Free chapter · Read without an account

20

by Sumayya Usman · MENE NE ABIN YI..?

    *Page 20*

Washe gari da safe lafiya lau na farka kamar ba nice jiya na shiga mawuyacin halinnan ba,duk da a cikin raina tunani ne kala-kala na ma rasa wanne 'bangare zan d'auka, tun kafin Nanny ta farka na shiga kchine na fara k'ok'arin had'a abinda zamuyi kalaci da shi,duk da ba wani abin kirki na iya ba a 'bangaren amma haka na baje basirata wajen ganin na birge Nanny,tun around 9am nake abu d'aya har wajen k'arfe 11am ban ga wani abun arziki dana aikata ba.

Alamun motsin tafiyar mutum naji a bayana ya sa na juyo, Nanny na gani tsaye bakinta abud'e sai faman bin kchine d'in da kallo take,tayata kallon wurin nayi sai a lokacin nima naga irin ta'asar da na aikata zaro idanuwa waje nayi,fuskata d'auke da tarin mamaki to wai ma duk yaushe na aikata wannan 'barnar ba tare da na sani ba,sosa kaina na fara yi gami da duk'ar da shi k'asa na ma rasa mai zance domin kare kaina da kuma k'ok'arin 'boye asalin gaskiyar da ke akan fuskata.
" Hmmmmm dole kike duk'ar da kanki kasa ki kasa kallona saboda ke kanki kin san kin aikata ba dai-dai ba,kalli abinda ki ka aikata a kalla kin 'bata tukunya kusan guda hud'u ,to wai ma duk me kika dafa da kika haukata kchine d'in har haka?",Nanny ta k'are zancenta da sigar tambaya.
Cikin in-ina na bud'e baki na bata amsa da cewa,"Am......uhm.... Nanny breakfast fa nake had'a mana"....
"A iya breakfast d'in ne kika haukata kchine d'in haka,kamar wacce take taron biki ko suna,to duk ma me kika dafa ?",ta katse ni cikin sauri da tambaya .
"Nayi toasting d'in bread ne,sai na dafa tea daganan sai na dafa d'an wake da waina"....
"Kamar ya sai kika dafa d'an wake da waina dama ita waina dafata ake yi ?","to ai naji rannan kince kina son sune shiyasa nace bari inyi maki nasan tunda kina son su to zan birge ki".
"Kai Mahnoor wannan wane irin shirme ne haka ina kika ta'ba ganin anyi wannan kwamacalar don Allah,to wai Ina ma kika sami kullun wainar ,nasan dai bamu da shi a cikin gidannan har gwarama garin d'an waken da akwai sa",ta k'ara jeho min da wata tambayar ranta a 'bace da irin ta'asar da na aikata .
"Da Garin semo nayi amfani,na kwaba shi sannan sai na"......,"ya isa haka fita ki bani guri".ta katse ni da sauri muryarta d'auke da fushi,cikin yanayin shagwab'a na fara yi mata magiya da ban hakuri amma ina hakan ko kad'an bai yi tasiri ba ,hakanan inaji ina gani na fita ina mai zun'buro baki da kuma tarin takaicin rashin samun nasarar abinda ke a cikin raina.
     Lokaci mai tsawo ta d'auka kafin ta fito daga kchine d'in hannunta jik'e da laimar ruwa da alama dai aiki ta sha tuk'uru a cikinsa,har ta kusa k'arasowa inda nake ta koma zuwa inda ta fito da alama mantuwar wani abun tayi ,fitowa ta sakeyi hannunta d'auke da tire wanda yake shake da kayan breakfast,kai tsaye Dining area ta nufa gami da aje komi akan muhallinsa in da ya dace,ajiyar zuciya ta sauke mai k'arfi gami da Jan kujera ta zauna tare da mai do kallonta inda nake tana mai cewa cikin alamun gajiya da kuma rashin k'arfin jiki kasancewar ba wata isasshiyar lafiya ce da ita ba,"zaki taso muyi breakfast dinne ko sai nazo na d'auke ki da kaina ne",sukuku nayi jiki ba kwari na taso na nufo wurin na zauna ,ganin bata k'ara bi ta kaina ba yasa nak'ara jin badad'i akan abinda na aikata,cikin alamar dana sani na fara bata hakuri,tsuru kawai tayimin har na karaci ban bakin da zanyi ba tare da tace da ni komai ba har sai da na hakura nayi shiru sai daga can naji ta jeho min tambaya kai tsaye.
"Menene yake damunki Mahnoor ina son sani yanzu ba tare da 'bata lokaci ba?".
"Eyeeeehhh...... Na'am......nifa ba abinda yake damuna kawai nayi ne don in birge ki ne".
"Bana son karya kinsan halina tun wuri ki gaya min abinda kike 'boyewa wannan ba itace fuskar ki ta asali ba,dole da akwai wani abun da kike shiryawa a cikin ranki".
"Allah ni ba abinda nike shiryawa kawai ina son in koyi wani sabon abu ne a rayuwata don sa ran zai rik'a d'ebe min kewa da kuma tarin damuwar da nake ciki".
"Okay bazaki fad'a min gaskiya ba ko,ko har sai kin kai ga gani asalin 'bacin raina sannan zaki fad'a min?'.
Kuka na fashe dashi,sai ga hawaye wani na korar wani suna ta zarya a saman fuskata ina mai cewa,"Ni dai wlh iya gaskiyata kenan ,bayan ita ban san komi ba,kuma ni duk nayi ne saboda ke amma ke zargina ma kike da niyar aikata wani abu mara kyau",na k'are zance da addu'ahr Allah yasa ta amince domin ina da tabbacin in ta cigaba da wannan bin kwakwafin to ba makawa zata iya gano abinda nike son 'boye mata.
"Ya isa haka ni duk abin bai kai nan ba,ni dai na san a iya zamana dake na nasan ba abinda kika fi tsana sama da girki yau rana tsaka in ganki kina k'ok'arin had'a mana abinci dole wani abu ya d'arsu a raina,amma tunda kince ba komi na yarda fatana kuma Allah yasa hakan ya d'ore kuma yasa itace gaskiyar".
"Ameenn ameenn my Aunty ina k'ara gode ma Allah da ya had'a ni dake", Na k'are maganar ina mai tasowa na rungumeta zuciyata fes gami dajin dad'in saurin saukowarta.
"Kinga ni sake ni kar kije ki yasar dani a k'asa dama kin san bawata lafiya isassa nake da ita ba".
"Ohhhh ya ALLAH,sorry kinji Nannyta in Sha Allah zaki warke nan kusa".
"Allah ya amince ki rik'a had'awa da Addu'ahr akan Allah yayi min maganin rashin jiki gami da tada zaune tsayen da kike min".
Baki na bud'e ba tare da na ce mata komi ba har sai daga k'arshe nace mata,"dama na fiti ne ki ko Nanny?".
"Kai³ ni ina ni ina fad'in wannan maganar,ai ban isa ba ,kinga sake ni inje in d'auko  magungunana insha ko na samu d'an k'arfi a jikina tunda  kin sa duk na k'arar da shi a wurin gyaran 'barnar da kika aikata".
"Oh sorry,zauna ki huta inje in d'auko miki da kaina",kainta kawai ta d'aga min gami da sakar min da wani murmushi, ban wani d'au lokaci ba sai gani na dawo  d'auke da magungunan a Hannuna na mik'a mata,'bata fuska naga tayi wanda hakan yasa na fiddo idanuwana waje ina mai jiran jin mai zata ce na aikata kuma yanzu tunda ni nasan zai yi wuya inyi abu kiga yayi dai-dai kamar na sauran mutane,na tsinkayo muryarta ta na cewa ,"tom ina kika baro sauran ko su kad'ai ne?","Yah Allah bari in koma in d'auko miki ban kula bane","dawo zauna inje da kaina in d'auko don zaki iya zuwa ki d'auko d'aya kice baki ga sauran ba ko ma kice duka ne baki gani ba","kai Dan Allah Nanny","to ai hali na sani",ta fad'i hakan tans mai barin wajen ,"dama da biyu na  baro sauran kafin ki gansu na gama aiwatar da k'udirina a kanki",na fad'i hakan k'asa-kasa yanda bazata ji ba,da sauri na janyo robar maganin nata guda d'aya daga ciki na d'ebo kwaya ukku daga ciki na zuba acikin tea d'inta na matso da sauri dan ya narke kafin ta zo inda Allah ya taimakeni maganin colour less ne bai nuna alama ba, addu'ata d'aya ALLAH yasa bashi da wani d'and'anon da za'a iya ganewa da sauri na kai cokalin bakina na d'and'ana, hankalina ya kwanta danaji ba wata alama ko canzawa da yayi ,duk ina wannan aikin ne cikin gaggawa domin gudun kar ta dawo ta iske ni,da sauri na koma kan kujerata na zauna gami da gyara zaman rigata da saita bugun numfashina yanda bazatai saurin zarginba,ko da ta dawo bata bi ta kaina ba,ci gaba tayi da cin abincinta har ta kamla,ni dama ban koma takan abinci ba , babban burina inga feedback d'in da zai biyo baya akan abinda na aikata,minti biyar baya naga ta fara rik'e kanta alamun aikin maganin ya fara yi mata yawa a jikinta.
"Nanny lafiya ko dai jikin ne?",na jefo mata da tambaya.
"A'a bana tunanin haka amma bari dai in d'an shiga da ga ciki in kwanta muga kome kenan zuwa anjima", Tom muje in rakaki",haka na bita a baya har bedroom d'inta,kwanciya tayi inda ba'a d'auki wani lokaci ba barci ya d'auketa na janyo bargo na k'ara rufa mata,hawaye ne masu zafi suka zubo min a saman fuskata ba tare da na bi ta kansuba na fara fad'in abinda ke a raina a fili, "na gaji bazan iya jurewa ba an zo kan ga'bar da ban ta'ba yin hakuri ko kawaici ba ,dole zan d'auki mataki abun yayimin girman da bazan iya cigaba da rayuwa da shi ba,kiyi hakuri tun farko nayi abinda nayi don mu kawa wannan mataki ne,har ta kai ga nayi abuse d'inki kuma na wahalal dake amma kiyafe min ,na fahimci cutarwarsu ba a iya ni kad'ai bace wa AL'UMMA baki d'aya ne , shiyasa na yanke hukunci abinda zan aikata kodai inyi nasara ko kuma yazama silar ajalina,kawar da kaina nayi daga kallon da nake mata tare da d'aukar keys d'in d'akin na rufeta ta waje............✍✍✍✍


Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol