Free chapter · Read without an account

Page 4

by Sumayya Usman · MENE NE ABIN YI..?

  *MENENE ABIN YI?*
      
      By
    
    
    Sumayya Usman 
                (*Cwt-sumiey* )
    
    Repost

    ***

*YOTA*

*Page 4*

"Doctor ban gane mai kake son fad'a min ba?, maganganunka duk sun bi sun birkita min kwakwalwa,da kuma tunanina gabad'aya ".
"Tabbas maganar da na fad'a maki itace ainihin gaskiya,a binciken da mu ka yi mun samu tabbacin akan  ya samu rauni mai zurfi a cikin kansa , wanda hakan ya sa komi na kwakwalwarsa juyewa ,duk wani abun da ya faru da shi a baya yana nan ,ba wai ya manta shi ba ne ko ya goge ,a'a sunanan sai da me yana ganin su ne tamkar a mafarki ko a matsayin hallucination or imagination,suna yi masa gizo kenan,sai abu na k'arshe da muka samu shine, shi kurma ne ba ya iya magana amma yana jin duk abun da zaka fad'a,kuma ba wai a wanna accident d'in ya samu matsalar ba wannan shine sakamakon binciken da mukayi".
"Inalillahi wa'innan ilaihirraju'una,hakan fa duk ta faru da shi ta sanadiyyata,amma dama kamar mun so mu fahimci baya magana tun farkon da muka fara samun damar ganin sa ,so a time d'in mun yi tunanin ko hakan ya faru ne sanadiyar accident d'in ,ka ga kenan muna sa ran zai samu sauk'i tunda a rana tsaka abun ya same shi a she ba haka ba ne".ta fad'i hakan cikin yanayin sanyi jiki.
"Kwarai kam don a binciken mu da muka yi mun gano cewar an haife shi da wannan lalurar ne,ba wai rana tsaka ya same ta ba".
  "Dan Allah doctor ka taimaka min ka yi masa wani abinda zai taimaka masa yayi recovery da wuri,ban sanma ta ina zan fara neman ahalinsa ba".
"Babba matsalar da muke fuskanta a yanzu itace yanda zai had'u da iyayen sa da y'an uwansa ko da ma kin yi k'ok'ari har sun kaiga had'uwa to tabbas ba makawa ba zai ta'ba yarda da su ba ,balle har ya kai ga amincewa da su,saboda shi a wurin sa sun had'u ne a mafarki,idan har su kai yunk'urin ganin sai sun fahimtar dashi matsayin su a wurin sa ,to tabbas kwakwalwarsa zata k'ara hautsinewa kuma zata iya kaiwa matakin da ba zamu iya samun damar da zamu ceto sa ba".
"Ya Allah,yanzu doctor MENENE ABIN YI... ,kaina ya kulle narasa me zanyi,ban san wanne kalar tunani ya kamata inyi ba?".
"Ku dakatar da duk wani bincike ko sanarwa da kuke akan neman ahalinsa,ki barsa a hannunmu ,zamu cigaba da d'orasa a kan magunguna gami da kulawa har sanda Allah zai ba shi lafiya ya koma cikin hayyacinsa,wannan shine abun da ya kamata kiyi".
"Barin shi a cikin hospital d'innan da akwai risk,don wata rana wani nasa zai iya ganinsa ,kaga  kenan anyi ba ai ba kenan,duba da kasancewar nan asibiti ne ka zo na zo ,kai kowa ma na iya zuwa,ka ga kenan komi na iya furtawa don wata rana abokinsa,yan uwansa ko wani wanda yake da alak'a da shi zai iya zuwa,idan ba damuwa zan iya tafiya dashi can gidanmu kasan zai samu kulawa ta musanman ko ma ince fiye da nan d'in?".
"Wannan ba matsala ba ce Brr. Shuraimah in har za'a kula da 'bangaren shan maganin sa to lafiya lau ne".
"In sha Allah za'a kula sosai".
"Zan iya rubuta maki sallama ma yanzu,idan gida ki ka yi kaitsaye, don tuni bandage d'in da yake d'aure a kansa an kwance shi, a physically in kika ganshi za ki ce ya samu sauk'i sai dai raunin da ke cikin kansa ne ya yi saura kawai kuma shima in har zaku dage kamar yanda ki ka ce zai saurin samun sauk'i".
   "Ba damuwa rubuta mana sallamar kawai ,don tashi na daga wurin aiki kenan".
     Paper ya d'auko yayi d'an rubuce-rubucensa ya bani , na kar'ba gami dayi masa godiya na nufi d'akin da yake,a kwace na iske shi alamu sun nuna kai tsaye barci yake,kujerar da ke gefan gadonsa na jawo a hankali na zauna gami da tsare sa da idanuwana,ba abinda nake tunawa sai ranar da na bige sa da motata , wajen wata biyu kenan, har kawo yanzu bana cikin natsuwata,ko da wasa bazaka ce yana rayuwa a cikin matsi ko takurin rayuwa ba,don ko kusa ba shi da wannan alamar,dai-dai kwargwado za'a ce,daga yanayin sa na fuskanci hakan.
     Ban san sanda hawaye suka fara zubo min ba,waya ta najawo sakamakon k'arar da naji tana yi ,na d'aga tare da yin masa sallama cikin sheshekar kuka.
      "Ya salam Daughter meye kuma yake faruwa,ko dai kin koma hospital ne bayan kin tashi daga wurin aiki?",a ka fad'a daga can 'bangaren.
    "Eh Dad yanzu haka Ina ciki mun had'u ma da doctor ya fad'a min komi".
  "Ehhyaa ban so ya fad'a maki ba ,nasan zaki k'ara shiga damuwa ne,any way yanzu wanne hukunci ki ka yanke?,don d'azu da safe kafin in tafi meeting d'in da zan je na biyo ta wurin sa ya man bayanin komai nima".
       "Zan tafi da shi nan gida har zuwa sanda zai samu sauk'i sai a nemi hanyar da za'a samu ahalinsa daga baya".
       "Kin tabbata hakan ya yi maki,kuma zai baki kwanciyar hankali in kina tare da shi?".
   "Eh Dad na tabbata da hakan sosai"
"To ba damuwa bari in kira Mom sai tasa a gyara masa d'akin da zai zauna ,in ya so in kun isa sai ki duba mai ne ne babu sai in tura maki kud'i ki sa a saya masa".
"Okay Dad thanks a lot,amma ina da kud'i a account d'i na".
"Ai na sani,amma kuma hakan bai hana ince zan baki wasu ba,so just accept it".
"Tom shikenan Dad na gode".
"Don't mention it again,sannan ki share hawayen haka nan ,ki tashi ki shirya abinda da zai iya yi maku amfani zan turo Iro driver sai ya mai da ku gida".
"Ka barshi ba sai Iro yazo ba don nazo da mota ne".
"Okay ba damuwa but take care kinji ".
"In sha ALLAH Dad sai ka dawo", dai-dai san da zan aje wayar na sauke Idanuwana a saman fuskarsa,mu kai ido hud'u da shi ya na kallo na,ga fuskata tayi sha'be-sha'be da hawaye ,rasa me ya kamata inyi nayi ,sai da ga k'arshe dabarar k'ik'irar murmushi ta zo min gami da taimaka masa ya tashi zaune,sosai na k'i bari mu sake had'a ido da shi sai faman kauce-kaucen fuska na ke masa ,har na kammala had'a kayan da nake buk'ata,shi kam sai faman bi na da idanuwa kawai ya ke,ganin na gama had'a duk wani abun da nake so ne yasa nayi shahadar k'uda na juyo ina kallon sa gaba d'aya,kamar wanda ya ke jira, ina juyowa ya fara yi min nuni da hannu yana tambaya ta me ya ke faruwa ya ga hawaye a saman fuska ta?, tsuru-tsuru nayi don na ma rasa mai zan ba shi a matsayin amsar tambayar da yayi min,da kyar na samu na fusgo numfashina ina mai cewa da shi.
"Am....uhm....ba komi kawai nima yau ba ni da lafiya ne,amma naje wurin Doctor ya bani magani ma,kuma kasan abu mafi farin ciki?,ba tare da na tsaya ya ce wani abun ba na d'ora da cewa,"Doctor ya ce ka warke yanzu haka ma ya sallame mu  gida kawai zamu tafi yanzu",ko kad'an bai nuna min alamar ya amince da abinda na fad'a masa ko akasin haka ba,sai k'ok'arin saukowa daga saman bed d'in da ya ke ,da sauri na jawo masa takalmansa ya sa muka fita,muna fita kiliners d'in hospital d'in suka zo suka amshi kayan da ke hannuna suka raka mu har gaban motata ,muna fitowa sai da gabana ya yanke ya fad'i don har Allah -Allah nake in ga mun bar harabar hospital d'in kar a ce wani wanda ya san shi ya zo wucewa ya gan mu,ko da muka shiga cikin motar gaba d'aya na yi sama da duk glasses d'in motar, in da nai sa'ar gaba d'ayansu tinted ne,da sauri naja motar muka bar hospital d'in gabad'aya,sai da muka isa gida sannan hankalina ya kwanta .
Muna shiga muka iske Mom a parlour kamar tana zaman jiranmu ,da sauri ta tashi tare da kamo hannayensa ta shigar da shi ciki gami da zaunar da shi saman sofa tare da cewa,"masha Allah yarona jiki ya yi kyau ,sai fatan Allah ya kyauta gaba".
Murmushi ne kwance a saman fuskar sa wanda ya ke nuni da yaji dad'in abinda ta ke fad'a,ita kanta fuskarta sai da ta nuna taji dad'in yanda ta ganshi kasancewarsa mutum mai saurin sabo ,ko hakan ya samu nasaba da ciwon nasa ne oho.
"Yanzu abinda ya kamata ki tashi ki kai sa d'akin sa ya fara yin wanka,ke ma ki samu ki d'an watsa ruwan, sai ku fito kuci abinci".
"To Mom an gama gyaran d'akin ne?".
"Eh mana,tare da ni ma akai aikin".
"Ohhhh thanks a lot Mom,bari  muje mu ga ni ",
"Okay tom sai kun fito".
Kusan duk a tare muka mik'e da shi kasancewar ya na jin komi da a ke cewa, sosai gyaran d'akin ya yi kyau kasancewar an aje komi in da ya dace.
Da sauri na fito na isa inda Mom ta ke na rungume ta cikin farin ciki gami da jin dad'in abinda ta yiman.
"Ke...ke.... meye haka sai faman wujijigani ki ke salon kije ki kada ni".
"Kai Mom taya zan iya kada ki ,farin ciki fa na ke yi".
"Farin ciki ko dai yarinta ke da baki girma." 
"Ni ba wannan ba Mom, wai yanzu da wanne sunan zamu rik'a kiransa da shi?,kin ga yanzu ya dawo zama tare da mu".
"To fa yanzu shi fa ba wanda yasan sunansa na asali ko?".
"Eh mana"
"Bari mu gani yanzu wanne suna ya kamata asa mashi ,to ko dai mu kira shi da sunan yayanki wanda ya rasu tunda yanzu shi bama tare da shi?".
"That's my Mom shiyasa nake k'ara son ki a kullum,amma kina ganin Dad zai bari mu rik'a kiran sunan kai tsaye kuwa tunda kinga sunan babban abokinsa ne?".
"To ba shi ma sai mu rik'a kiran sa da Nadeen d'in ba".
"Eh kuma haka ne ,nasan kuma shima zai ji dad'in haka".
"Kin ga tashi kije wajen sa wata k'ila yana buk'atar wani taimako,tunda har yanzu da sauran sa,Ni babbar matsalata yanda zan rik'a magana da shi kin san ba iya wannan yaren na kurame na yi ba".
Wata y'ar tak'aitacciyar dariya nayi kana nace mata ,"Mom ai a hankali zaki iya,domin ni kaina sai da wannan tunanin ya zo min da ban iya irin maganar su ba an samu wata K'arinmatsalar kenan,amma in kina so sai in koya miki".
"To ba laifi bari mugani in hakan zai yiwu,amma da kamar wuya gurguwa da Auren nesa,don kamar ni yanzu Ina ni ina wani koyan wani abu,ke dai tashi kije wajen sa ko yana buk'atar taimakonki a tare da shi".
"To Mom bari in je".
A gefan mirror na iske shi yana kallon kansa a ciki sai faman shafa gashin fuskar sa da na kansa yake,alamu sun nuna bai saba ganin kansa a irin wannan yanayin ba,duk da dai ko sanda muka bige sa da akwai tarin suma a kan sa don d'aure take ma a bayan sa,yanzu kam har da gemu ya tara sakamakon kwanciyar asibitin da ya yi,ganin hakan da nayi  ya sa na fita da sauri na nufi bedroom d'in Dad na d'auko shaving cream da clipper d'in sa,kasancewar a gida Mom ke masa amfani da su,yanda na barsa haka na iske sa, stool d'in da ke ajiye a gefe na jawo masa tare da nuni a kan ya zauna,ba musu ya zauna yana mai bina da idanuwa,sai da na k'ara matsowa kusa da shi kana na fara yi masa magana a hankali kamar mai tsoran wani kar ya jita.
"Ka amince da ni ?",kai ya d'aga min alamun ya amince da ni.
"Okay tom rufe idonka ina so ne in gyara maka gashin kan ka ne".
"A'a kar ki damu ba sai kin wahalal da kan ki ba na iya da kai na ma zan gyara",duk yana wannan maganar ne da yin nuni ko ince da yaran su na kurame.
Cikin yanayin shagwab'a na ke ce masa,"don Allah ka bar ni in yi maka na iya sosai bazan 'bata maka fuska ba".
"Shikenan na yarda ,amma mudin ki ka 'bata min kai ,ba zan kyale ki ba sai na rama,don sai na d'ebe miki rabin gashin kan ki ke ma". 
"Ban san sanda dariya ta kwace min ba sakamakon jin cewa zai d'ebe min rabin gashi kai na in har na 'bata masa fuska,har ga Allah Ina da dalilin da yasa na ke son in yi mashi gyaran fuskarsa da kai na ,don ina tsoran in bar sa yayi irin wanda ya saba yi a baya,kun ga kenan da zaran anyi rashin sa'ah wani wanda ya san sa ya ganshi zai saurin gane sa,wannan shine dalilina ko ince abinda zuciyata ke fad'a min kenan.
"Naji na yarda kuma in sha Allah,sai ka sha mamaki yanda zaka koma in har na gama".
Sai da na kwashe wani lokaci mai tsawo ina ta faman aiki yanda kasan irin wata professional d'in nan,har ya kai ga ya gaji yana k'ok'arin bud'e idanunsa ,ni kuma ina ta faman rik'onsa akan ya rufe na kusa gamawa,ko da na gama tsaye nayi ina k'are masa kallo,iya matuk'ar k'arshe ya yi min kyau,gashin kansa yana da matuk'ar tsawo don ko wata macen ma albarka,rage masa tsowo nayi na mai da shi irin na zamani yanda matasa ke tarawa sannan na zubo masa da wani a saman fuskar sa, don ya kusa rufe kwatar fuskar sa,a hankali na juya dashi saitin mirror yanda da ya bud'e idanunsa zai yi tozali da sabuwar fuskar sa.
Nasha mamakin yanda ya nuna a lokacin da ya ga kansa a madubin ya yaba min sosai ni har abun ma ya soma bani dariya .
Ganin yanda nake dariyar ne ya sa ya fara bani wani labari cikin harshen su na kurame ma'ana yana yi yana min nuni da hannu yana mai cewa,"kin san a baya na ta'ba yin mafarki makamancin irin abun da ya faru yanzu"......
Gaba na ne yai wata irin fad'uwa da sauri na tambaye shi ,"kamar ya ban gane ba?".

"Eh mana wai gani a gidana da wata mata a matsayin matata take wai har muna da baby ,tana yimin gyaran fuska sai ga...........Na yi saurin katse shi ta hanyar rufe masa baki tare da cewa,"ka ga irin wannan mafarki ba gaskiya bane , ba'a son mutum ma yana irin sa ,da yazo maka kar ka kuskura ka yarda da shi ,kayi saurin goge shi ka d'auka ma bai ta'ba faruwa ba kaji".
"To saboda me?".
"Saboda ba gaskiya ba ne".
"To amma ni a y'an kwankinnan ina yawan yin mafarki irin wannan kala-kala".
"To duk ba gaskiya bane ka manta da su gabad'aya".
"To amma ai nasan shi dama mafarki ba lalle ne in kayi sa ya zama gaskiya ba,amma me yasa duk kika tada hankalinki don na fad'i hakan?".
"Ka ga ba komi kawai ni d'in ce ban fiye son mafarki ba amma ya wuce bari in had'a maka ruwan wanka kasan Mom nacan na jiran mu",da haka na samu na shi ga bathroom d'in don kar ya k'ara jefo min wata tambayar ,tun yanzu mun fara irin wannan da shi to yake nan zuwa nan gaba?, tambayar da bani da amsar ta...........✍✍✍✍✍✍


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.