Free chapter · Read without an account
Episode 9
PAGE 9
A ranar da Alhaji Sani ya fara zuwa wajen Humaira, bayan gaisuwa bata ƙara ɗago kai ta kalle shi ba, har ya gama maganar da zai yi, ganin kamar she is not even interested in him yasa yace; "Humaira, ko dai ban yi miki bane?"
A nan ma shiru ta yi bata kula shi ba.
"Ba ki sona?" Ya kuma tambaya.
Kai ta gyaɗa mishi, tace; "Ba kai kaɗai ba, bana son duk wani namiji da zai ce yana sona yanzu, Ni ƙaramar yarinyace, karatu kawai nake son yi ba soyayya ba."
Yadda take maganar calmly, ƴar ƙaramar bakinta na motsi kamar bai son yi, hakan yasa Alhaji Sani ya ji son da yake mata ya ninku a zuciyar shi, miƙewa ya yi, yace; "Zan tafi, amma zan dawo, don ina ji a jikina ke ɗin tawace."
Wani kallon kar ma ka ɓata lokacinka Humaira ta yi masa, tana zaune a waje har ya fita, a hankali ta miƙe jiki babu ƙwari ta tashi, ɗakin Ya Kausar ta shiga ta kife kanta a kan gado tana silent kuka, lokacin Ya Kausar na ɗakin Mallam Lawal. Ko da ta dawo Humaira ta yi kukan har ta yi bacci.
Washegari da sassafe Humaira ta fara harhaɗa kayakinta, Ya Kausar da ta fita sallamar Lawal ta dawo ta sameta a hakan. Humaira ta ji shigowarta, amma sai ta yi kamar ba ta ji ba, ta cigaba da abinda take yi. Ya Kausar ta ƙaraso ta zauna a gefenta tace; Humaira haɗa kayan me kike yi da sassafen nan?"
Wasu siraran hawaye ne suka gangaro mata, ta yi amfani da bayan hannunta ta goge, Lokaci ɗaya Kausar ta ji zuciyarta ya fara bugawa, ta fara tunanin kar dai wani abu suke wa Humaira a gidan ba su sani ba, ga Humaira da zurfin ciki ba faɗa za ta yi ba, riƙe hannunta Kausar ta yi, tace; "Kukan me kike yi?"
Girgiza mata kai Humaira ta yi, murya a shaƙe ta ce; "Babu."
"Babu shine kike kuka kina haɗa kaya? Dan Allah Humaira idan wani abu na yi miki ki faɗa min, kar ki yi min haka please." Cewar Kausar cikin damuwa.
Humaira ta ɗan ja hanci, tace; "Wallahi ba ki yi min komai ba Ya Kausar, kawai ina son na koma gida ne."
"Kina son ki koma gida haka kawai? Ta yaya kike son na yarda ba wani abu na yi miki ba shiyasa kike son barin min gidana?" Kausar ta faɗa tana kallon Humaira sosai don tana son ta gano gaskiyarta a kwayar idonta.
Humaira tace; "Wallahi ba ki yi min komai ba, kewar gida nake yi, jiya da tunanin su na kwana."
At some point Kausar ta yarda da abinda Humaira ta faɗa, don haka Humaira take, a duk lokacin da ta zo gidanta ba ta wuce sati ɗaya take komawa gida, amma kukan na menene?
Kamar Humaira ta san abinda ke yawo a zuciyar Kausar, sai ta goge idanunta ta ce; "Kar ki damu da hawayen da kika gani a idona, tunanin irin rayuwar da zan je na tarar nake yi."
Hannunta Kausar ta riƙe, ta kwantar da murya ta fara lallashin Humairan tana ƙarfafata.
A ɓangaren Humaira kuwa ba kewar gidane ainahin dalilin da yasa take son komawa gida ba, ba ta son Alhaji Sani ya ƙara zuwa wajenta ne, ba ta ƙaunar wani ya ƙara yi mata maganar soyayya.
Ya Kausar ta tayata arranging kayakinta, sai ta kira Lawal ta sanar dashi cewa za ta raƙa Humaira tasha, ya ce su jira shi yana zuwa yanzu.
Lawal ma da ya dawo ya rinƙa tambayar Humaira ko dai wani abu ne aka yi mata da kawai za ta tashi da maganar tafiya gida all of a sudden, amma abinda ta faɗawa Kausar shi ta faɗa masa shima.
Fita suka yi daga gidan Lawal na riƙe da akwatin Humaira, Humairan kuma da Kausar suna biye dashi a baya zuwa bakin titi. Suna tsaye a bakin titi suna jiran adaidaita da zai kai Humairan zuwa tasha, wata baƙar mota ta wuce ta gabansu, a hankali motar ta fara dawowa da baya, daidai gabansu motar ta tsaya, a hankali gilashin window ta fara sauka a hankali, Alhaji Sani dake cikin motar yace; "Wa zai yi tafiya ne?"
Hannu Lawal ya bashi suka gaisa, sai yace; "Mutumiyarka ce yau ta tashi da kewar gida."
Alhaji Sani ya kalle Humaira dake tsaye daga gefe, ta ɓata rai, sai ya yi murmushi yace; "Shiga to na kai ki gidan."
Kafin Humaira ta kai ga yin magana Lawal ya buɗe backseat ya ajiye ƙaramin akwatin Humaira yana faɗin; "Da ka kyauta kuwa."
Humaira kamar ta fashe da kuka, tace; "Yaya Lawal kar mu takura shi, kawai zan tafi tasha na shiga mota."
"Babu zancen takura a yi wa wanda rai yake so hidima." Alhaji Sani ya faɗa yana wani kallon Humaira.
Ya Kausar ne ta yi wa Lawal magana ƙasa-ƙasa ta yadda shi kaɗai zai ji, jinjina kai ya yi, sai ya kalle Alhaji Sani yace; "Errm Alhaji ina ganin ka yi tafiyarka kawai, za mu je tasha mi shiga mota, na manta noma akwai Ni da ɗan uzuri a Dalar."
Alhaji Sani ya yi murmushi yace; "Ba damuwa, ku shiga kawai na kai ku."
Hankalin Humaira ya ɗan kwanta jin tare da Malam Lawal za su tafi, Kawai ya buɗe mata backseat ta zauna a gefen akwatinta, shi kuma ya shige front seat yana yi wa Alhaji Sani godiya, Kausar ta ɗaga musu hannu tana musu Allah ya kiyaye hanya.
___________________
A ranar da Hunaif ya cika sati guda da dawowa Brazil, ya shirya don ziyartar Abban shi a Saudi bisa ga matsin da Mami ta rinƙa yi masa akan lallai ya tafi.
Da yamma jirginsu ya yi landing a Saudi Arabia, wani friend ɗinshi dake zama a Saudin ya kira don ya zo ya ɗauke shi, yana fita daga jirgin friend ɗin nashi Mus'ab ya hango shi, hannu ya ɗaga masa daga jikin koyarwa da yake tsaye, Hunaif ya ja ƙaramar box ɗinsa zuwa motar Mus'ab, yana ƙarasowa bakin motar Mus'ab ya bashi hannu suka tafa, yace; "Mutunina kenan, You look good."
Kofar front seat HUNAIF ya buɗe ya zauna, kafin yace; "You don't look bad either."
Rufe masa kofar Mus'ab ya yi, ya ɗauki box ɗinsa ya saka a backseat, he can see from Hunaif's eyes that he's stressed, zama ya yi a driver's seat ya ha motar.
A gidan Mus'ab Hunaif ya sauka, ya yi wanka ya huta, matar Hunaif ta yi serving ɗinsu abinci suka ci, kafin ya kira Abbansa ya faɗa masa hotel ɗin da ya sauka.
Mus'ab ya kai Hunaif har hotel da su Abba suke, ya yi dropping ɗinsa kafin ya koma gida.
Alhaji Mahmud na zaune a falon hotel room ɗinsu suna cin fruits suka ji doorbell, Anty ta tashi ɗauke da murmushi a fuskarta tace; “That should be my son I guess.“
Aikuwa tana buɗe ƙofa ta gan hunaif a tsaye sanye da headset akansa, hannunsa ɗaya a aljihunsa, rungumeshi Anty ta yi tana faɗin; “Welcome my son, I miss you so much.“
Murmushin dake ƙara masa kyau yayi, ya yi hugging ɗinta shima, yace; “I miss you too.“
Riƙo hannunshi ta yi ta ja shi cikin.
“Ya hanya?“
“It was stressful but Alhamdulillah.“
Har ƙasa Hunaif ya durƙusa ya gaishe da mahaifinsa, sannan ya ƙara gaishe da Anty. Cikin few minutes ta kawo masa fruits, da lemu da ruwa, tana faɗin,; “Bari na order maka abinci."
Da sauri ya girgiza kai, tace; "Daga gidan friend dina nake, na ci abinci a can.“
Alhaji Mahmud ya nunawa Hunaif waje a gefensa, yace; "Zo ka zauna kusa da Ni ɗana."
Hunaif ya matso kusa da Abban na shi.
“Ya kasuwa Abba.“ Ya tambaya yana taunar Apple da Anty ta kawo mishi.
“Lafiya ƙalau alhamdulillah. Ya naka business ɗin?“
“Alhamdulillah it's progressing."
"Masha Allah, haka nake son ji. Amma ya batun ƙwallon, kwana biyun nan you have not been performing well on the field."
Ɗan sosa kansa Hunaif ya yi, yace; "I guess rashin training sosai ne, amma zan gyara In Sha Allah.“
“Masha Allah, Allah ya yi taimako."
“Aameen."
Daga nan suka cigaba da hira gabaki ɗayansu, Anty ta ɗau waya ta kirasu Mami, ta haɗa conference call da sauran yaran gidan aka rinƙa hira.