Free chapter · Read without an account
6
*6*
Free Book.
Yau ya kasance juma'a. Ƙofar gidan na Tsohon Alƙali Dikko Habib cike yake da ɗumbin mutane masu zuwa karɓan sadaqa, yara da manya musamman ma magidanta marasa ƙarfi, haka gidan yake kasancewa a duk wata juma'a, zaka ga mutane babu masaka tsinke tun an idar da sallar asubahi sun bi layi suna jiran fitowar Mai gidan.
Dikko Habib babban tsohon alƙali ne wanda ake damawa da shi a manyan shari'ar da ta shafi cikin ƙasa da wajenta, kuma alƙalin da gwamnatin tarayya ke ji da shi. Dattijon ƙwarai mai halin dattako da nagarta, Yawancin zamansa a america yayi tun yarinta, karatunsa ma tun daga secondry har matakin phd duka acan yayi.
Matansa Biyu Hajiya Ramla da Hajiya Madina amma ainihin sunanta Aina'u, Ƴaƴansa 6, uku maza uku mata. Kuma kaf cikinsu babu wanda ke karatu a nigeria duka waje yake fitar da su. Turaki ne ma kawai yayi secondry a nigeria.
Idan ya zo zai bawa kowa sadaqa zai ba da kuɗi dubu uku, sai ma'aikatan gidan maza su bika da kwanon shinkafa, taliya guda biyu da kwalaban farin mai da manja. Alƙali Dikko baya taɓa barin wajen har sai ya tabbatar da kowa ya samu, duk kuwa da uban yawan da mutanen ke da, baya gajiyawa kuma baya ƙosawa, hakana duk nisan tafiyar da yayi duk irin muhimmancinta zai katse kome yake yi ya dawo alhamis dan kawai waɗannan mutanen da Allah ya ba shi ikon taimaka musu.
Ya faɗa saveral times ga ni yake idan har ba shine da kansa ba to ba za'a riƙe amana kamar yanda ya bayar ba, saudiya kawai yake tafiya ya iya haƙura, shima kuma sai ya kira Muhammad Turaki a duk inda yake ya dawo ya tsaya akan ragamar abun, dan shi kaɗai yake ganin zai iya kwatankwacin abin da shi zai yi da kansa.
Kuma a wannan juma'ar ne ma'aikatan gidan basa samun hutu ko kaɗan, dan tun daga safe har dare suna rabon abincin sadaqa.
Ƙarfe goma da rabi Baffa ya dawo cikin gidan daga rabon sadaqar da ya fita, Khalil da ke ƙoƙarin shiga motarsa zai fita ya hange shi, hakan yasa ya rufe motar ya taho da sauri.
Ya rissina a gaban mahaifin nasa cike da girmamawa yana faɗin,"Barka da dawowa Baffa". Tare da miƙa hannu don karɓar jakar hannunsa, wadda yake zuba kuɗin sadaqa ya fita da ita.
Baffan ya dube shi yace,"Ba fita zaka yi ba?".
"Fitar ba wata mai muhimmanci ba ce".
Ya faɗa yana ƙara miƙa hannu don amsar jakar. Baffan ya miƙa masa, shi kuma yana masa sannu tare da addu'ar Allah ya bada lada a irin ayyukan alkhairan da yake yi.
Tare suka jera suna tafiya, suna entrance na shiga parlo Baffa ya ce da Khalil.
"Muhammadu ya dawo ne?".
"A'a bai dawo ba".
"Amma ɗazu sai na ga motarsa".
"Ai dama ba da ita ya tafi ba, da GLK ya tafi".
Baffa bai ce komai ba ya shiga katafaren parlonsa bayan Khalil ya buɗe masa ƙofa. Hajiya Madina coming down from stairs take welcoming nasa. Khalil ya miƙa mata jakar hannunsa ta ce ya wuce ya kai bedroom ɗin Baffa.
Tana gyara dining area take cewa Baffa, "Yau ka dawo da wuri, hala ba'a taru ba yanda aka saba".
"Ba haka bane, jikina nake jinsa babu daɗi".
"Subhanallahi". Ta faɗa tana saurin barin abin da take yi ta dawo kusa da shi ta zauna.
Tana taɓa jikinsa looking worried ta ce,"I hope ba ciwonka ne zai tashi". Tayi maganar tana ɓalle maɓallin gaban rigarsa. Sannan ta miƙe tana cewa,"Let me reduce the AC".
Kayan breakfast ta ɗauko ta dawo da shi gabansa ta aje saman wani medium glass table. His favorite dish kunun gyaɗa da awaran ƙwai, da kanta take feeding nasa tana jera masa sannu, bayan ya gama ta ba shi drugs sannan ta buƙaci da ya tashi ya koma bedroom ya ce a'a ta barshi nan.
Ƙasa ya sauko ya zauna kan tattausan carpet ɗin dake malale, haɗuwar parlon da tsaruwarsa ka ce turakar sarki, ya kishingiɗa da tum tum ɗin dake gefensa, in a state of misery ya ce.
"Ban san me ya riƙe yaron nan ba".
Yayi maganar yana sosa gashin gemunsa.
Hajiya Madina ta sauke nunfashi kamin ta ce,"Ya ce yana hanya ai. Ka kwantar da hankalinka please ba wani abun damuwa ba ne. Duk yadda akai aiki ne yayi masa yawa".
"To Allah yasa lafiya ɗin". Ya faɗa fuskarsa na nuni da damuwar da ke ransa, na rashin dawowar Turaki gida tun a ranar da ya dawo ya kirasa ya sanar masa ya dawo gida yana da buƙatar ganinsa.
Suka cigaba da magana akan rayuwa, a haka har ya fara samun relief na ciwon kan da ya fara gallabansa ɗazu. Yay nisa ya ce,"Yaran nan ba su tashi ba ne?".
Hajiya Madina ta ce,"What is the time now?". Ta faɗa tana duban agogo tukunna ta ƙara cewa,"Masu baccin dama Zaytuna da Nihal ne, Samha ta tashi yanzu. Itama tana tunanin baka shigo ba ne shiyasa baka ganta ba, tun da time ɗin dawowanka bai yi ba".
Yayi murmushin manyace ya ce,"Da asuba da na je gaida Boɗejo ina jinta ita da Zaytuna".
Ya ƙarasa maganar yana ƴar ƙaramar dariya, yayin da Hajiya Madinan ke taya shi dan lamari indai aka ammabaci Boɗejo a ciki to za'a dara.
Fararan haƙoransa a waje yake faɗa mata cewar,"Da asubar nan fa ko lazimi bata gama ba take mitan Allah kaimu safiya ta bar gidan ita ba zata iya da gorin da ake yi mata ba".
Hajiya Madina ma tayi dariya sosai, lokacin kuma hankalinsu ya karkata kan yaransu da ke shigowa parlon bakunansu ɗauke da sallama.
Shigar jikinsu kaɗai zata shaida maka ƴaƴan wani ƙusan ne, ballanta azo ga kallon fatar jiki da zata tabbatar maka da hutu, jin daɗi da gata ya zauna.
Baffa ne ke amsa sallamar ta su yana miƙewa zaune daga kishingiɗar da yay a jikin tumtum.
Samha, Zaytuna da Nihal suka zube a gabansa, cike da tsantsar girmamawa da ladabi suka gaishe shi cikin taushin murya. Ba sai an faɗa ba, irin zaman ma da su ka yi a gabansa shi zai baka tabbacin an gina tarbiyarsu bisa bigere na addini, duk da Alƙali Dikko ɗan boko ne hakan bai sa yayi watsi da koyarwar addini da al'ada ta fulani ba ya ɗauki ɗabi'ar bature ya gina iyalinsa akai.
Idanuwansa na bin kowacce da kallon so da ƙauna dake tsakanin uba da ɗansa yake amsa musu cikin farin ciki da annashuwa. Addu'a yake jero musu iya addu'a su kuma suna amsawa da amin, Zaytuna wadda ke da idon hawaye tuni idanuwanta suka ciko da ƙwalla, haka ma muryarta tayi rauni wajen amsa albarkar da mahaifinsu ke saka musu.
Da yake shi mutum ne me barkwanci acikin iyalinsa ya kalla Nihal cike da zolaya yace,"Auta ya naga kinyi fari har kin fi Boɗejo, saura ƙiris ki koma Zabiya fa".
Babu shiri Nihal tayi dariyar da duka haƙoranta suka bayyana a waje tana rufe bakinta da hannu.
Baffa ya ƙara cewa,"Ki sammawa Mamanki abin da kike shafawa ko ta ƙara yin kyau ta koma ƴan mata". Yayi maganar cike da barkwanci.
Bata bar dariya ba ta ce,"Baffa ni babu abin da nake shafawa tsabagen hutu ne kawai".
Yayi murmushi, Hajiya Madina ta ce,"Yo Allah na tuba ni wa zai ganni ma ya ce na ajiye maka waɗannan yaran. Ni jikina ai yafi na wata budurwar, man bature kuwa ai sai dai mu barwa wasu dan mu da namu farin daga Allah ne".
A cikin amon yanda tayi maganar zaka tsinci tsagoron kishi duk da cewar maganar anyita ne for raha becouse of ayi dariya.
"Zaytuna na ga hannun naki". Hajiya Madina ta ce tana duban inda Zaytuna ke zaune, gefen mahaifinta tamkar zata shige cikinsa. Ta taso ta dawo kusa da ita tana nuna mata hannun.
"Ya fara sauƙi ai. Da zafi har yanzu?".
"Ehh Maama yana zafi".
"Sannu, did you take your drugs?".
Tace,"Ehhh".
"Allah ya sauƙe".
Baffa ya ce,"To wai ba za'a nemo wata ƴar aikin bane? Kuma ke har kina shirmen me da kika bari ruwan zafi ya taɓa ki".
Hajiya Madina ta ce,"Tsautsayi dai da ba ya wuce ranarsa, ita kasan kamar inji ba son zama take yi ba. Amma idan yau Jamilar bata dawo ba sai nayi magana da Yami ta samo wata, ai dama sati ɗaya Jamilar ta ce zata yi".
Sahma ta ce,"Ai Maama a nemi wata kawai, dan bana tunanin Jamila zata dawo, don na ji Sha'awanatu na cewa kamar aurenta za ayi".
"Ai da hakan ne zata faɗa, ko ta kira waya ta sanar".
Baffa na riƙe da hannun Zaytuna yake cewa da ita,"Please Babyn Baffa a daina shiga kitchen kin ji, bana so wani abu ya dinga taɓa min lafiyarku. Ubangiji yayi wadatar da baku buƙatar yin komai da kanku sai abin da ya zama dole. So mu gode masa".
Sameer da suka shigo shi da Khalil ya ce,"To wai a yanke hannun mana". Zaytun tayi masa wani kallo ta ce,"Sai ka zo ka yanke ai".
Ya ce,"Kar ki bari a barmu daga ni sai ke a gidan nan ki ga aiki da cikawa". Bl
Baffa with full of smile on his face ya ce,"Ƙyale shi haushi yake ji hannunki yafi na budurwarsa kyau, kuma nan gani nan bari...".
Tun bai ƙarasa ba Samha da Nihal da ita Zaytunan suka ƙarashe faɗin,"Ɗumamen mayya ba". Su kai maganar suna dariya.
Sun ɗau tsawon lokaci suna hira kafin yaran su tashi su tafi, suna fita Baffa ya kamo hannun matarsa yana cewa,"Haba ƴar shawalwalata ɓata fuskan kuma na menene?".
Bai jira me zata ce ba yaci gaba,"Kema dai ai kin san waɗannan idanun tsufan nawa kallon jaririya ma suke miki ba budurwa ba, me za'ai da wata ƴan mata ina da ke ƴar shila, kin fa riga kin rufe ƙofar tuntuni, to mene kuma wani batu zai sa ki ɓata fuska ummm Babyn Baby, please saki ran karki ɓatan kwalliyan da aka yi mani na ke kallo ina jin daɗi".
Ya ƙarasa maganar yana shafo fuskarta ita kuma tana ƙoƙarin danne murmushin jin daɗin da ke neman suɓuce mata, yanda yake yi mata kamar ƙaramar wata yarinya, har sai da yayi nasarar sakata yin murmushin da ya haɗe da dariya.
"Yauwa ko ke fa gimbiyata, sarauniya a fadar zuciyata, ina sonki fa, ina sonki da yawa wallahi. Allah dai ya ƙara miki kyau".
Ya faɗa yana kamo dogon hancinta. Sai kuma ya kai bakinsa saitin kunnenta yana cewa,"Wai yaushe zamu ƙara tafiya honeymoon ne?".
Hajiya Madina ta ce,"Da gaske fa na yi zaton ko ka ƙyalla ka gano wata ƴar baturiyar ne".
Ya ce,"Waa! Niii! Rufani ki saya". Yana nuna idanuwansa ya ce,"Ai wannan idanuwan babu wadda suke gani sai ke, ke ɗaya tallin tal Aina'u ta Habibullahi".
"To yanzu tashi mu koma ɗaki ka samu ka rama baccin asuba da baka koma ba. Nima na samu na tafi guest parlo kasan yau ranar amsar koken mata ne".
Suka miƙe tsaye tare yana faɗin,"Ai na yi zaton idan mun je ɗakin soyayya zamu sha".
Tayi murmushi ta kama hannunsa. "To kai dai mu je mana Your Excellency". Da haka suka haura stairs.
****
"Ni kuwa na godewa Allah, wai ko Allah Fullo ba za ki daina wannan kukan alluran haka ba".
Kaka ce ke maganar tana daga cikin ɗaki tana gyara, dan yau tun before 7 ta tafi kai Fullo asibiti, dalilin ma da ya sa suka dawo da wuri saboda Amir ne ya kai su, a can asibiti suka tarar da shi dan da wuri yaje ya kama musu layi, tun daren jiya ya kasa zaune ya kasa kwance saboda yanayin yanda ya tafi ya barta da jikinta.
Tun wancan ranar da Fullo ta ƙona asirin nan shikenan ta kwanta ciwo, har sati guda tana kwance jiki sai dai yayi ta tsamari ba sauƙi. Sai ma yau ɗin da ta ɗanji daɗi.
A yau ɗin ne Kaka ta ƙara ƙudurtar cewar Fullo bata da wani miji a wannan duniyar sai Amir, saboda samun namiji a wannan zamanin kamarsa babu shi, yau ta daɗa yabawa da hankalinsa, yana da duk wasu good qualities da ake buƙata a wurin ɗa namiji, ga uwa uba ilimin addini.
Ko sisinta bata kashe ba shi ya biya komai da aka yi bill, duk da ba kuɗi ne da shi ba, amma akwai zuciyar nema da kuma kyauta, babu yanda ba tayi ba akan ya karɓa ya ƙara amma yaƙi. Dai-dai da ruwan sha wannan sai da ya siya mata na Faro da suka dawo, da kayan marmarinsa iya koƙarinsa. Tana lure da shi banda tayi masa da gaske a ɗazun bai so tafiya ba.
Fullo dai kukanta take rerawa da ƙarfin sauti ba kaɗan ba, da Kaka ta gaji da halinta tayi mata banza. Har ta gama duk abin da take Fillo dai bata daina kuka ba, kukan da bana komai ba ne sai na allurar da aka yi mata. Allurar da taja akaita fushi da masoyin da ake ji da shi, dan har Amir ya ƙaraci zamansa a parlon nan ya tafi bata ko saurari duk kalar lallashin da yake yi mata ba.
"Kinga yau burabusko aka yi. Allah sarki su Yami sun sha aiki".
Maganar Kaka ke yi tana ɗiban burabuskon dake cikin kwano ta saka a baki. Ta kalli Fillo ta ce,"Tun da kina son sa daure ki tashi ki ci".
Fullo taja majinar hancinta tana ƙoƙarin tsaida kukan da take yi tance,"Miyar mene?".
Kaka ta ce,"Miyar ganye ce, kuma yayi daɗi sosai".
Fullo ta koma ta kwanta,"Ki aje min zanci anjima". Ta faɗa sannan ta cigaba da kukan kamar ƙanƙanuwar yarinya.
"Allah ya shirya min ke. Ni banga wani hankali a tare dake ba da Amir ya gani ya na ce miki".
"Ni daga yau ai babu ni babu shi, can ya je ya nemi wata ba dai ni Haliman Dada ba, dan ba zan je gidan da za'a kassara rayuwata ba".
Kaka ta taɓe baki,"To dama Fullo wa ya ɗauko shi ya kawo miki. Ke kika yayibo abinki".
Kaka na sauraron radio aka yi sallama daga bakin ƙofa, ta amsa tana cewa a shigo. Zaytuna ta ɗaga labulen ɗakin da ya sha jiki ta shiga ta ƙara yin sallama.
"Jaɓɓama lale". Kaka ta faɗa a tana bin Zaytuna da ido da rashin gane wacece. Ita kuma ta nemi wuri zata zauna a ƙasa Kakan ta ce,"Ah haba dai ga darduma yi haƙuri ki shimfiɗa hannuna da maiƙo".
Zaytuna ta karɓi darduman ta shimfiɗa ta zauna akai. Kaka ta ce,"Sai dai ban gane wacece ba wallahi".
Tayi maganar fuskarta ɗauke da fara'a, tana so kuma ta gano a inda ta san kamannin da ke fuskar.
"Ehh ba lallai ki shaidani ba gaskiya. Daga cikin gida dai nake".
Kaka ta washe baki ta ce,"Ƙwarai kuwa ga kamannin Alhaji nan. Sannu da zuwa, baƙuwar tamu ashe babbace. Bari na kawo miki ruwa".
Ta miƙe Zaytuna ta ce,"W'a wallah Inna ki barshi ai yanzu zan wuce".
Kaka ta ce,"Ai ko ba za ki sha ba sai na kawo". Ta faɗa tana nufar inda kwandon wanke-wankensu yake ta ɗauko farantin roba, Allah ya taimaka akwai purewater wanda Amir ya siyo musu ɗazu mai sanyi kuwa, ta sako guda biyu ta ajiye agaban Zaytuna suna daɗa gaisawa.
Zaytuna bata da niyyar shan ruwan saboda a ƙoshe take, amma gudun kar Kaka ta ji babu daɗi dole ta ɗauka tasha, tasan tsohuwar zata iya ganin kamar ko ƙyanƙyami ne ya hanata sha. Balle ita bata ma ga rashin tsabta a wajen ba, komai fes-fes wajen ɗal-ɗal an share, shi kansa ɗakin sai ƙamshin turaren wuta ɗan tsinke yake, duk idon da ya ga wajen dai ba zai ce wurin ƙazamai bane.
Ɓangaren masu aikin a haɗe yake, amma kuma kowa da gefen da yake.
Kan Kaka a ƙasa ta ce,"Ranki ya daɗe Allah sa dai ba wata matsala bace".
Zaytun ta ce,"A'a Inna lafiya lau, kawai dai na shigo ɓangaren naku ne ina gaidaku".
"Allah sarki aikuwa mun gode".
Zaytun ta miƙawa Kaka farar leda mai kauri irin ta store ta ce,"Ga wannan, atamfofin marasa ɗinkin naki ne. Akwai doguwar riga guda biyu sai a bawa yarinyar, ban ma san da ita ba ne sai da Maijidda ke gaya min. Da yake Maijiddan kawai na sa ni sauran duk sai yanzu nake ganin fuskokinsu".
Kaka ta ce,"Allah sarki, ai Maijidda ita ta jima a gidan nan, su kam ai duk sai daga baya suka zo. Itama ta wurin nawa bayan rasuwar mahaifiyarta na ɗaukota".
Lokaci ɗaya idon Zaytuna ya kawo ruwa, kewar tata mahaifiyar ya kamata, tayi saurin danne hawayen dake ƙoƙarin zubo mata, wannan ciwon dake manne a zuciyarta ya taɓu.
Muryarta so cool ta ce,"Allah ya jiƙan waɗanda suka rasu".
Kaka ta amsa da amin, ita kuma ta yunƙura ta miƙe, dubu biyu ta ciro a purse ɗin dake hannunta ta ajiyewa Kaka, a lokacin da kuɗi suke da matuƙar daraja, don wannan dubu biyun kusan dubu ɗari biyun yanzu ce.
"Ga shi ayi addu'a wa iyayenmu".
Kaka dake ta zabga godiya ta koma jero addu'oi kala-kala, ita kuma tana ta amsawa da amin cike da jin daɗi. Yayin da taji ƙaunar Kaka ta shiga ranta, dan ita a rayuwa babban abin da zaka yi mata a duk duniya ka burgeta shine ka yiwa iyayenta addu'a, tabbas kai mata hakan zata girmamaka kuma zata mutuntaka. Kuma har gaban abadan ba zata taɓa mantawa da kai ba, kuma haka ta dinƙa maka alkhairi kenan.
Har ta fita bata lura da Fillo dake gefe ɗaya a rakuɓe ba, ta nannaɗe jiki da wani mayafin Kaka mai kauri saboda sanyin da take ji, fuskar nan tayi jajur tsabar ansha kuka an ƙoshi. Ta haɗe rai babu annuri ko kaɗan. Ƙememe tana ganin Zaytuna amma taƙi gaisheta, kuma tana lura da yanda Kaka ke aikin jefa mata harara amma tayi fuska, shiyasa itama Kaka ɗin ta yi ta addu'a a ranta Allah yasa kar Zaytuna tura da ita balle ta bata kunya.
Kaka da ta dawo daga rakiya ta ce da Fillo. "Ke dai ki sauya hali dan gidan wani za ki je, kuma wannan halin naki dai ba halin zama uwa ta gari ba ne".
Maijidda ta shigo, tayi wajenta tana yi mata dariya tare da tsokanarta akan kukan allura. Bata kulata ba tayi mata shiru, ita kuma ta miƙa mata ƴar ƙaramar waya ƙirar nokia irin ta da can wadda aka fara sakawa sunan rakani kashi, wayar duk ta jeme tasha kyauraye, banda Yami babu ma me iya riƙe wayar.
"Amir ne ya kira ya ce na kawo miki. Wai ya kira ta Kaka a kashe".
Kaka ta ce,"Ai ita ta tsinka cajar garin shirmen banzanta".
Fullo ta kalli wayar da ke kan cinyarta, sannan ta kalli Maijidda da jajayen idanuwanta da suka sha kuka suka ƙanƙance ta ce,"Kin ɗauke min ita a jikina ko sai na ƙarasa kasheta".
Sanin cewar zata aikata Maijidda tayi saurin ɗaukewa tana faɗin,"Yadda Yami ke ji da wayar nan kika fasa ai ni za ki jawa faɗa".