarantar yasa tafaki idonsa tamiqe dagudu saida takai qofa sannan taleqo tana fadin "sorry baby,nama fasa tafiyan dakai,I'll call lilly to come and pick me up tunda kaxama lazy boy,can you imagine the great sameer S fulani yanxun kullum seyayi latti," murmushi yay yana miqewa kafin yace "who's always keeping me awake during the night," yay kmr xebita dagudu tafice dariya yasaki yana wucewa bathroom shower yasakarma kansa yasoma tinanin how far rayuwansu yakawo betaba tsammanin after everything they went through xasu wuce wnn stage dinba,her mom,his,the CBT center everything he could remember lokacinda yafara kaita CBT center dinsa taga AYSAM jiki she almost burst out in tears, komai na rayuwarsu natafiya cikin simplicity rayuwan dayake tinanin aysha baxata taba iyawa ba segashi takarba wnn rayuwan hannu bibbiyu bata taba nuna masa gajiyawanta dahakan har itama tasoma dan small online business kmr yajja yakeyi lokaci xuwa lokaci tana karbo kaya daga gurin baffa bayan kulle mata accounts dinta dayan uwanta suka sa ayi sunyi tinanin xatakoma gurinsu roqon kudi kowani abu, hakan bata taba faruwa ba tanada xuciyar nema idan tadaura kayan a social media handle's dinta tun suna binta da witty remarks har akasoma tatambaya ana siya bayajja beba tadena amman tace ita batason taxauna kawai taxama useless or something like that she want to help,almost all their expenses yanxun ta iya maintaining dinsa bakamar farkon aurenba datake spending abundantly kuma Lilly namatuqar guiding dinta kan wasu abubuwan sosai da sosai. Don't forget to Vote Comment and Share. It's Fatoums Passion

AYSAM Its Fatoums Passion's Love,passion,betrayal,romance,hatred and power between two different world's. Quote of the day "Sometimes glass glitters more than diamonds because it has more to prove.". "The better you feel about yourself, the less you feel the need to show off.".

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol